Liverpool ba za ta shiga ƴan huɗu ba saboda cinta da ake ta kwana da bugun tazara, Arne Slot
Arne Slot ya ce da ƙyar Liverpool ta shiga ƴan huɗun farko a teburin Premier League, sakamakon cin da ake musu ta kwana da bugun tazara da kuma jifa.
Ƙungiyar Anfield tana mataki na biyar a teburi da maki iri ɗaya da na Chelsea, bayan da za a ci gaba da wasannin mako na 18 daga karshen mako.
An ci Liverpool ƙwallo 11 daga bugun ko dai kwana ko na tazara ko kuma jifa, yayin da ta ci uku.
Haka kuma Liverpool na fama da masu jinya, bayan da Alexander Isak zai yi jinyar watanni, saboda raunin da ya ji a gidan Tottenham a Premier League.
Slot na fatan Cody Gakpo da kuma Conor Bradley za su murmure, domin buga wa Liverpool wasan da za ta buga da Wolverhampton.
Mohamed Salah yana buga wa Masar gasar Afcon, yayin da Wataru Endo ke jinya, sannan an dakatar da Dominik Szoboszlai.