An ga watan Sallah a Saudiyya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage

  1. Juma'a take Ƙaramar Sallah ma a Nijar

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da ganin jaririn watan Shawwal a ranar Alhamis ɗin nan.

    An ga watan sallar ne a jihohin Diffa da Dosso da Zinder da Agadez da Tahoua da ku ma Tillabery.

    Hakan na nufin al'ummar Musulmi a Nijar sun kawo ƙarshen azumin watan Ramadan na bana.

    Majalisa ƙoli kan harkokin addinin Musulunci ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar ce ta ba da sanarwar ganin watan.

  2. Buhari ya amince da dakatar da Hudu Ari

    PRESIDENCY

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin hukumar zaɓen ƙasar na dakatar da kwamishinanta na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, ya zuwa lokacin da za a kammala bincike.

    Tuni dai hukumar zaɓe ta damƙa batun Hudu Ari hannun babban sufeton 'yan sanda don ya binciki halayyar kwamishinan a lokacin zaɓen cike giɓi na jihar Adamawa.

    Shugaba Buhari ya umarci gudanar da bincike da gurfanar da Hudu Ari gaban shari'a, matuƙar an same shi da hannu.

    Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na Sakataren Gwamnatin Tarayya Willie Bassey ya fitar, ta kuma ambato Buhari yana umartar babban sufeton 'yan sanda da babban daraktan hukumar tsaron farin kaya DSS da babban kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defence, su ma su gudanar da bincike kan rawar da jami'ansu suka taka wajen taimaka wa Barista Hudu Yunusa Ari.

    Ya kuma buƙaci ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda aka samu da laifi.

  3. Rufewa

    To yau a nan za mu rufe wannan shafi wanda ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye. Mun yi farin cikin kasancewa da ku a tsawon wannan rana ta Alhamis.

    Da fatan gobe Juma'a, Haji Babbar Rana! Za ku iya ci gaba da bibiyar mu a wannan shafi na BBC Hausa.

    Buhari Muhammad Fagge tare da abokin aiki Mukhtari Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya!

    Ku duba ƙasa don ci gaba da karanta labaran da muka wallafa muku.

  4. Hotunan Masallacin Ka'aba da launukan Barka da Sallah

    MASJID AL-HARAM

    Asalin hoton, MASJID AL-HARAM

    MASJID AL-HARAM

    Asalin hoton, MASJID AL-HARAM

  5. Sallah sai ranar Asabar a Iran

    BBC

    Ofishin Jagoran addinin na Iran Ali Khamenei ya sanar da cewa ba a ga jaririn watan Shawwal ba a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023, don haka watan Ramadan zai ƙare ranar Juma'a 21 ga watan Afrikun, Asabar ta zama sallah 1 gawatan Shawwal.

    A cewar rahotanni kimanin ƙungiyoyi 100 aka aika yankuna mabambanta domin aikin ganin jaririn watan na Shawwal.

    Rahotannin sun ce wasu daga cikin waɗanda suka yi aikin duba watan a ƙauyen Qom yanayin duhun gari ne ya hana su ganin shi.

  6. Tsakanin mutum 10,000 zuwa 20,000 sun gudu daga Sudan zuwa Chadi - MDD

    BBC

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa tsakanin mutum 10,000 zuwa 20,000 ne suka tsere daga Sudan zuwa makwabciyarta Chadi domin tsira da rayuwarsu.

    Hukumar da ke lura da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce wannan ba ƙaramin tashin hankali ba ne da rikicin Sudan ya haifar, kuma ta ce mafi yawan waɗanda suke isa Chadin mata ne da ƙananan yara.

    "Abin da za a fi bai wa muhimmanci a yanzu shi ne buƙatarsu ta ruwa da abinci da wurin zama sannan a kare ƙananan yara da kuma kare mata daga cin zarafi," kamar yadda sanarwarsu ta bayyana.

    Babu wanda zai iya cewa ga yadda wannan rikicin da aka kwashe kwanaki shida ana yi zai ƙare.

    Yarjejeniya biyu da aka yi ta tsagaita wuta ba ta yi aiki ba, yayin da shugaban sojin Sudan ya shaida wa Al Jazeera cewa baya ganin tattaunawar a matsayin mafita.

  7. Mutum 214 aka kashe cikin wata uku a Kaduna

    l

    Asalin hoton, ElRufa'i Facebook

    Mutane ɗari biyu da goma sha huɗu ne suka mutu tsakanin watan Janairu da Maris din shekarar 2023, a hare-haren ‘yan bindiga da rikicin ƙabilanci da hare-haren ɗaukar fansa a jihar Kadunan a Najeriya.

    A cikin wannn adadi 14 mata ne a yayin da huɗu yara ne ‘yan ƙasa da shekaru 18.

    A gundumar Kaduna ta Tsakiya, an samu rahoton mutuwar mutane 115 (kashi 54 bisa dari na yawan adadin).

    Ɗari da takwas na waɗannan adadi sun faru ne a yankunan ƙananan hukumomin Birnin Gwari, da Giwa, da Igabi, Chikun da kuma Kajuru.

    Ƙananan hukumomi Giwa da Birnin Gwari duka sun samu yawan adadin mutane 32 da suka mutu, karamar hukumar Chikun 25, Igabi 13, sai Kajuru shida a watannin ukun farkon shekarar 2023.

    A yankin kudancin Kaduna an samu mutuwar mutane 61 a daidai irin wannan lokaci.

    Yanayin kai hare-hare da na daukar fansa, da munanan tashe-tashen hankula na addini da na kabilanci – tsakanin hare-haren ‘yan bindiga – sun faru a karamar hukumar Zangon Kataf, inda mutane 19 suka rasa rayukansu.

    Mutane 12 ne kuma aka kashe a ƙaramar hukumar Sanga a cikin watanni ukun farko na shekarar 2023.

    Yankin arewacin jihar ya shaida mutuwar mutane 38 a watanni ukun farko, inda aka samu mutuwar mutane 22 a karamar hukumar Zaria.

  8. Labarai da dumi-dumi, An ga watan Sallah a Saudiyya

    Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023.

    An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29.

    Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

  9. Labarai da dumi-dumi, Ba a ga wata a lardunan gabashin Saudiyya ba

    Haramain

    Asalin hoton, Haramain

    Hukumomin Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal na ƙaramar sallah ba a lardunan gabashin ƙasar ba, yan mintina bayan faɗuwar rana.

    Tuni aka sanar da kotun ƙoli game da wannan lamari a ƙasar ta Saudiyya, kamar yadda shafin Haramain ya wallafa.

    Sai dai hukumomin sun ce za a ci gaba da duba watan a yankunan tsakiyar Saudiyya.

  10. An kashe yara tara a rikicin Sudan - Unicef

    Rikicin Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Unicef ya ce yara za su ci gaba da ɗanɗana kuɗarsu

    Akalla yara tara ne suka mutu yayin da wasu 50 suka jikkata a Sudan a faɗan da ake ci gaba da gwabzawa wanda ya shiga rana ta shida, a cewar asusun kula da ƙananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya.

    Hukumar ta ce wasu yaran suna matsuguni a makarantu da cibiyoyin kula da lafiya, yayin da aka tilasta wa asibitoci kwashe yaran a daidai.

    “Yakin da ake gwabzawa ya kawo cikas ga aikin ceton rayuka da aka kiyasta ya kimanin yara 50,000 da ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki. Waɗannan yara suna bukatar kulawa ba dare ba rana, inda suke cikin haɗari sakamakon karuwar tashe-tashen hankula," in ji Unicef.

    Ya ce idan ba a dakatar da faɗan da ake yi ba, "yara za su ci gaba da ɗanɗana kuɗarsu".

    Sama da alluran riga-kafi dala miliyan 40 na cikin haɗarin lalacewa saboda katsewar wutar lantarki da ba a taɓa ganin irinsa ba a rikicin Sudan, in ji Unicef.

    Ya zuwa yanzu, an kashe mutum 270 a faɗan da ya ɓarke tun ranar Asabar, a cewar wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Khartoum.

  11. Yadda ƴan bindiga suka addabi masu sana'ar sayar da itace a Nijar, Tchima Illa Issoufou: BBC Hausa, Nijar

    Masu sana'ar sayar da itace a Jamhuriyar Nijar sun koka kan yadda ƴan bindiga suka addabe su a kan hanyarsu ta zuwa neman itatuwa tsakanin Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso.

    Masu sana'ar sun ce da farko ƴan bindigar na musu gargaɗin cewa su daina zuwa wuraren, sai dai a yanzu sun koma yin duka da kuma cinna wuta kan motocinsu har ma da kisa.

    A karshen makon jiya ne ƴan bindigar suka ƙona wasu treloli sama da 50 waɗanda ke ɗauke da ganyayyakin albasa da wasu ababen hawa abu kuma da ya sa wasu kamfanonin sufurin dakatar da aikin zuwa waɗannan yankuna.

    Dann lasifikar da ke kasa domin sauraron rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai.

    Bayanan sautiDann lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton Tchima Illa Issoufou
  12. Sau nawa aka kara tsakanin Real da Man City a Champions?

  13. Rikicin Sudan: An kwashe sojojin Masar 177 daga ƙasar

    Sojoji a Sudan sun ce an kwashe sojojin ƙasar Masar 177 waɗanda dakarun RSF suka kama ranar Asabar.

    An kwashe su ne cikin wasu jiragen yakin soji na Egypt ɗin guda huɗu.

    Dakarun RSF sun cafke takwarorin nasu na Masar ɗin ne yayin da suke wani sintiri tare da sojin gwamnatin Sudan a ranar Asabar.

    Kwaso mutane daga Sudan dai a halin da ake ciki abu ne mai matukar wahala domin kuwa an ga yadda aka far wa jami'an ƙasashen waje da kuma masu aikin agaji.

  14. Ko United za ta iya fitar da Sevilla a Europa a Sifaniya?

  15. Musulmi sun zargi gwamnatin Kenya da kawo ruɗani a ganin wata

    Watan Sallah

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sashe na al'ummar Musulmai a Kenya sun zargi gwamnatin ƙasar da kawo ruɗani a ganin wata bayan ta ayyana Juma'a a matsayin ranar hutun sallah.

    Ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki ne ya ayyana hutun a ranar Laraba a wata sanarwar da gwamnati ta fitar.

    Shugaban Majalisar Koli ta Musulmi a Kenya, Hassan Ole Naado, ya shaida wa shafin intanet na Nation cewa sanarwar da gwamnatin ƙasar ta yi ya ruɗa al'ummar musulmi domin bai kamata ba har sai an ga watan sallah.

    Mista Naado ya ce ba gwamnati ce ke da hurumin sanar da kawo karshen watan Ramadan ba, inda ya ce shugaban majalisar koli ta Musulmi shi ke da ikon yin hakan.

    “Ya kamata gwamnati ta tuntuɓi Musulmi kafin ta yanke hukunci. Wannan babban kuskure ne kuma mai ruɗarwa,” inji shi.

    Musulmai da dama a ƙasar sun yi Alla-wadai da matakin gwamnatin a shafukan sada zumunta.

  16. Yadda za mu ɗore da kyawawan ayyukan da muka koya a Ramadan

  17. Rikicin Sudan: "Ɓangarorin da ke faɗa ba su damu da rayukan fararen hula ba'

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Faɗa da ya ɓarke a Sudan ya shiga kwana ta biyar

    Wani ɗan Sudan da ke zaune a birnin Omdurman ya shaida wa BBC cewa ɓangarorin da ke faɗa da juna a rikicin ƙasar "ba su damu da rayukan fararen hula ba".

    Mohamed, wanda kawai ya bayyana sunansa na farko, ya ce "ya fusata" da kuma tunanin cewa ko za a dakatar da faɗan.

    Ya kara da cewa "babu wani tsagaita buɗe wuta", duk da hasashen da aka yi a daren Laraba cewa ɓangarorin biyu sun amince da hakan.

    Ya ce an dakatar da faɗa ne kawai lokacin da ake kwashe sojojin Masar daga Sudan, amma an sake ci gaba da gwabzawa bayan sun tafi.

    Mohamed ya kuma ce an rufe tsarin bankin ƙasar, wanda ya ƙara janyo wahala wa mutane wajen sayen kayan abinci da kuma ruwa.

    Ya ce yawancin mutane a Sudan ba sa ɗaukar tsabar kuɗi, inda suke amfani da intanet wajen biyan kuɗaɗen abubuwan da suka saya wanda ya sa yanzu suke cikin wahalhalu.

  18. An fara shirin duban watan sallah a Saudiyya

    Watan Sallah

    Asalin hoton, Haramain Sharifain/Twitter

    Bayanan hoto, An girke na'urori domin aikin duban watan

    Saudiyya ta kammala shirin duban watan sallah a daidai lokacin da al'ummar Musulmi suka ɗauki azumi na 29.

    Shafin Masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa daga yau Alhamis za a fara duban watan na Shawwal.

    An girke manyan na'urorin hangen nesa domin aikin duban watan Shawwal.

    Ana sa ran fara duba watan Shawwal ne a birnin Sudair da misalin ƙarfe 06:09na yamma, sai garin Tumair inda za a fara duba da 06:22na dare.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A Najeriya ma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bukaci al'umma su fara duban jaririn watan Shawwal daga yau Alhamis 29 ga watan Ramadan.

  19. An kaddamar da bincike kan turmutsusun da ya jawo mutuwar mutane a Yemen

    Jami'ai a Sanaa, babban birnin Yemen sun kaddamar da bincike kan turmutsusun da ya jawo mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu a Yemen.

    Iyalan waɗanda suka jikkata ko kuma aka kashe na jiran su ji abin da ya haddasa turmutsutsun.

    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani jami'in bincike na duba sauran kayayyakin da suka rage a wurin da lamarin ya faru
    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutane sun taru a wajen wani asibiti domin jin labarin halin da ƴan uwansu ke ciki
    Yemen

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu kuma sun taru a wajen wurin da aka samu turmutsutsun da safiyar yau Alhamis
  20. Matashi sabon jini da ya ƙwaci kujerar majalisar wakilai daga tsohon hannu