Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza
Sai da safe!
Nan muka kawo ƙarshen wannan shafi na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana da aka gudanar da zaɓukan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da Imo na Najeriya.
Amma yanzu a madadin duk waɗanda suka bayar da gudunmawa, Haruna Ibrahim Kakangi ke cewa ku kasance tare mu a shafinmu na gobe Lahadi.
INEC ta ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnonin Kogi da Bayelsa zuwa Lahadi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta jinkirta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi zuwa ranar Lahadi.
Inec ta ce za a buɗe zauren karɓar sakamakon zaɓen ne da ƙarfe 10 na safe a Lokoja da ke babban birnin jihar ta Kogi.
Tuni dai hukumar ta sanar da dakatar da zaɓe a mazaɓu tara na jihar ta Kogi.
A jihar Bayelsa ma hukumar zaɓen ta dakatar da karɓar sakamakon zaɓen har sai ranar Lahadi da ƙarfe 10 na safe.
Abubuwan da suka faru a Gaza ranar Asabar
Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila ta ce gobe Lahadi za ta taimaka wajen duba halin da jariran da ke kwance a asibiti mafi girma a Gaza suke ciki, wato asibitin Al Shifa, bayan samun buƙatar hakan daga hukumomin asibitin.
Rundunar sojin Isra'ila ta amince cewar an gwabza faɗa tsakanin dakarunta da na Hamas a kusa da asibitin, sai dai ta musanta kai hari cikinasibitin.
Tun farko wani likita a asibitin Al Shifa ya shaida wa BBC cewar lantarki da ruwa da abinci sun katse a asibitin, kuma lamarin ya shafi ɗakin kula da marasa lafiya masu neman agajin gaggawa.
Wata ƙungiyar likitoci ta ce jarirai biyu sun mutu a asibitin Al Shifa sanadiyyar katsewar lantarki yayin da rayukan wasu jariran su 37 ke cikin hatsari. Isra'ila ta ce za ta kwashe jariran a gobe Lahadi zuwa wani wuri mai tsaro.
Ƙungiyar likitoci masu ayyukan jin-ƙai ta MSF ta ce an riƙa yi wa asibitoci daban-daban a Zirin Gaza ruwan wuta cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Kafafen yaɗa labaru a Lebanon sun ce Isra'ila ta kai hari a wuri mafi nisa cikin ƙasar Lebanon tun bayan rikicin da ya ɓarke makonnin da suka gabata. Babu rahoton kisa ko jikkatan wani.
Sama da mutum 300,000 sun gudanar da zanga-zanga a kan titunan birnin Landan na Birtaniya domin kira da a kawo ƙarshen ruwan wuta da ake yi a Gaza. Babu rahoton wani hargitsi a lokacin zanga-zangar, sai dai ƴan sanda sun ce sun kama mutum 82 waɗanda ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan Isra'ila.
Ƙasahen Musulmi da na Larabawa sun gana a Saudiyya tare da yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza. Kuma sun yi watsi da batun cewa ruwan wuta da Isra'ila ke yi a Gaza tana yi ne domin kare kanta.
Ƙasashen Musulmi sun buƙaci a dakatar da yaƙin Gaza nan take
Asalin hoton, Getty Images
Sanarwar ƙarshe ta taron ƙasashen Larabawa da na Musulmi 57 da ya gudana a Saudiyya ya nuna cewa ɗaukacin ƙasashen sun buƙaci a tsayar da rikicin Gaza nan take.
Mai masaukin baƙi Saudiyya ta zargi ƙasashen duniya da nuna bambanci tsakanin ƙasashe.
Ministan harkokin waje na Saudiyya ya ce kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza wajen sauke nauyin da ke kansa saboda ya gaza hukunta Isra'ila kan abubuwan da ta aikata.
EFCC ta kama masu sayen ƙuri'a da kuɗi naira miliyan 11 a Kogi da Imo da Bayelsa
Asalin hoton, EFCC
Hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce ta kama mutum 14 a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi bisa zargin su da yunƙurin sayen ƙuri'u daga masu zaɓe a zaɓen gwamnonin jihohin da ya gudana a yau Asabar.
Kuma hukumar ta ce ta ƙwace kuɗi naira miliyan 11,040,000 daga irin waɗannan mutanen.
An kama waɗanda ake zargin ne a garin Otueke da Adawari na jihar Bayelsa, da kuma wasu a jihohin Kogi da Imo.
EFCC ta ce ta samu nasarar hakan ne sanadiyyar bayanan sirri da ta tattara tun gabanin ranar gudanar da zaɓukan.
Bugu da ƙari hukumar ta samu nasarar ƙwace motoci biyu daga masu ƙoƙarin aikata laifukan na zaɓe.
Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala gudanar da bincike a kansu.
A wannan Asabar ɗin ne INEC ta gudanar da zaɓukan gwamnan a jihohin na Kogi da Imo da Bayelsa, zaɓukan da aka samu koke-koke na tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankuna daban-daban.
Rahoto kan zaɓen gwamna a jihohin kogi da Bayelsa da Imo, Daga Chris Nwoko
A yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihohin Kogi da Imo da Bayelsa, bari mu yi duba kan zaɓen na yau.
An samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a zaɓukan jihohin uku.
Sannan kuma an samu rahotonnin zarge-zargen cike takardun sakamakon tun kafin fara kaɗa ƙuri'a a wasu yankunan jihohin uku.
A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya hukumar INEC ta soke zaɓe a wasu mazaɓun jihar, sakamakon zargin cike takardun sakamako, tun kafin fara kaɗa ƙuri'a.
A jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin ƙasar, an samu rahotonnin garkuwa da jami'in zaɓe, kodayake daga baya INEC ɗin ta ce an sako shi
Mai sanya idanu na cikin gida a zaɓen ya shaida wa manema labarai cewa an samu rahotonnin razanar da masu kaɗa ƙuri'a da rigingimu a jihar ta Bayelsa.
A jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar kuwa, an ga wasu mazauna jihar na kan layin ɗiban ruwa a maimakon layin zaɓe.
Sun ce babu wutar lantarki da ruwan sha a jihar, sakamakon yajin aikin ƙungiyar kwadago a jihar.
Gwamnan jihar Hope Uzodinma na neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen.
INEC ta dakatar da zaɓe a wasu mazaɓun jihar Kogi
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce ta dakatar da zaɓuka a mazaɓu tara daga cikin 10 a ƙaramar hukumar Ogori/Magongo a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta samu bayanan aikata kura-kurai, musamman kan batun cike takardun sakamako kafin fara kaɗa ƙuri'a.
Sanarwar ta ce hukumar ta samu rahotonnin aukuwar irin wannan al'amari a ƙananan hukumomin Adavi, da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene
Hukumar zaɓen ta jaddada cewa ba za ta amince da duk wani sakamako wanda ba daga rumfar zaɓe ya samo asali ba.
Haka kuma INEC ɗin ta ce tana gudanar da bincike a sauran ƙananan hukumomin, ta kuma ce da zarar ta kammala binciken za ta bayyana matakin da za ta ɗauka nan da sa'o'i 24.
Tottenham ta yi rashin nasara karo na biyu a jere
An shirya ɗakunan tattara sakamakon zaɓen gwamna a Imo da Bayelsa
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta kammala shirye-shiryen fara tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Imo a ɗakin tattara sakamakon zaɓen da ke birnin Owerri.
A ɗakin ne za a karɓi sakamakon zaɓen kowacce ƙaramar hukuma da ke fadin jihar.
Can ma a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin ƙasar hukumar INEC ɗin ta kammala shirya ɗakin tattara sakamakon domin fara karɓar sakamakon daga ƙananan hukumomin jihar
Bayanan hoto, INEC ta ce tana sa ran fara karɓar sakamako daga ƙananan hukumomin da misalin ƙarfe 9:00 na dare
A halin yanzu dai ana kan tattara sakamakon a matakin mazaɓu, da ƙananan hukumomi
Arsenal ta doke Burnley, yayin da United ta sha da ƙyar
'Asibiti ɗaya tal ke aiki a Gaza'
Daya daga cikin likitocin tiyata uku da ke aiki a asibitin Al-Ahli ya ce a ''yanzu asibitin ne kaɗai ke aiki' a birnin Gaza.
Dakta Ghassan Abu Sitta ya aiko wa BBC saƙon murya daga asibitin Al-Ahli, inda ya ce likitocin suk kafa asibitin wucin-gadi, domin ci gaba da aiki, bayan da wani hari ta sama ya faɗa kan asibitin cikin watan Oktoba.
"Mu uku ne ke tiyata, kuma a yanzu muna da marasa lafiya kimanin 150 a asibitin kwance kan katifu a ƙasa,'' in ji Sitta.
An sako jami'an INEC da aka yi garkuwa da shi a Bayelsa
Hukumar zaɓen Najeriya ta ce an sako jami'inta da aka yi garkuwa da shi gabanin fara zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a yau Asabar.
Cikin wata sanarwar da INEC ɗin ta fitar, ta ce an sako jami'in nata kuma yana cikin ƙoshin lafiya.
INEC ta kuma gode wa duk waɗanda suka taimaka wajen ganin an sako ma'aikacin nata.
Asalin hoton, INEC
Fatan mazauna Kogi ga wanda zai zama sabon gamnan jihar
Mazauna jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya sun bayyana fatan da suke da shi kan duk wanda ya yi nasarar zama sabon gwamnan jihar a zaɓe da aka gudanr yau Asabar.
Tuni dai aka rufe rumfunan zaɓe, inda aka fara ƙirga ƙuri'u da tattara sakamakon zaɓen.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Motocin da za a raba wa ƴan majalisa bashi ne - Gagdi
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi da Imo da Bayelsa
'Mun ga yadda ake sayen ƙuri'a a Bayelsa' - Mai sanya ido kan zaɓe
Daya daga cikin masu sanya idanu a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa ya ce sun ga yadda aka riƙa sayen ƙuri'un jama'a a lokacin zaɓen.
Sylvester Okoduwa daga ƙungiyar sanya idanu ta 'Transition Monitoring Group' na ɗaya daga cikin masu sanya idanu na cikin gida a zaɓen, ya kuma shaida wa BBC cewa mutane da dama ba su fito zaɓen kamar yadda ya kamata ba.
"Abu ɗaya da ya fito ƙarara shi ne yadda ake yawaitar, sun riƙa sayen ƙuri'a a bainar jama'a. Duk da cewa ba na son cewa da hannun jami'an tsaro a ciki, amma haƙiƙa batun sayen ƙuri'u ba abu ne mai kyau ga jihar Bayelsa ba,'' in ji shi.
Yadda ake ci gaba da ƙirga ƙuri'u a rumfunan zaɓe a jihar Kogi
Bayan rufe rumfunan zaɓe a sassan jihar kogi, tuni jami'an zaɓe suka fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa a matakin rumfar zaɓe.
Daga nan ne kuma za a ɗauki ƙuri'un da sakamakon da aka samu zuwa mazaɓa, kafin a wuce zuwa ƙaramar hukuma.
'Yan takara 18 ne dai suka fafata a zaɓen na yau, sai dai ana ganin takarar ta fi zafi ne tsakanin manyan jam'iyyu uku.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Jam'iyyu sun ba mu kuɗi, amma mun zaɓi ra'ayinmu
Wani da ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, ya yi zargin cewa wasu jam'iyyu sun bayar da kuɗi domin a zaɓe su.
To sai dai ya ce sun karɓi kuɗin, amma sun zaɓi abin da suke so.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Yariman Saudiyya ya yi Allah-wadai da Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya ya yi Allah-wadai da Isra'ila tare da ɗora mata alhakin abin da ya kira "laifukan da ake tafkawa a kan Falasɗinawa."
Yariman ya kuma yi kira da a kawo ƙarshen mamayar da aka yi wa Zirin Gaza tare da samar da ƙasar Falasɗinawa bisa yarjejeniyar 1967.
Sarki Abdallah II na Jordan da kuma shugaban Falasɗinawa duk sun amince da batun na yariman na Saudiyya.
Shi kuwa shugaban Turkiyya, Raceb Tayyib Erdogan ya yi kakkausar suka ne a kan Isra'ila, tare da bayyana ta a matsayin sangartacciyar ƙasa.
Ya yi kira ga ƙasashe da su fito fili su yi magana kan rashin abin da ke faruwa a Gaza, da kuma buƙatar Isra'ila ta biya diyya ga Falasɗinawa.
Haka nan ya buƙaci a hukunta Isra'ila kan laifukan da ta aikata kan Falasɗinawa.
An fara ƙirga ƙuri'u a jihar Kogi
An rufe kaɗa ƙuri'a a hukumance a rumfunan zaɓe.
A wannan rumfar zaɓen mai lamba Kyanchi Open Space 008 da ke birnin Lokoja na jihar Kogi, tuni aka fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa.