Kada Sallar Idi ta wuce awa ɗaya a Abuja – FCTA

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Jama'a nan muka kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.

    Umar Mikail ke gode muku da kasancewa tare da BBC a kodayaushe.

    Mu haɗe gobe idan Allah ya kai mu da lafiya.

  2. Italiya za ta tsawaita dokar ta-ɓacin yaƙi da korona

    Italiya

    Asalin hoton, EPA

    Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya nemi majalisar ƙasar da ta amince da tsawaita dokar ta-ɓaci har zuwa watan Oktoba a cigaba da yaƙi da cutar korona.

    Zagayen da ake ciki na dokar zai ƙare nan da ƙarshen watan nan.

    Idan aka tsawaita dokar, hakan na nufin dokokin da aka saka na rage yaɗuwar cutar za su ci gaba da zama daram, waɗanda suka bai wa jihohi da gwamnatin tarayya ƙarin ƙarfin iko.

    "Cutar na ci gaba da hayayyafa kuma har yanzu ba ta kai ƙarshe ba," in ji Mista Conte. "Abu ne maras dacewa a ce an ɗage irin waɗannan dokoki masu amfani."

  3. Kada Sallar Idi ta wuce awa ɗaya a Abuja – FCTA

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    An bai wa Musulmi mazauna birnin Abuja ƙarfe 8:00 zuwa 10:00 na safe a matsayin lokacin da za su gudanar da Sallar Idi, a cewar wata sanarwa da hukumar FCTA ƙarƙashin ministan birnin ta fitar.

    Sannan kuma kada sallar ta wuce tsawon sa'a ɗaya.

    Wannan umarni ɗaya ne daga cikin sharuɗan da hukumar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja (FCTA) ta bayar na gudanar da sallar a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar cutar korona.

    Kazalika ba za a gudanar da sallar a filin idin Abuja ba na National Eid Prayer Ground da ke kan Titin Umaru Musa Yar Adua.

    "An umarci mutane da su gudanar da sallolin a masallatan Juma'ar unguwanninsu," a cewar sanarwar.

    "Dukkanin bukukuwan Idi za a yi su a cikin gidaje sakamakon dokokin da aka saka na rufe wuraren shaƙatawa da wasanni da nisshaɗi suna nan daram."

    Kafa sharuɗɗan sun biyo bayan wani taro ne da Minista Muhammad Bello ya yi tare da majalisar malaman Abuja ta Abuja League of Imams Initiative ranar Litinin.

    Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya ta ce ranar Juma'a za a gudanar da Idin na Babbar Sallah sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis da Juma'ar a matsayin hutu a ƙasar baki ɗaya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Atiku ya taya Adesina murnar wanke shi daga zargin zamba a bankin AfDB

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya taya Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adesina murna biyo bayan wanke shi da aka yi daga zargin cin hanci.

    A ranar Litinin ne wani kwamiti mai zaman kansa ya wanke Adesina daga zargin cin hanci da ɓangaranci da ma fifita 'yan Najeriya wurin bayar da kwangiloli da ayyukan bankin.

    "Wanke Adesina daga zargin zamba da kwamiti mai zaman kansa ya yi ya tabbatar da cewa ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi," in ji Atiku, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    Adesina ya yi ministan ayyukan gona a Najeriya daga 2011 zuwa 2015 kafin ya lashe zaɓe na zama shugaban bankin na Africa Development Bank (AfDB).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Rahama Sadau ta yi tir da rikicin Kudancin Kaduna

    Fitaccciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta yi tir da rikicin da ke faruwa a Kudancin Kaduna.

    Tauraruwar, wacce haifaffiyar jihar Kaduna ce, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su tattabar da zaman lafiya a yankin na Kudancin Kaduna.

    "Ina kyamar kashe-kashen da ake yi a Kudancin Kaduna. Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su tabbatar da zaman lafiyar dukkan 'yan Najeriya," in ji ta a sakon da ta wallafa a Twitter ranar Talata.

    Bangarorin al`umma da ke kudancin jihar na ci gaba da ɗora wa juna alhakin rikicin da ya ƙi ya ƙi cinyewa a yankin, wanda kuma ke haddasa asarar rayuka da dukiyar jama`a.

    A halin da ake ciki, gwamnati ta kafa dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi biyu da nufin magance matsalar.

    Amma masana harkokin tsaro na ganin cewa aiwatar da shawarwarin da wasu kwamitocin bincike suka bayar a baya, ita ce sahihiyar hanyar dawwamar zaman lafiya a yankin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Mutum miliyan 45 na cikin haɗarin yunwa a Kudancin Afirka

    'Yan Afirka

    Asalin hoton, Getty Images

    Kusan mutum miliyan 45 ne a kasashen kudancin Afirka ke cikin hadarin fuskantar yunwa sakamakon fari da ambaliyar ruwa da kuma annobar korona.

    Kasashen da ke yankin dai sun kai 16, kuma cutar korona kusan ta shafi mai shi da maras shi, inda ta jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali.

    Dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya a kusan ko'ina a duniya ta taka rawa wajen jefa mutanen yankin cikin masifa saboda dukkan harkokin kasuwancinsu sun tsaya cak.

    An samu matsalar rashin aikin yi, kasuwanni sun tsaya, dole mutane suka daina sayar da kayayyakinsu.

    Mutane sun koma sayar da kayan amfanin gidajensu suna sayan abinci.

    Yara na shan wuya, yayin da aka yi hasashen cewa yara miliyan takwas ne za su fuskanci matsalar rashin abinci mai gina jiki.

    An rufe makarantu, abin da ya sa miliyoyin yara ke zaune a gida babu abin yi kuma ba sa samun abincin da ake ba su a makarantun.

  7. Ƙarin mutum 119 sun mutu a Birtaniya saboda korona

    Birtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙarin wasu mutum 119 sun mutu a Birtaniya sakamakon cutar korona, abin da ya sa jumillar adadin ya zama 45,878.

    Sai dai Hukumar Lafiyar na duba yanayin yadda suke tattara yawan alƙaluman, waɗanda aka riƙa haɗawa da waɗanda suka kamu da cutar watanni kafin su rasu.

    Kazalika wasu 581 sun harbu da cutar cikin sa'a 24 da suka wuce - jumillar adadin ya zama 300,692.

  8. Buhari na shan suka saboda 'nuna wa mata wariya'

    Shugaba Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na shan suka tun bayan da ya sanya sunan mace guda a cikin jerin sunayen da ya sanya wa wasu tashoshin jiragen kasa.

    A ranar Litinin ne shugaban ya sanya wa tashoshin jiragen kasa 23 sunan wasu fitattun mutane da suka yi wani abin bajinta a kasa ko kuma suka bayar da wata gudunmuwa ga kasa.

    Daga cikin sunayen da ya sa har da sunayen tsoffin shugabannin kasar da ministoci da kuma mutumin da ya karbi kyautar Nobel Wole Soyinka.

    To sai dai kuma ya sanya sunan Funmilayo Ransome-Kuti, wata mai fafutuka kuma mahaifiyar mawakin nan marigayi Fela Kuti a cikin daya daga cikin jiragen kasan da ya sanya wa suna.

    Wasu mutane a shafukan sada zamunta sun danganta wannan radin suna da yadda shugaban ya yi a 2019, lokacin da ya nada ministoci 43, inda 7 ne kawai daga cikinsu mata.

    Ma'abota shafukan na sada zumunta sun ce akwai mata da dama da ya kamata a karrama a sanya sunansu a wasu tashohin jirgin kasan kamar, Stella Adadevoh, likitar da ta mutu a yayin da take kokari wajen kare yaduwar cutar Ebola.

    Sai kuma Dora Akunyili, wadda ta sha gwagwarmaya wajen hana shigo da jabun magunguna cikin kasar da ta mutu a 2014.

    Tsohon sanata a Najeriya, Shehu Sani, ya tambayi shugaban kasar da ya sanya sunan tashar jirgin kasa ta Kaduna sunan matukiyar jirgin yakin nan da ta rasu makonni biyu da suka wuce, Tolulope Arotile.

  9. Twitter ya dakatar da shafin babban dan Donald Trump

    Donald Trump Jr

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Twitter ya dakatar da shafin babban dan shugaban Amurka, Donald Trump Junior na tsawon awa 12.

    An dakatar da shafin ne bayan da Donald Trump Jr ya wallafa wani bidiyo kan mahimmancin maganin hydroxychloroquine.

    Da dama cikin har da shugaba Trump sun nuna cewa maganin na iya warkar da cutar korona duk da cewa kwararru sun ce ba haka lamarin yake ba.

    A cewar Twitter bidiyon na labaran karya ne.

    Twitter Donald Trump Jr

    Asalin hoton, Twitter

  10. Shugaban kasar Tanzania ya fashe da kuka

    An hango shugaban Tanzania John Magufuli yana share hawaye a yayin da yake jawabi kan mutumin da ya gada Benjamin Mkapa lokacin taron yi masa bankwana a babban filin wasan kasar.

    “Mr Mkapa ya rike min tamkar dansa, shi gwarzo ne a gare ni, ya nuna min kauna, wasu lokutan hawaye kan zuba, don haka kada ku yi mamaki,” in ji Mr Magufuli.

    Dubban mutane ne a babban birnin kasar, Dar es Salaam, suka taru a filin wasa domin nuna girmamawar bankwana ga tsohon shugaban kasar.

    Wakilai daga Burundi da kuma mawaka sun halarci taron.

    Sai dai rahotanni sun ce an juya da wakilan kasar Kenya bisa dalilan da ba a bayyana ba.

    Ranar Talata za a kai gawar Mr Mkapa mahaifarsa wato kauyen Lupaso, wanda ke kudancin Tanzania.

    Mr Mkapa, wanda ya shugabanci kasar tsakanin 1995 zuwa 2005, ya mutu yana da shekara 81 a wani asibiti da ke Dar es Salaam ranar Alhamis.

  11. Eid-el-Kabir: Za a yi hutun aiki a ranar Alhamis da Juma'a a Najeriya

    Babbar Sallah

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin tarrayar Najeriya ta tabbatar da ranar Alhamis 30 ga watan Yuli da kuma Juma’a 31 ga watan Yulin, 2020 a matsayin ranakun hutu domin shagulgular babbar Sallah a kasar.

    Babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gidan Najeriya, Georgina Ehuriah ce ta sanar da haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

    Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola a jawabinsa a madadin gwamnatin kasar, ya taya musulmi murnar zagayowar babbar sallah.

    “Ina kira ga musulmai su yi koyi da Annabi Muhammadu – SAW wajen kasancewa masu nuna kauna da jin kai a wannan lokacin,” in ji Aregbesola.

  12. Jam'iyya mai mulkin Uganda ta tsayar da Museveni takarar zaben 2021

    Museveni

    Asalin hoton, Reuters

    Jam'iyyar National Resistance Movement (NRM) mai mulki a kasar a Uganda ta tsayar da shugaba Yoweri Museveni a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 202.

    Amma dole sai hukumar zaben ta amince da takararsa a cikin watan Nuwamba.

    Idan har ya lashe zaben, Mr Museveni wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 34, zai kara shekaru biyar a mulki.

    Koda yake sauran jam'iyyu a hukumance ba su tsayar da 'yan takara ba, amma bisa dukkan alamu babban abokin hammayarsa shi ne mawaki kuma dan majalisar dokoki, Robert Kyagulanyi, wanda ake kira Bobi Wine, wanda matasa ke goyon bayansa.

  13. Minti Daya da BBC na Rana 28/07/2020

    Latsa hoton da ke kasa don sauraren labaran Minti Daya da BBC na Rana 28/07/2020.

    Bayanan sautiMinti Daya da BBC na Rana 28/07/2020
  14. Abba ya gurfanar da Ganduje a gaban kotu

    Ganduje da Abba

    Abba Kabir Yusuf, mutumin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kayar a zaben gwamna na shekarar 2019, ya gurfanar da Ganduje a gaban kuliya.

    Sai dai wannan karon ba batu ne na zargin yin magudin zabe ba.

    Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara gaban kotu yana mai kalubalantar matakin da Gwamna Ganduje ya dauka na mallaka wa wasu fitattun 'yan kasuwa, otal din Daula da kuma tashar motoci ta Shahuci da ke cikin birnin na Kano.

    Lauyan tsohon dan takarar gwamnan, Barista Bashir Yusuf, ya ce hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da yake magana kan hakkin mallakar ƙasa ko fili.

    Sai dai bangaren gwamnati ya ce har yanzu ba su da labarin shigar da karar.

    Abin da ya faru a kotu

    Kazalika lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce akwai batun bashi na gina layin dogo mai amfani da lantarki da gwamnatin ta shirya ciyowa daga kasar China wanda ya ce idan aka karbo za a jefa Kano a cikin mawuyacin hali na durkushewar tattalin arziki.

    Sai dai lauyan gwamna wanda kuma shi ne Kwamishina Shari'a na jihar Kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko kadan babu kanshi gaskiya a cikin labaran da ake yadawa game da bayar da filayen.

    Shahuci
    Bayanan hoto, Tashar mota da ke Shahuci na cikin wuraren da aka kai kara a kansu.

    Ya ce an bai wa wani kamfani tashar motar zamani ta Shahuci ne don yin shaguna na zamani da zai sayar da su ga 'yan kasuwa kamar yadda gwamnatin jihar ta yi a kasuwar Dangauro da ke titin Zaria a Kano.

    Ya kara da cewar layin dogon kuma tsohon aiki ne domin kuwa sai da gwamnati ta sami amincewar Gwamnatin Tarayya sannan ita kuma gwamnatin China ta bayar da bashin da ake magana a kai.

    Daula

    Barista Musa Lawan ya ce otal din Daula ma kwatankwacin hadin guiwa da gwamnatin Kano ta shiga da sauran kamfanoni ne amma ba ta mallakawa kowa shi ba.

    A cewarsa, hasalima tana duba yiwuwar yadda za a bai wa masu sha'awar zuba jari dama, sannan kasuwar zamani za a samar a wurin kamar dai yadda shi mai kamfanin ya nema.

  15. Fyade: Abin da ya sa 'yan sanda suka dakatar da bincike kan D'Banj

    Dbanj

    Asalin hoton, Getty Images

    ‘Yan sanda a Najeriya sun jingine bincike kan zargin yin fyade da ake yi wa shahararren mawakin kasar D’Banj.

    “Mun dakatar da binciken saboda babu hujja a kan wanda ake zargi", in ji kakakin ‘yan sanda Umar Sanda.

    Wata mata Seyitan Babatayo ta zargi D’Banj wanda asalin sunansa Oladapo Oyebanjo da yi mata fyade a cikin wani otal a shekara ta 2018 a Lagos.

    Ya musanta zargin.

    Sanarwar ta ‘yan sanda na zuwa ne kwana guda bayan da Misis Babatayo ta ce ba ta da niyyar ci gaba da neman hakkinta kan batun bayan ta tattauna da wakilan D’banj.

    A cewarta hakan shi ne ya fi fa'ida domin a zauna lafiya tsakaninta da mawakin da kuma iyalanta.

    A baya lauyoyin da ke kare kare Seyitan Babatayo, sun shigar da koke a wajen 'yan sanda cewa an kama ta ba bisa ka'ida ba.

  16. Jamus ta gargadi 'yan kasarta kan tafiya Sufaniya

    Sufaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta gargadi 'yan kasar game da yin balaguro zuwa yankuna uku na kasar Sufaniya.

    A cikin wata sanarwa, ta bayyana lardunan Aragon, Catalonia da kuma Navarra da cewa suna "cike da masu dauke da cutar korona kuma suna cikin yanayin kulle."

    An samu gagarumin karin masu kamuwa da cutar korona a lardunan.

    Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da cibiyar Robert Koch Institute (RKI) ta kasar Jamus ta ce rashin kulawa ne ya haddasa karuwar masu kamuwa da cutar korona a kasar.

    "Abubuwan da ke faruwa a Jamus sun daga min hankali," a cewar shugaban RKI Lothar Wieler.

    Adadin wadanda suka kamu da cutar korona a Jamus ya kusa ninkawa ranar Talata zuwa mutum 633, kuma cibiyar RKI ta dora alhakin hakan kan haduwar da mutane suke yi a wuraren aiki da wuraren shakatawa.

    Ta yi kira ga mutane su rika bin dokar nesa-nesa da juna

  17. An ƙi amincewa da tayin Man Utd kan Sancho, Coutinho zai yi nazari kan tafiya Arsenal

    Sancho

    Asalin hoton, Getty Images

    Borussia Dortmundta ki amincewa da tayin da Manchester Unitedta yi na sayen dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a kan £89m, a cewar mujallar wasanni ta Bild, wacce ta ambato jaridar Mail.

    Sai dai jaridar Telegraphta ce har yanzu United ba ta mika bukatar dauko Sancho ba, kuma duk da cewa Dortmund na so a ba ta £110m kan dan wasan, wato sama da darajar da kungiyar ta Premier League ta yi a kansa, an yi amanna za a cimma matsaya.(Telegraph - subscription required)

    Kocin Manchester United Ole Gunnar yana son dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish sai dai tuni aka gaya wa dan wasan na Ingila mai shekara 24 cewa da farko mai yiwuwa ba za a rika sanya shi a wasa duk mako ba idan ya tafi Old Trafford.(Independent).

    Latsa nan don karanta cikakken labain wasannin:

  18. Kun san nisan da ke tsakanin duniyarmu da duniyar Mars?

    Wannan bidiyon yana bayani kan yadda ake sauka a duniyar Mars.

    Akan shafe wata bakwai ana tafiya kafin isa duniyar ta Mars, wacce ake yi wa lakabi da jar duniya.

    Bayanan bidiyo, Kun san nisan da ke tsakanin duniyarmu da ta Mars?
  19. 'Yan sandan Sydney sun hana gangamin kare hakkin batar fata na Black Lives Matter

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    A yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Australia, 'yan sandan Sydney sun samu umarni daga kotu domin hana gudanar da gangamin kare hakkin bakaken fata wadda masu fafutukar Black Lives Matter suka yi aniyar gudanarwa ranar Talata.

    Sai dai tuni gomman masu zanga-zanga suka halarta a wani dandali amma 'yan sanda sun tarwatsa su.

    “Ba ma adawa da zanga-zanga. Amma ba ma so a rika yinta ana tsakiyar wannan annoba,” a cewar wakilin rundunar 'yan sandan New South Wales (NSW).

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu zanga-zangar sun ce hana su gudanar da ita tamkar keta hakkinsu ne na dimokradiyya a yayin da aka bar gidajen sayar da abinci, da kasuwanni da 'yan kwallo suna gudanar da sana'o'insu.

    Ranar Talata hukumomin birnin na New South Wales sun ce an samu karin mutum 14 da suka harbu da cutar korona, yayin da birnin Victoria da ke makwabtaka – inda ya kasance cibiyar yaduwar cutar – ya bayar da rahotanni karin mutum shida da suka mutu sannan mutum 384 suka kamu da cutar.

  20. An 'wanke' Akinwumi Adesina daga zargin cin hanci

    Adesina

    Asalin hoton, Reuters

    Kwamiti mai zaman kansa da aka kafa don bincike kan shugaban bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina, ya wanke shi daga zarge-zargen cin hanci da nuna ɓangaranci, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Tsohuwar shugabar Ireland Mary Robinson ce ta shugabanci kwamitin na kwararru da ya wanke Mr Adesina, kuma mambobin kwamitin sun hada da Ministan shari'ar Gambia Hassan Jallow da Leonard McCarthy, mataimakin shugaban sashen tsare gaskiya na Bankin duniya.

    Kamfanin dillancin labaran na AFP ya ambato wani rahoto yana cewa an wanke Mr Adesina daga dukkan zarge-zargen da wasu ma'aikata da ba a ambaci sunansu ba suka yi masa.

    Wasu masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa. Sai dai ya musanta zarge-zargen.

    Tun da farko hukumar gudanarwar bankin ta ce bata nemi shugaban bankin, Akinwumi Adesina, ya sauka daga mukaminsa ba.

    Amurka ta yi watsi da wani bincike da aka yi a kansa game da zarge-zargen nuna ɓangaranci.