'Yan bindiga sun kashe mutum biyar a masallaci a Kaduna
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Arsenal za ta karɓi bakuncin Man United a Emirates
Tsohon ɗan ƙwallon Mali Salif Keita ya rasu
Asalin hoton, AFRO FC
Dan ƙwallon ƙafar da ya fara lashe kyautar gwarzon Afrika a 1970 - ɗan wasan Mali Salif Keita ya rasu.
Tsohon ɗan wasan ƙungiyar St Etienne ta Faransa ya rasu ne yana da shekara 76 a duniya.
Keita ya yi suna ne a ƙungiyar St Etienne, ta Faransa inda ya lashe kofuna uku a jere na lig din ƙasar.
Ya taimaka wa ƙasarsa zuwa wasan ƙarshe a gasar cin kofin Afirka a 1972.
Keita kuma ya taka leda ƙungiyoyi daban-daban a ƙasashen Faransa da Spain da Portugal
Son ya ci kwallo uku rigis karo na hudu a tarihi a Tottenham
Tinubu ya mayar da jakadun Najeriya gida
Asalin hoton, Dolusegun
Ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Najeriya ta ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya mayar da jakadun ƙasar da ke ƙasashen ƙetare.
Cikin wata sanaraw da fadar shugaban kasar ta wallafa shafinta na X da a baya aka fi sani da Twitter, ta ce umarnin ya shafi duka jakadun ƙasar a ƙashen ƙetare, in ban da wakilan ƙasar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a New York da Geneva, sakamakon babban taron Majalisar da za a yi nan gaba cikin wannan wata.
Hakan na zuwa ne bayan mayar da jakadan Najeriya daga Birtaniya Ambassador Sarafa Tunji Ishola.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambassador Yusuf Maitama Tuggar ya ce an mayar da duka jakadun ne bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu.
"Jakadu a matsayinsu na wakilan ƙasar, suna aiki ne da umarnin shugaban ƙasa, domin kuma shi ne ke da ikon aikawa da mayar da jakadun zuwa ga kowacce ƙasa'', kamar yadda sanarwar ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen ta bayyana.
Tun da farko shugaba Tinubu ya mayar da jakadan Najeriya a Birtaniya Ambassador Sarafa Tunji Ishola wanda tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ya naɗa a watan Janairun 2021.
Cikin takardar umarnin mayar da jakadan, ministan harkokin ƙasashen wajen Najeriya ya ce ''Ina amfani da wannan dama wajen bayyana godiyar shugaban ƙasa bisa aikin da ka yi a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya''.
Bellingham ya ci kwallo na biyar a wasa huɗu a jere a La liga
Sojojin Gabon sun bayar da umarnin sake buɗe iyakokin ƙasar
Asalin hoton, Reuters
Shugabannin mulkin sojin Gabon sun bayar da umarnin sake buɗe kan iyakokin ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.
An dai rufe iyakokin ƙasar ne bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Ali Bango ranar Larabar da ta gabata.
Mai magana da yawun sojojin ƙasar ne suka bayyana umarnin sake buɗe iyakokin a wani jawabi da ya yi a gidan talbijin.
A ranar Litinin ne za a rantsa da sabon shugaban mulkin sojin ƙasar.
Sojojin sun kifar da gwamnatin Ali Bango ne jim kaɗan bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shi a mastayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da ka gudanar karo na uku.
Haaland ya ci Fulham kwallo uku rigis a Premier League
'Yan sandan Isra'ila sun yi arangama da 'yan Eritrean masu neman mafaka
Asalin hoton, Getty Images
Gomman mutane ne suka jikkata, ciki har da masu raunin harbin bindiga, bayan da aka samu arangama tsakanin 'yan sanda Isra'ila da 'yan Ertrean masu neman mafaka a birnin Tel Aviv.
'Yan sanda sun amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla da alburusai wajen tarwatsa ɗaruruwan masu zanga-zangar.
Rikicin ya kaure ne bayan da 'yan gwagwarmaya da ke adawa da gwamnatin Eritrea suka ce sun buƙaci hukumomin Isra'ila su soke wani taro da aka shirya yi a ofishin jakandancin ƙasar ranar Asabar.
Matakin da bai yi wa magoya bayan gwamnatin Eretra daɗi ba, lamarin da ya haifar da arangama tsakanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani 'yan sanda su kwantar da tarzomar.
Rahotonni daga Isra'ila na cewa mazu zanga-zangar sun durfafi inda aka tsara gudanar da taron.
Da farko 'yan sanda sun sanya musu shinge, amma daga baya sun karya shingayen.
Mazauna birnin sun ce birnin ya kasance tamkar filin yaƙi yayin da 'yan sanda suka riƙa kewaye birnin da jirage masu saukar ungulu domin kwantar da tarzomar.
Masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sandan, inda suka lalata ƙananan motoci tare da lalata shaguna.
Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce jami'anta sun yi amfani da bindiga ne a lokacin da suka fahimci cewa rayuwarsu na cikin hatsari.
Rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Eritrea kan shugabancin Isaias Afwerki ya watsu har zuwa tsakanin 'yan ƙasar mazauna ƙetare.
Indiya ta aika kumbonta na farko zuwa duniyar rana
Asalin hoton, ISRO
Indiya ta harba kumbonta na farko zuwa ga duniyar rana, kwanaki kaɗan bayan da ƙasar ta kafa tarihin zama ta farko da kumbonta ya sauka a ɓaryar kudu na duniyar wata.
An harba kumbon mai suna Aditya-L1 daga tashar Sriharikota mai nisan kilomita 100 arewa da Chennai ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:50 agogon kasar.
Kumbon zai yi tafiyar kilomita miliyan 1.5 daga doron duniya zuwa inda rana take.
Hukumar sararin samaniyar ƙasar ta ce kumbon zai yi tafiyar wata huɗu.
An raɗa wa kumbon mafi girma da zai nazarci duniyar rana- sunan Surya, wato ubangijin rana da yaren Hindu da aka fi sani da Aditya.
Sannan L1 tana nufin ainihin wurin da ke tsakanin rana da duniya inda kumbon ya dosa.
Manufar wannan sabon shirin tura kumbon ita ce samar da wata tasha ta musamman da za ta rinƙa bincike - inda ta ke muradin zama ƙasa ta farko da za ta rinƙa lura da tauraruwar (rana) da ke kusa da duniyarmu da kuma gudanar da wani nazari game da ɗabi'u da yanayin falaƙai da yanayin iskar da ake samu kewaye da su.
Ra'ayi Riga: Kan rabon tallafin rage raɗaɗi
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya duba yadda aka fara rabon kayan tallafin rage raɗaɗi da wasu gwamnatocin jihohi suka fara.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
'Yan bindiga a jihar Kaduna sun kashe mutum biyar a masallaci
Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum bakwai yayin da suka buɗe wuta ana tsaka da sallar Isha'i a wani masallaci da ke yankin ƙaramar hukumar Ikara na jihar Kaduna ranar Juma'a.
Wani mazaunin garin da abin ya faru a kan idonsa, ya kuma buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana'izar mutanen kamar yadda addinin musulunci ya tanadar
Ya ce ''Muna cikin raka'ata ta uku a sallar isha'i ne sai ga wasu mutum uku sun shigi cikin masallacin ta ɓangaren arewa, sai kawai suka buɗe wuta inda suka kashe mutum hudu a cikin masallacin''.
"Sai sai mutum guda a waje, sannan kuma suka kashe wani mai mota da ya zo wucewa ta kusa da masallacin, sai wani shi ma da ya taho ta wurin", in ji ganau ɗin.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, tana mai cewa 'yan bindigar sun kashe ƙarin mutum biyu a cikin garin na Saya-Saya.
Maharan sun shiga garin tun da misalin ƙarfe 5:00 na yamma kafin su kai harin ana sallar Isha'i, a cewar mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Kaduna.
"Sai da suka shiga gari suna tambaye-tambaye da tattara bayanai, amma babu wanda ya lura da aniyarsu kafin su kai harin da misalin ƙarfe 8:00 na yamma," in ji shi.
Rundunar ta yi kira ga mazauna jihar da su dinga saka ido da kuma kai rahoton yunƙurin duk wani abu da ba su saba gani ba.
Matsalar rashin cin abinci a tsakanin 'yan mata
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Lafiya Zinariya:
A wannan makon, filin Lafiya Zinariya ya tattauna batun rashin cin abinci musamman a tsakanin 'yan mata.
Likita ta yi bayanin dalilan da ke sa mutum ya ƙi cin isasshen abinci na lalura da kuma masu yi da gangan.
Faransa ki bar mana ƙasarmu, in ji dubban masu zanga-zanga a Yamai
Asalin hoton, AC Media Elmaestro TV
Har yanzu dai game da zanga-zanga a Yamai.
Zauwa yanzu dubban masu zanga-zangar sun fi ƙarfin sojojin da ke yunƙurin hana su shiga sansanin sojan sama na Escadrille, inda sojin Faransa da na ƙasashen Yamma suke.
Da yawansu na ɗauke da kwalayen da ke cewa "sojojin Faransa ku bar mana ƙasarmu".
Sun fito ne domin amsa kiran ƙungiyoyin fararen hula da ke mara wa sojojin mulki baya na yin zanga-zanga da kuma zaman dirshan na kwana uku da zimmar korar sojojin Faransa daga ƙasar.
A jiya Juma'a sojojin mulkin suka sake zargin Faransa da "katsalandan" a harkokin ƙasarsu saboda ci gaba da goyon bayan hamɓararren Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum da take yi.
Tuni sojojin suka bai wa 'yan sandan ƙasar umarnin fitar da jakadan Faransa daga ƙasar bayan wa'adin da suka ba shi na ficewa ya cika.
Kazalika, a yau Asabar wa'adin wata ɗaya da suka bai wa sojan Faransar ke cika.
Labarai da dumi-dumi, 'Yan Nijar na zanga-zangar korar sojin Faransa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tun daga jiya aka fara zanga-zangar bayan kammala sallar Juma'a
Rahotannin da muke samu daga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar na cewa yanzu haka ana gudanar da wata gagarumar zanga-zangar ƙin jinin sojojin ƙasashen Yamma.
Hotuna da bidiyon da ke fitowa daga wurin sun nuna yadda ɗaruruwan masu zanga-zangar suke yunƙurin shiga sansanin sojan sama na Escadrille, inda sojojin Faransa da na sauran ƙasashen waje suke.
Sai dai sojojin ƙasar, waɗanda 'yan tsirari ne idan aka kwatanta da yawan mutanen, na ƙoƙarin hana su.
A tsakiyar mako ne ƙungiyoyin da ke goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki suka kira gagarumar zanga-zangar da kuma zaman dirshan na kwana uku da zimmar korar dakarun Faransa daga ƙasar.
Nijar ta umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga ƙasar
Bazoum ya shaida mana matsalolin da yake ciki - Ayarin Ecowas
Gwamnan Kano ya naɗa mutum 44 masu taimaka masa a shafukan zumunta
Asalin hoton, KNSG
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa jimillar mutum 196 a matsayin masu taimaka masa na musamman, inda 44 za su yi aiki a ɓangaren shafukan sada zumunta da ɗaukar rahoto.
A ranar Asabar ne mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya sanar da ƙarin mutum 115 da za su yi aiki tare da gwamnan, wanda ya ci zaɓe karon farko a jihar da ke arewacin Najeriya.
Goma sha huɗu daga cikin mutanen za su yi a matsayin mataimaka na musamman, 57 manyan mataimaka, 44 kuma "a matsayin 'yan gwagwarmaya a shafukan zumunta" da kuma masu rahoto na musamman.
A watan da ya gabata ma Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya naɗa mutum 47 a matsayin masu taimaka masa a ɓangaren yaɗa labarai.
Naɗe-naɗen na zuwa ne a lokacin da gwamnatoci a Najeriya ke kukan ƙarancin kuɗin shiga, inda ma'aikata a jihohi da dama ke shafe watanni ba tare da albashi ba.
Sojojin mulkin Nijar sun soke fasfo-fasfo na jami'an gwamnatin Bazoum
Asalin hoton, Radio Television Niger
Sojojin mulkin Nijar sun sanar da soke takardun fasfo na wasu jami'an gwamnatin Mohamed Bazoum da suka hamɓarar, kamar yadda kamfanin labarai na ANP ya ruwaito.
Jami'an sun ƙunshi Firaminista Ouhoumoudou Mahamadou, da Ministan Harkokin Waje Hassoumi Massaoudou, da kuma Jakadiyar Nijar a Faransa Kane Aichatou Boulama, a cewar rahoton.
Kazalika, an soke takardun mai bai wa minista shawara Rhissa AG Boula, da na mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Takoubakoye Daoudia Djibo.
Rahoton ya ce ma'aikatar harkokin waje ta umarci shugabannin ofisoshin jakadancin ƙasar su sanar da hukumomi da ƙasashen da matakin ya shafa.
Nijar mai arzikin ma'adanin uranium da man fetur ta afka rikicin siyasa ne tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatin Bazoum a ƙarshen watan Yuli, wanda ke ƙawance da ƙasashen Yamma.
Tuni sojojin suka bai wa 'yan sandan ƙasar umarnin fitar da jakadan Faransa daga ƙasar bayan wa'adin da suka ba shi na ficewa ya cika.
Babu fargabar juyin mulki a ƙasar nan - Gwamnatin Najeriya
Asalin hoton, @FMINONigeria
Gwamnatin Najeriya ta kawar da yiwuwar juyin mulki a ƙasar yayin da ƙasashen Afirka ke ci gaba da fuskantar hakan a baya-bayan nan.
Cikin wata hira da jaridar Punch ranar Juma'a, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce 'yan Najeriya sun gama rungumar dimokuraɗiyya.
"Ina tabbatar muku cewa babu wata fargaba kwatakwata. Mun wuce nan, saboda mun daɗe a cikin dimokuradiyya da kuma yadda ma'aikatu ke ƙara kafuwa a kan ta," a cewar ministan.
Sau biyar aka taɓa yin juyin mulki a Najeriya tun bayan samun 'yancin kai a 1960 - karo na ƙarshe da aka yi shi ne a 1993.
Ƙasar ta koma kan mulkin dimokuraɗiyya a 1999 bayan Janar Abdulsalami ya miƙa mulki ga farar hula, inda Olusegun Obasanjo ya lashe zaɓe a loakcin. Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk shekara huɗu.
Juyin mulki na ranar Laraba da aka yi a Gabon ne na baya-bayan nan a Afirka bayan wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnati a Nijar ranar 26 ga watan Yuli a ƙasar mafi maƙwabtaka da Najeriya.
Darajar naira na hawa da sauka a kasuwar gwamnati ranar Juma'a
Asalin hoton, Getty Images
Darajar kuɗin naira ta ɗan ɗaga a kan dalar Amurka a kasuwar canjin kuɗi ta gwamnati a ranar Juma'a, wadda ke kira Investors and Exporters (I&E).
Nairar ta farfaɗo da kashi 2.93 cikin 100, inda aka canzar da ita har a kan N720 zuwa N740.38 kan kowace dala ɗaya, kamar yadda rahoton kamfanin labarai na NAN ya nuna.
A ranar Alhamis, an canzar da nairar kan N762.71 kan dala ɗaya a kasuwar.
Sai dai kuma, rahotanni na nuna ta kai kusan N917 a kasuwar bayan fage ranar Juma'ar.
A kasuwar ta I&E, darajar nairar ta faɗi har zuwa N799.90 a kasuwar ta jiya Juma'a, kafin ta tashi a N775.17.
Kotu ta ɗaure maharin majalisar Amurka shekara 18
Asalin hoton, Reuters
Kotun Amurka ta sake yanke wa ɗan ƙungiyar Proud Boys masu tsattsauran ra'ayi hukunci, wanda aka naɗi bidiyonsa yana sahun gaba lokacin da suka kai wa majalisar kasar hari a 2021.
An yanke wa Ethan Nordean ɗaurin shekara 18 a kurkuku.
Wakilin BBC ya ce rawar da ya taka a lokacin a bayyane take a cikin bidiyon; shi ne riƙe da lasifika yana ƙara tunzura magoya bayan Trump da ke ƙoƙarin hana tabbatar da halascin nasarar Joe Biden.
An kuma yanke wa Dominic Pezzola shekara 10 a gidan yari, wanda cikin laifukansa har da cin zarafin ɗan sanda.