'Mutanen Ghana fiye da dubu 800 sun auka cikin talauci a 2022'
Bankin Duniya ya ce 'yan Ghana kimanin 850,000 ne aka jefa su cikin talauci bara, saboda tsadar rayuwa sanadin rashin kuɗin sayen kaya da ƙarin farashin abinci da kayan masarufi.
A cikin sabon rahoton Nkechi Ogbonna, wakiliyar kasuwancin Afirka ta Yamma, a kan Tattalin Arzikin Ghana mai suna: Tattalin Arziki: warware hauhawar farashin kaya a Kan Talauci da Wadatar Abinci, Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Ghana ya shiga mawuyacin hali saboda faduwar darajar cedi da hauhawar farashi da kuma karyewar jarin da ake juyawa a cikin gida a 2022.
Lamarin ya faru ne bayan ya fara farfaɗowa daga annobar korona a 2021.
Bankin ya ce hukumomi sun gaza aiwatar da muhimman sauye-sauye masu ɗorewa da ake bukata da nufin dawo da basuka da dorewar tattalin arziki a 2022 wanda ya samu ci gaba gaba ɗaya da kashi 3.1%, lamarin da ke nuna cewa ya ragu matuka daga kashi 5.4% da aka samu a shekarar da ta gabata.
Masana tattalin arziki a bankin sun ce hauhawar farashi, ya haifar da matsin rayuwa, da kuma ƙaranci wanda ya kai mafi girma cikin shekara 20 da kashi 54.1 a watan Disamban 2022.
Wani ɓangare na rahoton ya ce, yayin da farashin kayan abinci ke hauhawa, 'yan Ghana da dama sun ƙoƙarta wajen sayen abincin da ya dace da buƙatunsu abin da hakan ya nuna tsananin ƙarancin abincin da aka shiga.
Zuwa watannin uku na ƙarshen 2022, ana jin cewa kashi ɗaya cikin huɗu na jama'ar Ghana ba su da isasshen abinci, kuma ana sa ran adadinsu zai ci gaba da ƙaruwa a 2023.
A matsayinta na ƙasa mafi arziƙin zinari a Afirka, Ghana ta samu dala miliyan 600 cikin dala biliyan 3 daga asusun ba da lamuni na duniya da nufin daidaita tattalin arzikinta yayin da ta fara sake fasalin basuka da sauran manufofin tattalin arziki da nufin bunkasa kudaden shiga.















