'Yan sandan Najeriya sun kama Hudu Ari

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Ahmad Tijjani Bawage, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Rufewa

    Karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Laraba - idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku wasu rahotannin.

    A madadin abokan aiki - Nabeela Mukhtar Uba da kuma Mukhtar Adamu Bawa, Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Hatsarin kaɗaici ɗaya ne da na shan taba sigari - babban likitan Amurka

    Kaɗaici

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami'in lafiya na Amurka ya yi gargaɗin cewa ƙasar na fuskantar wani bala'i na zaman kaɗaici wanda hatsarinsa ya yi daidai da shan taba sigari kara 15 a rana.

    Babban likitan na Amurka, Vivek Murthy, ya fitar da bayanan shawarwarin ne inda ya yi kira a riƙa bai wa masu zaman kaɗaici kulawa sosai kamar yadda ake bai wa masu larurar taiɓa da jarabar shan ƙwaya.

    Bayanan shawarar sun yi gargaɗin cewa ana tsammanin kusan rabin Amurkawa daga kowanne fannin rayuwa ne, wannan matsala ta shafa.

    Mista Murthy ya kuma bayyana wani tsari na gwamnatin ƙasar don sake gina alaƙa tsakanin jama'a.

    An ba da rahoton cewa kaɗaici na ƙara hatsarin mutuwar fuju'a da kusan kashi 30% - ta hanyar larurori kamar ciwon suga da cutukan zuciya da rashin barci da kuma cutar tsananin mantuwa.

    Ana kuma alaƙanta rashin zumunci, da kasa taɓuka abin kirki a fagen neman ilmi da rashin ƙwazo a wajen aiki, in ji bayanan shawarwarin.

    Matsalar ta ƙara ta'azzara ne sanadin annobar korona, wadda ta sa mutane da yawa suka rage zumunci da sauran jama'a.

    Kaɗaici

    Wani nazari da rahoton ya ambato, ya gano cewa an samu raguwar kashi 16% na abokan zumunci a tsakanin mutanen da aka bibiyi rayuwarsu daga watan Yunin 2019 zuwa Yunin 2020.

    Idan ana son shawo kan wannan lamari, Vivek Murthy ya yi kira a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen "gyara igiyar zumuncin al'umma a ƙasarmu" ta yadda za a "daina tsangwamar masu fama da kaɗaici kuma a canza al'adunmu da kuma manufofin gwamnati da ke kula da lamarin".

    Tsarin da ya fitar na da turaku guda shida, a ciki har da ƙoƙarin ƙarfafa ababen more rayuwar al'umma a unguwanni, a wani ɓangare, da tattalin cibiyoyin kula da lafiya na gwamnati.

    Shawarwarin sun kuma yi kira a samu ƙarin "manufofin kyautata rayuwa masu inganta zumunci" da za a fito da su don taimaka wa wani bincike wanda zai shawo kan giɓin bayanai da ake da su game da illolin kaɗaici a cikin al'umma.

    Sun kuma nunar da buƙatar ƙara fayyace gaskiya wajen tattara bayanai daga kamfanonin fasahar sadarwa da kuma yin garambawul ga dandali-dandali na dijital.

    Shawarwarin wani ɓangare ne na faffaɗan ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Biden don shawo kan matsalar larurar ƙwaƙwalwa, a cewar sakatariyar yaɗa labarai ta fadar White House.

    Mayu shi ne watan da aka ware a Amurka don wayar da kai game da lafiyar ƙwaƙwalwa.

  3. Za mu ci gaba da ayyukan agaji a Afghanistan - MDD

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce za su ci gaba da ayyukan agaji a Afghanistan don miliyoyin mutanen da suke bukatar taimako duk da takunkumin da Taliban ta yi wa ma'aikatanta mata.

    Mista Guterres na wannan jawabi ne bayan taron kwanaki biyu a Doha.

    Mista Guterres ya ce hana matan Afghanistan su yi aiki a Majalisar dinkin duniya da kungiyoyi na gida ketare masu zaman kansu, ba a bu ne da za a laminta ba, kuma abu ne da ya jefa rayuwa cikin hadari.

    Jakadu daga kasashe daban-daban ne suka halarci taron na sirri inda aka cimma matsayar maido da zaman lafiya a Afghanistan duk kuwa da cewar babu wakilci daga yan Taliban din na kasar Afghanistan.

  4. Labarai da dumi-dumi, An kama wani mutum a wajen fadar Sarkin Ingila

    Fadar Buckingham

    An kama wani mutum da zargin tayar da abin fashewa a wajen fadar Sarkin Ingila, bayan da ya jefar da harsasan bindiga a harabar fadar, in ji 'yan sanda.

    An killace wajen fadar ta Buckingham bayan da ‘yan sanda suka tsare mutumin da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talata, bayan da ya tunkari kofar fadar.

    An kama mutumin ne bisa zargin mallakar wani makami mai kai hari, in ji ƴan sanda.

    Babu rahotannin harbin bindiga ko jikkata ƴan sanda ko kuma jama'a.

    An kuma samu mutumin da mallakar wata jaka da ba a yadda da ita ba, a cewar ƴan sanda.

  5. Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun amince da tsagaita wuta

    Shugabannin bangarorin da suke fada da juna a Sudan sun amince da tsagaita wuta na kwanaki bakwai da zai fara aiki daga ranar Alhamis.

    Tsagaita wutar da aka kulla a baya dai ba ta yi cikakkiyar nasara ba.

    Akalla fararen hula dubu dari biyar rikicin ya daidaita a tsakanin kwanaki 17 da aka kwashe ana gwabza fada a tsakanin Sojin sudan da dakarun RSF.

    Wakilin BBC ya ce sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki ranar Alhamis.

    Wata sanarwa da ma`aikatar harkokin wajen Sudan ta Kudu ta fitar ta bayyana cewar bagarorin biyu masu rikici da juna sun amince su sanar da wadanda za su wakilce su a tattaunawar sulhu.

    Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana aniyar shiga tsakani don sasanta rikicin na Sudan, kuma tuni aka zabe ta a matsayin guda daga cikin kasashen da za su jagorancin sulhun.

  6. Labarai da dumi-dumi, PSG ta dakatar da Messi kan ziyarar da ya kai Saudiyya

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Paris St-Germain ta dakatar da kyaftin ɗin Argentina Lionel Messi na tsawon makonni biyu, bayan ya tafi ƙasar Saudiyya, ba tare da izinin ƙungiyar ba a wannan makon.

    Tafiyar dai ta zo ne bayan rashin nasarar da PSG ta yi a gidan Lorient ranar Lahadi, inda Messi ya buga wasa tsawon minti 90.

    Messi ba zai yi atisaye ko buga wa PSG wasa a tsawon lokacin da aka dakatar da shi ba.

    An fahimci cewa ƙyaftin ɗin mai shekara 35 ɗin ya nemi izinin yin tafiya don gudanar da ayyukan kasuwanci amma PSG ba ta sahale masa ba.

    Messi yana da matsayin jakadan yawon buɗe ido ga ƙasar Saudiyya.

    Kwanturagin gwarzon ɗan kwallon duniyar na tsawon shekara biyu da PSG zai ƙare ne a wannan bazara.

  7. An kori minista saboda halartar taron ƴan adawa

    Ministan da aka kora

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Laberiya George Weah, ya kori Cooper Kruah kwanaki kaɗan bayan da ministan sadarwan ya halarci wani taron 'yan adawa.

    An ce mista Kruah ya je gangamin siyasa na jam'iyyar adawa ta Unity Party a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta bayyana ɗan takararta na shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen da za a yi a watan Oktoba.

    Matakin dai ya harzuka jiga-jigan jam'iyyar Coalition for Democratic Change mai mulki, inda suka bukaci a cire ministan daga gwamnati.

    Shugaba Weah ya naɗa Worlea-Saywah Dunah, tsohon ma'aikacin gwamnati domin maye gurbinsa.

    Naɗin nasa - wanda aka sanar da yammacin ranar Litinin - yana jiran amincewar majalisar dattawa.

    Ana sa ran za a gudanar da zaɓuɓɓukan da ake hasashen za a yi fafatawa mai zafi, inda shugaba Weah zai fuskanci kalubale daga ɗan takarar jam'iyyar Unity Joseph Boaka da Alexander Cummings na jam'iyyun siyasa masu haɗin gwiwa.

  8. Albashina 942,000 ne a wata, alawus ɗin bai taka kara ya karya ba – Ngige

    Chris Ngige

    Asalin hoton, Gwamnatin Najeriya

    Yayin da ake ta kiraye-kirayen a ƙara mafi ƙarancin albashi na N30,000 a Najeriya, ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya ce albashinsa da na sauran ministoci bai fi N942,000 ba.

    Da yake magana a wani shirin 'Siyasar mu a Yau' na gidan talbijin ɗin Channels, Ngige ya kuma ce ba su da alawus-alawus a matsayinsu na ministoci, sai alawus ɗin aiki kawai.

    “Duk ministan da ka gani, shi ne abin da yake samu, masu ba da shawara na musamman su ma suna samun kusan wannan adadin.

    Alawus ɗin bai taka kara ya karya ba, ba mu da wani alawus, sai idan za mu yi tafiya. Kuna iya samun alawus ɗin hutu kamar duk wani jami'in gwamnati," in ji Ngige.

    Ya kara da cewa a baya-bayan, an sake bitar kuɗaden alawus ɗin tafiye-tafiye na ministoci tare da na manyan sakatarori da sauransu.

    “An ƙara kuɗin zuwa N100,000 ga minista, na ƙaramin minista kuma zuwa N75,000, sai kuma na manyan sakataror N70,000, an ƙara na kowa, ba namu kaɗai ba,” a cewarsa.

    Da aka tambaye shi ko me ya sa gwamnati ta kasa magance batun rashin aikin yi a ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 33.3 a shekarar 2021, Ngige ya ce samar da ayyukan yi wani nauyi ne da ya rataya a kan kamfanoni, ba wai gwamnati kaɗai ba.

    Ya kuma ɗora alhakin ƙaruwar rashin aikin yi, a kan raguwar zuba jari daga ƙasashen waje.

  9. Wane hali ake ciki kan kwaso ɗaliban Najeriya da suka maƙale a Sudan?

  10. Gidajen yari a Madagascar sun yi cikar ban tsoro - MDD

    Madagascar

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa gidajen yarin Madagascar sun yi cikar ban tsoro, inda ta ce hakan na da matukar haɗari.

    Bayan ziyarar farko da ya kai tsibirin tekun Indiya, kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan hana azabtarwa, ya ce wasu wuraren suna ɗauke da fursunoni fiye da abin da gidan yarin zai iya ɗauka.

    Kwamitin ya ce kamata ya yi Madagascar ta sake yin la'akari da manufofinta na hukunta masu laifi, domin rage abin da ya kira babban cunkoso.

    Ya bayyana yanayin a matsayin zalunci da rashin mutunta ɗan adam da kuma saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

  11. Limamin cocin mai sa azumin mutuwa ya bayyana gaban kotu a Kenya

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Limamin coci mai sa azumin mutuwa Paul Mackenzie Nthenge, ya bayyana gaban kotu a Kenya kan mutuwar ɗaruruwan mutane.

    Malamin cocin ya janyo mutuwar ɗaruruwan mutane bayan sanya su yin azumi don haɗuwa da Yesu.

    An kuma gano gawarwakin mabiyansa fiye da 100 a manyan ƙaburbura a ƙasar a watan da ya gabata.

    Mackenzie, wanda tsohon direban tasi ne, an same shi da laifin cutar da mabiyansa ta hanyar hana su cin abinci har ta kai ga mutuwar ɗaruruwa, inda ya ce za su shiga aljanna kafin tashin duniya.

    Ana kuma shirin gurfanar da wani fasto na daban mai suna Ezekiel Odero a gaban kotu kan zargin kisan kai da kuma taimakawa masu kashe kansu da kansu.

  12. Barca ta ci Osasuna gida da waje a La Liga a bana

  13. Matsayar gwamnatin Najeriya kan ce-ce-ku-cen haramta cin taliyar 'Indomie'

  14. Ambaliya ta ɗaiɗaita dubban mutane a yammacin Kenya

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane sun fuskanci mummunar ambaliya a Yammacin Kenya a makon da ya gabata, kamar yadda hukumomin Lardin Kisumu suka shaida wa BBC.

    Kusan gidaje 5,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a yammacin Kenya cikin mako guda.

    Kawo yanzu dai, ba a samu asarar rayuka ba, amma ana fargabar lamarin na iya munana idan aka ci gaba da samun ruwan sama.

    Mukaddashin kwamishinan lardin na Kisumu, Hussein Alanson Hussein, ya shawarci waɗanda ke zaune kusa da tafkin Victoria da kuma bakin kogin Nyando da su matsa daga wurin domin tsira da rayuwarsu.

    "Za mu sami ƙarin ruwan sama kuma daga abin da muka shaida, muna son mutanen da ke zaune a bakin kogin Nyando su matsa zuwa wani wuri don tseratar da rayuwarsu," kamar yadda ya shaida wa BBC.

    Mista Hussein ya ce karamar hukumar ta kafa cibiyar kwashe mutanen da lamarin ya shafa, inda a halin yanzu iyalai ke zaune a wani matsuguni da aka samar.

    Ya yi kira ga cibiyar kula da bala`o`i ta kasa da ta taimaka wa waɗanda abin ya shafa da kayan masarufi.

    Sassan ƙasar da dama sun fuskanci mamakon ruwan sama a tsawon watan da ya gabata.

  15. Har yanzu Kofin Firimiya bai kuɓuce mana ba - Arteta

    Arteta

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Arsenal Mikel Arteta, ya ce har yanzu suna da damar cin Kofin Firimiyar bana.

    Arteta ya ce za su ci gaba da ƙwazo har sai tura ta kai bango a lokacin da aka kammala gasar ta bana.

    A ranar Lahadi ne Gunners ta koma ta biyu a teburin Firimiya, bayan Manchester City ta doke Fulham 2-1, inda yanzu City ke da kwantan wasa ɗaya.

    Arteta ya ce bayan kasa samun nasara a wasanni huɗu da kulob ɗinsa ya yi a baya, suna son dawo da abubuwa yadda suka kamata a wasan da za su fafata da Chelsea ranar Talata.

    "Har yanzu Firimiya ba ta kuɓuce mana ba, saboda akwai sauran wasa biyar a gaba, kuma abubuwa da dama za su iya faruwa," in ji Arteta.

    "Duk da cewa, damar da muke da ita a yanzu ba ta da yawa, amma abin da za mu yi shi ne cinye ragowar wasanninmu, mu kuma ga yadda City za su kaya a wasanninsu.

    "Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu manta abin da ya faru a makon jiya, mu ɗauki darasi, sannan mu fuskanci wasanmu na gaba."

  16. Afghanistan ce ƙasar da ta fi fuskantar rikici mafi muni a duniya - MDD

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana Afghanistan a matsayin ƙasar da ta fi kowacce ƙasa fuskantar rikicin yaki mafi girma yanzu a duniya.

    Mista Guterres na wannan magana ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kwanaki biyu a Doha.

    Ya ce kashi 97 na al`ummar Afghanistan na fama da talauci, kashi biyu cikin uku na mutanen ƙasar miliyan 28 ne za su bukaci tallafi a bana domin su rayu, yara miliyan shida na Afghanistan mata da maza na dab da fadawa yanayin rashin samun abinci.

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar ta ce wariyar da mata da yara ƙanana ke fuskanta take hakkin Yan Adam ne.

    Taron na sirri tare da wakilan ƙasashen ƙetare ya mayar da hankali ne kan cigaban alaƙa da shugabannin Taliban waɗanda ba a gayyata taron ba.

    Taron ya gudana ne lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke sake yin duba game da tallafinta a Afghanistan bayan haramta wa mata aiki da Majalisar Dinkin Duniyar.

  17. 'Yan Real Madrid da suka je Sociedad buga La Liga

  18. Labarai da dumi-dumi, 'Yan sandan Najeriya sun ce sun kama Hudu Ari

    Hudu

    Asalin hoton, Nig. Police

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama kwamishinan zaɓen jihar Adamawa da aka dakatar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce jami'an rundunar masu bibiyar harkokin zaɓe ne suka kama Hudu Ari, ranar Talata a Abuja babban birnin ƙasar.

    sanarwar ta ce kwamishinan na INEC yana hannunta don amsa tambayayoyi kan tuhume-tuhumen da ake masa game da ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen cike giɓi da aka gudanar ranar 15 ga watan Afrilu.

    Babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya ce rundunar za ta kama duk mutanen da ke da hannu a lamarin domin gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanada.

    Ya kuma sake jaddada ƙudurin 'yan sandan wajen tabbatar da adalci a cikin lamarin tare da gurfanar da duk mutanen da ke da hannu a lamarin gaban kotu.

    Matakin da kwamishinan zaɓen na jihar Adamawa ya ɗauka a lokacin zaɓen 15 ga watan Afrilu ya janyo ruɗani, bayan ya bayyana Binani a matsayin wadda ta yi nasara duk da yake ba a kammala tattara sakamako ba.

    Lamarin ya sanya hukumar zaɓe ta INEC ta dakatar da Ari, yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin gudanar da bincike a kan sa, da kuma jami'an tsaron da suka ba shi kariya a lokacin da abin ya faru.

    Yayin wata tattaunawa da BBC a ranar Litinin, Hudu Ari ya ce zai kai kansa ga ‘yan sanda domin amsa tuhumar da ake yi masa.

    Ya dai ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba, don kuwa a cewarsa abin da ya yi yana kan doka.

    Hudu Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karɓi cin hancin naira biliyan biyu, kafin ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara.

  19. Rikicin Sudan: Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci ministan harkokin waje

    Femi Gbajabiamila

    Asalin hoton, TWITTER/@HOUSENGR

    Majalisar wakilan Najeriya za ta gana da ministan harkokin wajen ƙasar, Geoffrey Onyeama da sauran manyan jami'ai masu alaƙa da aikin kwaso 'yan Najeriyan da rikici ya ritsa da su a Sudan.

    Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya ce jami'an sun haɗar da na hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna ƙetare (NIDCOM) da na hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA.

    Ya ƙara da cewa ''Sudan ta faɗa cikin rikici a 'yan makonnin da suka gabata, kuma abin taƙaici wannan rikici ya rItsa da 'yan Najeriya da ke zaune a ƙasar''.

    “An yi shiri domin tabbatar da kwaso 'yan ƙasarmu da suka haɗar da ɗalibai da 'yan kasuwa da sauran masu sana'o'i cikin kwanciyar kwanciyar hankali ba tare da ɓata lokaci ba'', in ji kakakin majalisar.

    “Na buƙaci shugaban kwamitin harkokin waje na majalisa, ya gayyaci ministan ƙasashen waje da jami'an hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna ƙetare (NIDCOM) da na hukumar ba da agajin gaggawa ta (NEMA) zuwa zauren majalisa, domin su bayar da bahasi kan halin da ake ciki game da aikin kwashe 'yan ƙasar daga Sudan''

    Mista Gbajabiamila ya ce majalisar na sane da irin wahalhalun da ake fuskanta game da aikin kwashe 'yan ƙasar daga Sudan din.

  20. Gasar kofin duniya ta mata: Fifa ta yi barazana ga wasu kasashen Turai