Ɗaruruwan mutanen 'Yar Nasarawar-Akubu na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, suna can suna zaman gudun hijira a maƙwabtan garuruwa, cikin mawuyacin hali.
Sun fuskanci jerin hare-hare uku da 'yan fashin daji suka kai musu tun daga ranar Talata har zuwa jiya Alhamis.
Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC cewa a halin yanzu babu kowa a garinsu kuma shi ma yanba magana ne daga mafakarsa.
"Mutane ne ke taimaka mana da abinci tunda a halin yanzu a gidan wasu muke a zaune. Da mu da matanmu da ƴaƴanmu.A takure muke, wasu daga cikinmu ma a shago aka ɗan raɓa mu muke kwana," a cewarsa.
Ya ce ranar Talata bayan sun idar da sallar la'asar ne ƴan bindigar suka shiga garinsu a kan babura kusan 40 suna harba bindigogi.
"A haka suka kashe mutum 12 sannan waɗanda suka tsere ma suka bi su daji suka rika harbinsu.
Ya ce bayan sun gama kashe mutane kuma sun ɗibi amfanin gona suka tafi da su.
"Sai maghariba suka bar garin amma wanshekare da safiyar laraba sun sake dawowa a lokacin da muke kokarin yin jana'izar mutanen da suka kashe a daren Talata," kamar yadda ya shaida mana.
Ya ce a nan ma sai tserewa mutane suka yi aka bar gawarwakin da ake shirin yi wa sutura. Ya ce maharan ba su kashe kowa ba ranar laraba amma sun kwahsi kayan abinci kuma sun ɓalla shaguna sun yi sata.
Ya ce jami'an tsaro sun isa garin ne da la'asar suka ba mutanen gari kariya har suka yi wa ƴan uwansu jana'iza.
Mutumin ya ce jami'an tsaron ba su tsaya sun ba mutanen garin kariya ba don ana gama jana'izar suka tafi kuma maharan sun sake dawowa ranar Alhamis da safe inda suka tarar da ƴan tsirarun mutane da suka je tattara sauran amfanin gonarsu.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ƴan bindiga masu satar mutane da ɓarayin daji.