An fara sallar jana’izarsa ne da misalin karfe uku na rana a gidansa da ke Shagari.
Dubban masu alhini ni ne daga sassa daban-daban suka yi wa gawar addu’a a yayin sallar ta tsawon mintuna biyu.
Daga cikinsu akwai tawagar gwamnatin kasar wadda ta kunshi ministoci da kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha wanda ya jagorance ta.
Haka ma gwamnonin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar.
Daga nan aka dauki gawar domin binne ta a wani kabari da aka haka a wani bangare na katafaren gidansa a yayin ‘ya’ya da jikokin da makusanta ke sharbar hawaye.
Lokaci ne dai mai sosa rai ga wanda ya gani.
Bayan da aka kammala binne gawar tsohon shugaban wata tawagar sojojin kasar ta zagaye kabarin domin yi bankwanan ban-girma. Sun yi harbi sau ukku a sama zagaye da kabari tsohon shugaban wanda ya shugabanci kasar a shekarun 70-80.