Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Bankwana

    Ƙarshen rahotannin shafin kai tsaye na BBC Hausa kenan a yau Litinin.

    Ku tara gobe Talata domin samun wasu sabbin rahotannin.

  2. Taliban za ta rufe ofishin jakadancin Afghanistan da ke Landan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Afganistan da ke Landan na shirin rufewa bayan korar ma'aikatansa da gwamnatin Taliban ta yi.

    Ofishin ya ce zai rufe a ƙarshen watan Satumba bisa buƙata a hukumance daga gwamnatin Burtaniya.

    Hakan na zuwa ne bayan sanarwar da ƙungiyar Taliban ta fitar a watan Yuli, cewa za ta yanke hulɗa da wasu ofisoshin jakadancin da gwamnatin da ta gabata ta kafa.

    Har yanzu, jami'an da aka naɗa a zamanin gwamnatin da ta gabata kafin dawowar Taliban ne ke gudanar da al'amuran ofishin.

    Cikin wani sako da wallafa a shafinsa na X, Jakadan Afghanistan a Birtaniya Zalmai Rassoul ya gode wa takwarorinsa da sauran waɗanda suka ba da haɗin kai ga ofishin jakadancin Afghanistan da ke Landan a wannan lokacin.

    Ya ƙara da cewa ofishin wanda aka kafa a shekarar 1922 zai rufe ƙofofinsa ne a ranar 27, ga watan satumba.

    Gwamnatin Birtaniya ta buƙaci jami'an diflomasiyyar Afghanistan su rufe ofishin jakadancin saboda ba ta da niyyar miƙa shi ga ƙungiyar Taliban.

    Rahotanni sun ce an shawarci jami’an diflomasiyyar Afghanistan da ke ofishin jakadancin da ke Princes Gate, Kensington da su bar Burtaniya ko kuma su nemi mafakar siyasa.

  3. Machado za ta ci gaba da jagorantar adawa a Venezuela bayan tserewar Gonzalez

    Maria Corina Machado

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar ƴan adawar Venezuela ta ce za ta ci gaba da zama a ƙasar, bayan ɗan takararta na shugaban ƙasa ya fice daga ƙasar.

    Maria Corina Machado ta ce za ta ci gaba da fafutika daga cikin Venezuela, yayin da Edmundo Gonzalez zai tallafa mata daga ƙetare.

    Tun da farko Mista Gonzalez ya nemi a tattauna, domin a warware badaƙalar siyasar da ta yi wa ƙasar dabaibayi.

    Hukumomin Venezuela sun ce shugaba mai mulki Nicolas Maduro ne ya lashe zaɓen da aka gudanar a watan Yuli, sai dai har yanzu ba su fitar da cikakkun bayanan da za su tabbatar da sakamakon ba.

    Ƴan adawa sun fitar da ƙididdigar ƙuri'un da suka ce sun nuna cewa Mista Maduro ya sha kaye da tazara mai yawa.

    Yawancin ƙasashen duniya sun ƙi amincewa da Mista Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

  4. NLC ta bai wa hukumomin Najeriya wa'adin tsakar daren ranar Litinin su sako Ajaero

    ...

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, ta bai wa hukuomin Najeriya, wa’adin zuwa tsakar daren ranar Litinin su sako shugabanta, Joe Ajaero.

    A wata sanarwar bayan taro da ta fitar, NLC ta yi alla-wadai da tsare Kwamared Joe Ajaero da gwamnatin Najeriya ta yi ba tare da wani dalili na shari'a ba.

    ''NLC ta yi la'akari da cewa Kwamared Ajaero yana gudanar da aikinsa na wakiltar ma'aikatan Najeriya bisa ƙa'ida, kuma bai aikata wani laifi da zai sa a ɗauki wannan mataki a kansa ba. Tsare shi cin zarafi ne ga haƙƙin ma'aikata da ƙa'idojin dimokraɗiyya na ƴancin walwala da faɗar albarkacin baki,'' in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Joe Ajaero ba mai laifi ba ne, kuma tsare shi wani aiki ne na tsoratarwa da nufin rufe bakin masu sukar gwamnati da kuma danne muryar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta kuma buƙaci gaggauta sauya ƙarin farashin man fetur da aka yi ya koma Naira 617 kowanne lita.

    Ƙungiyar ta kira taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa da ƙarfe 9:00 na safe a ranar Talata 10 ga watan Satumba 2024 domin ɗaukar ƙwararan matakai kan al'amuran da ke gudana a ƙasar.

  5. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 341 a Chadi - MDD

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 341 ne suka mutu a faɗin ƙasar Chadi sakamakon ambaliya ruwa da ƙasar ke fama da ita tun cikin watan Yuli.

    Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ambaliyar ta shafi duka lardunan ƙasar Chadi 23, yayin da kusan mutum miliyan ɗaya da rabi suka rasa matsugunansu.

    Ambaliyar ta haifar da mummunar ɓarna a faɗin ƙasar, inda ta lalata gidaje da asarar dukiyoyi tare da dakatar da muhimman ayyuka da yanke gadoji masu yawa, lamarin da ya sa a yanzu ba a iya zuwa wasu wuraren sai da kwale-kwale.

    Mutane da dama a yanzu na zaune a makarantu da wasu gine-ginen gwamnati.

    Ambaliya ta shafe dubban gonaki, yayin da ta yi awon gaba da dabbobi masu yawa.

    A makon da ya gabata ɗalibai 14 tare da malaminsu ne suka mutu lokacin da ginin makarantar ya rufta musu.

  6. An fara takun saka tsakanin Habasha da masar kan kogin Nilu

    ...

    Asalin hoton, Ethiopian government

    Habasha ta zargi Masar da ƙoƙarin ci gaba da yin iƙirarin mallakar kogin Nilu yayin da zaman ɗar-ɗar ke daɗa ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu.

    Cikin wata wasiƙa da ta aike wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, Habasha ta ce ta yi fatali da abin da ta kira jerin zarge-zarge marasa tushe da Masar ta yi game da taƙaddamar da ta shafi wata madatsar ruwa mai cike da cece-kuce da Habasha ta shafe shekara 13 tana gina wa a kogin Nilu.

    An kusa kammala ginin madatsar ruwan kuma tuni ta soma samar da hasken wutar lantarki.

    Wannan takaddamar t baya bayan nan zuwa ne a daidai lokacin da Masar ta kulla huldar soji da makwabciyarta Somalia, wadda ita ma ke da nata rashin jituwar da Habasha.

    Rikicin ya samo asali ne tun a shekara ta 2011 lokacin da Habasha ta fara gina babban madatsar ruwa ta 'Gerd' a kan kogin Blue Nile, inda kashi 85% na ruwan Nilu ke kwarara.

    Masar, tare da Sudan - wanda ita ma kogin Nilu ke bi ta cikinta, na ƙara nuna fargabar cewa za a iya fuskantar barazana ga hanyoyin samar da ruwan da suke buƙata, musamman idan aka samu fari na shekaru a jere.

  7. Harin bam ya kashe sama da mutum 20 a Sudan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Wata ƙungiyar likitoci a Sudan ta ce aƙalla mutum 21 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da 70 suka jikkata sakamakon luguden wuta a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama'a a kudu maso gabashin Sudan.

    Ƙungiyar likitocin ƙasar ta bayyana cewa, dakarun RSF ne ke da alhakin kai harin a birnin Sennar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta yi Allah wadai da shi a matsayin kisan kiyashi na fararen hula.

    Harin na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin Sudan suka yi watsi da shawarar da wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar na aikewa da dakarun ƙasa da ƙasa don kare fararen hula.

    Dubban mutane ne aka kashe yayin da sama da miliyan 10 suka tsere daga gidajensu tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa tsakanin sojoji da ƙungiyar RSF a watan Afrilun da ya gabata, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin matsalolin jin kai mafi muni a duniya.

    Tattaunawar zaman lafiya da dama da Saudiyya da Amurka suka shiga tsakani sun gaza kawo ƙarshen rikicin.

    Ana zargin ɓangarorin biyu a rikicin Sudan - sojoji da RSF - da laifin aikata ta'asa kan fararen hula.

  8. An damƙa wa kowane gwamna tallafin shinkafa ban da na Kano - Kwankwaso

    ...

    Asalin hoton, Rabiu Musa Kwankwaso

    Jagoran jam'iyyar NNPP, mai mulkin jihar kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta hannun Gwamnonin su, amma ban da Jihar Kano.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Jagoran Kwankwasiyyar ya yi zargin cewa gwamnatin tarayyar ta miƙa kason jihar Kano hannun jiga-jigan jam'iyyar APC, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa dimikraɗiyya.

    ''Wannan babban cin fuska ne ga dimokradiyya da kuma tsarin mulkin ƙasar mu. Wannan mataki dai nuna ɓangaranci ne da ya wuce gona da iri,'' in ji jagoran jam'iyyar NNPP.

    Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya gagguata dakatar da abin da ya kira karan-tsaye wa tsarin dimikraɗiyyar ƙasar.

    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce an aike da daraktocin hukumar DSS har guda uku zuwa jihar Kano, tare kuma da sauya su duka cikin mako biyu zuwa uku, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga tsaron jihar.

  9. NLC ta buƙaci a gaggauta sakin shugabanta

    Shugaban NLC

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta buƙaci hukumomin ƙasar su gaggauta sakin shugabanta ba tare da wani sharaɗi ba.

    Da safiyar ranar Litinin ne hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama Mista Ajaero a filin jirgin saman Abuja, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya domin halartar taron ƙungiyar kwadago TUC, ta Birtnaiya

    Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ƙungiyar, Benson Upah ya fitar, ya ce ta sanya rassanta na jihohi da manyan ƙungiyoyin da ke ƙawance da ita cikin shirin ko-ta-kwana, kan lamarin da ta kira mai ''tayar da hankali''.

    “Ƙungiyarmu ba za ta zuba ido tana ganin ana tozarta shugabanni da mambobinta ba, don haka muke buƙatar a gaggauta sakin Kwamared Ajaero, ba tare da gindaya kowane irin sharaɗi ba'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske..

    Sanarwar ta ci gaba da cewa ''an tsare mista Ajaero a wani wuri da ba a sani ba, don haka ba a san halin da lafiyarsa ke ciki ba, duk wani yunƙuri na jin halin da yake ciki ya ci-tura''.

    NLC ta kuma ce yanzu haka ta shiga taron sirri da manyan shugabanninta, tana mai cewa za ta bayyana wa duniya abin da tattauna da zarar ta kammala.

  10. Adadin mutanen da suka mutu a harin da Isra'ila ta kai Siyria ya kai 18

    Hari

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiyar Syria ta ce adadin mutanen da suka mutu a hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan sansanonin soji a tsakiyar ƙasar ya kai 18.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar, Sana ya ambaoto ministan lafiyar ƙasar, Hassan al-Ghabbash na cewa wasu mutum 37 sun jikkata a hare-haren da aka kai lardin Hama ranar Ladahi da daddare.

    To sai dai wata ƙungiyar da ke sanya idanu ta Birtaniya, ta ce mutum 26 ne aka kashe a harin da aka nufi wata cibiyar binciken kimiyya da ake zargin ana ƙera makamai a cikinta a kusa da sansaninin soji na Masyaf.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba za ta yi tsokaci ba a kan rahoto kafafen yaɗa labaran ƙasashen waje.

  11. Guguwar Typhoon Yagi ta karya babbar gadar Vietnam

    Gadar Phong Chau

    Asalin hoton, Getty Images

    Guguwar Typhoon Yagi ta karya wata babbar gada a arewacin Vietnam.

    Mataimakin firaiminista Ho Duc Phoc ya ce motoci 10 da babura biyu sun rufta cikin ruwa lokacin da gadar ta karye a yau Litinin.

    Mutane aƙalla uku aka ceto kawo yanzu yayin da ake ci gaba da neman wasu 13 da suka faɗa gadar ta Phong Chau da ke a yankin Phu Tho.

    Mista Ho ya ƙara da cewa kawo yanzu babu tabbacin ko mutum nawa suka mutu a wajen.

    Akwai wani ɓangare na gadar mai tsawo mita 375, kuma an tura sojoji domin gina gadar wucin gadi cikin gaggawa.

    Guguwar Yagi ita ce annoba mafi muni a nahiyar Asiya a bana, kuma kawo yanzu ta kashe mutum 59 tun daga lokacin da ta fara shiga Vietnam a ranar Asabar.

  12. Tinubu ya jajanta wa iyalan mutanen da haɗarin tanka ya kashe a Neja

    Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Bola Tinubu ya tura saƙon jaje ga gwamnatin jihar Neja da kuma jama'ar jihar a bisa mutuwar mutane a wani haɗarin tankar mai a kan titin Bida-Agaie-Lapai, a ranar Lahadi.

    Haɗarin tankar ya kashe mutum 48 da kuma dabbobi 50.

    Kakakin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya yi ta'aziya ga iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma yi fatan samun lafiya ga waɗanda suka samu rauni.

    Sanarwar ta kuma ce shugaba Tinubu ya yi jaje ga ƴan kasuwa, masu shaguna a wajen da haɗarin ya faru.

    Ya yi fatan Allah ya bai wa waɗanda suka ji rauni sauƙi.

    Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumomin da alhakin kula da hanyoyi ke hannunsu, su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan su na kare rayukan jama'a.

  13. Shugabar Tanzania ta bayar da umarnin binciken kisan ɗan adawa

    President Samia

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar Tanzania, Samia Suluhu, ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan kisan jigo a jam'iyyar adawa ta Chadema.

    Ta yi allwadai da kisan Ali Mohammed-Kibao, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci muzgunawa ƴan adawa ba.

    An gano gawar Mr Kibao a wani yanki da ke kusa da Dar-es-Salaam a ranar Lahadi.

    Wasu rahotanni sun ce an yi garkuwa da shi ne a makon jiya, lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Tanga.

    Lamarin ya janyo damuwa kan tunanin ƙasar za ta iya komawa salon muzgunawa ƴan adawa da aka yi fama da shi a lokacin mulkin mariganyi shugaba John Magufuli.

  14. SERAP ta ce jami'an DSS sun yi wa ofishinta ƙawanya

    ...

    Asalin hoton, DSS/X

    Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS) sun kai samame ofishin ƙungiyar SERAP, mai fafutikar yaƙi da cin hanci da Rashawa a Abuja.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa jami’an tsaron sun yi wa ofishinsu ƙawanya ba bisa ka’ida ba, tare da neman ganawa da manyan daraktocin ƙungiyar.

    Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasar, Bola Tinubu da ya shiga tsakani, sannan ya umarci jami’an su daina abin da ƙungiyar ta kira ''tsangwama da cin zarafi, da kuma take haƙƙin ‘yan Najeriya''.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Kawo yanzu dai babau cikakken dalilin da ya sa jami'an tsaron suka mamaye ofishin SERAP ɗin.

    Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar NLC, ta sanar da cewa jami'an na DSS sun kama shugabanta, Joe Ajero a filin jirgin saman Abuja.

  15. Ba mu ƙara harajin kayayyaki ba - Gwamnatin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa ta ƙara yawan harijin kayayyaki zuwa kashi 10%, daga kashi 7.5%.

    Ministan kuɗi na Najeriya, Wale Edun a cikin wata sanarwa ya ce har yanzu dokokin ƙasar sun ƙayyade cewa hariji kayayyakin da ake biya kashi 7.5% ne.

    Ya ce: “Harajin kayayyaki a Najeriya yana nan a kashi 7.5% , kuma hakan gwamnati ke karɓa. Domin haka gwamnati da dukkan hukumomin ta suna biyayya ga wannan tanadi na doka, kuma ba za su saɓa ba.

    Rahotan da aka riƙa yaɗawa game da ƙarin harajin kayyakin a Najeriya ya janyo martani daga ɓangarori da dama, ciki harda na ƴan siyasa.

    Tuni dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi allawadai da matakin.

    Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sada zumuntansa na X.

    Ya bayyana matakin a matsayin wani abu da zai yi mummunar illa ga al’ummar Najeriya, yana mai hasashen cewa hakan zai kara ta’azzara matsalar tsadar rayuwa da ƙasar ke fama da ita da kuma kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

    "Ƙara kuɗin haraji zai zama wuta mai zafi da za ta cinye ainihin mutanenmu." in ji Atiku.

    "Wannan matakin zai haifar da koma baya da ƙara zurfafa matsalar tsadar rayuwa a cikin gida da kuma ƙara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin ƙasar ne kawai"

  16. Bangaladesh na tuhumar Sheikh Hasina da kisan gilla

    Sheikh Hasina

    Asalin hoton, EPA

    Sabon mi gabatar da ƙara da aka naɗa a Bangaladesh ya ce zai fara wani shiri na neman a dawo da tsohuwar firaiministar ƙasar, Sheikh Hasina gida daga India.

    Mohammad Tajul Islam shi ne ke jagorantar wani kwamiti da ke binciken keta haƙƙin ɗan Adam a ƙasar a 2010.

    Ya zargi tsohuwar firaiministar da aikata kisan gilla, kuma ya ce dole ta fuskanci shari'a.

    A farkon watan Ogusta Sheikh Hasina ta gudu Inida, bayan gagarumar zanga-zangar da ta karaɗe ƙasar, ta kuma kawo ƙarshen mulkin ta na shekara 15.

    Jmai'an tsaro sun yi amfani da ƙari wajen tarwatsa masu zanga zangar.

  17. DSS ta kama shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero

    Joe Ajaero

    Asalin hoton, @NLCHeadquarters/X

    Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero.

    Kungiyar ta NLC ta bayyana a shafin sada zumuntarta na X cewa an kama shugaban nasu ne a yau, Litinin da safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

    Ƙungiyar ta NLC ta ce "har yanzu ana ci gaba da cin zarafin ma'aikatan Najeriya yayin da shugabanmu Joe Ajaero ya shiga hannun jami'an DSS da safiyar yau."

    "Jami'an sun kama shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Birtaniya."

    NLC ta ce yanzu haka ana tsare da shugaban a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA.

    A baya dai, shugaban NLC ɗin ya mutunta gayyatar da ƴansanda suka yi masa kan zarginsa da hannu a tallafawa ayyukian ta'addanci, da kuma cin amanar ƙasa

  18. An fara gwajin ƙwayar halittar yaran da suka ƙone a makarantar Kenya

    Makarantar Kenya

    Asalin hoton, Ephantus Maina

    An fara gwaji ƙwayar halitta na DNA domin tantance gawarwakin ƴan makarantar da suka ƙone a Kenya.

    Gawar mutane 19 aka kwaso daga ginin da ya ƙone ƙurmus a lardin Nyeri, yayin da wasu biyu suka mutu a asibiti.

    A ranar Talata za a gwada gawarwakin domin tantance abin da ya kashe su.

    Ana zaman makokin kwana uku a Kenya domin jimamin mutuwar mutum 21, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa a game da tabbatar da tsaro a makarantu.

    An ƙaddamar da bincike domin gano abin da ya yi sanadin tashin giobarar.

  19. Matashiya mai aikin birkila da mata ƴanuwanta ke tsangwama

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon matashiya mai aikin birkila
  20. Harin Isra'ila ya kashe mutane 14 a Syria

    Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe mutane aƙalla 14 a harin sama da Isra'ila ta kai wasu cibiyoyin soji a tsakiyar Syria.

    Kamfanin dillancin labaran Syria ya ambato wani shugaban asibiti na cewa wasu mutanen 43 sun samu rauni a hare-haren na ranar Lahadi a Masyaf, da ke yankin Hama.

    Tun da farko dai wata ƙungiyar Birtaniya mai sanya ido a kan lamarin ta ruwaito cewa an kashe sojoji aƙalla huɗu da fararen hula uku a hare-haren da suka tarwatsa cibiyar binciken kimiyya ta dakarun soji, inda mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran ke ɗaukar zama.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba za ta yi tsokaci ba a kan rahoto kafafen yaɗa labaran ƙasashen waje.

    Amma ta amsa cewa a baya ta kai irin waɗannan hare-hare a maɓoyar masu laifi a Syria, waɗanda ta ce Iran na goya wa baya.

    Rahotanni sun ce hare-haren Isra'ila sun ƙaru tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktobar bara, a matsayin martani ga harin da Hezbollah ta kai arewacin Isra'ilan, wanda take zargin ya samu goyon bayan Lebanon da Syria.

    Wata majiyar sojin Syria ta ce jirgin yaƙin Isra'ila ya ƙaddamar da hare-hare a kan wasucibiyoyin soji a ranar Lahadi, amma an yi nasarar harbo da dama daga cikin rokokin da jirgin ya harba.