Gomman mutane ne suka jikkata, ciki har da masu raunin harbin bindiga, bayan da aka samu arangama tsakanin 'yan sanda Isra'ila da 'yan Ertrean masu neman mafaka a birnin Tel Aviv.
'Yan sanda sun amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla da alburusai wajen tarwatsa ɗaruruwan masu zanga-zangar.
Rikicin ya kaure ne bayan da 'yan gwagwarmaya da ke adawa da gwamnatin Eritrea suka ce sun buƙaci hukumomin Isra'ila su soke wani taro da aka shirya yi a ofishin jakandancin ƙasar ranar Asabar.
Matakin da bai yi wa magoya bayan gwamnatin Eretra daɗi ba, lamarin da ya haifar da arangama tsakanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani 'yan sanda su kwantar da tarzomar.
Rahotonni daga Isra'ila na cewa mazu zanga-zangar sun durfafi inda aka tsara gudanar da taron.
Da farko 'yan sanda sun sanya musu shinge, amma daga baya sun karya shingayen.
Mazauna birnin sun ce birnin ya kasance tamkar filin yaƙi yayin da 'yan sanda suka riƙa kewaye birnin da jirage masu saukar ungulu domin kwantar da tarzomar.
Masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sandan, inda suka lalata ƙananan motoci tare da lalata shaguna.
Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce jami'anta sun yi amfani da bindiga ne a lokacin da suka fahimci cewa rayuwarsu na cikin hatsari.
Rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Eritrea kan shugabancin Isaias Afwerki ya watsu har zuwa tsakanin 'yan ƙasar mazauna ƙetare.