Karanta bayanai da labarai game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari, shugaba na farko mai cikakken iko wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Haruna Shehu Tangaza
Allah Ya jikan Shehu Shagari
A nan muka kawo karshen bayanai kai-tsaye da muke kawo maku game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari wanda ya rasu a ranar Juma'a 28 ga watan Disamban 2018.
An binne shi ne a mahaifarsa garin Shagari a jihar Sakkwato.
Asalin hoton, AFP
Kalli bidiyon kabarin Shehu Shagari
Mutane da dama ne ke zuwa suna wa kabarin tsohon shugaban na Najeriya addu'a.
Gidan marigayin a garin Shagari ya cika makil da mutane da ke zuwa gaisuwar ta'aziya.
Sakon da muka samu
Sakon da muka samu
Inda aka binne Shehu Shagari
An binne gawar tsohon shugaban na Najeriya a mahaifarsa garin Shagari a jihar Sakkwato bayan ya rasu a ranar juma'a 28 ga watan Disamban 2018 a asibitin kasa a Abuja.
Bidiyon yadda aka yi wa Shagari Sallar Jana'iza
An fara sallar jana’izarsa ne da misalin karfe uku na rana a gidansa da ke Shagari.
Dubban masu alhini ni ne daga sassa daban-daban suka yi wa gawar addu’a a yayin sallar ta tsawon mintuna biyu.
Daga cikinsu akwai tawagar gwamnatin kasar wadda ta kunshi ministoci da kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha wanda ya jagorance ta.
Haka ma gwamnonin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar.
Daga nan aka dauki gawar domin binne ta a wani kabari da aka haka a wani bangare na katafaren gidansa a yayin ‘ya’ya da jikokin da makusanta ke sharbar hawaye.
Lokaci ne dai mai sosa rai ga wanda ya gani.
Bayan da aka kammala binne gawar tsohon shugaban wata tawagar sojojin kasar ta zagaye kabarin domin yi bankwanan ban-girma. Sun yi harbi sau ukku a sama zagaye da kabari tsohon shugaban wanda ya shugabanci kasar a shekarun 70-80.
Bayanan bidiyo, Yadda aka yi wa Shagari Sallar jana'iza
Kalli bidiyon yadda aka shiga da gawar Shagari
Yadda aka shiga da gawar marigayi Shehu Shagari domin sallar Jana'iza a mahaifarsa da ke Shagari
Bayanan bidiyo, Yadda aka shiga da gawar Shagari don Sallar Jana'iza
Yadda aka yi wa gawar Shagari sallar Jana'iza
Asalin hoton, @Manirudaniya
Asalin hoton, @Manirudaniya
Sakon da muka samu a Facebook
Kalli bidiyon yadda gawar Shagari ta iso Sakkwato, Shehu Shagari ya rasu
Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon yadda gawar Shagari ta iso Sakkwato.
An kammala sallar Janaiza
Ana shirin binne marigayi tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari a mahaifarsa garin Shagari a Sakkwato
Yadda mutane suka cika gidan Marigayi Shagari
Sakon da muka samu daga Facebook
Sakon da muka samu a Facebook
Gawar Shagari ta isa mahaifarsa garin Shagari
Daruruwan mutane ne suka taru suna jiran isowar gawar tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari domin yi ma sa Sallar Jana'iza a mahaifarsa garin Shagari.
Asalin hoton, @Manirudaniya
Asalin hoton, @Manirudaniya
Asalin hoton, @Manirudaniya
Sarautar Turakin Sakkwato, Shehu Shagari ya rasu
Wani matsayi da Alhaji Shehu Shagari ya rike har karshen
rayuwarsa shi ne na Turakin Sakkwato.
Babban wakili ne a majalisar koli
ta fadar Mai martaba sarkin Musulmi .
Tun a shekarar 1962 ne aka ba shi
wannan mukamin wanda kuma ya rike har ranar da ya koma ga mahaliccinsa.
Malam
Bello N. Junaidu, shugaban cibiyar bincike da adana tarihin daular Sakkwato ya
yi wa Haruna Shehu Tangaza Karin bayani game da sarautarsa ta Turaki da kuma irin gudummuwar da ya bayar ga ci
gaban masarautar ta Sarkin musulmi:
Ya ce an ba shi sarautar ne a matsayin jagoran ilimi, kuma garkuwa ga ilimi a masarautar Sarkin Musulmi.
Sannan ya ce Turakin Sakkwato Alhaji Shehu Shagari ya bayar da gudunmuwa wajen bunkasa ilimi a lardin Sakkwato inda ya hada kan 'yan boko da kuma tabbatar da mutane sun tura 'ya'yansu zuwa makaranta
Asalin hoton, Family
An tafi da gawar tsohon shugaban zuwa mahaifarsa Shagari
Bayan isowar gawar marigayin tsohon shugaban Najeriya daga nan an saka ta cikin wata mota mallakar
rundunar sojin sama ta kasar inda ba da bata wani lokaci ba ta zarce zuwa garinsu
na Shagari inda za a yi masa jana’iza.
Gwamna Tambuwal ne ya jagoranci karbar gawar
Gwamnan jihar Aminu waziri Tambuwal ne ya jagoranci sauran
fitattun mutane a jihar da kuma iyalan marigayin wajen karbarta daga sojojin
kasar a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III.
Yadda gawar Shagari ta isa Sakkwato
Gawar ta iso da karfe daya na ranar Asabar cikin wani jirgi
mallakar gwamnatin kasar mai lamba 5N FGZ.