Wata yarinya 'yar shekara 10, Suliya Abubakar, ta ce ta jefa ɗan uwanta mai wata 20 da haihuwa cikin rijiya saboda mahaifiyar yaron kuma mariƙiyarta tana ƙuntata mata.
Yarinyar ta bayyana haka ne a jiya Juma'a yayin da Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Ondo, Salami Bolaji, ke gabatar da ita tare da wasu mutum 34 da ake zargi da aikata laifuka, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.
Suliya ta ce ta cilla Usman rijiyar ne ba don ta kashe shi ba, ta yi hakan ne kawai saboda ɓacin rai na ƙuntatawar da matar ubanta ke yi mata.
"Mahaifiyata ta rabu da mahaifina bayan ta haifi yara tara da kuma biyu da suka mutu, saboda haka yanzu mahaifiyar Usman ce a gidan kuma ita ce take yi mana girki," in ji Suliya.
"Sun fi son Usman sama da ni. Duk lokacin da ya yi fitsari ko bayan gida a kan abincina sai mahaifiyarsa ta ce sai na cinye a haka babu abin da zai faru da ni.
"Sai mahaifiyar Usman ta cire daidai wajen da ya yi fitsarin kuma ta ce na cinye, idan ban ci ba sai ta dake ni.
"Wata rana da dare, Usman ya ɓata jikinsa bayan gida, sai aka ce na wanke masa. Shi kuma sai ya biyo, ni kuma na cilla shi a rijiyar.
"Na faɗa wa mahaifiyarsa cewa wani ne ya zo ya ɗauke Usman. Sai ta ce idan muka je wurin 'yan sanda na ce mahaifiyata ce ta yi garkuwa da shi.
"Shi ma mahaifinmu da na faɗa masa sai ya ce eh na faɗa wa 'yan sanda hakan babu abin da zai faru da ni. Ni kuma gaskiya ba zan iya yi wa mahaifiyata sharri ba.
"Ni ce na jefa Usman a rijiya amma ban san zai mutu ba."
Kwamishinan ya ce yarinyar ta aikata laifin ne ranar 15 ga watan Disamba a Owode da ke Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke jihar ta Ondo.
An gabatar da mutanen ne ga manema labarai bisa zargin laifukan da suka haɗa da fashi da makami da kisa da sata da zamba da kuma mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba.