Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a muhawarar jihar Gombe

Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Gombe.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahya and Mustapha Kaita

  1. An kawo karshen muhawara

    A nan muka kawo karshen wadanna bayanai kan muhawarar da 'yan takarar gwamnan Gombe suka tafka.Da fatan za ku tara ranar 31 ga watan Janairu don ganin yadda za ta kaya a muhawar jihar Kano.

    Sunanmu Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita muke cewa sai mun sake haduwa.

  2. Jawabin kammalawa

    Shugaban sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh ya yi jawabin godiya ga 'yan takara, mahalarta taro da kuma wadanda suka kasance da mu kai tsaye domin kallo ko sauraron wannan muhawara. Ya yi kira ga abi ka'ida wajen fita daga dakin gudanar da muhawarar.

  3. Hotunan tashi daga muhawara

  4. Kai tsaye daga wurin muhawara

    Ana dai cigaba da gudanar da muhawarar, zaku iya bin mu a shafin mu na Facebook, Twitter da Instagram.

  5. Shin ya Abdulganiyu na PRP zai kawo karshen matsalolin da 'yan fansho ke fuskanta?

    Ya ce zai tabbatar da kawo karshen matsalar ta hanyar samo tallafi domin biyansu hakkinsu.

  6. Dole ne a biya mafi karancin albashi - Nafada

    Usman Bayero Nafada ya ce jihar Gombe na da ma'aikata 66,000, saboda haka dubu 30,000 mafi karancin albashi dole a biya shi.

    Zai yi kokari ya ba matasa ilimi nagari ya koya musu sana'oi da ba su ayyukan yi sannan a basu shawarar yin aure don tabbatar da cikar mutuntakarsu.

  7. Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Bello Shatima: Sai fa an dakile rashawa da cin hanci, a kuma mayar da hankali ga tatso albarkatun kasa da Allah ya hore wa jihohinmu domin kara samun kudin shiga ba a tsaya jiran kudin mai ba.

    Sarki Abubakar Bala: Jama'a kada a dubi girman riga, party ko dadin baki, a lura da tambayoyi da ake masu, sai a tantance karya da yaudara.

  8. Zan samar da ilimi mai kyau ga mata- Inuwa

    Inuwa zai samar da ilimi mai kyau ga mata don su san yadda za su tallafi rayuwarsu da ta iyalansu matansa biyu duk ma'aikata ne don haka dole ya bai wa mata dama. A bangaren tattalin arziki zai yi garanbawul. Zai rage kashe kudi wajen gudanar da sharholiya.

    Inuwa ya ce ba zai lamunci bangar siyasa a tafiyarsa ba kuma zai fitar da duk mai yin haka a tafiyarsa. Maganar maadinai ya ce babban abu ne a tsarinsa. Zai yi sabbin masana'antu kamar kamfanin sumunti na Ashaka

  9. Zan bai wa mata 'yancinsu - Wali

    Wali Modibbo zai ba wa mata 'yanci su yi takara yadda ya kamata. Zai samar da asibitoci don duba lafiyar mata.

    Ya kuma ce zai inganta rayuwar nakasassu ta hanyar ba su mukaman gwamnati kamar daraktoci da permanent secretaries.

    Wali Modibbo ya ce an san mutanen Gombe da karamci da mutunta juna, ya ce inda sukai kuskure a yafe masa, su duk 'yan uwan juna ne don haka ba gaba sai zumunci.

  10. Zan binciki gwamnatin da na gada- Abdul-Ghaniyu

    Abdulganiyu Bello na jam'iyyar PRP ya ce zai binciki gwamnatin da zai gada idan bukatar haka ta taso idan har ya zama gwamna.

  11. Ma'aikatan BBC a bakin aiki

    Wadannan wasu daga cikin ma'aikatan BBC Hausa, Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita, ke sabunta shafinmu na intanet, bbchausa.com a kan muhawarar 'yan takarar gwamnan jihar Gombe.

  12. Shin Nafada yana goyon bayan a zabi Buhari?

    Ya ce ba ya goyon bayan Muhammadu Buhari, inda ya yi kira ga magoya bayansa su zabi dan takarar jam'iyyarsu ta PDP Atiku Abubakar.

  13. An fara amsa tambayoyi

    An fara bai wa mahalarta muhawarar dama domin su fara tambayoyi ga 'yan takarar gwamna:

  14. Wasu daga cikin ma'aikatan BBC kai tsaye a wurin muhawara

    Wasu daga cikin ma'aikatan BBC Hausa kenan kai tsaye a lokacin da ake gudanar da muhawarar.

  15. Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Zaidu Bala Kofa Sabuwa: Don Allah 'yan takarar gwamnan jihar Gombe kada ku bar farfajiyar taron BBC sai kun kulla yarjejeniyar zaman lafiya a zaben 2019.

    Mu'awiyya S Kumo: Tambayata ga kowane dan takara ita ce, ya rike wani mukami a baya? To kowa ya fadi me ye ya yi wa jahar na ci gaban al'umma.

    Sanusi SB Aliyu: Ya kamata 'yan siyasa su sani cewa yin alkawura kafin hawa kan mulki shi ne babbar matsalar da suke fuskanta. Saboda basu la'akari da abin da za su cimma idan suka gaji kujerar mulki sai su kasa cika alkawarin.

  16. Zauren muhawara ya cika makil

    Zauren da ake tafka muhawarar ya cika makil da jama'a kamar yadda kuke gani a wadannan hotuna.

  17. Haruna Tangaza ne ke sanya ido kan muhawara

    Daya daga cikin masu shirya muhawarar BBC kenan watau Haruna Tangaza yake jagorantar masu sanya ido wajen gudanar da muhawarar.

  18. An girke jami'an tsaro a wurin muhawarar

    An girke jami'an tsaro a zauren da ake tafka muhawara a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

  19. 'Zan biya hakkin masu fansho da bunkasa ilimi'

    Dan takarar gwamnan na Jam'iyyar APGA, Wali Modibbo ya gabatar da kansa. Ya ce biyan hakkin masu fansho da bunkasa ilimi da noma da kiwon lafiya zai fi sanya wa a gaba, da kuma sadarwa da tsaro.

  20. Zan bunkasa ilimi da noma - Abdul-Ghaniyu

    Dan takarar PRP Abdulganiyu Bello yayin da yake gabatar da kansa ya ce ya fito takara ne saboda amsa kiran jama’a kuma yaki da jahilci da talauci ne zai fi sa gaba.

    Ya ce zai yaki jahilci da bunkasa ilimi, zai zauna da masana domin diba hanyoyin bunkasa ilimi, ya kuma yi alkawalin bayar da ilimi kyauta ga mutanen Gombe.