Ƙarshen rahotonni
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Talata.
Muna tafe da wasu rahotonnin gobe da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/03/2025
Ibrahim Haruna Kakangi da Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Talata.
Muna tafe da wasu rahotonnin gobe da safe.
An tambayi Sakataren Harkokin Wajen Amurka game da martanin da suke samu daga Rasha game da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Rubio ya ce "Ukraine ta shirya dakatar da buɗe wuta da kuma fara tattaunawa".
Ya jaddada cewa yana fatan Rasha za ta yarda da yarjejeniyar, amma idan suka ƙi "to mun san wanda ba shi son zaman lafiya".
Ya ce Shugaba Trump ya nanata cewa burinsa shi ne a daina mutuwa, a daina harbe-harbe.
Da aka tambaye shi game da ko akwai wa'adi, sai ya ce suna fatan su cimma hakan "da gaggawa".
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya faɗa wa manema labarai cewa Amurka ta miƙa tayin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha ta wata ɗaya.
Ya Ukraine ta amince da yarjejeniyar, wadda za ta bayar da damar tattunawar kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya.
Ya bayar da sanarwar ne jim kaɗan bayan tattaunawa da tawagar Amurka da ta Ukraine suka yi a Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci hukumar sadarwa ta ƙasar NCC da ta umurci kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa.
Majalisar ta cimma matsayar ne bayan wani ƙudiri da ɗanmajalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki, ya gabatar.
Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Najeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar ba.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai "addini", inda manyan addinan ƙasar suka haramta batsa da kuma nuna tsiraici.
Ɗanmajalisar ya kuma bayyana gargaɗin da masana halayyar ɗan'adam suka yi kan mummunan tasirin da kallon bidiyon batsa ke da shi, ciki har da yiwuwar karfafa yin zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon ta.
Majalisar ta kuma buƙaci hukumar NCC ta hukunta duk kamfanin samar da intanet da ya ƙi bin umarnin.

Asalin hoton, PSC Nigeria
Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ƴansandan jihar Kano, inda zai maye gurbin CP Salman Garba Dogo wanda ya samu ƙarin girma zuwa mataimakin sifeto janar na ƙasa (AIG).
Kafiin naɗin nasa, CP Bakori ya kasance kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen binciken kisan jama'a a hedikwatar ƴansandan ƙasar da ke Abuja.
Shugaban hukumar ƴansandan, DIG Hashimu Argungu mai ritaya ya nemi sabon kwamishinan na Kano da ya tabbatar an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Ya ƙara da cewa ya yi ƙoƙarin wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansa wajen tabbatar da an daƙile ƙaruwar aikata laifuka a jihar mai yawan jama'a.
Jihar Kano dai na fama da matsalolin dabanci da ƙwacen waya da sace-sace da kuma a baya-bayan nan rikicin masarautar Kano da ya janyo al'umma suka sauya tunaninsu kan rundunar ƴansandan jihar.

Asalin hoton, Nigeria Police
Mutum 1,010 ne aka kashe a faɗin Najeriya sakamakon hare-haren 'yanbindiga da na jami'an tsaro cikin watan Fabrairun da ya gabata, a cewar rahoton kamfanin Beacon Security and Intelligence.
Alƙaluman na watan Fabrairu sun nuna cewa an samu raguwar sace mutane zuwa 955 daga 1,101 a watan Janairu, amma kuma kashe-kashe ya ƙaru - bayan samun 991 a watan Janairu.
Sabon rahoton na watan Fabrairu ya ce daga 1 zuwa 28 ga watan, an kai hare-hare ko kuma tashin hankali 716 jimilla, waɗanda suka jawo sacewa ko kuma garkuwa da mutum 955.
Kazalika, hare-haren sun ragu da kashi 2.19 idan aka kwatanta da watan Janairu, inda aka samu 732.
Mutum 592 (kashi 58.6 cikin 100) na mutanen da suka mutu fararen hula ne, inda 'yanbindiga suka kai hari 478 (kashi 66.76), jami'an tsaro suka kai 177 (24.72), in ji rahoton.
Jihohin Katsina, da Kaduna, da Neja, da Zamfara, da Sokoto, da Borno, da Kebbi ne suka fi fuskantar ƙaruwar hare-hare a watan, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 26 sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Aliero da Gwandu da kuma Jega.
Kwamishinan lafiya na jihar Musa Isma'ila, shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Birnin Kebbi a yau Talata.
Isma'ila ya ce an kuma samu mutum 248 da ake zargin sun kamu da cutar.
Ya ce gwamnatin jihar ta ware naira miliyan 30 don sayan magunguna da kuma sauran kayayyaki domin taimakawa a ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.
Baya ga kisa, illar da cutar ke yi wa waɗanda suka kamu da ita sun haɗa da makanta, da kurmancewa da farfaɗiya da kuma wasu ciwuka na daban.
Alamomin cutar sun haɗa da tsananin tari da ciwon kai da wuya da kuma amai.

Asalin hoton, Reuters
Ƴantawayen Ƙurdawa waɗanda ke iko da arewa maso gabashin Syria sun saka hannu kan yarjejeniyar shiga gwamnatin Syria, a cewar fadar shugaban ƙasar.
Yarjejeniyar, wadda ta kunshi dakatar da faɗa a cewar dakarun Syria na SDF da Amurka ke goyon baya, za ta kuma tabbatar da cewa an miƙa dukkan iyakokin yankin da filin jirgin sama da kuma filayen mai da na iskar mas masu muhimmanci.
Gwamnatin Syria ta kuma amince da Ƙurdawa marasa rinjaye "a matsayin masu muhimmanci a tsarin shugabancin ƙasar" kuma ta ba da tabbacin bai wa kowane ɗan ƙasar hakkinsa da wakilci da ya kamata a tsarin siyasa.
Kwamandan SDF Mazloum Abdi ya kira yarjejeniyar da "dama ta musamman na gina sabuwar Syria".
"Muna da zimmar samar da makoma mai kyau da za ta bai wa dukkan ƴan Syria hakkinsu da kuma cika musu burinsu na wanzuwar zaman lafiya," kamar yadda ya faɗa a shafinsa na X bayan saka hannu kan yarjejeniyar a Damascus ranar Litinin tare da shugaban ƙasar na wucin-gadi Ahmed al-Sharaa.
Yarjejeniyar na zama a matsayin babban mataki ga burin Sharaa na haɗa kan ƴan ƙasar bayan da ƙungiyarsa ta Sunni ta jagoranci boren da ya tumɓuke shugaba Bashar al-Assad a watan Disamba da kawo karshen yaƙin basasar ƙasar na tsawon shekara 13.
Hakan kuma zai rage barazanar rikici tsakanin SDF ɗin da makwaftanta Turkiyya da kuma wani ɓangare na tsohuwar ƙungiyar ƴan tawaye a Syria da Turkiyya ke mara wa baya mai alaƙa da gwamnati.
An yi ta murna bayan sanar da amincewa da yarjejeniyar a kan titunan birane da dama ranar Litinin da daddare, inda mutane da yawa suka nuna farin cikinsu a daidai lokacin da Syria ke fuskantar sauran barazana ga ɗorewarta.
Kashe-kashen ƴan Shi'a Alawiyyawa a baya-bayan a yammacin ƙasar yayin artabu tsakanin jami'an tsaro da kuma masu goyon bayan Assad, ya janyo kiraye-kirayen bai wa masu addini da kabilu marasa rinjaye kariya daga ƙasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS ta ce za ta samar da dakarun ko-ta-kwana domin daƙile ta'addanci da wasu laifuka da ake yi kan iyakokin ƙasashen yankin.
Ministan tsaron Najeriya Mohammad Badaru ya bayyana haka ne a yau Talata a taron kwamitin hafsoshin tsaron ƙasashen ƙungiyar karo na 43 a Abuja, babban birnin ƙasar.
Badaru ya kuma ce bunƙasar tattalin arziƙin yankin ya ta'allaƙa ne ga samun dawwamammen zaman lafiya.
Ministan tsaron ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar mambobin ƙungiyar su haɗa kan jami'an tsaronsu don tunkarar duk wata barazana ga yankin.
A ranar 29 ga watan Janairun 2025 ne dai ƙungiyar ta amince da ficewar tsoffin mambobinta uku, Burkina Faso da Mali da Nijar bayan sun buƙaci ficewa a shekarar da ta gabata.
Ƙasashen yammacin Afirka dai na ci gaba da fama da matsalar tsaro daga ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya da masu iƙirarin jihadi, lamarin da ake ganin yana kawo koma baya ga tattalin arziƙin yankin.

Asalin hoton, @officialEFCC
Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon kasa a Najeriya EFCC ta kama ƴan China huɗu da wasu ƴan Najeriya 27 bisa zarginsu da laifin haƙo ma'adinai ba bisa ƙai'da ba a jihar Filato.
Kakakin hukumar Dele Oyewale ne ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an kama mutanen ne a harabar kamfanin Jiasheng Nigeria Limited da ke Mangu a Jos.
Ya ce sun yi nasarar kama mutanen ne bayan samun sahihan bayanai da ke alaƙanta kamfanin da ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa ƙai'da ba.
Ya ƙara da cewa sun kuma wasu kayyayaki, ciki har da mota maƙare da buhuhunan albarkatun ƙasa na Monazite a harabar kamfanin.
Oyewale ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Najeriya ta cimma matsayar dakatar da ƙarin kuɗin da ake caji na cire kuɗi a na'urar ATM da kuma soke batun cire kuɗi kyauta daga ATM ɗin da ba na bankin mutum ba, wanda Babban bankin Najeriya CBN ya yi.
Ƙudirin wanda ɗan majalisa Marcus Onubun ya gabatar, ya janyo hankalin majalisar kan sanarwar CBN game da ƙarin.
Ƴan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda wannan ƙari zai ƙara takura wa tattalin arziƙin ƴan ƙasar.
Majalisar ta buƙaci CBN ya dakatar da tsarin gabanin yin tattaunawar da ta dace da kwamitocin kula da ayyukan bankuna da hada-hadar kuɗi da kuma cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe.
Tun a ranar 10 ga watan Fabrairun 2025 ne babban bankin ya sanar da cewa za a fara cazar kuɗi a duk lokacin da abokan hulɗar bankuna suka cire kuɗi daga na'urar ATM ɗin da ba ta bankinsu ba, kuma bankin ya ce za a fara aiwatar da hakan ne daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.
Wannan lamari ya janyo ce-ce-kuce a tsakanin ƴan ƙasar da ke fama da mastin tattalin arziƙi da kuma tashin farashin kayan masarufi.
Ministan tsaron Faransa ya yi watsi da batun kassara rundunar sojin Ukraine a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya.
Sebastien Lecornu ya shaida wa wani taron shugabannin sojin ƙasashen Turai da na NATO da ake yi a Paris cewa har yanzu sojojin Ukraine su ne ''babban tabbacin tsaron ƙasar''.
Rasha na so a kassara sojojin Ukraine - wani abu da Kyiv ta ƙi amincewa da shi kai-tsaye.
Ana sa ran tattaunawar da ake yi a taron zai haɗa da yadda kila ƙasashen Turai za su taimaka wajen haɗa dakarun wanzar da zaman lafiya.
Fadar Kremlin ta ƙi amincewa da shirin jibge dakaru daga ƙasashen ƙungiyar NATO a Ukraine.

An aika wata ƴar TikTok ƴar Indonesia gidan yari bayan ta yi wa hoton annabi Isah shaguɓe tana cewa ya yanke gashin kansa.
Ratu Thalisa, wata musulma da ta sauya jinsi, ta yi hakan ne a matsayin martani ga kalaman wani, a lokacin da ta ke bidiyo kai-tsaye a shafin TikTok inda ya ce mata ta yanke gashin kanta domin ta yi kama da namiji.
Wata kotu a Sumatra ta yanke wa Thalisa hukuncin zaman gidan yari na kusan shekara uku saboda yaɗa kiyayya, ƙarƙashin dokar hana kalaman ɓatanci a intanet mai cike da sarƙaƙiya.
Fiye da mutane 400 ne aka hukunta a ƙarƙashin wannan dokar, akasari saboda yin saɓo.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Pakistan sun ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba da ke ɗauke da makamai sun kai hari kan wani jirgin ƙasa da ke ɗauke da ɗaruruwan fasinjoji a kudu maso yammacin ƙasar.
Wasu daga cikin fasinjoji da matuƙin jirgin sun samu raunuka.
Jirgin na Jaffar Express da ke ɗauke da aƙalla mutane 400, na hanyarsa na zuwa Peshawar daga Quetta da ke lardin Balochistan.
Wata ƙungiyar ƴan a-ware na Baloch ta ɗauki alhakin kai harin kuma ta ce ta yi garkuwa da wasu daga cikin fasinjojin.
Tuni dai jami'an tsaron Pakistan suka isa wurin da aka kai harin.

Asalin hoton, Manchester United
Ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da aniyarta ta gina sabon katafaren filin wasa - wanda zai iya ɗaukar masu kallo kusan 100,000 - Babu kuma wanda zai kai shi a faɗin Birtaniya.
Za a gina filin wasan ne kusa da filin wasanta na yanzu Old Trafford, kuma zai lakume kuɗi dala biliyan 2.5.
United na ɗaya daga cikin sanannun ƙungiyoyin kwallon kafa a duniya, sai dai ta samu koma baya a baya-bayan nan da kuma rashin kataɓus.
Ƙungiyar na da bashin da ya kai dala biliyan 1.3 a kanta a halin yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'ian kiwon lafiya a jihar Legas sun ƙaddamar da shirin riga-kafi na gaggawa bayan samun ɓarkewar cutar Diphtheria da ya yi sanadiyyar mutuwar wani ɗalibi mai shekara 12 a wata makarantar sakandare.
Aƙalla mutane 34 suka yi mu'amala da shi kuma ana sanya musu ido, yayin da ɗalibai 14 daga makarantar kwanan mai suna King's College suka nuna alamu kuma aka tabbatar da cewa 12 daga cikinsu na da cutar, inda tuni aka fara ba su magani.
A cewar ma'aikatar lafiya ta jihar Legas, yaron ya fara nuna alamu ne na ciwon maƙoshi da kuma zazzaɓi a cibiyar lafiya ta makarantar a ranar 22 ga watan Fabrairu, inda kuma ya rasu a ranar 6 ga watan Maris.
A yanzu haka an fara gangamin yi wa mutane riga-kafi musamman yara da jam'ian kula da lafiya na makarantar, wanda hukumomi ke ganin za a faɗaɗa shi zuwa jihar baki-ɗaya.
Wata takardar gargaɗi kan lafiya ta buƙaci mazauna jihar su mayar da hankali kan tsafta da kuma guje wa shiga cunkoson mutane kuma su garzaya asibiti da zarar sun fara jin alamu irin na cutar diphtheria.
Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar wa da alumma cewa babu buƙatar su tayar da hankalinsu ganin cewa ana iya ƙoƙari wajen daƙile ɓarkewar cutar, kuma za a ci gaba da ɗaukar matakai domin kare su daga kamuwa da ita.
A shekarar 2023 ne aka samu ɓarkewar cutar diphtheria mafi girma a Najeriya inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 600 akasari yara, kuma cutar ta shafi jihohi 19 cikin 36 da ke ƙasar.

Asalin hoton, AFP
Uganda ta tura dakaru na musamman Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, yayin da zaman tankiya ke ƙara tsananta tsakanin Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar.
Shugaban sojin Uganda Janar Muhoozi Kainerugba ne ya tabbatar da hakan a yayin da ake samun ƙaruwar fargaba na yiwuwar komawa yaƙin basasa.
Rikice-rikicen baya bayanan, da kuma kama ministoci biyu da manyan jam'ian soji masu goyon bayan Mista Machar ya sa an soma nuna damuwa kan ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya na 2018.
Yarjejeniyar ta kawo ƙarshen rikicin da aka shafe shekara biyar ana yi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 500,000.

Asalin hoton, Reuters
Mutane bakwai daga cikin tawagar jami'an kula da lafiyar shahararren ɗan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona kafin rasuwarsa za su gurfana gaban kotu a yau Talata saboda laifin kisa ba da gan-gan ba.
Maradona ya fara samun sauƙi bayan tiyatar da aka mishi gabanin mutuwarsa sakamakon samun bugun zuciya a shekarar 2020 a lokacin ya na da shekara 60.
Shekara ɗaya bayan hakan, masu gabatar da kara su ka ƙarƙare cewa mutuwarsa abu ne da za a iya guje mawa inda su ka ɗaura laifin kan sakaci.
Tawagar jam'ian kula da lafiyar sun ce Maradona ya ƙi amincewa a bashi kulawa, kuma ya kamata a ce ya zauna a asibitin na tsawon lokaci kafin ya tafi gida bayan tiyatar.
Shari'ar za ta saurari ba'asi daga shaidu fiye da 100, kuma a na sa ran cigaba da shari'ar har watan Yuli.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Philippines sun ce ƴansanda sun kama tsohon shugaban ƙasar Rodrigo Duterte jim kaɗan bayan ya sauka a filin saukar jirgin saman Manila a wani jirgin da ya taso daga Hong Kong.
Sun ce an tsare shi ne sakamakon sammacin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar dangane da ƙazamin yaƙin da ya yi da miyagun kwayoyi na tsawon shekaru bakwai da ya fara a shekara ta dubu biyu da goma sha shida.
A lokacin dai ya sha alwashin kawar da fataucin miyagun kwayoyi, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa wani abu daban, inda ake zargin ƴansanda da kashe dubban mutane, ciki har da waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu.
Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da Oyo da Kogi da Nasarawa da kuma Benue.
Sauran sun haɗa da Enugu da da Anambra da Abia da Ebonyi da Cross River da birnin tarayya Abuja.
Sai kuma Taraba da Adamawa da Plateau da Kaduna da Zamfara da kuma Sokoto.
Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3.
Ta kuma shawarci al'umma da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin - su kuma yi amfani da fanka da na'urar sanyaya ɗaki da kuma zama a wurare masu inuwa.