Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/12/2025.
Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Channels TV
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Duk da cewa babu cikakken bayani game da ziyarar, wasu a ƙasar na ganin ba ta rasa nasaba da batun shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da rai cikin watan da ya gabata.
A baya-bayan nan ne jaridun ƙasar suka ruwaito cewa gwamnan Abia ya kai ziyara da jagoran Biafran a gidan yarin Sokoto da yake ɗaure.
A lokacin ziyarar zuwa Villa, gwamnan Abin na tare da ƙanin Nnamdi Kanun, Emmanuel Kanu da kwamishinan shari'ar jihar, Ikechukwu Uwanna (SAN) da wasu jami'an gwamnatin jihar, kamar yada gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Leo ya gargaɗi gwamnatin Trump kada ta yi amfani da ƙarfin soji wajen sauya gwamnatin Venezuela.
Leo na 14 - fafaroma na farko da aka haifa a Amurka - ya ce zai fi kyau idan Amurka za yi amfani da lalama ko matsin tattalin arziki idan ana son kawo sauyin.
Shugaba Trump na sanya idanu kan dakarun Amurka da aka jibge a yankin Caribbean, inda ya zargi gwamnatin Nicolas Maduro da hannu a sakafar miyagun ƙwayoyi, wani Mista Maduro ya musanta.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Manyan hafsoshin sun isa fadar shugaban ƙasar da maraicen yau Talata, inda suka yi ganawa har ta tsawon sa'o'i uku, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Ba a dai bayyana dalilin ganawar ba, amma wasu na ganin ba ta rasa nasaba da matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Ganawar tasu na zuwa ne sa'o'i bayan Tinubu ya sanar da naɗin tsohon babban hafsan tsaron ƙasar, CG Musa a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan saukar Badaru.
A cikin watan da ya gabata ne ƴanbidindiga suka sace wasu ɗalibai a makarantun jihohjin Kebbi da Neja, wani lamari da ya tayar da hankula a ƙasar.
Shugaban Serbia Aleksandar Vucic ya ce matatar mai ɗaya tilo da ke ƙasar na shirin rufewa.
Ya ce har yanzu Amurka ba ta amshi buƙatar da aka gabatar mata ba na ɗage takunkuman da ta sanya kan matatar ta NIS, wadda mallakin Rasha ce.
Amurka ta lafta wa matatar takunkumi a tsakiyar watan Oktoba, wanda ke nufin ta daina samun ɗanyan mai ta bubutun Croatia.
Matatar mai ta NIS ce ke samar wa Serbia fiye da kashi 80 cikin 100 na man fetir da man dizel da kuma bakiɗaya man jirgin sama da wasu na'uinkan mai.
Rahotonni daga Tunisiya na cewa an kama ɗaya daga cikin fitattun ƴan hamayyar ƙasar, Ayachi Hammami.
Bayanai na cewa kamen wani ɓangare ne na aiwatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar da aka yanke masa kan haɗin baki domin yi wa tsaron ƙasar zagon ƙasa.
Iyalansa da lauyansa sun ce an tsare shi kwanaki bayan ya kasance cikin wasu jagororin hamayya 40 da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke musu hukucin ɗaurin shekara 45.
Masu suka sun yi Allah wadai da ɗaurin, inda suke zargin shugaban ƙasar, Kais Saied a matsalar mai nuna alamun mulkin kama karya.

Asalin hoton, Kano State Gov.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara wasu yankunan jihar da ke fama da hare-haren ƴanbindiga.
Yayin da yake jawabi a ƙauyen Kamaye na ƙaramar hukumar Tsanyawa, gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda ya ce ƴanbindiga daga Katsina ke tallakawa jihar domin ƙaddamar da hare-hare da sace mutane.
''Abin takaici ne yadda ƴanbindiga za su yi sulhu a Katsina amma su tsallako mana Kano su riƙa kashe mana mutane da sace wasu''.
Gwamnan wanda ke tare da manyan jami'an tsaron jihar ya nemi haɗin kan al'ummar yankin wajen bai wa jami'an tsaro bayanan sirri domin magance matsalar.
''Ina kira gare ku, ku saka idanu tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su bayanan sirri kan ƴanbindigar da zarar kun samu labarin zuwansu'', in ji Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan ya kuma jajanta wa al'ummar yankin kan kashe-kashen da ƴanbindigar suka yi tare da sace wasu a yankunan.

Asalin hoton, Kano State Govt
Hukumar zaɓen Guinea-Bissau ta ce ba za ta iya wallafa sakamakon zaɓen shugaban ƙasar ba saboda yadda wasu jam'ian tsaro sanye da abubuwan rufe fuska suka lalata ƙuri'u da takardun rubuta sakamakon a lokacin juyin mulkin makon da ya gabata.
Sojoji sun ƙwace mulkin ƙasar gabanin bayyana sakamakon zaɓen.
Ƙungiyoyin fararen hula da ƴan hamayya sun zargi shugaban ƙasar da aka hamɓarar, Umaro Sissoco Embaló,da kitsa juyin mulki saboda ya hango faɗuwa a zaɓen.
Kawo yanzu dai Mista Embalo - wanda ya tsere zuwa Congo - bai ce komai ba game da zarge-zargen.

Asalin hoton, EPA
Shugaba Putin na Rasha ya ce buƙatun da ƙasashen Turai suka gabatar kan sharaɗin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ba ababen amincewa ba ne.
Mista Putin ya ce Rasha ya ce ba ta son yaƙi da manyan ƙasashen Turai, amma a shirye take a gwabza idan suna buƙatar hakan.
Jakadan Trump na musamman, Steve Witkoff tare da surukin Trump, Jared Kushner na Fadar Kremlin domin tattaunawa kan sharuɗɗan yarjejeniyar.
Amurka da jami'an Ukraine, bisa goyon bayan Turai sun sake nazarin sharuɗɗan daga na ainihin da Rasha ta sani tun da farko.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce a shirye yake ya cimma babbar manufarsa ta kawo ƙarshen yaƙin, kuma dole a tilasta wa Rasha domin amincewa da hakan.
Tun da farko a yau ne Fadar Kremlim ta ce sojojin Rasha sun kammala ƙwace garin Pokrovsk mai muhimmanci a Donbas, bayan shafe fiye da shekara guda ana gwabzawa.
To amma dakarun Ukraine sun dage cewa suna ci gaba da fafatawa a yankin.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tura sunan Janar Christopher Gwabin Musa ga Majalisar Dattawa domin ta amince da naɗa shi a matsayin sabon ministan tsaron ƙasa.
Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin da tsohon minista, Badaru Abubakar ya yi a ranar Litinin, wanda hakan ya bar gurbin da ake buƙatar cike wa cikin gaggawa.
A cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken tabbacin sa kan ƙwarewar Janar Musa, yana mai cewa zai iya jagorantar ma’aikatar tsaro tare da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.
Janar Musa, wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya shafe lokaci mai tsawo yana gudanar da manyan muƙamai a rundunar sojin Najeriya tun bayan kammala karatunsa a NDA a shekarar 1991.
Majalisar Dattawa na sa ran fara duba tabbatar da nadin nasa a makonni masu zuwa.

Asalin hoton, Godswill Akpabio
Majalisar Dattawa ta sanar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta, musamman na tsaro da na tattara bayanan sirri sakamakon ƙalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga kwamitin zaɓe na Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
A sabon tsarin, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi daga kujerar kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri makon da ya gabata.
Haka kuma, Sanata Mustafa Musa daga Yobe ya karɓi ragamar shugabancin kwamitin tsare-tsare na Kasa.
A bangaren kwamitin Sojin Sama kuma, Sanata Osita Ngwu daga Enugu wanda shi ne mataimakin shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa ya zama muƙaddashin shugaban kwamitin bayan rashin lafiya ta hana tsohon shugaban ci gaba da aiki.
Majalisar ta ce waɗannan canje-canjen na da nufin ƙarfafa aikin sa ido da inganta martani kan batutuwan tsaro da ke tasowa a fadin ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Rikici ya sake kunno kai tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun RSF, yayin da ɓangarorin biyu suka yi iƙirarin mallakar garin Babanusa da ke kudu maso yammacin jihar Kordofan.
RSF ta bayyana a jiya ta Telegram cewa ta ƙwace Babanusa da sojoji ke da iko da shi amma sojin Sudan sun ƙaryata hakan a yau ta Facebook, suna cewa sun daƙile harin da aka kai musu.
RSF ta yi wa garin Babanusa, wanda shi ne babbar wurin da sojin ƙasar ke iko da shi ƙawanya tsawon sama da shekaru biyu.
Ana zargin ta da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ayyana a ranar 24 ga Nuwamba ta hanyar yawan kai hare-hare har garin ya faɗi.
Sai dai RSF ta musanta hakan, tana zargin sojin Sudan da kai mata hare-hare sau takwas a lokacin tsagaita wutar.
RSF ta ce, “Wannan hari shi ne karo na takwas da soji suka karya yarjejeniyar kwanan nan, wanda ke nuna rashin bin ka’idojin jin kai da doka.”
Rundunar sojin Sudan kuwa ta ce tsagaita wutar da RSF ta ayyana “dabarar yaɗa labarai ce don yaudarar al’umma na cikin gida da na ƙasashen duniya.
A watannin baya-bayan nan, yaƙi ya fi karkata zuwa yankin Kordofan na tsakiya, wanda ke da matukar muhimmanci ga ɓangarorin biyu a rikicin da ke ci gaba da addabar kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin kula da Kasafin Kudin Majalisar Wakilai ta Amurka zai gudanar da wani taron hadin gwiwar majalisa a ranar Talata don duba zargin azabtarwa da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
Dan majalisar Amurka Riley Moore ne ya sanar da hakan a shafinsa na X inda ya tabbatar da cewa za a jagoranci taron ne da Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai kuma Shugaban Kwamitin Kula da Tsaron Kasa, Mario Díaz-Balart.
Za a samu hadin kai daga wasu membobin Kwamitin Kasafin Kudi da kuma Kwamitocin Harkokin Waje da Sabis na Kudi in ji sanarwar.
Za a tattara bayanai don shirya cikakken rahoto kan kisan Kiristoci a Najeriya da matakan da majalisa za ta ɗɗauka wajen shawo kan lamarin.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Najeriya kan tsaro, bayan ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da kuma ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban tawagar ECOWAS ya nemi shugabannin juyin mulki a Guinea-Bissau da su koma hanyar da ƙudin tsarin mulkin ƙasar ta yarda da ita nan da nan wato mulkin farar hula kuma su bayyana sakamakon zaɓe.
Shugaban Sierra Leone, Julius Maada Bio, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya yi Allah wadai da kifar da tsohon Shugaba ƙsar, Umaro Sissoco Embalo.
Shugaba Bio ya ce, “Mun sake tabbatar da jajircewarmu wajen dawo da tsarin mulkin doka.” Sai dai Shugaba na wucin gadi, Janar Horta N’Tam, ya ce sun yi juyin mulkin ne don hana ‘yan ta’adda shafar tsarin dimokuradiyya.
An dakatar da Guinea-Bissau daga harkokin ECOWAS da AU, yayin da sojoji suka kafa gwamnati mai membobi 28 ta riƙon ƙwarya don tafiyar da ƙasar.
Za a yanke hukuncin makomar ƙasar a taron shugabannin ƙasashen ECOWAS a ranar 14 ga Disamba.

Shugaban Hong Kong, John Lee, ya umurci kafa wani kwamitin musamman don bincikar musabbabin gobarar da ta kashe aƙalla mutum 151.
A ranar Laraba da ta gabata ne gine-ginen hasumiyoyi bakwai daga takwas a cikin ginin Wang Fuk Court – wanda ake yi masa manyan gyare-gyare suka kama da wuta.
Masu bincike sun gano cewa wani rufin kariya da aka yi wa gine-ginen bai cika ƙa’idar hana gobara ba.
An kama mutum akalla 13 bisa zargin laifin kisan rai, ciki har da daraktocin wani kamfanin gine-gine.
Wannan gobara ce mafi muni da birnin ya gani cikin shekaru fiye da 70, kuma adadin mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa yayin da jami’an ke ci gaba da aikin ceto.
Shugaba Lee ya ce kwamitin zai kasance ƙarkashin jagorancin alƙalin kotu kuma zai gudanar da “gyare-gyare masu zurfi”, inda ya kara da cewa zai yi aiki don “hana faruwar irin wannan masifar a nan gaba.”

Asalin hoton, Getty Images
An ruwaito cewa Niger ta fara sayar da uranium da aka kwace daga tsofaffin ma’adinan da kamfanin Orano na Faransa ke gudanarwa, kamar yadda shafin LSI Africa ya bayar da rahoto.
Wannan mataki ya biyo bayan furucin shugaban mulkin soja, Janar Abdourahmane Tchiani, a kan gidan rediyon gwamnati Tele Sahel a ranar 30 ga Nuwamba, inda ya ce kasar na da hakkin ta na sarrafa albarkatun kasar kuma ta sayar wa duk wanda yake son siya cikin ‘yanci da ka’idojin kasuwa.
Wannan na nuna ƙin yarda da hukuncin da ICSID, hukumar sulhu ta zuba jari ta Bankin Duniya, ta yanke a watan Satumba, wacce ta haramta sayar da uranium daga ma’adinan da ake rigima a kansu.
A ranar 27 ga Nuwamba, kamfanin Orano ya bayyana cewa ci gaba da jigilar uranium da suka sarrafa ba bisa ƙa'ida bane kuma ya yi alƙawarin ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda ya shiga mu’amala da makamashin uranium din.

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta ce sojojinta sun ƙwace ikon wani gari mai muhimmanci a Pokrovsk da ke gabashin Ukraine, kodayake ba a tabbatar da sahihancin rahoton ba.
Ma'aikatar tsaron Rashan ta wallafa wani bidiyo wanda ya nuna dakarunta sun ɗaga tutarsu a tsakiyar wani dandali da ke Pokrovsk.
A watan daya gabata ne Ukraine ta ƙara tura sojoji yankin domin dakile hare-haren Rashan kuma sannan har yanzu Ukraine bata amince cewa Rashan ta ƙwace ikon yankin ba.
Sanarwar Rashan ta zo ne a yammacin ranar da za ayi wata ganawa a Moscow tsakanin shugaba Putin da kuma wakilin Donald Trump na musamman, Steve Witkoff.

Asalin hoton, facebook/AA Sule
Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na kafa rundunar ‘yan sandan jiha idan kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da hakan.
Kalaman sun fito ne daga kwamishinan tsaro da harkokin sauran al’amura, CP Usman Baba yayin wani taron manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce tun daga zuwan gwamnatin jihar a 2019, an fifita harkar tsaro, tare da ba rundunonin tsaro tallafi na ababen hawa da kayan aiki da sauran kayan aikace-aikace.
Ya jaddada cewa gwamna Abdullahi Sule ya ƙuduri aniyar tabbatar da cewa jihar ta kasance amintacciya ga masu zuba jari da kuma wuri mai cike da zaman lafiya ga al’ummarta.
Haka kuma, ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa makarantu a yankunan da ake ganin barazana ce, da manyan wuraren ibada a babban birnin jihar da kuma dukkan ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Game da matsalar garkuwa da mutane, kwamishinan ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro, ‘yan sa kai da masu sa ido a unguwanni domin magance lamarin.
Ya gargadi masu aikata laifi cewa jihar za ta zama “wuri mai zafi” gare su, inda duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Asalin hoton, X/Mohammed Badaru CON mni
Ministan tsaron Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙaminsa, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanguga ya fitar ranar Litinin da daddare, ya ce Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar ya aika wa shugaba Bola Tinubu.
Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.
Hakan na zuwa ne a wani lokaci da kasar ke fama da sake dawowar garkuwa da mutane a yankin arewacin kasar.

Asalin hoton, Adeleke/X
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, wacce ta ba shi dama ya zama sanata sannan daga baya gwamna.
Adeleke ya sanar da hakan ne ta shafinsa na X a daren Litinin, inda ya wallafa kwafin takardar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 4 ga Nuwamba, 2025.
A cikin takardar, Adeleke ya bayyana rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a matsayin dalilin ficewarsa.
Ya rubuta cewa: “Sakamakon rikicin da jam'iyyar ke fama da shi, na yanke shawarar ficewa daga cikinta daga yau.”
Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta bashi ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Osun West (2017–2019) da kuma Gwamnan jihar Osun.
Adeleke dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba bayan barin PDP.