Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa yakin da ake yi a Ukraine na barazanar haifar da yunwa da talauci da ba a taba ganin irin su ba a duniya.
Antonio Guterres ya ce tasirin yakin kan wadatar abinci da makamashi da kuma kuɗi, mai tsanani ne kuma mai ci gaba da ƙaruwa.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen fitar da rahoto na biyu na Majalisar Dinkin Duniya kan tasirin rikicin.
Mista Guterres ya ce tilas ne a kawo ƙarshen mamayar Rasha, domin kawo ƙarshen abin da ya kira guguwa.
Ya kuma yi kira da a ɗauki matakin gaggawa a duniya domin ceto rayuka.
Rasha dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan ta kawo karshen killace tashoshin jiragen ruwan Ukraine. Yayin da Moscow ta musanta zarginta da ake na hana fitar da hatsi daga Ukraine.