Sai an jima
A nan muka kawo karshen labarai da sharhi game da gasar kofin duniya ta shekarar 2018.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da sharhi game fa da wasan karshe na gasar kofin duniya na shekarar 2018 da ake yi a birnin St Petersburg na Rasha
Abdulwasiu Hassan
A nan muka kawo karshen labarai da sharhi game da gasar kofin duniya ta shekarar 2018.
Amma bakaar fata nawa ne a cikin 'yan Faransan ma?
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya nun murnarsa.
Sau biyu kenan da kocin Faransa ke cin kofin duniya da kasar.
Shi ne keftin dinsu a lokacin da suka ci kofin a shekara 1998.
Faransa ta ci kofin duniya bayan ta doke Croatia 4-2.
Minti biyar aka kara. Shin wani abu ka iya sauyawa cikin minti biyar dinnan?
Saura minti uku kafin a tashi. Croatia za ta iya yin wani abu kuwa?
Fekir ya maye Oliver Giroud
A yau dai Paul Pogba yana kusan ko ina ne a cikin filin wasa. Ga taswirar yadda taka ledarsa ya kasance
Ta farke kwallon ta kuskuren mai tsaron gidan Faransa. Mario Mandzukic ne ya ci wa Croatia kwallon yayin da mai tsaron gidan Faransa ya barar da kwallon yana kokarin yanke dan wasan na Croatia.
Mabappe ne ya ci wa Faransa kwallo ta hudu!
N'Golo Kante bai yai wani wasan azo-a-gani ba in aka kwatanta da yadda yake yi a da - sau 19 ne kawai ya taba kwallo .
Paul Pogba ne ya ci wa Faransa. Hanya Crotai ba za ta sha kaye ba kuwa?
Nzonzi ya maye Kante.
Pogba ya tura Mbappe kwallo, kuma dan wasan mai cike da kuruciya ya bi kwallon da karfi har cikin gidan Croatia. Sai dai mai tsaron gidan Croatia ya samu ya tare kwallon.
Sai ka rasa abin da ya sa Croatia ke kasa da Faransa a wajen ci kwallo. Amma suna gaba da Faransa a taka leda. Paul Pogba ya rasa kwallo a tsakiya , Ivan Rakitic ya tura wa Ante Rebic kuma mai tsaron gidan Faransa ya ture kwallon da ya buga!
An dawo daga hutun rabin lokaci. Yaya za ta kaya ne?
Sau daya ne kawai wata kasa ta taba yin nasara bayan an ci ta kafin hutun rabin lokaci a tarihin gasar kofin duniya.
Uruguay ce kawai ta taba yin haka a wasan karshe na gasar ta farko a shekarar 1930 inda daga baya ta yi nasara a kan Argentina.
Shin Croatia za ta iya yin hakan?
An tafi hutun rabin lokaci, kuma Faransa na gaba da Croatia da 2-1 duk da cewa Croatia ta fi ta wasa cikin minti 45 na farko.