Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 28 ga watan Agustan 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a wannan rana.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.

  2. MDD ta amince da ci gaba da shirin wanzar da zaman lafiya a Lebanon

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsawaita aikin dakarun kiyaye zaman lafiya a kudancin Lebanon har zuwa ƙarshen shekarar 2027.

    An gabatar da shawarar janye dakarun na UNIFIL bayan da Amurka ta yi barazanar yin amfani da ikonta idan aka tsawaita aikin ba tare da ƙayyade wa’adin ƙarshe ba.

    Amurka da Isra’ila sun daɗe suna fafutikar ganin an janye dakarun UNIFIL, an kuma miƙa alhakin tsaron ga gwamnatin Lebanon.

    Dakarun UNIFIL na gudanar da sintiri a kan iyakar kudancin Lebanon tun bayan mamayar Isra’ila a shekarar 1978, sai dai masu suka na cewa ta gaza wajen rushe ƙungiyar Hezbollah.

  3. Gwamnan Kebbi ya naɗa sabon sarkin Zuru

    Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da nadin Alhaji Sanusi Mika'ilu a matsayin sabon sarkin Zuru.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ahmed Idris ya fitar ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne sakamakon shawarar kwamitin zaɓen sabon sarkin.

    Yayin da yake miƙa wa sabon sarkin takarakar nadin kwamishin ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, Hon. Garba Umar Dutsin-Mari ya buƙaci sabon sarkin ya nuna halin dattakon da aka tsammata daga gare shi.

    Naɗiin sabon sarkin na zuwa ne bayan mutuwar tsohon sarkon Marigayi, Alhaji Muhammad Sani Sami wanda ya rasu ranar 16 ga watan Agustan da muke ciki.

  4. Kofarmu a buɗe take ga duk jam'iyyar da ke son tattaunawa da mu - Kwankwaso

    Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya Sanata Rabi'u Kwankwanso ya ce suna jin daɗin jam'iyyarsu, kuma a halin da ake ciki babu wani ƙawance da suka ƙulla da wata jam'iyya.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar ƙoli na jam'iyyar da aka gudanar a Abuja, Sanata Kwankwaso ya ce ba gaggawa suke yi ba.

    ''Ƴaƴan jam'iyyarmu ba gaggawa suke yi ba, komai muna yinsa a hankali'', in ji shi.

    Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce ya ce kawo yanzu babu wata jam'iyya da suke tattaunawa da ita domin ƙulla ƙawance, sai dai ya ce hakan ba yana nufin ba za su tattauna da wata ba.

    ''Mu ƴansiyasa ne kuma a shirye muke mu tattauna da duk wanda ke son tattaunawa da mu'', in ji.

    An dai jima ana raɗe-raɗin Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC, tun bayan zaɓen 2023, inda har aka riƙa hasashen ba shi minista, lokacin da Tinubu ya ce zai yi aiki da ƴan hamayya a gwamnatinsa.

  5. Manyan ƙasashe Turai sun zargi Iran da zama barazana ga zaman lafiya duniya

    Birtaniya da Faransa da Jamus sun ce Iran ta kasance babbar barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro ta hanyar shirinta na nukiliya.

    Manyan ƙasashen Turan uku sun yi imanin cewa Iran ta saɓa wa yajejeniyar 2015 da ta taƙaita ayyukan nukiliya.

    Ƙasashen sun ce a yanzu sun ɗauki matakin farko na sake ƙaƙaba wa ƙasar takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta wajabta.

    Sun kuma bai wa Tarayyar Turai kwana 30 da ta mayar da martani.

    Ƙasashen uku sun kuma nuna damuwa kan inda kilogram 400 na sinadarin uranium da aka inganta ya shiga.

    Sinadarin ya kusan kai wa matakin da ake buƙata don ƙera makamin nukiliya.

    Iran ta ce matakin ƙasashen na Turai haramtacce ne, kuma zai kawo tarnaƙi a tattaunawa da hukumar kula da makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya.

  6. MDD ta yi gargaɗin mummunar illa kan matakin kwace Birnin Gaza

    Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi gargaɗin cewa matakin Isra'ila na shirin ƙwace birnin Gaza zai iya janyo mummunar illa.

    Ya yi Allah wadai da abin da ya kira mummuna halin da Gaza ke ciki, yana mai cewa yankin cike yake da ɓaraguzai da gawarwaki, da kuma misalin abin da ya bayyana da saɓa wa dokokin duniya.

    Mista Guterres ya ce bayyana cewa wanzuwar yunwa a Gaza ta faru ne sakamakon matakin hana shigar da manyan abubuwa buƙata.

    Isra'ila ta gargaɗi mazauna Gaza kusan miliyan guda - waɗanda da yawan su suka bar yankin ko suka faɗa ƙangin yunwa - da su koma kudancin Zirin.

  7. Tarayyar Turai ta yi kakkausan martani kan harin Kyiv

    Shugaban hukumar gudanarwar Tarayar Turai, Ursula von der Leyen, ta yi kakkausan martani kan mummunan harin da Rasha da kai Ukraine da ya lalata ofishin jakadun ƙungiyar EU da ke birnin Kyiv.

    Aƙalla mutum 19 ne suka mutu ciki har da ƙananan yara huɗu - gommai suka jikkata a hare-haren boma-boman, kamar yadda jami'an Ukriane suka bayyana.

    Harin ya lalata wani gini mai hawa biyar tare da lalata ofishin jakaancin EU da ke kuda da ofishin jakadancin Birtaniya.

    Cikin wani kakkausan martani da ta fitar, von der leyen ta ce makaman Rasha sun faɗa kusa da ofishin jakadancin EU.

    Ukraine ta ce Rasha ta aika jirage marasa matuƙa kusan 600, tare da matsakaitan makamai masu linzami fiye da 30 da wani babba guda a babban harin da aka kai wa birnin a wannan wata.

    Da dama cikin waɗanda suka mutu a Kyiv na cikin ginin mai hawa biyar da ke kudu maso gabashin gundumar Darnytskyi da ke birnin Kyiv.

  8. Shugabannin sojin Afrika sun kammala taron tsaro a Abuja

    Shugabannin sojin Afrika sun kammala wani taro na ƙoli a Abuja wanda ya mayar da hankali kan yawaitar matsalolin tsaro a nahiyar.

    Shugabannin tsaro daga ƙasashe irin su Nijar da Somaliya da Ghana da Masar sun hallara a babban birnin Najeriya domin tattaunawa kan dabarun zaman lafiya da tsaro na cikin gida.

    An kammala wannan taro mai tsawon kwanaki uku a ranar Laraba.

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya yi jawabi ga mahalarta a lokacin buɗe taron, inda ya buƙaci kasashen Afrika su zama masu fito da sabbin fasahohi a fannin tsaro, tare da gargadin cewa dogaro da hanyoyin waje ba zai dore ba.

    Haka kuma, ya jaddada buƙatar ƙara zuba jari a tsaron shafukan sada zumunta da na intanet, ganin yadda barazanar da ba a gani da kuma ta zamani ke karuwa.

    Nahiyar na ci gaba da fuskantar matsaloli kamar ta’addanci da laifukan ƙungiyoyi da fashi da makami da hare-hare ƴan bindiga da tasirin sauyin yanayi.

    Kungiyar Tarayyar Afrika da ECOWAS sun dage wajen karfafa hadin gwiwar soja, amma hakan ya ci tura sakamakon ƙarancin kuɗaɗe da matsalolin kayan aiki da sabanin siyasa.

    Daya daga cikin muhimman batutuwa a taron shi ne kafa Rundunar Tsaron ko-ta-kwana ta Afrika wadda aka daɗe ana shirin kafa ta domin amsa kiran gaggawa, amma aiwatar da ita ya tsaya sakamakon matsaloli wajen dabaru da ƙa’idoji da kuɗade.

    Mahalarta sun amince cewa Afrika dole ta samar da sabon tsarin tsaro – wanda ‘yan Afrika za su jagoranta kuma su tsara shi domin magance matsalolin nahiyar.

  9. Harin Isra’ila ya kashe sojojin Siriya shida - Damaskus

    Hare-haren jiragen yaƙi marasa matuki na Isra’ila a kusa da Damaskus sun hallaka sojojin Siriya shida, a cewar gwamnatin ƙasar.

    Ma’aikatar harkokin wajen Siriya ta la’anci harin da aka kai ranar Talata, tana cewa ya saɓawa dokokin kasa da kasa kuma ya ƙeta ikon mulkin ƙasar.

    Rundunar sojin Isra’ila ta shaida wa BBC cewa ba ta yin tsokaci kan rahotannin ƙasashen waje.

    Bayan kifar da tsohon shugaban Siriya Bashar al-Assad a watan Disamba, Isra’ila ta kai hare-hare da dama a sassan Siriya, lokacin da tsoffin ‘yan tawaye suka kafa gwamnati mai goyon bayan masu iƙirarin jihadi.

    A bana kaɗai, Isra’ila ta kai hare-hare 95 a Siriya – hare-haren sama 85 da kuma hare-haren ƙasa 10 – a cewar hukumar SOHR.

  10. Cutar kwalara ta hallaka mutum 167 a Yammacin Kordofan ta Sudan

    Aƙalla mutum 167 ne suka mutu sakamakon cutar cholera daga cikin mutum fiye da 1,200 da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Yammacin Kordofan da ke Kudancin Sudan tun bayan da aka sanar da ɓarkewar cutar a watan Yuli kamar yadda gidan rediyon Dabanga ya ruwaito.

    Ministan Lafiya na jihar, Mohamed Nourin ne ya sanar da hakan.

    Cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 12, inda El-Nuhud da Abu Zabad suka fi fuskantar illar cutar.

    Garin El-Nuhud shi kaɗai ya samu addadin mutane 657 da suka kamu da cutar tare da waɗanda suka mutu 61.

    A fadin ƙasar, kwalara ta kashe aƙalla mutum 2,470 tare da shafar fiye da mutum 100,000 tun bayan da aka ayyana ɓarkewar cutar a watan Agustan 2024.

    Matsalar ta ƙara tsananta ne sakamakon rugujewar tsarin kiwon lafiya a Sudan saboda yaƙin basasar da aka daɗe ana yi tun daga watan Afrilun 2023.

  11. Abincin da ake raba wa yara masu tamowa a Najeriya zai ƙare nan da wata uku - Rahoto

    Wata ƙungiyar kare yara ta Save the children ta ce aƙalla ƙasashe huɗu a Afirka, ciki har da Najeriya da Kenya, Somalia da Kudancin Sudan na iya fuskantar ƙarewar abincin tamowa a cikin watanni uku masu zuwa idan ba a samu ƙarin taimako ba, lamarin da ke sanya yara masu ƙarancin abinci mai gina jiki cikin haɗarin mutuwa.

    Abincin tamowa abinci ne mai ƙarfi da sinadaran gina jiki.

    A cikin shekaru 30 da suka gabata, wannan abincin gaggawa ya ceci rayukan miliyoyin yara masu ƙarancin abinci mai gina jiki.

    Yaro mai ƙarancin abinci mai gina jiki sosai yana cikin haɗarin mutuwa sau tara fiye da yaron da ke da lafiya idan suka kamu da cututtuka na yau da kullum.

    A Najeriya, yara kusan miliyan 3.5 da ke ƙasa da shekaru biyar suna fama da ƙarancin abinci mai gina jiki mai tsanani musamman a arewa maso gabas da arewa maso yamma, kuma suna cikin haɗarin mutuwa idan ba a basu kulawa da abincin da ya kamata ba da wuri.

    Najeriya na buƙatar aƙalla kwalayen abincin tamowa 629,000 domin kula da waɗannan yara, amma har yanzu kaso 64 kacal aka samo.

    A Kenya, musamman a Turkana, yara na ƙara fuskantar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da rashin tsaro na abinci saboda fari da ambaliyar ruwa da ake fuskanta.

  12. Najeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo

    Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da ƙarin farashin yin fasafo wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025, domin inganta inganci da tsaro a tsarin fasafo ɗin ƙasar.

    A cewar hukumar, farashin fasafo na shekaru biyar mai shafi 32 wanda a baya yake kan naira 70,000 yanzu zai tashi zuwa naira 100,000, yayin da na shekaru 10 mai shafi 64 wanda a baya yake kan naira 120,000 zai koma naira 200,000.

    Sai dai, farashin fasafo da ‘yan Najeriya ke yi a ƙasashen waje ba zai canza ba, inda za a ci gaba da biyan dala 150 kan fasafo na shekara 5 da dala 230 kan fasafo na shekara 10.

    Hukumar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na nufin tabbatar da daidaito a ayyukan fasafo, tare da sauƙaƙa damar samun fasafo ga duk ‘yan Najeriya.

  13. Ba na so na tsaya takara a 2027 – El-Rufai

    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ya tunanin tsayawa takara a zaɓen ƙasar na shekara ta 2027 ba.

    Ya ce dawowarsa harkar siyasa kwanan nan "ba don neman muƙami ba ne, sai don tallafa wa shugabanci nagari a dukkan matakai".

    El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin wani taron siyasa a jihar Kaduna ranar Laraba.

    "Asalin shirina bayan barin gwamna a 2023 shi ne na huta daga siyasa, amma abubuwan da suka faru kwanan nan ne suka tilasta min dawowa, ba don kaina ba, amma domin na bayar da goyon baya," in ji El-Rufai.

    El-Rufa'i ya ce "ni dai ba zan sake yin gwamna ba, ba na so na je senate (Majalisar Dattijai), ba na wata takara".

    Ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda ya ce ta gaza.

    Nasir El-Rufa'i na cikin manyan ƴan siyasar Najeriya da suka yanke shawarar kafa hadakar ƴan adawa domin ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar a zaɓen ƙasar na 2027.

    Tsohon gwamnan na daga cikin wadanda suka mara wa APC baya a zaɓen 2023 da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Tinubu ya yi nasara, sai dai ɗan siyasar ya raba gari da jam'iyyar watanni bayan hawan Tinubu kan mulki, inda ya koma jam'iyyar SDP.

    Daga baya kuma ya bayyana cewa zai kasance cikin jam'iyyar ADC wadda a yanzu haka ƴan adawar ke amfani da ita a matsayin lemarsu.

  14. Goodluck Jonathan na son a sauya yadda ake zaɓen shugaban INEC

    Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira da a samar da sabon tsarin zaɓen shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), inda ya ba da shawarar kafa wani tsarin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa don ƙara wa hukumar sahihanci kafin zaɓen gaba na 2027.

    Jonathan ya bayyana wannan ra’ayi ne a ranar Laraba a Abuja, a yayin gabatar da shirin ƙasa na gyaran harkokin zaɓe, wanda Makarantar Nazarin Zamantakewa da Siyasa ta Abuja ta shirya.

    Kiran ya zo ne a wani lokaci na siyasa mai ɗaukar hankali, yayin da wa’adin shugaban INEC na yanzu, Prof. Mahmood Yakubu, ke ƙarewa a watan Oktoba na wannan shekara.

    Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓukan 2019 da 2023, ya riga ya yi wa’adin aiki biyu, kuma zaɓen wanda zai gaje shi na janyo ƙarin hasashe a al’umma.

    Masana na ganin cewa wanda zai zama sabon shugaban INEC zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihancin zaɓen 2027.

    Jonathan, wanda a baya an yi hasashen cewa zai iya komawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce; “Ina ganin Najeriya na iya inganta tsarin zaɓe ta hanyar kafa wani kwamitin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa, wanda zai ƙunshi wakilai daga kotuna da ƙungiyoyin fararen hula jami’o’i da ƙungiyoyin da kwararru."

    "Wannan kwamitin zai tantance kuma ya bayar da jerin sunayen ‘yan takarar da ke neman shugabancin INEC da suka cancanta, daga cikinsu shugaban ƙasa zai iya zaɓa shugaban INEC ɗin."

    "Wannan zai rage tunanin son zuciya da ƙara amincewar jama’a da inganta sahihancin hukumar zaɓe INEC.” tsohon shugaban ƙasar ya ƙara da cewa.

  15. 'Matsalolin sauyin yanayi masu tsanani ke ta'azzara gobarar daji a sassan Turai' - sabon bincike

    Wani sabon bincike ya ce yanayin ta'azzarar gobarar daji da aka rinka gani a sassan Turai a wannan shekarar na da alaƙa da matsaloli masu tsanani na sauyin yanayi.

    Masu bincike daga wata ƙungiyar masu nazartar yanayi a duniya, sun ce wannan yanayi na da alaƙa da raguwar sanyi da kashi 14 cikin 100.

    Sannan zafi ya ninku sau 13, wanda tabbas ke nuna tsananin dumamar yanayi.

    Sakamakon shi ne gobarar daji da ta kone milyoyin hecta.

    Masana kimiyia dai sun yi gargaɗin yanayin zai fi haka muni muddin ba a rage fitar da sinadarai ba.

  16. Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan ziyartar Japan da Brazil

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala ziyarar kwanaki uku a Brazil.

    Da misalin karfe 1:20 na daren Laraba ne jirgin shugaban ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin ƙasar Abuja, inda ya sami tarba daga manyan jami'an gwamnati da jagororin siyasa.

    Tun da farko Shugaban ya soma ne da zuwa Japan inda ya halarci taron bunkasa yankin Afrika karo na 9 a birnin Tokyo kafin zuwa Brazil.

    Ziyarar tasa zuwa ƙasashen biyu na nuna yadda Najeriyar ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da ta diflomasiyya da manyan ƙasashen duniya.

    Ziyarar ta kuma mayar da hankali kan yin tattaunawa kan kasuwanci da tsaro da noma da makamashi, da nufin janyo hankalin masu zuba hannun jari.

    Shugaban ya shafe kusan makonni biyu a tafiyar ta sa.

  17. China ta gayyaci Kim Jong-un da Putin faretin sojin cika shekara 80 da ƴaƙin duniya na biyu

    China ta sanar da cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, zai halarci faretin sojoji da aka haɗa domin bikin cika shekara 80 da kawo karshen yaƙin duniya na biyu.

    Zai kasance ɗaya daga cikin shugabanni 26 da ake sa rai za su je Beijing, harda shugaba Putin na Rasha.

    A yanzu dai za a zuba ido a gani, ko China na da rawar da za ta taka wajen shawo kan shugabanni biyu kan batun kawo ƙarshen mamayar Ukraine.

    Shugaban Rasha ba kasafai ya ke barin ƙasar sa ba, kuma wannan ne karo na farko da zai je China cikin shekara shida.

  18. Rasha ta yi luguden wuta a Ukraine cikin dare

    Ukraine na fuskantar hare-hare masu tsanani daga Rasha.

    Birnin Kyiv ya tsinci kansa cikin yanayi mai tsanani na hari da jirage marasa matuƙa da ruwan makamai masu linzami.

    Shugaban sojoji a birnin, Timur Tkachenko ya ce sama da wurare 20 aka yi wa illa.

    Wani gini mai hawa biyar ya ruguje sakamakon hare-haren, kuma ana ta kokarin aikin ceto mutane daga ɓaraguzan gini.

    Rahotanni sun ce an sami tashin gobara a wani gini mai hawa 25, akwai kuma makarantar yara da ke ci da wuta.

    Zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum uku, sannan 18 sun jikkata.

    Cikin mamatan akwai yarinya yar shekara 14.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyar mu, barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, inda za mu kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.