Babban jami'in lafiya na Amurka ya yi gargaɗin cewa ƙasar na fuskantar wani bala'i na zaman kaɗaici wanda hatsarinsa ya yi daidai da shan taba sigari kara 15 a rana.
Babban likitan na Amurka, Vivek Murthy, ya fitar da bayanan shawarwarin ne inda ya yi kira a riƙa bai wa masu zaman kaɗaici kulawa sosai kamar yadda ake bai wa masu larurar taiɓa da jarabar shan ƙwaya.
Bayanan shawarar sun yi gargaɗin cewa ana tsammanin kusan rabin Amurkawa daga kowanne fannin rayuwa ne, wannan matsala ta shafa.
Mista Murthy ya kuma bayyana wani tsari na gwamnatin ƙasar don sake gina alaƙa tsakanin jama'a.
An ba da rahoton cewa kaɗaici na ƙara hatsarin mutuwar fuju'a da kusan kashi 30% - ta hanyar larurori kamar ciwon suga da cutukan zuciya da rashin barci da kuma cutar tsananin mantuwa.
Ana kuma alaƙanta rashin zumunci, da kasa taɓuka abin kirki a fagen neman ilmi da rashin ƙwazo a wajen aiki, in ji bayanan shawarwarin.
Matsalar ta ƙara ta'azzara ne sanadin annobar korona, wadda ta sa mutane da yawa suka rage zumunci da sauran jama'a.
Wani nazari da rahoton ya ambato, ya gano cewa an samu raguwar kashi 16% na abokan zumunci a tsakanin mutanen da aka bibiyi rayuwarsu daga watan Yunin 2019 zuwa Yunin 2020.
Idan ana son shawo kan wannan lamari, Vivek Murthy ya yi kira a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen "gyara igiyar zumuncin al'umma a ƙasarmu" ta yadda za a "daina tsangwamar masu fama da kaɗaici kuma a canza al'adunmu da kuma manufofin gwamnati da ke kula da lamarin".
Tsarin da ya fitar na da turaku guda shida, a ciki har da ƙoƙarin ƙarfafa ababen more rayuwar al'umma a unguwanni, a wani ɓangare, da tattalin cibiyoyin kula da lafiya na gwamnati.
Shawarwarin sun kuma yi kira a samu ƙarin "manufofin kyautata rayuwa masu inganta zumunci" da za a fito da su don taimaka wa wani bincike wanda zai shawo kan giɓin bayanai da ake da su game da illolin kaɗaici a cikin al'umma.
Sun kuma nunar da buƙatar ƙara fayyace gaskiya wajen tattara bayanai daga kamfanonin fasahar sadarwa da kuma yin garambawul ga dandali-dandali na dijital.
Shawarwarin wani ɓangare ne na faffaɗan ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Biden don shawo kan matsalar larurar ƙwaƙwalwa, a cewar sakatariyar yaɗa labarai ta fadar White House.
Mayu shi ne watan da aka ware a Amurka don wayar da kai game da lafiyar ƙwaƙwalwa.