'Amurka ce za ta riƙa kula da sayar da man Venezuela'
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin makamshi na Amurka ya ce Amrka ce za ta yi iko da sayar da man Venezuela har illa ma sha Allah.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban Trump ya bayyana cewa gwamnatin rikon ƙwarya a Venezuela za su riƙa bai wa Amurka gangar mai aƙalla dubu hamsin.
China, wadda ita ce kan gaba wajen sayen man Venezuela, ta zargi Washington da yin zalunci da kuma kawo cikas ga samar da makamashi a duniya.
Ministan harkokin wajen China ya ce za su kare hakkokinsu da ke Venezuela.
Rasha ta yi Alla-wadai kan ƙwace jirgi ɗauke da tutar ƙasar
Asalin hoton, US European Command
Moscow ta yi Alla-wadai da kama wani jirgi ɗauke da tutar ƙasar da Amurka ta yi, inda ta buƙaci a kula da ƴan Rasha da ke ciki yadda ya kamata sannan a sake su su koma gida.
Ma'aikatar harkokin sufuri na Rasha ta ce ta bai wa jirgin dakon man, mai suna Marinera damar amfani da tutar ƙasar.
Don haka ta ce babu wata ƙasa da take da ikon amfani da ƙarfi wajen ƙwace jiragen da ke da rajista da wata ƙasa.
Kotu ta bayar da umarnin wucin-gadi na ƙwace wasu kadarorin Abubakar Malami
Asalin hoton, Abubakar Malami
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 na tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami na wucin-gadi.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta ce kadarorin mallakin Malami da ƴaƴansa biyu - Abdulziz Malami da Abiru-Rahman Malami ne, kuma take zargin an mallake su ne ta hanyar da ba ta dace ba.
Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin, bayan lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho ya buƙaci hakan.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an ƙiyasta darajar kadarorin za ta kai naira N213,234,120,000 da ya mallaka a jihohin Kebbi da Kano da Kaduna da Abuja.
Kotun ta ce a wallafa hukuncin ƙwace kadarorin na wucin-gadi, sannan ta yi kira ga "duk wanda da ke da alaƙa da kadarorin kuma yake ganin bai kamata a ƙwace na dindindin a miƙa wa gwamnatin tarayya ba da ya fito ya yi bayani a cikin kwana 14."
A ƙarshe alƙalin ya ɗage shari'ar zuwa raar 27 ga Janairu domin ci gaba.
An kama mutum biyu kan zargin shigar da ƙwaya a gidan yarin Kano
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da yunkurin shigar da ƙwaya da kuma tabar wiwi a gidan yarin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gidajen yarin jihar, Musbahu Lawan ya fitar, ya ce an kama mutanen ne Usman Khalid da Bello Musa ƴan shekara 25 da 24 lokacin da suke ƙoƙarin shigar da ƙwaya zuwa cikin gidan yarin.
Hukumar ta gargaɗi mutane kan yunkurin shiga cikin fursunoni, musamman lokacin zirga-zirga zuwa kotu, saboda irin barazanar tsaro da hakan ke tattare da shi, kuma yana da hukunci mai tsauri.
Sanarwar hukumar ta ce aikinta shi ne gyara hali da kuma sauya tunanin fursunoni, don haka ba za ta lamunci ɓata mata aiki ba.
Hukumar ta ba da umarnin miƙa mutanen zuwa hannun jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA domin ci gaba da bincike.
Ta kuma ce aikinta shi ne tabbatar da tsaro da kuma hana ayyukan tu'amalli da miyagun ƙwayoyi a faɗin gidajen yari da kuma kotuna da ke faɗin jihar.
Faransa da Turai na shirin mayar da martani kan barazanar Amurka ga Greenland
Asalin hoton, Getty Images
Faransa ta ce tana aiki tare da wasu ƙasashen Turai kan shirin mayar da martani ga duk wata barazanar da Amurka ta yi wa Greenland.
Ministan harkokin waje ƙasar ta ce Jean Noel Barrot, ya ce Faransa na so ta ɗauki mataki tare da abokan hulɗarta na Turai.
Anjuma a yau ne zai gana da takwarorinsa na Jamus da Poland.
A jiya Talata ne Fadar White House ta ce Shugaba Trump na tattauna irin matakan da zai ɗauka, ciki har da amfani da ƙarfin soji wajen ƙwace Greenland.
Sai dai Barrot ya ce sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya soke batun yin amfani da ƙarfin soji, a wata tattaunawa ta waya da suka yi.
Barrot ya kara da cewa Greenland ba na siyarwa ba ne, hakazalika hukumomin Greenland da Denmark ne kawai za su iya yanke hukunci kan makomarsa.
Amurka ta ƙwace jirgin dakon man fetur ɗauke da tutar Rasha
Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a Amurka sun ce sun ƙwace jirgin dakon man fetur da ke ɗauke da tutar Rasha a arewacin tekun Atalantika.
Jirgin wanda a baya ke dakon ɗanyan man Venezuela na tsakanin Iceland da Birtaniya.
Rasha ta aika da jirgin yaƙi na karkashin teku da wasu kayayyakin sojin ruwa domin rakiyar jirgin ruwan.
Masu gadin teku na Amurka sun yi ƙoƙarin kama shi a baya bayan da ya ƙeta wani shingen da aka sanya wa jiragen da aka sa wa takunkumi a gaɓar Venezuela.
Tuni dai jirgin dakon man ya sauya sunansa tare da sauya tutarsa zuwa ta Rasha.
Iran ta rataye mutumin da ake zargi da yi wa Isra’ila leƙen asiri
Asalin hoton, Getty Images
Sashen yaɗa labarai na ma'aikatar shari’ar Iran ya sanar da rataye wani mutum mai suna Ali Ardestani bisa zargin yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad, aiki.
An aiwatar da hukuncin ne a safiyar Laraba.
A cewar Mizan, Ardestani ya kasance “babban jigo” na Mossad a cikin Iran, inda ya tattara tare da tura muhimman bayanai game da ƙasar zuwa Isra’ila.
Rahoton ya ce yana ɗaukar hotuna da bidiyo na wasu wurare na musamman tare da tattara bayanai kan batutuwa masu matuƙar muhimmanci, sannan ya miƙa su ga Isra’ila domin musayar kuɗin intanet ta Crypto, da nufin samun bizar Birtaniya da ladan kuɗi har dala miliyan ɗaya.
Hukumar shari’ar ba ta fitar da hotonsa ba, kuma ba ta bayyana lokacin da aka kama shi da tsawon zaman da ya yi a tsare ko wurin da aka aiwatar da hukuncin ba.
Wannan shi ne karo na biyu da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa kan irin wannan zargi cikin ‘yan watannin baya, bayan rataye Aqeel Keshavarz a ranar 19 ga Disamba bisa zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri da ɗaukar hotunan wuraren soja da tsaro.
Somaliya ta yi allawadai da ziyarar ministan harkokin wajen Isra’ila a Somaliland
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar harkokin wajen Somaliya ta yi allawadai da ziyarar da ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Sa’ar ya kai birnin Hargeisa na Somaliland, tana mai cewa ziyarar take ƴancin ƙasae ne da iyakokin Somaliya.
Ziyarar, wacce jami’an Somaliland suka bayyana a matsayin muhimmiyar al’amuran diflomasiyya, ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Isra’ila ta zama ƙasa ta farko daga mambobin Majalisar Dinkin Duniya da ta amince da ‘yancin Somaliland.
Shugaban Somaliland, Abdirahman Mohamed Abdullahi ya yi maraba da ziyarar, inda ya ce a shiye suke su ƙarfafa hulɗa da Isra’ila.
Somaliya ta yi kira ga ƙungiyoyi kamar su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da Kungiyar Larabawa da da dai sauransu da su tsaya tare da ita wajen kare iyakokinta.
Kiraye-kirayen cewa na ajiye takara cin amanar ƴan Najeriya ne - Atiku
Asalin hoton, Atiku Abubakar/X
Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya ajiye takara a yaƙin neman shugabancin kasa ƙarkashin jam’iyyar haɗaka ta ADC, yana mai cewa hakan cin amanar ‘yan Najeriya ne.
Sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na ganin Atiku ya ajiye takara zai goyi bayan manufofin kama-karya ne kawai tare kuma da tauye hakkin dimokuradiyya a Najeriya.
Sanarwar ta ce a cikin shekaru kusan uku da suka gabata, ‘yan Najeriya sun fuskanci wahalhalu masu tsanani sakamakon manufofin tattalin arziƙi a ƙarkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin mayar da siyasar Najeriya ta zama ƙarƙashin jam'iyya ɗaya ta hanyar raunana jam'iyyun adawa.
Sanarwar ta kara da cewa "Jam’iyyar ADC za ta ci gaba da gudanar da tsarin tsayar da ɗan takararta kuma duk wani matsin lamba daga APC ko masu tsoma baki daga waje ba zai yi tasiri ba saboda ba su da ikon yin zagon ƙasa kan wanda ADC za ta tsayar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Yadda maganar sauya sheƙar tsohon Ministan Tsaro, Badaru ta samo asali
Tsohon Ministan Tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sheka daga jam'iyyarsa ta APC mai mulkin kasar zuwa jam'iyyar hamayya ta ADC.
A wata sanarwa da tsohon ministan ya sanya wa hannu da kansa, ya ce wannan zancen, labarin kanzon kurege ne, kuma wani yunkuri ne kawai na bata masa suna, da kuma kassara harkar siyasarsa.
A tattaunawarsa da BBC wani hadimin tsohon ministan, Kwamared Abba Malami, ya ce su wannan labari ya zo musu ne ma da mamaki:
''Na farko dai babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana kuma ta zo mana da mamaki kwarai da gaske.
Ƴansanda sun ɗauke makeken bam ɗin da aka gani a jihar Neja
Asalin hoton, Zakari Adamu
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Neja ta kwance tare da ɗauke wani makeken bam da aka gani a dajin Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu.
A wata tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Mashegu, Umar Igade ya ce bayan samun kiran waya daga ƙauyen Zugurma, cewa an ga wani abu kamar bam a ƙasa "na kira DPO na wannan yanki, inda ya tura jami'an tsaro domin su duba gaskiyar al'amarin.
"Bayan da suka isa wurin sun tabbatar da cewa bam ne. Bam ne mai girma, guda ɗaya."
A baya-bayan nan an samu rahotanni daga wasu ƙauyuka a arewacin Najeriya kan yadda al'umma suke tsintar abubuwan fashewa, bayan wani hari da Amurka ta kai a ƙarshen watan Disamba kan wani yanki mai fama da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makami.
Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya ce ya zuwa yanzu ba su da tabbas kan ko wannan bam da aka tsinta na daga cikin waɗanda Amurka ta yi amfani da su wajen kai harin na ranar 25 ga watan Disamba.
Ya ce "jami'an tsaro sun dauki bam din kuma suna kan bincike, saboda haka su ne za su tabbatar mana ko irin bam din da aka gani ne a Sokoto da Kwara waɗanda Amurka ta yi amfani da su wajen kai hari."
"Masu warware bam sun zo daga Minna, sun kwance shi sun saka shi a mota kuma sun tafi da shi zuwa babban ofishin ƴansanda da ke garin Minna domin ci gaba da bincike," a cewar Igade.
Neja na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ƴan bindiga wadanda ke kai hare-hare kan ƙauyuka suna kashewa da garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa.
A cikin ƙarshen makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar ta Neja inda ake zargin sun kashe mutum sama da 40.
Kuma a cikin watannin da suka gabata ƴan bindiga sun kai hari kan ƙauyen Papiri, inda suka yi garkuwa da sama da mutane 200, waɗanda suka hada da ɗalibai da malamai, waɗanda daga baya aka sako su.
An daƙile yunƙurin jiyun mulki a Burkina Faso
Asalin hoton, Reuters
Hukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa sun gano tare da kuma daƙile wani shirin juyin mulki da aka tsara don kashe shugaban sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, da kawo rashin kwanciyar hankali a kasar a karshen mako da ya gabata.
Ministan tsaro ƙasar, Mahamadou Sana, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi a daren ranar Talata, inda ya nuna wani bidiyo da ke nuna yadda aka shirya kai hari ga shugaban kasar ko dai ta hanyar harbin shi kai tsaye ko kuma ta hanyar sanya bam a gidansa a daren 3 ga watan Janairu, kafin a kai farmaki ga sauran manyan jami’an soja da na farar hula.
Ministan ya kuma zargi tsohon shugaban kasar da aka hamɓarar a shekarar 2022, Laftanar Kanar Henri Damiba, da tsara juyin mulkin.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya tara sojoji da magoya bayansa fararen hula inda ya samu kudade kimanin CFA miliyan 70 daga Côte d’Ivoire sannan ya tsara lalata sansanin harba jirage marasa matuƙa kafin sojojin ƙasashen waje su shiga tsakani.
Ministan ya ce an kama mutane da dama kuma ana ci gaba da bincike, inda za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Tun bayan karɓar mulki a 2022, Traoré ya fuskanci yunƙuri da dama na juyin mulki da tashin hankali daga kungiyoyi masu iƙirarin jihadi.
Sojoji sun ceto mutum shida da aka sace a Kajuru da ke Kaduna
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun samu nasarar ceto mutum shida da aka sace a yankin Kajuru/Kujama na jihar Kaduna.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, sojojin sun gudanar da aikin ceton ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, a matsayin wani ɓangare na manyan jerin ayyukan tsaro da aka tsara a yankunan Chikun, Kajuru, Kachia da Kagarko, ciki har da iyakokin al’ummomin da ke kusa da kan iyakar Kauru.
Sanarwar ta ce aikin ya mayar da hankali ne kan taƙaita ayyukan ‘yan bindiga da masu aikata laifuka a yankunan.
Rundunar ta ce, bayan samun kiran gaggawa kan motsin ‘yan bindiga a kusa da tsaunukan Kasso, sojojin da ke gudanar da aikin share fage a yankin Kujeni suka hanzarta zuwa wurin.
"Da isarsu, sojojin suka yi artabu da ‘yan bindigar, wanda ya tilasta musu tserewa cikin daji inda dakarun suka bi sawunsu nan take, har suka samu nasarar kuɓutar da mutanen shida da aka sace," in ji sanarwar.
Rundunar ta ce an mika mutanen da aka ceto ga wakilan ƙaramar hukumar Kajuru da majalisar masarautar Kajuru domin mayar da su hannun iyalansu.
Kotu ta bayar da belin Abubakar Malami
Asalin hoton, Malami/
Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
Kwanakin baya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Amurka na shirin ƙwace Greenland
Asalin hoton, Getty Images
Fadar gwamnatin Amurka ta ce Shugaba Donald Trump tare da manyan jami’an gwamnatinsa na tattauna hanyoyi daban-daban da Amurka za ta iya mallakar yankin Greenland.
Fadar ta bayyana cewa amfani da ƙarfin soji na daga cikin zaɓuɓɓukan da ake duba.
Mai magana da yawun Shugaba Trump, Karoline Leavitt, ta ce shugaban ya fito ƙarara cewa wannan mataki na da nasaba da tsaron ƙasa, yana mai cewa zai taimaka wajen kange makiyan Amurka a yankin.
A nasa ɓangaren, Firaministan yankin ya yi maraba da sanarwar haɗin gwiwa da shugabannin Turai suka fitar, wadda ta jaddada aniyar kare dokokin duniya da ‘yancin cin gashin kai na Greenland, wanda ke ƙarƙashin ƙasar Denmark.
INEC ta gargadi jama’a kan shafin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi na bogi
Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta fitar da sanarwar gargadi ga al’ummar Najeriya dangane da wani shafin intanet na bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke iƙirarin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadin hukumar na shekarar 2026.
INEC ta bayyana cewa shafin ba shi da wata alaƙa da hukumar, tare da jaddada cewa dukkan bayanai da ƙididdiga ko takardun neman aiki da ke cikinsa ƙarya ne kuma an ƙirƙire su ne domin yaudarar jama’a.
Hukumar ta ce tana gudanar da ɗaukar ma’aikata ne kawai ta shafin ta na hukuma mai suna INECPRES.
Hukumar ta shawarci masu neman aikin da su riƙa tantance sahihancin duk wani bayani ta shafukanta na hukuma kuma su guji shafukan da ba su dace ba, tare da kaucewa bayar da bayanan sirri kamar BVN da takardun bayanan mutum ko bayanan asusun banki.
Hukumar ta kuma buƙaci duk wanda ya yi rajista a shafin ta bogi da ya dakatar nan take, ya sake nema ta hanyoyin da INEC ta amince da su.
Ƙasashen Turai sun cimma matsaya kan tsaron Ukraine a Paris
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yaba da matsayar da ƙawayen ƙasarsa suka cimma a taron da aka gudanar a Paris, a yayin da ake ƙoƙarin samar da daftarin shawarwari na bai ɗaya da Amurka za ta gabatar wa Rasha.
Zelensky ya ce wannan ci gaba na nuna yadda Turai da gamayyar masu aniya ke aiki tare domin tabbatar da tsaron Ukraine, ko da za a cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta.
Wakilin musamman na Shugaba Trump, Steve Witkoff, ya bayyana goyon bayansa ga matakan, yana mai cewa an tsara su ne domin hana duk wani sabon hari ko ƙarin tashin hankali a Ukraine.
A cewar bayanan yarjejeniyar, Faransa da Birtaniya sun amince su sanya hannu kan alƙawarin tura dakaru a matsayin karonsu na sojojin taron dangi na ƙasashe, bayan dakatar da yaƙin.
Sai dai har yanzu akwai muhimman batutuwa da ba a kammala tattaunawa a kansu ba, yayin da a baya Rasha ta yi watsi da wasu daga cikin shawarwarin, ciki har da batun tura sojojin ƙungiyar NATO zuwa Ukraine. do a headline for this different from Zelensky ya yaba da shirin tsaron Ukraine bayan taron Paris.
Za mu riƙa karɓar gangar mai kimanin miliyan 50 daga Venezuela - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce hukumomin riƙon-ƙwarya na Venezuela za su rika ba wa Amurkar, gangar mai tsakanin miliyan 30 zuwa 50 na abin da ya kira man da aka sanya wa takunkumi.
A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce za a riƙa sayar da man ne a farashin kasuwa - sannan kuma shi zai sarrafa kuɗin inda ya ce, kudin zai amfani al'ummar Venezuela da kuma Amurka.
Hukumomin Venezuelar dai ba su tabbatar da wannan shiri ba.
Tun da farko, shugabar rikon kwarya ta Venezuelar, Delcy Rodriguez, ta ce babu wani dan ƙasar waje da ke mulkin kasarta.
PDP ko APC: Wace jam'iyya ce ta fi ƙarfi a lokacin ganiyarta?
Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na cigaba da tumbatsa da yin kane-kane a harkokin siyasar ƙasar.
Manya da kananan ‘yan siyasa, daga gwamnoni zuwa sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi na jam’iyyun adawa na ta tururuwar komawa cikin ta, lamarin da ya kai ga wasu ‘yan siyasa na fargabar cewa kasar na neman komawa tsari na jam’iyya daya tilo.
Sai dai wasu sun nuna cewa duk ƙarfin da APC take da shi a yanzu, a baya PDP ma ta yi irin ƙarfin, ta tumɓatsa kafin ta fara fashewa, har ta kai matsayin da take a yanzu na rashin tabbasi.
Duk da cewa PDP ce ta zo ta biyu a babban zaben kasar na 2023, amma ya zuwa yanzu ta yi asarar wasu daga cikin jigoginta, kamar dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar, da wanda ya mara masa baya a takarar, Ifeanyi Okowa, inda suka sauya sheka.
Masu bibiyarmu, Barkanmu da war haka, da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.
Kamar kullum, a yau ma wannan shafi na Kai Tsaye zai kawo rahotanni da labarai na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran kasashe makwabta.
Sai ku ci gaba da bibiyar mu domin sanin halin da duniya take ciki a yau Laraba.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.