Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2025
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, EPA
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa yarjejeniyar da ya rattaɓa wa hannu da shugaban gamnatin Jamus Friedrich Merz, irinta ce ta farko.
Yayin da yake ganawa da Mista Merz lokacin da suke amsa tambayoyin ƴan jarida a Landan, Keir ya ce yarjejeniyar shaida ce ta irin kusancin da ƙasashen biyu ke da shi.
Yarjjeniyar ta haɗa da haɗin-kai a fannin tsaro da batun ƙaura da kuma kasuwanci.
Mista Merz ya ƙara da cewa ya yi mamaki wannan ce yarjejeniya ta farko tsakanin ƙasashen biyu tun bayan yaƙin duniya na biyu.

Asalin hoton, Federal Government
Ɗan marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, ya gode wa shugaba Bola Tinubu da kuma nuna farin cikinsa kan yadda aka karrama mahaifinsa ta hanyar yi masa jana'izar ban-girma.
Ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja yau Alhamis domin yi wa Buhari addu'o'i.
Yusuf wanda ya halarci taron tare da ƴan uwansa, ya gode wa gwamnatin shugaba Tinubu saboda irin goyon baya da ya bai wa mahaifinsa da kuma iyalansu.
Ya kuma gode wa majalisar tarayya, gwamnan jihar Katsina Dikko Radda, sauran gwamnoni da kuma ƴan Najeriya saboda taya su alhinin rashin da suka yi.
"Karramawa da mahaifina ya samu, ya nuna ƙarara cewa kallon da ake yi masa ya zarce na siyasa kaɗai, sai dai ɗaukarsa a matsayin aboki da kuma uba. Ina godiya ga dukkan mambobin majalisar zartaswa saboda irin kula da kuma jana'izar ban-girma da suka yi wa mahaifina," in ji Yusuf.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kulen Allah ta yi Alla-wadai da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ƴanbindiga suka yi a karamar hukumar Riyom na jihar Filato.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta buƙaci dukkan ɓangarori su rungumi zaman lafiya da kuma adalci.
"Kashe-kashen Riyom suna da raɗaɗi musamman ma ganin cewa sun faru ne a yanzu da ake makokin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari," in ji sanarwar.
KACRAN ta ƙara da cewa babu wata hujja da za ta sa a yi wa gidajen mutane ƙawanya tare da kashe su babu gaira ba dalili.
Ƙungiyar ta kwatanta abin da ƴanbindigar suka yi na kashe mata da yara a matsayin babban laifi, wanda kuma ba shi da muhalli a cikin al'umma.
Don haka ne ta yi kiran kawo karshen rikice-rikicen da ake samu a jihar.
Ta kuma yi kira ga dukkan ɓangarori, ciki har da ƴanbindiga da su daina kai hare-haren kan ƙauyuka da kuma lalata duƙiyoyi.

Asalin hoton, Reuters
Wata ƙungiya mai sa-ido kan yaƙe-yaƙe ta ce sama da mutum 350 aka kashe a lardin Sweida da ke Siriya bayan ɓarkewar rikicin ɓangaranci ranar Lahadi.
Hukumar kare hakkin ɗan'adam mai cibiya a Birtaniya ta ce farar-hula 80 dakarun gwamnati da wasu mayaƙan Druze suka kashe.
Sojojin gwamnati da dama sun janye daga Sweida, bayan Isra'ila ta fara kai hare-hare ta sama.
Firaminista Benjemen Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da amfani da karfi don kare mabiya addinin Druze.

Asalin hoton, Godswill Akpabio
Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba.
Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa tsohon shugaban addu'o'i, ya ce masu sukarsa ma sun san cewa bai yi almubazzaranci da duƙiyar ƙasa ba lokacin da yake mulki.
"Maganar gaskiya ita ce Buhari mutum ne wanda ba a isa a tankwarashi ba. Bai guje wa nauyin da aka ɗora masa ba, mutumin da kuma ya bauta wa ƙasarsa yanda ake so.
"Shugaba ne da ya jajirce wajen yin mulki yanda ya kamata duk da kalubale da ya fuskanta. Hakan bai sa gwiwarsa ta sare ba, amma duk da haka wasu sun ki aminta da shi," in ji Akpabio.
Taron majalisar zartaswar na musamman ya samu halartar shugabancin majalisar tarayya, ministoci, gwamnoni da kuma ƴaƴan marigayin.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari, marigayi shugaban Najeriya.
Tinubu ya sanar da haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
"Kafin mu fara addu'o'i domin karrama Buhari, ina sanar da ku cewa mun sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari," in ji Tinubu.
Manyan jami'an gwamnati da dama ne suka halarci taron addu'o'in, ciki har da wasu daga cikin ƴaƴan marigayin.

Asalin hoton, BBC/Getty Images
Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari, Iyalansa sun bayyana yadda ya tarbiyantar da su.
A wata hira da BBC karon farko tun bayan rasuwarsa, ƴaƴa da jikokin marigayin sun bayyana yadda mu'amala ta kasance tsakaninsu da tsohon shugaban na Najeriya.
Muhammadu Buhari ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan, bayan ya yi fama da jinya.
Makusantan marigayin sun bayyana shi da mutum mai son zumunci da ƙaunar danginsa.

Asalin hoton, NTA
An gudanar da addu'o'i ga marigayi shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a taron majalisar zartaswa da ake gudanarwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ne ya jagorantar taron addu'o'in.
Tsohon shugaban ƙasar ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan bayan fama da jinya.
An binne shi ranar Talata a Daura garin mahaifarsa da ke jihar Katsina.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin sojin Myanmar ta ce ta sake karɓe ikon wasu birane masu muhimmanci daga hannun ƴan tawaye bayan fafatawa ta tsawon lokaci.
Birnin Nawnghkio da ke arewa maso gabashin Myanmar na da tazarar kilomita 40 tsakaninsa da makarantar horas da sojoji, kuma shi ne nasara ta farko da dakarun gwamnatin Burma ta samu tun da suka fara mayar da martani a farkon wannan shekara.
Soji sun karɓe iko shekaru huɗu da suka gabata, kuma tun daga lokacin suka shi ga yaƙin basasa.

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Ghana sun tuhumi wani tsohon shugaban hukumar kula da harkokin man fetur da cin hancin dala miliyan 28.
Ofishin mai gabatar da ƙara na musamman ya ce Mustapha Abdul-Hamid da wasu mutum shida, za su fuskanci tuhuma game da karkatar da kuɗaɗen man fetur zuwa kamfanin shell.
Sai dai mista Abdul-Hamid ya karyata zargin da ake yi masa.
A watan da ya gabata ne aka kafa sabuwar hukumar kula da albarkatun man fetur a Ghana, wadda aka ɗora wa alhakin hana fitar da mai ba bisa ka'ida ba da gurɓata shi da kuma bayar da lasisi.

Asalin hoton, Festus Keyamo
Ministan sufurin jiragen sama da bunƙasa harkokin samaniya na Najeriya, Festus Keyamo ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kan sauya sheƙa da ya yi daga jam'iyyar PDP a daidai lokacin da ake makokin rasuwar marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A wani sako da Keyamo ya wallafa a shafin X, ya yi Alla-wadai da matakin da Atiku ya ɗauka inda ya ce yana son karkatar da hankalin ƴan ƙasa daga zaman makoki da ake yi.
"Duk da cewa yana da hakkin da kundin mulki ya ba ka na sauya jam'iyyar siyasa a kowane lokaci da kake so, amma sanar da sauya sheƙa daga PDP a wannan mako da ake makokin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Buhari, yunkuri ne kawai na karkatar da hankalin mutane daga abin da ke faruwa zuwa kansa.
"Hakan ya nuna ƙarara cewa buƙatar da kake so ta zama shugaban ƙasa ba ta da tausayi ko kuma jimami," kamar yadda Keyamo ya rubuta.
Sai dai mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya kwatanta kalaman Keyamo da cewa maganganu ne na son rai.
"Ina Keyamo yake lokacin da Atiku yake jagorantar sojoji a fagen daga? Ina yake? Ɓabatu kawai yake yi, kuma lokacin yin maganganu na son rai ya zo karshe," in ji Paul Ibe yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channnels.
A ranar Laraba ne Atiku ya sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP, inda ya yi zargin cewa ta sauka daga turba na asali da aka kafata a kai.

Asalin hoton, Reuters
Mutum biyu ne suka mutu sakamaon hari kan cocin Katolika da ke Zirin Gaza yayin da wasu da dama suka jikkata - ciki har da babban limamin cocin.
Hotunan da aka nuna wa BBC sun nuna yadda tagogi da rufin gini suka lalace.
Firaiministar Italiya Georgia Meloni, wadda ta dora alhakin lamarin kan Isra'ila, ta ce ba za a amince da kai wa fararen hula hare-hare ba.
Isra'ila ta dage cewar ba ta kai wa gine-ginen addini hari amma tana bincike.
Mabiya addinin Kirista da dama da muhallansu suka rushe sun koma rayuwa a coci. Marigayi Fafaroma Francis ya yi ta tuntuɓar su a kowacce rana.
Wakiliyar BBC ta ce hotuna sun nuna yadda Cocin Holy Family ta lalace. Akwai hoton da ya nuna wani jagoran addini da ya ji rauni a ƙafa yayinda yake magana da wani majinyaci a asibiti.

Asalin hoton, Presidency Nigeria
An gudanar da addu'o'i na musamman don neman gafara ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke garin Daura.
Taron addu'ar na zuwa ne bayan addu'ar uku da aka gudanar jiya a Daura a gaban tawagar wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa BBC cewa cikin waɗanda suka halarci taron addu'o'in har da tsohon Shugaban Ƙasar Benin Thomas Boni Yayi.
Haka nan, akwai gwamnoni da ministoci da suka hallara a gidan tsohon shugaban.
Nan gaba a yau Shugaba Bola Tinubu zai jagoranci wasu addu'o'in da kuma zaman majalisar zartarwa a Abuja.

Asalin hoton, Presidency Nigeria
Ruwan sama mai ƙarfin gaske ya kashe aƙalla mutum 63 a lardin Punjab na ƙasar pakistan tare da raunata wasu 290 cikin sa'a 24.
Gidajen da suka dinga rushewa ne suka raunata waɗanda suka jikkata, yayin da sauran suka nitse ko kuma wayoyin lantarki suka kashe su.
Hukumomi a birnin Rawalpindi da ke kusa da Islamabad babban birnin ƙasar sun bayar da hutun aiki a yau Alhamis sakamakon ruwan da aka fara yi tun daga safiyar Laraba.
Hukumomin na ci gaba da gargaɗin mazauna kusa da kogin da ya ratsa birnin da su ƙaurace wa gidajejnsu.

Asalin hoton, @MNJTFOfficial
Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi MNJTF ta ce ta yi nasarar kashe kwamandan ƙungiyar da mayaƙansa biyar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Laraba ta ce dakarunta sun fafata da mayaƙan ne a yankin Koulfoua bayan kai musu hari, inda suka kashe kwamandan mai suna Amir Dumkei da wasu 'yanbindiga biyar.
"'Yanta'addan ne suka fara kawo hari da farar safiyar Talata a sansanin sojan MNJTF da ke Koulfoua, amma kuma sai suka hadu da ruwan wutar da ya fi ƙarfinsu," a cewar sanarwar da Kanal Olaniyi Osoba ya fitar.
Ta ƙara da cewa ta ƙwace makamai da dama a hannunsu da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 tara, da ƙananan jiragen ruwa uku, da ƙunshin harsasai mai girma.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na ci gaba da alhinin mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin "aboki, ɗan'uwa, kuma mai kishin ƙasa".
"Mai Gaskiya ba tsohon shugaban ƙasa ba ne kawai, mutum ne mai kyawawan ɗabi'u na musamman kuma mai ƙwarin rai a ɓoye, wanda ya ƙaunaci Najeriya hatta a lokacin da aka dinga sukarsa," a cewar Tinubu cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na zumunta.
Tinubu ya ce yana alhinin mutuwarsa "sosai, ba don kawai ni ne magajinsa ba sai don kasancewarsa tsohon abokin gwagwarmya wajen gina ƙasa".
A ranar Talata ne Tinubu ya jagoranci jana'izar Buhari a gidansa da ke garin Daura na jihar Katsina. A yau kuma zai jagoranci zaman addu'o'i da na majaliar zartarwa duk domin girmama Buhari.
"Najeriya ta yi rashin ɗa na gari. Ni kuma na yi rashin abokina Shugaba Buhari," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da mayaƙan RSF suka kai a yankin Arewacin Kordofan ya kai 450.
Jaridar Sudan Tribune ta ruwaito shugabar asusun, Catherine Russell, na cewa aƙala yara maza 24 da yara mata 11 ne ke cikin waɗanda aka kashe a ƙauyuka Bara mai nisan kilomita 40 daga birnin na Kordofan.
Ta ƙara da cewa adadin zai iya ƙaruwa saboda har yanzu akwai mutanen da suka ɓace, sannan kuma akwai yara da yawa da aka raunata.
"Bai kamata a kai wa yara hari ba kwatakwata," a cewar Russel.
An ce hare-haren da aka fara kaiwa tun a watan Yuni, mayaƙan RSF ne suka kai su, inda suka hari ƙauyuka da yawa da kuma aikata sace-sacen kayan mutane.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai jagoranci taron addu'o'i na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar ta ce taron - wanda za a gudanar da misalin ƙarfe biyar na maraice agogon ƙasar - zai samu halartar ministocin gwamnatin ƙasar.
Taron - wanda za a gudanar a fadar shugaban ƙasar - zai kuma samu halartar shugabannin majalisun dokoki da wakilai daga fannin shari'ar ƙasar.
Taron addu'ar na zuwa ne bayan addu'ar uku da rasuwar tsohon shugaban da aka gudanar a Daura a gaban tawagar wakilan gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da taron addu'o'i na musamman ranar Juma'a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.

Asalin hoton, Getty Images
A yau ne Faransa ke kammala miƙa wa Senegel sansanonin sojinta da suka rage, domin kawo ƙarshen shekara 65 da sojojinta suka ƙwashe a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Yammacin Afirka.
Ficewar dakarun Faransa na ƙarshe su kusan 350 na zuwa ne bayan buƙatar hakan daga shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
A watan Fabrairu ne Faransa ta janye dakarunta daga Ivory Coast.
Su ma gwamnatocin mulkin soji a ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da kuma Chadi sun kori dakarun Faransa da na sauran ƙasashen Yamma daga ƙasashen nasu.
Gwamnatocin mulkin sojin sun kuma ƙulla ƙawancen tsaro da Rasha domin yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a ƙasashensu.
Kawo yanzu akwai sauran dakarun Faransa 1500 a Djibouti da ke gabashin Afirka.