Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Umar Mikail, Umaymah Sani Abdulmumin, Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya
Mu kwana lafiya
A nan za mu rufe wannan shafi mai kawo muku bayanai kai-tsaye. Ku kasance da mu gobe da safe domin ci gaba da samun labaran da suka shafi rayuwarku.
Sai dai kuna iya ci gaba da karanta labarai da rahotanni a shafinmu na bbchausa.com, sannan kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta.
Mu kwana lafiya
Atiku ya fi karfin Tinubu, in ji PDP
Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta ce tana jin tausayin tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Tinubu wanda APC ta tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2023.
A wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafinta na Tuwita bayan an bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a APC, ta ce abin takaici ne yadda ya samu tikitin takara a jam'iyyar da ba ta tsinana wa 'yan kasar komai ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
"Jam'iyyarmu tana kuma tausaya wa Asiwaju bisa bin hanyar da ba za ta bille ba domin kuwa shi ba sa'an dan takarar PDP Atiku Abubakar, wanda ya fi kwarewa da kuma shiryawa wajen zaman shugaban kasa; mai hada kai wanda shi ne zabin jama'a," in ji PDP.
PDP ta siyasar Najeriya ba irin ta Jihar Lagos ba ce inda ta yi zargin cewa Bola Tinubu yana amfani da karfi wajen tursasa wa jama'a.
Yakin Ukraine 'zai haifar da yunwar da ba a taba ganin irin ta ba a duniya'
Asalin hoton, Getty Images
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa yakin da ake yi a Ukraine na barazanar haifar da yunwa da talauci da ba a taba ganin irin su ba a duniya.
Antonio Guterres ya ce tasirin yakin kan wadatar abinci da makamashi da kuma kuɗi, mai tsanani ne kuma mai ci gaba da ƙaruwa.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen fitar da rahoto na biyu na Majalisar Dinkin Duniya kan tasirin rikicin.
Mista Guterres ya ce tilas ne a kawo ƙarshen mamayar Rasha, domin kawo ƙarshen abin da ya kira guguwa.
Ya kuma yi kira da a ɗauki matakin gaggawa a duniya domin ceto rayuka.
Rasha dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan ta kawo karshen killace tashoshin jiragen ruwan Ukraine. Yayin da Moscow ta musanta zarginta da ake na hana fitar da hatsi daga Ukraine.
WHO ta yi gargadi kan barkewar cutar ƙyandar biri a wuraren ba a saba samun ta ba
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar lafiya ta
duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar ƙyandar biri ta samu wurin zama
a ƙasashen da ba a saba samunta ba.
Amma shugaban
WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ana iya magance faruwar hakan.
Fiye da mutum
dubu aka bayar da rahoton sun kamu da cutar ba tare da ta yi kisa ba, a wasu ƙasashen da ba Afirka ba, tun ɓarkewar cutar a yanzu.
Dr Tedros ya ce
abin takaici ne ga duniyar da muke ciki cewar sai yanzu da ta kama ƙasashe masu
arziki ne aka damu da ita.
A Afirka, ƙyandar biri ta kashe mutane fiye da sittin a bana.
An yanke wa dan sanda hukuncin daurin rai da rai saboda kisan wani mutum
Wata kotu a kasar Thailand ta yanke hukuncin
daurin rai da rai ga wani dan sanda da ake kira Joe Ferrari da wasu mutum biyar
bisa laifin kashe wani da ake zargi da safarar ƙwayoyi bayan azabtar da shi.
Wani bidiyo da aka fitar ya nuna Jami’in ɗan sandan da wasu ƴan sanda suna azabtar da shi tare da neman ya ba
su dala dubu sittin.
Daga baya, hukumomi sun gano motoci na alfarma sama da arba'in a
gidan Joe Ferrari a Bangkok.
Lamarin ya
ƙara fito da zarge-zargen da ake yi wa ƴan sanda na ƙuntatawa da kuma
rashawa a Thailand, lamarin da ya ƙara bijiro da buƙatar yin gyara.
NNPP ta tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban Najeriya
Wakilai ko daliget na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, daga kananan hukumomi 774 na fadin Najeriya sun tabbatar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben 2023.
Jam'iyyar ta tsayar da tsohon gwamnan na Kano ne ba tare da hamayya ba a taron da ta gudanar ranar Laraba a Abuja, babban birnin kasar.
Yanzu ke nan, Kwankwaso zai fafata da Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC da sauran 'yan takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Sanata Kwankwaso ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya zai kyautata harkokin ilimi da tsaro da ilimi da kuma share wa talakawa hawayensu.
An zabi Malik Ado-Ibrahim a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar YPP
Asalin hoton, Twitter/@realMalikAdo
Dailget na jam'iyyar Young Progressives Party, YPP, sun zabi shugaban Reset Nigeria Initiative, Yarima Malik Ado-Ibrahim, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben 2023.
An gudanar da zaben fitar da gwanin ne ranar Laraba a Abuja, babban birnin kasar.
Ya yi nasara da kuri'a 66 yayin da abokiyar takararsa Mrs. Ruby Issac ta samu kuri'a hudu kacal.
Ban yi tsammani zan lashe zaben fitar da gwani na APC ba - Tinubu
Tsohon gwamnan Jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai yi tsammanin zai lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba.
Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi bayan ya yi nasara a zaben da kuri'a 1,271.
Mutanen da dama ne suka fafata a zaben fitar da gwanin, ciki har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya samu kuri'a 235.
Tinubu ya ce bai kullaci kowa a game da nasarar da ya yi ba.
Atiku ya taya Tinubu murnar lashe zaben fitar da gwani
Asalin hoton, ATIKUABUBAKAR
Ɗan takara a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya taya Bola Ahmed Tinubu, murnar nasara a zaɓen fitar da gwani na APC.
Atiku ya ce zaɓen ya kasance wanda aka fafata sosai, sai dai nasarar Tinubu na sake tabbatar da jajircewarsa.
Sannan ya kara da cewa ana iya boye abubuwa da dama, sai dai batun gazawar gwamnatin APC ba abin da zai ɓoyu ba ne.
Sannan Atiku ya ce, zaben 2023 zai kasance wani kuri'ar jin ra'ayi kan gazawar da gwamnatin APC ta nuna a mulkinta.
Buhari ya mika wa Tinubu tutar takara a APC
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika wa Bola Tinubu tutar takarar shugabancin kasar \a karkashin jam'iyyar APC.
Ya mika masa tutar ce bayan ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar inda ya samu kuri'u 1, 271.
Ganduje da Sanwo-Olu sun taya Tinubu murnar nasara
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da na Legas Babajide Sanwo-Olu sun taya Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe zaben fitar da gwani na APC.
Gwamnonin biyu sun ce nasarar Tinubu, alamun nasara ce a zaben 2023.
A cewarsu, Tinubu ne ya fi dacewa da mulkin Najeriya saboda kwarewarsa ta shekara da shekaru.
Sannan sun ya bi shugaba Buhari bisa rawar da ya taka wajen ganin an gudanar da taron da zaben cikin kwanciyar hankali.
Labarai da dumi-dumi, Bola Tinubu ya samu tikitin takara a APC bayan lashe zaɓen fitar da gwani
Jagoran jam'iyyar APC kuma ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaɓen fitar da gwani bayan kammala kidaya kuri'u.
Sama da kashi 50 cikin 100 na daliget da suka kada kuri'a sun zaɓi Tinubu.
Tinubu ya samu kuri'u 1,271. Yan takara 8 cikin 23 da suka janye sun nuna goyon-bayansu ga Tinubu.
Labarai da dumi-dumi, Tinubu ya lashe zaben fitar da gwani da kuri'u sama da dubu
NNPP na gudanar da babban taronta na kasa a Abuja
Sabuwar jam'iyyar adawa ta NNPP na gudanar da babban taronta na kasa a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Ana gudanar da taron ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke birnin Abuja.
A wannan taron ake sa ran daliget za su zabi mutumin da zai tsayawa jam'iyyar takarar shugaban kasa, duk da cewa ana ganin tabbatarwa kadai za a yi sakamakon Sanata Kwankwaso ne kadai ɗan takararta.
Ana sa ran daliget 774 ne za su hallara a wurin taron daga duka kananan hukumomin Najeriya.
Labarai da dumi-dumi, Ikeobasi Mokelu bai samu kuri'a ba
Labarai da dumi-dumi, Sanata Ben Ayade ya samu kuri'u 37
Labarai da dumi-dumi, Ahmed Lawan ya samu kuri'u 152
Labarai da dumi-dumi, Ogbonnaya Onu ya samu kuri'a 1
Labarai da dumi-dumi, Yahaya Bello ya samu kuri'u 47
Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya tafawa kansa bayan sanar da yawan sakamakon kuri'un da ya samu.
Labarai da dumi-dumi, Rochas Okorocha bai samu kuri'a ko guda ba