Kwana uku a jere ƴan fashi na kai hari ƙauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara
Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da suaran ƙasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail
Na fi damuwa da shiga 'yan huɗun farko fiye da cin Arsenal - Mourinho
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce ya fi damuwa da ƙare kakar wasa ta bana a cikin 'yan huɗun farko fiye da samun nasara kan Arsenal a wasan da za su fafata ranar Lahadi mai zuwa.
Ƙungiyar ta Mourinho ta bai wa Arsenal tazarar maki bakwai a mataki na 7. Tottenham ta kammala gasar Premier League sau huɗu a jere a saman Arsenal, abokan hamayyarsu na birnin Landan.
"Sama nake kallo, ba na kallon ƙasa. Da a ce Arsenal ne ke samanmu da maki bakwai da sai na kalle su," in ji Mourinho.
"Amma saboda mun ba su tazarar maki bakwai, ba na kallon ƙasa."
Tottenham na ƙasan Chelsea da tazarar maki biyar, wadda ke mataki na huɗu kuma na ƙarshe a cikin waɗanda za su je gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Ministan mai a Najeriya ya nemi afuwa kan ƙarin kuɗin fetur
Asalin hoton, @HETimipreSylva
Ƙaramin ministan man fetur na Najeriya ya nemi afuwar 'yan ƙasar kan "wahalhalun da suka shiga" bayan ɓullar labarin ƙarin kuɗin man a safiyar yau Juma'a, wanda ya bayyana da "abin baƙin ciki".
Da sanyin safiyar Juma'a ne hukumar kula da farashin fetur (PPRA) ta mayar da litar man zuwa naira 212 daga 163, amma daga baya ta ce yadda ake cinikin man a kasuwa kawai ta bayyana ba ƙari a kan yadda talakawa ke saya ba.
Timipre Sylva ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa daga shi har Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban ministan man fetur, babu wanda ya amince da ƙarin zuwa naira 212 kan kowace lita.
Ya ƙara da cewa duk da bai san daga inda aka samu labarin ba, "ina so na tabbatar muku cewa ƙarya ce zallanta".
Lamarin ya jawo ɓacin rai daga 'yan Najeriya, inda suka riƙa sukar gwamnatin Shugaba Buhari, wadda ta haƙiƙance cewa ba za ta ƙara kuɗin man ba a cikin watan Maris.
PPRA ta goge bayanan farko da ta wallafa a shafinta na intanet game da ƙarin kuɗin man.
Labarai cikin minti ɗaya
Bayanan sautiMinti Ɗaya da BBC na Yamma 12/03/2021
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina arewacin
Najeriya ta kama mutum 18 da ake zargi da aikata laifukan fyade da shiga
kungiyar asiri da fataucin mutane da kuma sace-sace a jihar. Daga cikin mutanen har da wani dan shekara 70 da ake zargi da yi
wa ‘yar shekara 14 fyade
Mayaƙan da ke fafutikar ɓallewa daga
ƙasar Kamaru sun yi garkuwa da ɗaruruwan mutane tun daga shekarar 2017, a cewar
ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch (HRW). Cikin wani rahoto da
ta fitar, HRW ta ce daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗalibai da masu kuɗi da
'yan siyasa da ma'aikatan agaji
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi ya kori babban hafsan sojin
kasa da na sama tare da maye gurbinsu da wasu a daidai lokacin da ake fuskantar
hare-haren masu ikirarin jihadi a yankunan arewacin kasar
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce babu dalilin daina amfani
da rigakafin annobar korona na AstraZeneca. Sanarwar WHO na zuwa
ne jim kadan bayan Bulgaria da Thailand sun bi sahun kasashen arewacin Turai
guda uku da suka dakatar da karbar allurar
Gwamnonin Najeriya na goyon bayan ‘yancin majalisun jihohi - Gwamna Tambuwal
Asalin hoton, @AWTambuwal
Gwamnan
jihar Sokoto a arewacin Najeriya, Aminu Tambuwal, ya bayyana tabbacin cewa gwamnonin ƙasar na goyon bayan samun ‘yancin kai ta fuskar sarrafa kudade ga ‘yan
majalisar jihohi da ɓangaren shari’a.
Tambuwal ya bayyana haka ne yayin ganawar da ya jagoranta tsakanin shugaban kungiyar ‘yan majalisar jihohin kasar 36 da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari.
Yayin da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, Tambuwal ya ce an yi ganawar ce tare da sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Gwamnan Plateau Simon Lalong, wanda tsohon kakakin majalisar
dokokin jihar ne, da kuma na jihar Zamfara Bello Matawalle.
Aminu tambuwal ya
bayyana cewa gwamnonin za su gana a cikin mako mai zuwa don karkare hanyoyin da
za a bi wajen aiwatar da batun ‘yancin cin gashin kai ta fuskar sarrafa kudade.
'Yan tawayen Kamaru suna 'garkuwa da mutane don kuɗin fansa'
Asalin hoton, Getty Images
Mayaƙan da ke fafutikar ɓallewa daga ƙasar Kamaru sun yi garkuwa da ɗaruruwan mutane tun daga shekarar 2017, a cewar ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch (HRW).
Cikin wani rahoto da ta fitar, HRW ta ce daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗalibai da masu kuɗi da 'yan siyasa da ma'aikatan agaji.
Kusan a kodayaushe 'yan bindigar kan nemi kuɗin fansa kafin su saki waɗanda suka kama.
Rahoton na HRW ya bayar da misalin wani likita da aka yi garkuwa da shi ranar 27 ga watan Fabarairu, amma aka sake shi bayan an biya dala 544.
Kazalika, an san masu fafutikar da kashe waɗanda suka kama bisa zarginsu da haɗa baki da sojojin Kamaru, a cewar HRW.
Ta bayar da misalin wasu sarakunan gargajiya da 'yan bindigar suka kashe a garin Essoh Attah da ke kudu maso yammacin ƙasar ranar 13 ga Fabarairu saboda sun ƙi su bayar da ribar da suka samu daga noman gahawa da suka yi da kuma shiga zaɓukan ƙananan hukumomi da aka yi a watan Disamba.
Ƙungiyar ta ce su ma sojojin Kamaru sun aikata laifukan cin zarafi a kan 'yan tawayen.
An kori shugabanni sojoji daga aiki a Mozambique
Asalin hoton, AFP
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi ya kori babban hafsan sojin kasa da na sama a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar matsalolin tsaro a yankunan arewacin kasar.
Shugaban ya naɗa Manjo Janar Cristovao Chume a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa.
Wakilin BBC ya ce duk da cewa babu wani dalili a hukumance da shugaban ya bayar kan korarsu, akwai damuwar da ake nunawa ganin sojoji sun kasa dakile hare-haren mayakan jihadi a yankin Cabo Delgado.
BBC ta tattauna da mutane a garin Palma da suka tsere kwanan nan daga kauyuka kuma sun bayyana yadda aka rika kashe 'yan uwansu da kona gidajensu.
Sun ga yadda aka rika yi wa iyalai yankan rago da garkuwa da mutane.
Kungiyoyin agaji sun roki a kai wa dubban farar hula da yanzu haka suka makale a Palma agaji bayan mayaka sun datse hanyoyin da ke bayar da damar shiga garin.
'Yan sanda sun kama mutum 18 da laifukan fyaɗe da sata a Jihar Katsina
Asalin hoton, Getty Images
‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da aikata laifukan fyade da shiga kungiyar asiri da fataucin mutane da
kuma sace-sace a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
Yayin da ake bayyana wadanda ake
zargin a harabar hedikwatar ‘yan sandan a ranar Juma’a, kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya sanar da cewa an cafke su ne a
wurare daban-daban a faɗin jihar.
Huɗu daga cikin wadanda ake zargin an cafke
su dauke da takardun kudaden jabu na dalar Amurka da Sefa da kuma Naira da suka kai miliyoyi.
Akwai mutum hudu da ake zargi da
aikata laifukan fyaɗe da suka haɗa da wani mutum mai shekara 70, Danladi Habibu, da aka kama da yi wa wata ‘yar shekara 14 fyade da kuma yi mata ciki.
Sauran mutane
biyar da aka cafke daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma ne, waɗanda ake
zargi da kafa ƙungiyar asiri da ake yi wa lakabi da ‘’Black X and Aye’’.
WHO ta ce babu dalilin daina amfani da rigakafin AstraZeneca
Asalin hoton, Reuters
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce babu dalilin daina amfani da rigakafin annobar korona na AstraZeneca.
Sanarwar WHO na zuwa ne jim kadan bayan Bulgaria da Thailand sun bi sahun kasashen arewacin Turai guda uku da suka dakatar da karbar allurar.
Wannan matakin nasu ya biyo bayan rahoton daskarewar jini da wasu mutane suka fuskanta bayan an yi musu allurar, kodayake babu cikakkun shaidu da ke tabbatar da alakarsu da rigakafin.
Ko a jiya Laraba, sai dai hukumar tabbatar da ingancin magunguna ta Tarayyar Turai ta nuna goyon bayanta ga rigakafin na AstraZeneca, tana mai cewa ingancinsa ya fi tunanin haɗarin da ake da shi.
Gobara ta ƙone ofisoshi 11 a barikin sojoji na Kano
Asalin hoton, AFP
Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta kashe wata wuta da ta ƙone ofisoshi guda 11 a sansanin sojoji na Bukavo da ke jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a yau Juma'a, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.
Yusuf ya ce wutar wadda ta tashi da misalin ƙarfe 9:10 na dare, ta lalata wurin ajiyar kayayyaki guda huɗu da kuma banɗaki a ginin.
"Muna samun labari, nan take muka tura tawagarmu zuwa wurin da ƙarfe 9:19," in ji shi.
Ya ƙara da cewa an kashe wutar kuma ba a samu asarar rai ba. Ana kan bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, a cewarsa.
Bidiyon kwalejin da ƴan bindiga suka sace ɗalibai a Kaduna
Bayanan bidiyo, An kubutar da wasu daga daliban Kaduna da aka sace
Kwamishinan tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce kawo yanzu ba'a san inda dalibai 30 suke ba amma sojojin Najeriya sun ceto mutum 180 da akasari ɗaliban kwalejin ne.
"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.
'Yan bindigar su da yawa sun kai hari a makarantar ne da misalin karfe sha daya da rabi na daren Alhamis, inda suka sace dalibai da dama har da malamai.
Labaran BBC cikin Minti Ɗaya
Bayanan sautiMinti Ɗaya Da BBC Na Rana 12/03/2021
Kwana uku a jere ƴan fashin daji na kai hari ƙauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara
Asalin hoton, Zamfara Government
Ɗaruruwan mutanen 'Yar Nasarawar-Akubu na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, suna can suna zaman gudun hijira a maƙwabtan garuruwa, cikin mawuyacin hali.
Sun fuskanci jerin hare-hare uku da 'yan fashin daji suka kai musu tun daga ranar Talata har zuwa jiya Alhamis.
Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC cewa a halin yanzu babu kowa a garinsu kuma shi ma yanba magana ne daga mafakarsa.
"Mutane ne ke taimaka mana da abinci tunda a halin yanzu a gidan wasu muke a zaune. Da mu da matanmu da ƴaƴanmu.A takure muke, wasu daga cikinmu ma a shago aka ɗan raɓa mu muke kwana," a cewarsa.
Ya ce ranar Talata bayan sun idar da sallar la'asar ne ƴan bindigar suka shiga garinsu a kan babura kusan 40 suna harba bindigogi.
"A haka suka kashe mutum 12 sannan waɗanda suka tsere ma suka bi su daji suka rika harbinsu.
Ya ce bayan sun gama kashe mutane kuma sun ɗibi amfanin gona suka tafi da su.
"Sai maghariba suka bar garin amma wanshekare da safiyar laraba sun sake dawowa a lokacin da muke kokarin yin jana'izar mutanen da suka kashe a daren Talata," kamar yadda ya shaida mana.
Ya ce a nan ma sai tserewa mutane suka yi aka bar gawarwakin da ake shirin yi wa sutura. Ya ce maharan ba su kashe kowa ba ranar laraba amma sun kwahsi kayan abinci kuma sun ɓalla shaguna sun yi sata.
Ya ce jami'an tsaro sun isa garin ne da la'asar suka ba mutanen gari kariya har suka yi wa ƴan uwansu jana'iza.
Mutumin ya ce jami'an tsaron ba su tsaya sun ba mutanen garin kariya ba don ana gama jana'izar suka tafi kuma maharan sun sake dawowa ranar Alhamis da safe inda suka tarar da ƴan tsirarun mutane da suka je tattara sauran amfanin gonarsu.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ƴan bindiga masu satar mutane da ɓarayin daji.
Sarkin ƙabilar Zulu na Afrika ta Kudu ya rasu
Asalin hoton, Reuters
Shugabannin siyasa a Afrika ta Kudu suna ci gaba da ta'aziyyar mutuwar Goodwill Zwelithini, Sarkin Ƙabilar Zulu wanda ya mutu yana mai shekaru 72.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce za a rika tuna sarki a matsayin mai hangen nesa kuma wanda ya ba da gagarumar gudunmuwa ga al'ada da ci gaban tattalin arzikin yankin KwaZulu-Natal.
Shugaban jam'iyyar Africa National Congress, Gwede Mantashe ya bayyana cewa ya taka rawa wajen ganin Afrika ta Kudu ta yi watsi da wariyar launin fata da wariyar jinsi.
Sarki Goodwill Zwelithini ya yi mulkin al'ummar Zulu tsawon shekaru hamsin, inda ya zama mai karfin faɗa a ji.
Ya mutu ya bar mata shidda da ƴaƴa 28.
Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗauri kan Joshua Dariye
Asalin hoton, EFCC
Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekarar 10 kan tsohon gwamnan jihar Filato Senata Joshua Dariye, bisa laifin cin amana da kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta yanke masa.
Sai dai kotun ƙolin ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar na laifin almundahana da kuɗi inda aka yanke wa Dariye hukuncin ɗaurin shekara biyu.
A lokacin da suke karanta hukuncin, alkalan kotun ce hukuncin da aka yanke waDariye tun farko dai-dai ne saboda laifin da ya aikata ya saɓawa ɓangare na 3115 na dokokin Penal Code.
A shekarar 2014 ne kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wa Dariye hukuncin ɗaurin shekara 14 amma aka rage zuwa shekara 10.
NAFDAC na gwajin magungunan gargajiya kan cutar korona
Hukumar NAFDAC mai sa ido kan ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta ce ana nan ana gwajin magungunan gargajiya 14 a ƙasar da a kan cutar korona.
Shugaban hukumar Farfesa Adeyeye ta ce magungunan sun wuce matakin farko na gwaji kawo yanzu kuma ana duba yiwuwar amfani da su kan cutar korona.
Ta ce "a yanzu mun amince da waɗannan magunguna 14, mun tabbatar ba sa yi wa jikin ɗan Adam illa amma ba mu san yadda za su yi aiki kan kwayar cutar korona ba shi ya sa za mu shi gaba da bincike a kan su," a cewarta.
Ta kuma ce gwamnati ta samar da wani shiri na bincike inda ta ce tana da yakinin za a samu daga cikin magungunan waɗanda za su iya kashe ƙwayar cutar korona.
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Burkina Faso na tattaunawar sulhu da ƴan bindiga
Gwamnatin Burkina Faso na wata ganawar sirri tsawon watanni da ƙungiyar al-Qaeda a yankin Sahel, Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM).
Firaiminista Christophe Dabire ya bayyana cewa gwamnati a shirye ta ke ta tattauna da masu ikirarin jihadi.
Wata kafar yada labarai a kasar, Omega Rdaio ta ce Burkina Faso ta saki sama da ƴan ta'adda 21 a shekarar 2020, cikin sulhu da aka yi da ƙungiyar ta JNIM,
NNPC ya ce ba za a yi ƙarin farashin mai a wannan watan na Maris ba
Kamfanin Mai na ƙasa NNPC ya dage kan cewa ba za a yi ƙarin farashin man fetur a wannan watan na Maris ba duk da sanarwar da Hukumar PPPRA mai sa ido kan farashin mai a kasar ta fitar da ke cewa litar mai zai kai Naira 212.
NNPC ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Da safiyar Juma'a ne Hukumar PPPRA ta fitar da sanarwar da ke cewa farashin mai na iya kai wa Naira 209.61 zuwa Naira 212.6.
Amma kawo yanzu sun goge sanarwar daga shafinsu na intanet.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Miliyoyin mutane na cikin haɗarin mutuwa dalilin yunwa
Asalin hoton, AFP
Miliyoyin mutane, ciki har da yan wasu kasashen Afrika na cikin haɗarin mutuwa dalilin yunwar da rikici ya haifar a cewa Majalisar Dinkin Duniya.
Sakatare-Janar na Majalisar Antonio Guterres ya ce annobar cutar korona da sauyin yanayi sun kara taɓarɓara lamarin.
Sama da mutum miliyan 30 a yankunan Sahel da Arewacin Afrika da Sudan ta Kudu da Yemen da Afghanistan sun daf da faɗawa matsananciyar yunwa.
"Idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, miliyoyin mutane za su auka yunwa da ma mutuwa," in ji Mista Guterres.
A Sudan ta Kudu, Mista Guterres ya ce kashi 60 cikin 100 na mutanenta na cikin ƙaruwar yunwa.
Haka kuma Mista Guterres ya nuna matukar damuwa kan rikicin Tigray na Ethiopia.
A halin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya na neman agajin dala biliyan 5.5 don taimakawa kasashen da yunwa ta fi shafa, in ji Mista Guterres.
Ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai a jihar Kaduna
Ƴan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.
Har yanzu ba a san adadin daliban da aka sace ba sai dai BBC ta tuntuvbi kwamishinan harkokin tsaro na jihar Samuel Aruwan wanda ya ce yanzu haka yana cikin makarantar kuma suna bincike kan lamarin.
Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.
'Gwamnatin Najeriya ba za ta yi sulhu da ƴan fashin daji ba'
Mashawarcin shugaban Najeriya kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar ta danganta tsaikon da ake samu wajen shawo kan taɓarɓarewar tsarokan rashin isowar wasu kayan yaƙi, duk da maƙudan kuɗaɗen da ta ce an fitar don sayo su.
Gwamnati ta ce ba za ta sulhunta da 'yan fashin daji ba, saboda ba mutane ba ne masu amana da alƙawari, don haka ƙarfin soja ne kawai maganinsu.
Ya bayyana wannan da ma wasu batutuwa hirarsa da AbdusSalam Ibrahim Ahmed.
Bayanan sautiMuryar Babagana Monguno kan matsalar tsaro a Najeriya