Yadda Faransa ta lashe kofin duniya

Labarai da sharhi game fa da wasan karshe na gasar kofin duniya na shekarar 2018 da ake yi a birnin St Petersburg na Rasha

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan

  1. Sai an jima

    A nan muka kawo karshen labarai da sharhi game da gasar kofin duniya ta shekarar 2018.

  2. Murnar cin kofin duniya, Faransa 4-2 Croatia

    Amma bakaar fata nawa ne a cikin 'yan Faransan ma?

    Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

  3. 'Yan Faransa na murna, Faransa 4-2 Croatia

    Murnar cin kofin

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Emmanuel Macron ya ji dadi

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya nun murnarsa.

    Macron

    Asalin hoton, EPA

  5. Deschamp ya ci sau biyu

    Sau biyu kenan da kocin Faransa ke cin kofin duniya da kasar.

    Shi ne keftin dinsu a lokacin da suka ci kofin a shekara 1998.

    Deschamp

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Deschamp da Griezmann na murna
  6. FULL-TIME, Faransa 4-2 Croatia

    Faransa ta ci kofin duniya bayan ta doke Croatia 4-2.

  7. An kara minti 5, Faransa 4-2 Croatia

    Minti biyar aka kara. Shin wani abu ka iya sauyawa cikin minti biyar dinnan?

  8. Crotai na da minti uku, Faransa 4-2 Croatia

    Saura minti uku kafin a tashi. Croatia za ta iya yin wani abu kuwa?

  9. Faransa ta sake canji, Faransa 4-2 Croatia

    Fekir ya maye Oliver Giroud

  10. Yadda kwallon Pogba ta kasance, Faransa 4-2 Croatia

    A yau dai Paul Pogba yana kusan ko ina ne a cikin filin wasa. Ga taswirar yadda taka ledarsa ya kasance

    .

    Asalin hoton, .

  11. GOAL, Faransa 4-2 Croatia

    Ta farke kwallon ta kuskuren mai tsaron gidan Faransa. Mario Mandzukic ne ya ci wa Croatia kwallon yayin da mai tsaron gidan Faransa ya barar da kwallon yana kokarin yanke dan wasan na Croatia.

    .

    Asalin hoton, .

  12. GOAL, Faransa 4-1 Croatia

    Mabappe ne ya ci wa Faransa kwallo ta hudu!

    Mbappe

    Asalin hoton, Reuters

  13. Yadda Kante ya taka leda

    N'Golo Kante bai yai wani wasan azo-a-gani ba in aka kwatanta da yadda yake yi a da - sau 19 ne kawai ya taba kwallo .

    Kante

    Asalin hoton, Opta

  14. GOAL, Faransa 3-1 Croatia

    Paul Pogba ne ya ci wa Faransa. Hanya Crotai ba za ta sha kaye ba kuwa?

  15. Faransa ta yi canji, Faransa 2-1 Croatia

    Nzonzi ya maye Kante.

  16. Mbappe!, Faransa 2-1 Croatia

    Pogba ya tura Mbappe kwallo, kuma dan wasan mai cike da kuruciya ya bi kwallon da karfi har cikin gidan Croatia. Sai dai mai tsaron gidan Croatia ya samu ya tare kwallon.

  17. Croatia ta fara far ma Faransa

    Sai ka rasa abin da ya sa Croatia ke kasa da Faransa a wajen ci kwallo. Amma suna gaba da Faransa a taka leda. Paul Pogba ya rasa kwallo a tsakiya , Ivan Rakitic ya tura wa Ante Rebic kuma mai tsaron gidan Faransa ya ture kwallon da ya buga!

    Modric

    Asalin hoton, Reuters

  18. An dawo, Faransa 2-1 Croatia

    An dawo daga hutun rabin lokaci. Yaya za ta kaya ne?

  19. Ba kasafai ake yin sa ba..., Faransa 2-1 Croatia

    Sau daya ne kawai wata kasa ta taba yin nasara bayan an ci ta kafin hutun rabin lokaci a tarihin gasar kofin duniya.

    Uruguay ce kawai ta taba yin haka a wasan karshe na gasar ta farko a shekarar 1930 inda daga baya ta yi nasara a kan Argentina.

    Shin Croatia za ta iya yin hakan?

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Hutun rabin lokaci, Faransa 2-1 Croatia

    An tafi hutun rabin lokaci, kuma Faransa na gaba da Croatia da 2-1 duk da cewa Croatia ta fi ta wasa cikin minti 45 na farko.

    .

    Asalin hoton, .