Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/11/25

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/11/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Akwai masu cin amanar ƙasa a majalisar Amurka - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya bayyana wasu 'yan majalisar Amurka na jam'iyar Democrat a matsayin masu cin amanar kasa, da kuma ya dace a yanke wa hukuncin kisa.

    'Yan majalisar sun bukaci jami'an sojin kasar su bijirewa duk wani umurnin kai hari wata kasa da ya sabawa doka.

    Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta yana zargin 'yan siyasar shida da cewa sun yi kalaman da ya dace a dauki mataki mai tsauri a kansu ta hanyar zaratas musu da hukuncin kisa.

    'Yan majalisar na jam'iyyar Democrats sun fitar da wani bidiyo kwanan nan inda suke cewa kundin tsarin mulkin Amurka na fuskantar barazana.

    To sai dai ba su yi karin haske akan umurnin da suka nemi a bijirewa ba.

  2. Ƴan jarida sun gudanar da zanga-zanga a Tunisia

    Tunisia

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan jarida a Tunisiya na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a kusa da a fadar gwamnati, da ke babban birnin kasar Tunis.

    Masu zan-zangar na neman a kawo karshen abin da suka kira cin zarafin 'yan jarida tun daga lokacin da shugaban kasar Kais Saied ya karbi mulki a shekarar 2021.

    Sun fito dauke da kwalaye da aka yi wa rubutu, a lokaci guda suna raira wakokin da ke ɗauke da saƙonni ciki har da cewa 'aikin jarida ba laifi ba ne'.

    Ƴan jarida a Tunisiya dai na yawan bayyana yadda gwamnati ke tauye 'yancin watsa labarai tun bayan zanga-zangar kasashen Larabara da ta kifar da gwamnatin Zainil Abidine Ben Ali a 2011.

    Sai dai gwamnatin Tunisiya ta musanta ana tauye 'yancin 'yan jarida a kasar.

  3. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 40 a Vietnam

    Vietnam

    Asalin hoton, Vietnam Red Cross

    Jami'an agaji a Vietnam sun yi nasarar ceto mutanen da suka makale a saman rufin gidaje bayan aukuwar wata gagarumar ambaliya a 'yan makonnin nan.

    Hukumomi sun ce fiye da mutum 40 ne ambaliyar, wadda mamakon ruwan sama ta janyo a ƙasar ta kashe.

    Ruwan saman ya sauka ne da karfi hade da iska, lamarin da ya haifar da ambaliyar da ta mamaye garuruwa da dama da ke kusa da gabar tekun Nha Trang.

    Masu aikin ceton na ci gaba da neman wadanda suka bace a yankunan da ke da matukar hadarin shiga sakamakon zaftarewar laka.

  4. Mun karɓi daftarin kawo ƙarshen yaƙi da Rasha - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ya samu daftarin tsare-tsaren tattaunawa daga Amurka inda aka nemi kasarsa ta rungumi shirin kawo karshen yakin da take yi da Rasha.

    Wani bayani da ofishin Mista Zelensky ya fitar ya ce Washington ta yi amannar cewa tattaunawar neman tsagaita wutar za ta haifar da alfanu.

    Kawo yanzu dai ba a fitar da manufar shirin a bainar jama'a ba, amma a cewar wasu rahotanni matakin na da alaka da matsin lambar da Rasha ke yi na ganin an tsagaita wuta .

    Ofishin Mista Zelensky ya ce a shirye suke game da batun tattaunawa, kuma Ukraine ta gabatar da muhimman bukatunta a yayin ganawarsu da jami'an Gwamnatin Amurka.

  5. An yi garkuwa da manoma a Kwara kwana ɗaya bayan hari a coci

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahara sun sake kai wani harin a jihar Kwara, inda suka yi garkuwa da aƙalla manoma guda huɗu a ƙauyen Bokungi da ke ƙaramar hukumar Edu ta jihar Kwara.

    Wannan harin na zuwa ne kimanin awa 24 bayan wasu mahara sun kai hari a wani coci da ke garin Eruku na ƙaramar hukumar Ekiti a jihar, inda suka kashe mutum biyu, sannan suka yi garkuwa da wasu da dama.

    Wata majiya ta shaida wa tashar Channels cewa maharan sun yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke aiki a gonarsu ta shinkafa.

    "An yi garkuwa da mutum huɗu ne a lokacin da suke aiki a gona," kamar yadda majiyar ta bayyana.‎

    Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar ƴansandan jihar Kwara da gwamnatin jihar ba su fitar da sanarwa a hukumance kan harin ba.

  6. Harin Isra'ila ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin Gaza yau Alhamis ya yi sanadiyyar mutuwar mutum hudu ciki har da wata karamar yarinya.

    Sanarwar da wata asibiti da ke ƙarkashin ikon Hamas ta fitar ta ce daga jiya zuwa yau hare-haren Isra'ila ta sama sun kashe akalla mutum talatin da uku.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun ƙaddamar da harin ne saboda mayaƙan Hamas sun buɗewa dakarunsu wuta.

    Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce fiye da Falasdinawa ɗari uku ne Isra'ila ta kashe tun bayan soma yarjejeniyar tsagaita wuta.

  7. Gwamnatin Chadi na tauye haƙƙin ɗan'adam a rikicin mamona da makiyaya - Amnesty

    AMNESTY INTERNATIONAL

    Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Chadi ta gaza wajen kare fararan hula da rikicin makiyaya da manoma ke shafa a ƙasar.

    A wani sabon rahoton da ta fitar, Amnesty ta ce ana cin zarafin fararan-hula da raba ɗaruruwa da matsugunansu, baya ga wadanda ake kashe wa da jikkatawa.

    Kungiyar ta ce a rikice rikice 7 da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a larduna 4, waɗanda ake ganin matsalar sauyin yanayi ne ya ta'azzara samunsu, tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, alkalumanta sun nuna an kashe mutane 98 da jikkata sama da 100.

    Rahoton ya kuma ce jami'an tsaro ba sa kawo ɗauki a kan lokaci, kuma ba a hukunta waɗanda ke kashewa da sacewa da kuma lalata dunkiyoyin alumma, wanda ke ƙara nuna danniya da zalunci tsakanin al'ummomi.

  8. Kotu ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai

    Kanu

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

    Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samunsa da laifuka bakwai, waɗanda suke da alaƙa da ta'addanci da tunzura mutane.

    Alƙalin kotun, Mai Shari'a James Omotosho ya ce laifukan Kanu sun cancanci hukuncin kisa ne, amma ya ce kasashena ƙasashen duniya suna nuna rashin jin daɗi kan hukuncin kisa, sai ya mayar da hukuncin na ɗaurin rai da rai.

    Sai dai alƙalin ya ce a nema wa Kanu wani gidan yarin daban ba na Kuje da ke Abuja saboda a cewarsa yana da hatsari, sannan ya haramta masa amfani da waya da sauran na'urorin sadarwa, inda ya ce idan ma zama dole sai ya yi, "to ya kasance ana sa masa ido sosai," in ji alƙalin.

    Tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu sun haɗa da ta'addanci da tunzura jama'a su kashe ƴansanda da sojoji da kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta da kuma yaɗa farfagandar ta'addanci.

  9. An rufe makarantu a wasu ƙananan hukumomin Kwara

    Jami'an tsaro a makaranta

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun rufe makarantu a ƙananan hukumomi biyar da ke jihar sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a yankin.

    A cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar Lawal Olohungbebe ya fitar, ya ce hukumomin jihar sun ƙuduri aniyar daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane.

    Wannan matakin na zuwa ne bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai wani coci a jihar a ranar Talata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla masu ibada biyu, da sace gwammai.

    Ya kuma ce za a ci gaba da kulle makarantun ne har sai an samu rahoton tabbacin tsaro cewa lammura sun koma kamar yadda suke.

    Sanarwar ta ce an ɗauki matakin rufe makarantun ne a matsayin matakin tsaro na gaggawa, sakamakon yadda ake ganin ƴan bindiga na kai hari kan ɗalibai tare da sace su don neman kuɗin fansa.

    Ko a ranar Litinin da ta gabata, an sace wasu ɗalibai fiye da ashirin a wata makarantar kwana da ke jihar Kebbi, lamarin da ke ƙara nuna ta'azzarar matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar.

  10. An samu Kanu da laifukan ta'addanci

    Nnamdi Kanu

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu jagoran ƙungiyar ƴan awaren IPOB Nnamdi Kanu da aikata laifuka bakwai da ake tuhumarsa da su.

    Kanu shi ne jagoran ƙungiyar nan ta IPOB da ke fafutukar neman ɓallewa daga Najeriya, wanda ake tuhuma da laifukan ta'addanci da tunzura yin tashin hankali.

    Mai shari'ah James Omotosho ne ke jagorantar shari'ar.

    A yanzu ana jiran alƙalin ya yanke masa hukunci.

  11. An buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka

    jagoran Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu sanya ido kan ayyukan nukiliya na Majalisar ɗinkin duniya sun amince da wani ƙuduri da zai tilastawa Iran bayyana musu yawan makamashin nukilyarta.

    Kudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da damar ziyartar tashoshinta na nukilya, ciki har da waɗanda aka kai wa hari lokacin yaƙi tsakaninta da Isra'ila a watan Yuni.

    Ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Amurka ne suka bijoro da kudurin, inda kasashe sha tara suka kaɗa kuri'ar amincewa da shi yayin da Rasha da China da kuma Jamhuriyyar Nijar suka hau kujerar naki.

  12. Ana karanta wa Nnamdi Kanu laifukan da aka same shi da su

    Nnamdi Kanu a kotu

    Bayan fitar da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu daga kotu sanadiyyar hargowa da ya fara a lokacin da alƙali ya fara bayani, mai shari'ar James Omotosho ya ci gaba da karanto laifukan da aka kama Kanu da su.

    Dama alƙalin ya ce za a karanta hukuncin ba tare da Kanu na nan ba sanadiyyar "rashin kama kai da zafin kai da ya nuna".

    Daga nan sai alƙalin ya fara da batun tuhuma ta farko, wato "aikata ayyukan ta'addanci kan Gwamnatin Najeriya ta hanyar yaɗa shirye-shirye da yi wa mutane barazanar kisa da tsayar da komai cik".

    Alaƙalin ya ce "Da gangan Kanu ya riƙa yin abin da yake yi, amma ya yanke shawarar ci gaba ba tare da tunanin abin da zai faru ga mutane ba''.

    "Daga cikin ƙwararan shaidu da aka gabatar, a bayyane take cewa wanda ake tuhuma ya gudanar da ayyukan da za su haifar da ta'addanci.

    "Ya kamata a ce ya kare kansa game da haka, amma ya ƙi," in ji alƙalin.

  13. Ƴansanda sun daƙile yunƙurin satar mutane a Abuja

    kwamishinan ƴan sandan Abuja a wurin da aka yi yunkurin satar mutane a Bwari

    Asalin hoton, SP JOSEPHINE ADEH

    Rundunar ƴansandan Abuja, babban birnin Najeriya ta daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ƙauyen Guto da ke ƙaramar hukumar Bwari.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce da tsakar daren da ya gabata ne jam'iansu suka samu rahotan wasu ƴan bindiga da suka kai talatin, sun shiga ƙauyen da nufin yin garkuwa da wani magidanci da iyalinsa.

    Ta ce bayan samun rahoton, jam'ainsu da ke yankin Bwari, da haɗin gwiwar wasu jami'ai na musamman, sun yi gagagwar isa wuri, sai dai bayan ƴan bindigar sun hango su, sai suka buɗe wuta wanda ya sa ƴan sandan mayar da zazzafar martani, aka yi musayar wuta.

    A cewar sanarwar, a yayin da ake musayar wutar, jam'ian ƴan sandan sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga biyu, yayin da sauran suka tsere cikin dazukan da ke kusa.

    Sai dai SP Josephine ta ce ɗaya daga cikin jam'ian rundunar ya rasu bayan harbinsa da aka yi.

    Sanarwar ta ƙara da cewa tuni kwamishinan ƴan sandan Abuja CP Miller Dantawaye ya aike da ƙarin jami'an tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankin, ya kuma bayar da umurnin ƙaddamar da bincike domin gano ƴan bindigar.

    Yansanda a cikin daji a Bwari Abuja

    Asalin hoton, SP JOSEPHINE ADEH

  14. Gwamnatin sojin Nijar za ta gina kamfanin sarrafa albarkatun noma a Maradi

    Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar janar Abdourahamane Tiani, ya sanar da aniyar gwamnati ta samarwa jahar Maradi wani katafaren kamfanin sarrafa albarkatun noman damina da na rani da ke lalacewa.

    Gina wannan kamfanin zai laƙume kuɗin da suka kai CFA biliyan 60 domin bunkasa al’amuran noma a jahar Maradi.

    Shugaban kungiyar ci gaban birni da karkara a ƙasar Alhaji Ali Kalla, ya ce wannan babban ci gaba ne a ƙasar kuma suna maraba da shi domin zai ƙara bunƙasa jihar ya ɗaga martabarta.

    Ya ce kayyayakin da za a sarrafa sun haɗa da rogo, dankali, ayaba, da kayan lambu, da duk kayan da ake nomawa lokacin rani.

    A baya ya ce manoma kan yi noman a adadi mara yawa, ko su yi saurin rabuwa da amfanin gonarsu saboda gudun lalacewa.

    ''Maradi dama abin a ta fi ba ƙarfi shi ne noma da kiwo da kasuwanci, wannan kamfani zai samar wa matasa aiki, ya basu damar faɗaɗa noma.'' in ji shi.

    Ali Kalla ya kuma ce ci gaba da kamfanin zai a kawo wa Maradi ya haɗa da samun na'uikan abinci daban daban, iya nomawa da sarrafa abin da ta noma a cikin gida har ma a aika wa wasu ƙasashe.

  15. Ana ci gaba da neman mutum fiye da ashirin a Ukraine bayan harin Rasha cikin dare

    wani gini da aka kai wa hari

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce har yanzu ana ci gaba da neman mutum ashirin da biyar da suka ɓace bayan harin da Rasha ta kai a jiya Laraba a birnin Ternopil da ke yammaci.

    Harin da aka kai kan gidaje masu tsawo na zaman mutane, na daga cikin hare hare mafi muni a Yammacin Ukraine tun bayan mamayar Rasha.

    Mista Zelensky ya ce zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum ashirin da shida.

    Masu aikin ceto sun kwashe daren jiya suna neman masu sauran numfashi, kuma ana ci gaba da aikin.

  16. NAFDAC ta haramta amfani da abincin yara na Bledine

    Jam'ian hukumar NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC/X

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta gargaɗi ƴan kasar su kaucewa amfani da wani abincin yara mai suna Bledine, bayan rahotanni cewa ƙasar Chadi ta haramta abincin saboda fargabar gurɓacewa.

    A cikin wata sanarwa a shafinta na X, NAFDAC ta ce wani kamfanin Faransa mai suna Danone ne ke haɗa abincin, kuma sun haɗa da mai haɗin biskit da madara da ayaba.

    A cewar ta, bisa rahotanni da ta samu, hukumomi a Chadi sun haramta amfani da abincin yaran bayan ya gaza cika ƙaidojin da aka sanya ba kan sinadarin Aflatoxin B1, wani sinadari da hukumar ta ce na da illa ga ƙananan yara.

    Hukumar ta ce tuni wannan abinci ya soma yawo a kasuwanni a faɗin Najeriya, musamman a garuruwan da ke kusa da iyakokin ƙasar da Chadi.

    NAFDAC ta ce ta umurci Jami'anta da ke kowane shiyya ta kasar, da na matakin jihohi su soma bincikar kasuwanni tare da ƙwace abincin yaran.

  17. Tilastawa Falasɗinawa ficewa daga sansanonin ƴan gudun hijira laifin yaƙi ne - HRW

    Falasɗinawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch mai hedkwata a birnin New York ta bayyana matakin Isra'ila na tilastawa Falasɗinawa ficewa daga sansanonin ƴan gudun hijira uku da ke gaɓar yamma da kogin Jordan da ta mamaye a matsayin lafin yaƙi.

    Sama da Falasɗinawa da dubu talatin ne dai daga Jenin da Tulkarem da Nur Shams aka ba su umarnin ficewa daga gidajensu a watan Janairu da Fabrairu yayin wani farmakin da sojojin Isra'ila suka kai.

    Tun daga lokacin ba a bari sun koma gidajensu ba. An ruguza daruruwan gidajen domin samar da sabbin hanyoyin shige da ficen sojoji. Isra'ila ta ce tana tarwatsa abubuwan da ta bayyana a matsayin kayayyakin ayyukan ta'addanci ne a sansanonin.

  18. Trump ya amince ma'aikatar shari'a ta fitar da cikakken bayanan bincike kan Epstein

    Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wani ƙudirin doka da zai amincewa ma'aikatar shari'ar kasar fitar da bayanan binciken laifukan da ta yi kan mutumin da aka kama da laifin cin zarafin kananan yara, Jeffrey Epstein.

    A ranar Talatar da ta gabata ne dai majalisar dokokin kasar ta kaɗa kuri'ar amincewa da ƙudurin.

    Yanzu kuma ma'aikatar shari'a na da kwana talatin ta fitar da bayanan.

    Wakilin BBC ya ce, Kudurin dokar da Shugaba Trump ya sanya wa hannu, ya ba da damar kin fitar da duk wani bayani da zai iya kawo cikas ga duk wani binciken da ake gudanarwa a halin yanzu.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne Shugaba Trump ya ba da umarnin gudanar da bincike kan alaƙar Jeffrey Epstein da abokan hamayyar siyasarsa na jam'iyyar Democrat.

  19. An fitar da Nnamdi Kanu daga kotu kan yin hargowa

    Nnamdi Kanu a Kotu

    Alkali a babban kotun tarayya da ke Abuja, inda ake zaman yanke hukunci ya buƙaci a fitar da wanda ake ƙara Nnamdi Kanu daga zauren kotun, bayan jagoran na IPOB ya nemi tayar da hargitsi ta hanyar yin hargowa.

    Wanda ake ƙarar, kuma yake kare kansa bayan korar lauyoyinsa, ya soma hayaniya ne bayan alƙalin kotun ya soma jawabi.

    Tun farko an bai wa Kanu damar yin jawabi na ƙarshe, sai dai a daidai lokacin da alƙali ya fara nasa jawabi, Kanu ya riƙa yin katsalandan, yana nuna adawa da kalaman alƙalin.

    An buƙaci ya miƙa bututun maganar, amma ya ƙi, daga nan ne alƙalin ya buƙaci a yi waje da shi.

    A yanzu dai an ci gaba da zaman shari'ar, kuma kotun ta ce za ta yanke hukuncin a bayan idon wanda ake ƙarar.

  20. Kotu za ta yanke wa Nnamdi Kanu hukunci a yau

    Nnamdi Kanu

    A yau alhamis ne wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ke zaman yanke hukunci kan shari'ar jagoran ƙungiyar ƴan awaren IPOB Nnamdi Kanu kan zargin sa da laifukan 'ta'addanci'.

    Mai shari'ar James Omotosho ya ce zai yanke hukuncin ne a yau bayan Kanu ya kasa kare kansa bayan kwana shida da kotun ta ba shi domin yin hakan.

    Kotun ta ce bayan Kanu ya gaza amfani da damar da aka ba shi domin kare kansa daga tuhumar da ake yi masa, bai kamata ya ci gaba da iƙirarin da yake yi cewa an tauye masa damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na jin bahasinsa ba.

    A ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne kotun ta ɗage zamanta domin bai wa wanda ake ƙara damar kare kansa kamar yadda ya buƙata a baya.

    Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, inda ya buƙaci damar kare kansa.

    Ana kuma haska zaman shar'iar na yau kai-tsaye a gidajen talibijin na ƙasar.