Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Amma shafin sakamako kai-tsaye na nan.
Za mu kawo muku rahoton wanda ya lashe zaɓen a wani shafin daban - da zarar INEC ta sanar.
Sakamakon zaben gwamnan Anambra na 2021
Magoya bayan APGA sun fara murna
Ɗan takarar jam'iyya mai mulkin Anambra ta All Progressives Grand Alliance (APGA) ya nemi magaoya bayansa da kar su shiga bukukuwan murnar lashe zaɓen gwamnan jihar tukunna "saboda ba a gama fafatawa ba".
Ya zuwa yanzu hukumar zaɓe ta INEC ta sanar da sakamakon ƙaramar hukuma 19 cikin 21 kuma APGA ce ke kan gaba da nasarar lashe 17 daga cikinsu.
Yanzu haka Farfesa Charles Soludo na karɓar 'yan uwa da abokan arziki a gidansa da ke Isuofia na jihar, inda suke raye-raye da waƙe-waƙe.
Da yake jawabi ga magoya bayan, Mista Soludo ya gode musu bisa ruwan ƙuri'ar da suka yi masa sannan ya nemi su jira kafin su shiga murna.
Sai dai magoya bayan ba su ji kiran ba, inda tuni wuri ya ɓarke da sowar waƙe-waƙe da raye-raye.
An yi gasar Al Kur’ani ta ƴan ƙasa da shekara 13 a Ghana
An gudanar da gasar karatun Al Kur`ani ta ƙasa a Ghana a karon farko a Accra, tsakanin `ƴan kasa da shekara 13 daga yankuna uku na ƙasar da suka ƙunshi yankin Ashanti da kuma arewacin Ghana.
Yara biyar ne daga kowanne yanki suka samu nasarar zuwa zagayen ƙarshe na wannan gasa, inda suka fafata tsakaninsu a ɗakin taro na ƙungiyar malamai ta kasa.
Wakilin BBC na Ghana Fahd Adam ya halarci gasar kuma ya aiko da rahoto na musamman.
Bayanan sautiAn yi gasar Al Kur’ani ta ƴan ƙasa da shekara 13 a Ghana
INEC za ta yanke hukunci kan ƙaramar hukuma biyu
Ya zuwa yanzu, hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana sakamakon zaɓe na ƙaramar hukuma 19 daga cikin 21.
Ƙaramar hukumar Orumba ta Arewa da kuma Ihiala ne suka rage, sai dai akwai matsaloli game da yankunan.
Babban jam'in tattara sakamakon zaɓe na Orumba ta Arewa ya bayyana wa INEC cewa duk da an gudanar da zaɓe a yankin nasa, amma tilasta masa aka yi ya saka hannu kan takardar sakamakon zaɓen.
Ita kuwa Orumba ta Arewa, baturen zaɓe na ƙaramar hukumar ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen ba kwata-kwata.
Hukumar zaɓen ta ce za ta bayyana matsayinta game da ƙananan hukumomin idan aka dawo daga hutun da aka tafi na faɗar sakamakon da ake yi yanzu haka.
Ba a yi zaɓe a Ƙaramar Hukumar Ihiala ba
Shugaban hukumar zaɓe na Ƙaramar Hukumar Ihiala a Jihar Anambra ya sanar da cewa ba a gudanar da zaɓen ba a yankinsa.
Ihiala na da rumfunan zaɓe fiye da 300.
Sai dai INEC ba ta bayyana abin da zai faru ba game da rashin gudanar da zaɓen a yankin.
Anambra na da ƙaramar 21 kuma zuwa yanzu INEC ta sanar da sakamakon 19 daga cikinsu.
Jam'iyyar APGA mai mulkin jihar ce ke kan gaba, inda ta lashe 17 daga ciki. Sai kuma PDP da YPP da suka lashe ɗaya kowaccensu.
APGA ta yi nasara a Awka ta Arewa
Jam'iyyar APGA ta ci gaba da doke jam'iyyun hamayya, inda ta lashe Ƙaramar Hukumar Awka ta Arewa.
Sakamakon ya nuna:
APC – 755
APGA – 1,908
PDP – 840
YPP – 381
Jami'in tattara sakamako ya ce an tilasta masa wajen saka hannu
Babban jam'in tattara sakamakon zaɓe na ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa ya bayyana wa INEC cewa duk da an gudanar da zaɓe a yankin nasa, amma tilasta masa aka yi ya saka hannu kan takardar sakamakon zaɓen.
Jami'in ya yi zargin cewa wasu jami'an tsaro ne suka tsare shi har ma suka harba hayai mai sa hawaye a wurin.
Sakamakon zaɓe kai-tsaye
Kar ku manta, za ku iya samun sakamakon zaɓen Anambra kai-tsaye a nan:
Sakamakon zaben gwamnan Anambra na 2021
Labarai da dumi-dumi, APGA Nnewi ta Kudu
APGA ta sake lashe Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Kudu
Nnewi ta Kudu:
APC – 1,307
APGA – 3,243
PDP – 2,226
YPP – 1,327
Labarai da dumi-dumi, APGA ta lashe Ekwusigo
Ƙaramar Hukumar Ekwusigo ta shiga hannun jam'iyyar APGA.
Ita ce ta 12 da jam'iyyar mai mulki ta lashe.
Ƙaramar Hukumar Ekwusigo:
APC – 1,237
APGA – 2,570
PDP – 1,857
YPP – 727
Labarai da dumi-dumi, APGA ta sake lashe Aguata
Jam'iyya mai mulki a Anambra ta sake lashe Ƙaramar Hukumar Aguata.
Hakan na nufin APGA ta cinye ƙaramar hukuma 11 kenan cikin 13 da hukumar zaɓe ta INEC ta sanar.
Jam'iyyar PDP da YPP kowaccensu ta lashe ƙaramar hukuma ɗaya.
Ƙaramar Hukumar Aguata:
APC – 4,773
APGA – 9,136
PDP – 3,792
YPP – 1,070
Labarai da dumi-dumi, APGA ta lashe Onitsha ta Arewa
Jam'iyya mai mulki a Anambra ta sake lashe ƙaramar hukumar Onitsha ta Arewa.
Onitsha ta Arewa:
APC – 3,909
APGA – 5587
PDP – 3,781
YPP – 682
PDP ta lashe ƙaramar hukuma ta farko
Jam'iyyar adawa ta PDP a Jihar Anambra ta lashe Ƙaramar Hukumar Ogbaru wadda ita ce ta farko da ta yi nasara a zaɓen ranar Asabar.
Valentine Ozigbo na PDP ya samu ƙuri'a 3,445, yayin da Charles Soludo na jam'iyyar APGA mai mulkin jihar ke biye masa da 3,051.
Ga sakamakon:
APC – 1,178
APGA – 3,051
PDP – 3,445
YPP – 484
Cutar sankara na kama mutane miliyan biyar duk shekara
Cutar sankara na karuwa a duniya, inda sabbin mutane miliyan biyar ke kamuwa da cutar a duk shekara.
Kuma Najeriya na cikin ƙasashen da cutar ke ƙaruwa.
Ku saurari shirin Lafiya Zinariya na BBC.
Bayanan sautiLafiya Zinariya: Cutar sankara na kama mutane miliyan biyar duk shekara
Daular Larabawa ta ba waɗanda ba musulmi ba damar yin aure a ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sheikh Khalifa bin Zayed al-Nahayan
Masarautar Abu Dhabi
a Daular Larabawa ta yi wasu sabbin sauye-sauye ga dokokinta da za su ba waɗanda
ba musulmi ba damar yin aure da saki da kuma samun kulawar ƴaƴa.
A baya, aure da saki na ƙarƙashin
bisa dokokin shari’ar
Musulunci.
Sanarwar da shugaban Abu Dhabi, Sheikh Khalifa bin Zayed al-Nahayan ya
fitar, ta ce an ɗauki matakan ne da nufin janyo hankalin masu basira da hazaka daga
ƙasashen waje domin ci gaban masarautar.
Za a kafa wata sabuwar kotu da za ta gudanar
da harkokin iyali da waɗanda ba musulmi ba a Abu Dhabi, da za ta yi aiki a harshen
Ingilishi da Larabci.
Sheikh Khalifa
kuma shi ne shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - wacce a bara ta ɓullo da
wasu sauye-sauye na shari'a da suka haɗa da haramta saduwa kafin aure da shan
barasa.
APGA ta lashe ƙaramar hukumar Orumba ta kudu
APC – 2,060
APGA – 4,394
PDP – 1,672
YPP – 887
Yanzu ƙananan hukumomi 10 APGA ta lashe cikin 21 da aka sanar kawo yanzu yayin da YPP ta lashe ɗaya.
Ifeanyi Ubah na YPP ya lashe zaɓe a Nnewi ta arewa
APC – 1,278
APGA – 3,369
PDP – 1,511
YPP – 6,485
Zuwa yanzu ƙananan hukumomi 10 Inec ta sanar kuma APGA ce kan gaba inda ta
lashe ƙananan hukumomi tara a zaɓen gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar
Asabar.
APGA ta lashe ƙaramar hukumar Njikoka a Anambra
APC – 3,216
APGA – 8,803
PDP – 3,409
YPP – 924
Yanzu ƙananan hukumomi tara APGA ta lashe cikin
21 da aka sanar kawo yanzu.
APGA ta lashe ƙaramar hukumar Onitsha ta kudu
Sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Onitsha ta kudu
APC – 2,050
APGA – 4,281
PDP – 2,253
YPP – 271
Yanzu ƙananan hukumomi takwas APGA ta lashe
cikin 21 da aka sanar kawo yanzu.
APGA ta lashe ƙaramar hukumar Idemili ta kudu
APC – 1,039
APGA – 2,312
PDP – 2,016
YPP – 752
APGA ta sha gaban PDP ne da tazarar ƙuri’a
kusan 300 a Idemili ta kudu.
Yanzu ƙananan hukumomi bakwai APGA ta lashe
cikin 21 da aka sanar kawo yanzu.