Ana neman wanda ya kashe matarsa jim kaɗan bayan haifa masa ƴa mace
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Imam Saleh
Rufewa,
Masu bibiyarmu a wannan shafi a nan za mu dasa aya, wajen kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a sassa daban daban na duniya.
Don haka da fatan za ku kasance da mu a gobe Lahadi in Allah ya kaimu, inda za mu sake dawowa domin ɗorawa daga inda muka tsaya.
Nine Imam Saleh
Saduwar alheri.
An yi wa Firai ministan Isra'ila rigakafin cutar korona
Asalin hoton, Getty Images
Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya karɓi allurar rigakafin korona kai tsaye ana nuna shi ta talabijin, abin da yasa ya zama mutum na farko a Isra’ila da ya yi hakan, yayin da aka fara aikin riga-kafi a ƙasar.
Ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta ce a yanzu haka tana da dubunnan allurai na rigakafin waɗanda kamfanin Pfizer ya samar, tare da wasu miliyoyin da za su iso nan ba da jimawa ba.
Babban darakta-janar na ma'aikatar lafiya ta ƙasar ya yi gargaɗin cewa ana buƙatar sabbin dokoki don daƙile yaɗuwar cutar, don haka shiga dokar kulle karo na uku abu ne mai yiwuwa.
Isra'ila na da sama da mutane dubu ɗari uku da saba'in da da suka kamu, da kuma wasu mutum dubu uku da suka mutu sanadiyyar cutar
Kotu ta saki Musulmin da ake zargi da sauyawa Ba'indiya Addini
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a jihar Uttar Pradesh, a arewacin Indiya, ta bada umarnin gaggauta sakin wani Musulmi da ɗan’uwansa bayan ƴan sanda sun ce ba su samu wata hujja ba, da ke nuna cewa mutanen biyu sun tilastawa wata mace da ke bin addinin Hindu shiga musulunci bayan ya aure ta.
Ana zargin Rashid ya auri Pinky a watan Yuli domin ya sauya mata addini, sai dai makwanni biyu bayan ya nemi yin rajistar auren a kusa da garin Moradaba, sai mahukunta suka kama shi tare da ɗan'uwansa.
Ita dai Pincky ta ce ta ji ta kuma amince da wanda take so, bilhasalima da akwai so da ƙauna cikin lamarin.
A wasu jihohi da addinin Hindu ya yi mamaya a Indiya dai dole ne a sanar da mahukunta kowanne aure da aka shirya ɗaurawa tun kafin a yi, abinda masu ƙara ke zargin cewa ba a yi ba.
Messi ya kafa sabon tarihi
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi ya yi kan-kan-kan da Pele, wajen yawan ƙwallayen da kowannensuu ya jefawa ƙungiya daya tilo.
Ƙwallayen da Messi ya ciwa Barcelona sun kai ɗari shida da arba'in da uku a yanzu, kuma ya samu nasarar kaiwa wannan mataki ne bayan ya ci ƙwallo a wasan yau da Valencia.
Messi ya ya fara taka leda a Barcelona ne tun shekarar 2004,
Yayin da shi kuma fitaccen dan wasan Brazil Pele ya ci irin waɗannan ƙwallaye a shekaru goma sha tara tare da Santos
Ana neman mutumin da ya kashe matarsa jim kaɗan bayan haifa masa ƴa mace
Asalin hoton, Getty Images
Masu rajin kare hakkin mata a Afghanistan sun yi caa !, bayan da wani mutum ya bayyana cewa ya kashe matarsa saboda ta haifi ƴa mace.
Ƴan sanda a Kabul babban birnin kasar na neman Fraidoon, wanda ya aikata kisan jim kaɗan bayan haihuwar jaririyar.
Wasu rahotanni sun ce ya gudu tare da jaririyar da aka haifa.
Daga watanni 10 zuwa yanzu, hukumar Kare Haƙƙin Ɗan-Adam ta Afghanistan ta karɓi korafe ƙorafi ɗari biyu da goma sha biyu na cin zarafin mata, gami da na kisan kai ɗari da sittin da biyar.
Ba ta sauya zani ba: Ƴan Sudan na gudanar da sabuwar zanga-zanga
Asalin hoton, AFP
Shekaru biyu bayan fara juyin juya halin da ya hamɓarar da tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir, yanzu haka ana gudanar da zanga-zanga a duk fadin ƙasar inda mutane ke nuna adawa da rashin ganin wani canji a rayuwarsu ta yau da kullum.
Masu zanga-zangar sun riƙa kona tayoyi a wani yanki da ke gefen kudancin Khartoum kafin su nufi fadar shugaban ƙasar, suna kiran a yi musu adalci.
Wasunsu na ɗauke da hotunan waɗanda suka mutu yayin zanga-zangar bara.
Masu zanga-zangar na nuna takaicin abin da suka kira ''tafiyar hawainiya da ake samu a karkashin gwamnatin rikon kwarya'' musamman kan abinda ya shafi tattalin arziki, inda ake samun hauhawar farashin kayan masarufi
Ana zargin tsohon shugaban ƙasa da ƙitsa juyin mulki
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Dakarun sojin Jamhuriyyar Afrika Ta Tsakiya
Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta zargi tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize da yunƙurin juyin mulki yayin da ƙungiyoyin ‘yan tawaye ke ƙwace manyan hanyoyin da suka dangana zuwa Bangui, babban birnin ƙasar.
Bayanin ya fito ne jim kaɗan bayan da manyan ƙungiyoyin ƴan tawayen ƙasar su uku suka ayyana cewa za su haɗa ƙarfi da ƙarfe don kawar da gwamnati a zaɓen da za a yi a cikin wannan watan.
Ƴan adawar sun ce za a tafka maguɗi a zaben.
An tura dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya don daƙile ƙoƙarin hana shiga birnin Bangui.
Ma’aikatan agaji sun ce fararen hula na tserewa daga garuruwa yayin da ƴan tawayen ke shiga daga arewa da kuma yammacin ƙasar.
Aƙalla sojojin gwamnati biyu aka kashe yayin wata arangama da yan tawaye.
Fashewa ta kashe masu jinyar korona guda tara a Turkiyya
Asalin hoton, Getty Images
Mutum tara sun rasa rayukansu bayan wata na'urar taimaka wa numfashi ta ventilator ta fashe a asibitin kula da masu cutar korona da ke kudancin Turkiyya.
Wata sanarwa daga ofishin gwamnan yankin ta ce fashewar ta haddasa gobara a sashen kulawar gaggawa na asibitin mai zaman kansa da ke Jami'ar Sanko a garin Gaziantep.
Ɗaya daga cikin marasa lafiyar ya mutu a lokacin da ake ƙoƙarin sauya masa asibiti.
Mutum kusan miliyan biyu ne suka kamu da cutar korona a Turkiyya, 17,610 cikinsu suka mutu, a cewar alƙaluman Jami'ar Johns Hopkins.
Babu wanda ya jikkata daga wutar, wadda ta tashi da asubahin yau Asabar, wadda kuma aka kashe ta nan take.
Waɗanda abin ya shafa 'yan shekara 56 ne zuwa 85, a cewar asibitin cikin wata sanarwa.
An fara bincike domin gano dalilin da ya haifar da fashewar.
Mutum 10 ne suka mutu a harin bam a Somalia
Adadin waɗanda suka mutu a harin bam ɗin garin Galkayo da ke Somalia ya kai mutum goma.
An tayar da bam ɗin ne da yammacin jiya Juma'a a filin wasan ƙwallon kafa na Galkayo a daidai lokacin da shugabanni ke taro.
Rahotanni sun ce wasu manyan jami'an sojin Somalia na cikin waɗanda suka mutu a harin.
Tuni Ƙungiyar Al Shabab da ke da mayaƙa a yankin ta ɗauki alhakin kai harin.
A ranar 8 ga watan Agusta, kungiyar ta kai irin wannan hari a sansanin sojin Somaliya da ke Mogadishu, inda ya kashe mutum 14.
Switzerland ta amince da fara amfani da riga-kafin korona na Pfizer/BioNTech
Asalin hoton, Getty Images
Switzerland ta amince a fara amfani da riga-kafin korona da kamfanonin Pfizer/BioNTech suka samar bayan wata biyu ana tantancewa, a cewar cibiyar Swissmedic mai kula da harkokin lafiya a yau Asabar.
"Bayan tantancewa cikin tsanaki, Swissmedic ta tabbatar cewa riga-kafin korona ta Pfizer/BioNTech ba shi da illa kuma amfaninsa ya rinjayi haɗarinsa," in ji cibiyar cikin wata sanarwa.
Shi ne riga-kafin korona na farko da ƙasar mai arziki ta amince a fara amfani da shi.
Daraktan cibiyar ta Swissmedic, Raimund Bruhin, ya ce "kare marasa lafiya shi ne abin lura musamman game da amince wa wani riga-kafi".
"Mun samu damar cimma matsaya ne cikin sauri sakamakon hanyoyon da muka bi da kuma natsattsen kwamitinmu tare da cika sharaɗi uku na lafiya da aiki yadda ya kamata da kuma inganci na riga-kafin."
Ƙasar mai al'umma ƙasa da miliyan tara, ta karɓi raiga-kafin guda miliyan 15.
Yadda iyayen ɗaliban makarantar Kankara suka haɗu da 'ya'yansu
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji daga wurin da iyayen suka haɗu da yaransu
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya duba yadda iyayen ɗaliban makarantar Kankara ta Katisna suka haɗu da 'ya'yansu bayan sun shafe kwana shida a daji a hannun masu garkuwa.
Iyayen yara na ci gaba da tururuwa zuwa sansanin alhazai da ke garin na Katsina domin yin ido da ido da ‘ya’yan nasu bayan sace su a makon jiya.
An yi garkuwa da mutum 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla matafiya 35 ne aka yi garkuwa da su jiya Juma'a a kan babbar hanyar Damaturu zuwa birnin Maiduguri.
Majiyoyin tsaro sun faɗa wa TheCable cewa 'yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka wa rukunin matafiyan a kusa da garin Kondiri da ke Jakana da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.
'Yan bindigar waɗanda suka bayyana cikin kakin sojoji, an ce sun saka shingen duba ababen hawa a kan babbar hanyar, inda suka yi awon gaba da fasinjojin a motoci ƙirar Hilux.
"Da farko fasinjojin sun hango hayaƙin taya amma sai suka zaci daji ake ƙonawa ba tare da sun fahimci cewa motar Dangote ba ce, wadda 'yan bindigar suka tare kuma suka cinna wa wuta," kamar yadda wata majiya ta shaida wa TheCable.
"Akasarin fasinjojin sun fantsama daji, an kama 35 daga cikinsu sannan an ƙona wasu motoci ƙanana biyu da kuma ta ɗaukar kaya. Motocin fasinja guda tara aka bari a kan titi, an wawashe dukkanin kayan da suka bari."
Wani babban jami'in ɗan sanda ya ce an ceto mutum 10 daga cikinsu, yayin da aka kai waɗanda suka ji rauni Asibitin Ƙwararru na Maiduguri domin duba su.
Labarai da dumi-dumi, Matashiya ta kashe mutum uku da bam a Jihar Borno
Wata matashiya ta kashe mutum uku tare da jikkata biyu bayan ta tarwatsa kanta a taron jama'a a garin Konduga da ke Jihar Bornon Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wasu majiyoyin agaji da 'yan sa-kai na cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar.
"Mun ɗebe gawar mutum uku da kuma mutum biyu da suka ji manyan raunuka daga wurin," a cewar wani ma'aikacin agaji.
Wadda ta kai harin ta tayar da abin fashewar da ke jikinta a tsakiyar wasu mutane da ke shaƙatawa a kusa da gidan mai unguwa, a cewar wani shugaban ƙungiyar 'yan sa-kai.
Garin Konduga na da nisan kilomita 38 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, sai dai ya yi kama da irin wanda Boko Haram ta sha kaiwa ta hanyar amfani da ƙananan yara yayin taron jama'a.
'Yan Rasha ne suka kai mana harin intanet - Mike Pompeo
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya zargi Rasha da abin da ya kira harin intanet mafi girma a kan Amurka.
"Muna faɗa ƙarara cewa 'yan Rasha ne suka aikata hakan," a cewar Mista Pompeo jiya Juma'a.
Bai yi wani ƙarin bayani ba game da alaƙanta zargin da gwamnatin Moscow, ita ma Rasha ta musanta hannunta a cikin harin.
Harin wanda aka kai wa kamfanin SolarWinds na Amurka, an gano shi ne a makon da ya gabata duk da cewa an shafe watanni ana aikatawa.
Daga cikin ma'aikatun Amurka da aka kai wa harin har da mai kula da makaman nukiuliyarta. Sai dai sashen makamashi ya ce harin bai shafi lafiyar makaman ba.
Maharan sun hari cibiyoyi da dama a faɗin duniya ciki har da Birtaniya ta hanyar amfani da layin intanet guda ɗaya.
Masu bincike sun ce za a shafe shekaru ba a iya sanin haƙiƙanin abin da ya faru ba bayan harin, wanda suka yi wa laƙabi da Sunburst.
An gano wani sabon nau'in cutar korona a Afirka ta Kudu
Ministan lafiya na Afrika ta Kudu, Zweli Mkhize, ya ce masana kimiyya sun gano wani nau'in cutar Korona da ke sa cutar na ƙara munana a karo na biyu.
Mista Mkhize ya ce nau'in ya fi haɗari ga matasa kuma suna baza cutar ba tare da ta nuna a jikinsu ba.
A cewar wakiliyar BBC, ''masana sun ce sabon nau'in ya fi wanda aka fuskanta a baya saurin bazuwa duk da cewa ba su iya gano wanda ya fi muni ba daga cikinsu".
Afrika ta Kudu ce Korona ta fi yi wa ɓarna a ɗaukacin nahiyar Afrika, inda aka samu kusan mutum miliyan ɗaya ɗauke da ita.
Za a ci gaba da gasar lig ta Najeriya NPFL ranar 27 ga Disamba
Asalin hoton, @LMCNPFL
Hukumomi a Najeriya sun ce za a ci gaba da wasannin ƙwallon ƙafa na lig wato Nigerian Professional Football League (NPFL) a ranar 27 ga watan Disamba.
Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare, shi ne ya bayyana hakan jiya Juma'a yayin da yake zantawa da manema labarai a filin wasa na Surulere, Legas.
Kamar kowane lig na ƙasashen duniya, an dakatar da wasannin NPFL ne saboda annobar cutar korona.
Sai dai yayin da harkokin ƙwallon suka dawo ganga-ganga a ƙsashen duniya ba tare da 'yan kallo ba, masoya wasannin ƙwallo a Najeriya sun ci gaba da zama ba tare da abar ƙaunar tasu ba.
"Wajibi ne mu san adadin ƙungiyoyin da suka shirya kuma suka cika ƙa'idoji domin farawa. Za mu fara da duk adadin ƙungiyoyin da suka shirya. 27 ga wata ya yi daidai kuma a ranar za a fara lig," in ji ministan.
"Daga cikin dalilan da suka sa ba a ci gaba da wasanni ba bayan annobar korona, daga wurinsu ne masu shirya gasar, mun yi ta jiransu. Za mu tattauna da NFF da kuma NPFL domin gano bakin zaren."
Tuni aka fitar da Kano Pillars da Plateau United daga gasar Zakarun Afirka ta Caf Confedrations Cup a zagayen farko, abin da wasu ke alaƙantawa da rashin buga wasanni a gasar lig ta Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Yar shekara 10 ta jefa ƙaninta a rijiya 'saboda matar ubanta na ƙuntata mata'
Asalin hoton, Deccan Herald
Wata yarinya 'yar shekara 10, Suliya Abubakar, ta ce ta jefa ɗan uwanta mai wata 20 da haihuwa cikin rijiya saboda mahaifiyar yaron kuma mariƙiyarta tana ƙuntata mata.
Yarinyar ta bayyana haka ne a jiya Juma'a yayin da Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Ondo, Salami Bolaji, ke gabatar da ita tare da wasu mutum 34 da ake zargi da aikata laifuka, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.
Suliya ta ce ta cilla Usman rijiyar ne ba don ta kashe shi ba, ta yi hakan ne kawai saboda ɓacin rai na ƙuntatawar da matar ubanta ke yi mata.
"Mahaifiyata ta rabu da mahaifina bayan ta haifi yara tara da kuma biyu da suka mutu, saboda haka yanzu mahaifiyar Usman ce a gidan kuma ita ce take yi mana girki," in ji Suliya.
"Sun fi son Usman sama da ni. Duk lokacin da ya yi fitsari ko bayan gida a kan abincina sai mahaifiyarsa ta ce sai na cinye a haka babu abin da zai faru da ni.
"Sai mahaifiyar Usman ta cire daidai wajen da ya yi fitsarin kuma ta ce na cinye, idan ban ci ba sai ta dake ni.
"Wata rana da dare, Usman ya ɓata jikinsa bayan gida, sai aka ce na wanke masa. Shi kuma sai ya biyo, ni kuma na cilla shi a rijiyar.
"Na faɗa wa mahaifiyarsa cewa wani ne ya zo ya ɗauke Usman. Sai ta ce idan muka je wurin 'yan sanda na ce mahaifiyata ce ta yi garkuwa da shi.
"Shi ma mahaifinmu da na faɗa masa sai ya ce eh na faɗa wa 'yan sanda hakan babu abin da zai faru da ni. Ni kuma gaskiya ba zan iya yi wa mahaifiyata sharri ba.
"Ni ce na jefa Usman a rijiya amma ban san zai mutu ba."
Kwamishinan ya ce yarinyar ta aikata laifin ne ranar 15 ga watan Disamba a Owode da ke Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke jihar ta Ondo.
An gabatar da mutanen ne ga manema labarai bisa zargin laifukan da suka haɗa da fashi da makami da kisa da sata da zamba da kuma mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba.
Amurka ta amince da riga-kafin korona na biyu
Asalin hoton, Moderna
Ana shirin fara yi wa Amurkawa riga-kafin cutar korona na biyu bayan da hukumomi suka aminta da ingancin rigakafin annobar Korona na kamfanin Moderna.
Ƙasar ta yi odar guda miliyan 200 kuma ana sa ran fara yi wa kusan mutun miliyan shida riga-kafin ranar Litinin.
Sai dai akwai yiwuwar riga-kafin Moderna ya fi shiga karkara, kasancewar ba ya buƙatar a saka shi cikin sanyin da ba ya yankewa kamar na Pfizer da BioNTech.
Kawo yanzu annobar Korona ta kashe sama da mutu 300,000 a Amurka, abin da ya sa ta zama ƙasa ta farko da annobar ta fi yi wa illa a duniya.
Haka nan kusan mutum miliyan 17 ne suka kamu da cutar a ƙasar.
Korona ta sake kashe mutum 11 a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Mutum 11 ne suka mutu a Najeriya sakamakon annobar cutar korona a ranar Juma'a, abin da ya kawo jumillar adadinsu zuwa 1,212.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta NCDC ce ta bayyana hakan, inda ta ce an samu ƙarin mutum 806 da suka kamu da cutar korona a Juma'ar.
Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa da mutun 287, yayin da Abuja ke bi mata da mutum 255.
Koronar ta kuma kama mutum 36 a Kaduna, sai Akwa Ibom mai 29, Katsina mutum 25, sai jihar Rivers da ita ma ke da 25.
Jihar Kwara na da mutun 21, sai Bauchi ke binta da mutun 19, sai kuma Kano mai 15.
Ondo na da 14, yayin da Plateau ke da 13, Yobe 12, Nasarawa 11, Ebonyi 9, Gombe 8, Abia 7, sai Delta da Imo masu 4-4.
Har wayau a ranar ta Juma'a jihar Osun na da mutun 3, sai jihohin Anambra da Borno masu 2-2.
Jihohin Cross River da Edo da Ekiti da Jigawa da kuma Ogun ne suka kammala jadawalin na ranar da mutun 1 kowannensu.
A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bularta zuwa yanzu sun kai 77, 013, yayin da 67,484 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,212.
Maraba
Umar Mikail ke muku barka da hantsin Asabar tare da fatan kun tashi lafiya.
Ku biyo ni domin samun labarai kai-tsaye a wannan shafi na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar sauran sassan duniya.