Masarautar Abu Dhabi
a Daular Larabawa ta yi wasu sabbin sauye-sauye ga dokokinta da za su ba waɗanda
ba musulmi ba damar yin aure da saki da kuma samun kulawar ƴaƴa.
A baya, aure da saki na ƙarƙashin
bisa dokokin shari’ar
Musulunci.
Sanarwar da shugaban Abu Dhabi, Sheikh Khalifa bin Zayed al-Nahayan ya
fitar, ta ce an ɗauki matakan ne da nufin janyo hankalin masu basira da hazaka daga
ƙasashen waje domin ci gaban masarautar.
Za a kafa wata sabuwar kotu da za ta gudanar
da harkokin iyali da waɗanda ba musulmi ba a Abu Dhabi, da za ta yi aiki a harshen
Ingilishi da Larabci.
Sheikh Khalifa
kuma shi ne shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - wacce a bara ta ɓullo da
wasu sauye-sauye na shari'a da suka haɗa da haramta saduwa kafin aure da shan
barasa.