Mutane ɗari biyu da goma sha huɗu ne suka mutu tsakanin watan Janairu da Maris din
shekarar 2023, a hare-haren ‘yan bindiga da rikicin ƙabilanci da
hare-haren ɗaukar fansa a jihar Kadunan a Najeriya.
A cikin wannn adadi 14 mata
ne a yayin da huɗu yara ne ‘yan ƙasa da shekaru 18.
A gundumar Kaduna ta Tsakiya, an samu rahoton mutuwar mutane 115 (kashi 54 bisa
dari na yawan adadin).
Ɗari da takwas na waɗannan adadi sun faru ne a yankunan ƙananan hukumomin Birnin Gwari, da Giwa, da Igabi, Chikun da kuma Kajuru.
Ƙananan hukumomi Giwa da Birnin Gwari duka sun samu yawan adadin mutane 32 da
suka mutu, karamar hukumar Chikun 25, Igabi 13, sai Kajuru shida a watannin
ukun farkon shekarar 2023.
A
yankin kudancin Kaduna an samu mutuwar mutane 61 a daidai irin wannan lokaci.
Yanayin kai hare-hare da na daukar fansa, da munanan tashe-tashen hankula na
addini da na kabilanci – tsakanin hare-haren ‘yan bindiga – sun faru a karamar
hukumar Zangon Kataf, inda mutane 19 suka rasa rayukansu.
Mutane
12 ne kuma aka kashe a ƙaramar hukumar Sanga a cikin watanni ukun farko na
shekarar 2023.
Yankin arewacin jihar ya shaida mutuwar mutane 38 a watanni ukun
farko, inda aka samu mutuwar mutane 22 a karamar hukumar Zaria.