Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sarki Charles lll ya gana da shugabannin Commonwealth a Fadar Buckingham

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh, Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na BBCHausa.com nan muka kawo karshen labarai da rahotanni, kan rasuwa da makokin da ake ciki na rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa da wasu sabbin rahotannin, da halin da ake ciki a Birtaniya, da sauran kasashe.

    Abdullahi Bello Diginza, ke muku fatan alkhairi.

    Mun gode

  2. 'Yan Siyasar Wales sun yi jimamin rasuwar Sarauniya Elizabeth ll

    'Yan siyasa a kasar Wales sun bayyana alhininsu kan rasuwar Sarauniya Elizabeth ll a wani zama na musamman da suka yi a majalisar dokokin kasar.

    Yayin da yake jagorantar zaman, babban ministan kasar Mark Drakeford ya yaba da yadda Basarakiyar ta damu da al'umar Wales da dorewar Dimkoradiiya a kasar.

    Taron na zuwa ne bayan da aka yi bikin ayyana sabon Sarki a birnin Cardiff.

    An fara zaman ne da yin shiru na 'yan wasu mintuna

    Mista Drakeford ya ce Sarauniyar ta ''cimma abubuwa masu tarin yawa a tsawon rayuwarta''.

  3. Hotunan yadda aka jera furanni a Green Park domin girmamawa ga Sarauniya

    Ɗaruruwan mutane ne suka halarci dandalin Green Park wanda ke kusa da fadar Buckingham, da ke tsakiyar birnin Landan.

    Mutanen sun halarci wurin ne domin ajiye furanni da sakonnin alhinin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.

  4. Jerin abubuwan da suka faru a yau

    Abubuwa da dama sun faru a shirye-shiryen jana'izar Sarauniya Elizabeth ll da ake yi a Birtaniya ga wasu daga cikin abubuwan da suka farun a yinin yau.

    • An dauki gawar Sarauniya a mota daga fadarta ta Balmoral inda ta rasu zuwa Edinburgh babban birnin yankin Scotland
    • Dubban mutane sun taro a kan hanyar domin bayyana alhininsu tare da nuna girmamawa ga gawar Sarauniyar - wacce ta fi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya - ta hanyar tafi tare da daga Furanni.
    • A yanzu gawar Sarauniyar na fadarta da ke Holyroodhouse a Edinburgh kafin a wuce da ita zuwa birnbin Landan.
    • 'Yayan Sarauniyar uku wato Gimbiya Anne, da Yarima Andrew da Yarima Edward, na tare da gawar a Edinburgh, a yayin da a gobe shi ma Sarki Charles lll zai tafi birnin.
    • Tun da farko dai Sarki Charles ya gana da babbar Sakatariyar Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta Commonwealth a fadar Buckingham.
    • An kuma yi bukukuwan ayyana Sarki Charles a yankunan Scotland, da Wales da kuma Ireland ta arewa.
    • Yarima William ya gana da babban ministan Wales Mark Drakeford, inda ya sha alwashin rike mutanen yankin cikin ''mutuntawa da girmamawa'' a matsayinsa na sabon Yariman Wales
  5. Sarki Charles ya gana da shugabannin Commonwealth a Fadar Buckingham

    Sarki Charles lll ya karbi bakuncin Patricia Scotland, babbar sakatariyar kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta Commonwealth a Fadar Buckingham

    Sannan kuma Sarkin ya gana da manyan Kwamishinonin kasashen da ke karkashin ikon Birtaniya.

    Bayan ganawar ne kuma Sarkin ya fita wajen fadar domin gaisawa da dandazon jama'ar da ke wajen fadar.

    A gobe ne Sarkin tare da matarsa za su je dakin taro na Westminster, inda 'yan majalisar dokokin Birtaniya za su hallara domin yi masa ta'aziyya, daga nan kuma su hau jirgin sama zuwa birnin Edinburgh wajen da gawar Sarauniya take

  6. Yadda mutane suka wuni suna dakon isowar gawar Sarauniya zuwa Edinburgh

  7. Gimbiya Anne ce ta yi wa gawar Sarauniya rakiya zuwa Edinburgh

    Gimbiya Anne tare da mijinta wanda babban hafsan sojin ruwan kasar ne wato Vice-Admiral Sir Tim Laurence sun yi wa gawar sarauniyar rakiya zuwa Edinburgh daga fadarta da ke Balmoral a yankin Scotland.

    Bayan kwashe sa'o'i shida ana wannan doguwar tafiya a mota, a yanzu gawar ta isa fadar Sarauniyar ta Holyroodhouse, wadda ke birnin Edinburgh, kuma a cikin makon da za mu shiga ne za a wuce da ita zuwa birnin Landon domin yi mata jana'izar kasa.

    A yayin wannan doguwar tafiya da aka bi ta garuruwa manya da kanana da kauyuka, sun sha tarba da nuna girmamawa daga duk jama'ar da aka bi ta garuruwansu.

  8. Labarai da dumi-dumi, Gawar Sarauniya ta isa Fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh

    Gawar Sarauniya ta isa fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh bayan tafiyar sa'o'i shida a mota daga Fadar Balmoral inda ta rasu.

    A wannan fadar ta Holyroodhouse ne dai gawar za ta kwana kafin a wuce da ita zuwa cocin St Giles a gobe Litinin da rana.

    Inda mutane da dama za su ci gaba da zuwa domin nuna girmamawa gareta.

  9. Yadda mutane suka yi dafifi a birnin Dundee domin bankwana ga Sarauniya

  10. Yadda manoma suka jera taraktoci a gefen titi domin ta'aziyya ga Sarauniya

    Manoma a Aberdeenshire sun yi ta'aziya ga Sarauniya Elizabeth II a lokacin da ake wucewa da gawarta.

    Manoman sun jera tarakatocinsu a gefen titi domin nuna girmamawa ga sarauniyar.

    Bidiyon da aka ɗauko daga jirgin sama ya nuna yadda aka ajiye motocin a gefen hanya inda suke kallon titi

  11. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu - Rasuwar Sarauniya Elizabeth

  12. Sarki Charles III ya isa Fadar Buckingham

    Sarki Charles III ya isa Fadar Buckingham inda a nan ake sa ran zai tattauna da Babbar Sakatariyar Ƙungiyar Commonwealth, Patricia Scotland.

    An ga ɗumbin mutane suna ta ɗaga hannu ga Sarki Charles III a lokacin da yake shiga fadar.

  13. Ayarin motocin da ke tafe da gawar Sarauniya ya tsaya shan mai, direbobi kuma su huta

    Ayarin da ke tafe da gawar Sarauniya Elizabeth zuwa Edinburgh ya tsaya domin a ƙara wa motoci mai direbobi kuma su huta.

    Tafiyar da za a yi daga Balmoral zuwa Fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh tafiya ce mai nisan kilomita 281, kuma ana sa ran za su shafe sa'o'i shida suna tafiyar.

  14. Ukraine ta yi ikirarin ƙwace ƙarin wurare daga dakarun Rasha

    Rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun ƙwace sama da murabba'in kilomita 3,000 a harin ramuwar gayya da suke kaiwa a gabashin Ukraine ɗin ga dakarun Rasha.

    Idan hakan ta tabbata, lallai hakan na nufin dakarun na Kyiv su ninka wuraren da suka ƙwace sau uku a cikin kwana biyu kacal.

    Ko ranar Alhamis da dare sai da Shugaba Zelensky na ƙasar ya ce an ƙwace murabba'in kilomita 1,000.

    BBC dai daga ɓangarenta ba ta tabbatar da ikirarin gwamnatin Ukraine ba domin ba a bai wa ƴan jarida damar zuwa fagen daga ba.

  15. Yadda aka jefa furanni ga motar da ke ɗauke da gawar Sarauniya

    An samu wasu da suka jefa furanni ga motar da ke ɗauke da gawar Sarauniya Elizabeth a ƙauyen Banchory.

    Banchory na daga cikin ƙauyukan da aka wuce da gawar Sarauniya a kan hanyar zuwa Edinburgh daga Balmoral.

  16. Bidiyon yadda aka fito da gawar Sarauniya Elizabeth II daga Fadar Balmoral

  17. An yi tsit a lokacin da gawar Sarauniya ke wucewa ta ƙauyen Ballater

    An yin tsit na ɗan wani lokaci a lokacin da gawar Sarauniya ke wucewa ta cikin ƙauyen Ballater.

  18. Yadda helikwaftan BBC ke ɗaukar bidiyon ayarin motocin gawar Sarauniya daga sama

    A halin yanzu dai ana tafiya da gawar Sarauniya zuwa Edinburgh, kuma za ku iya kallo kai tsaye a tashar talabijin ta BBC NEWS yadda ake tafiya da gawar Sarauniyar.

    Helikwaftan BBC ne ke ɗaukar bidiyon ayarin motocin da ke raka gawar Sarauniyar uwa Edinburgh

  19. Yadda ɗumbin mutane suka tsaya a kan hanya domin yin bankwana ga Sarauniya

    A ƙauyen Ballater kusa da Balmoral, mutane da dama ne dai suka kafa kayi a kan tituna inda suke jiran wucewar gawar Sarauniya.

    Gawar ta bar Fadar Balmoral zuwa Fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh

  20. Labarai da dumi-dumi, Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth ya bar Fadar Balmoral

    Akwatin gawar Sarauniya Elizabeth II ya bar Fadar Balmoral zuwa Edinburgh.

    An saka akwatin ne a cikin wata mota ƙirar marsandi inda wasu motoci ke biye da motar gawar.

    Dubban mutane ne suka kafa layi inda suke jiran fitowar Sarauniyar.

    A ranar 19 ga watan Satumba ne ake sa ran za a gudanar da jana'izarta.