Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya - Laraba, 04-12-2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Laraba, 04-12-2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye da muke kawo muku daga nan sashen Hausa na BBC.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Rundunar ƴansanda ta dakatar da jami'anta kan zargin satar kuɗi

    Rundunar ƴan sandan Najeriya ta dakatar da wasu manyan jami’anta guda huɗu da aka samu da zargin sun saci kuɗin da yawansu ya kai naira miliyan arba’in da uku na wani ma’aikacin wani kamfani da suka kama ba tare da an ba su umurni ba a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

    Bincike ya tabbatar da cewa sun kama mutumin ne a shekarar 2023 da ta gabata lokacin da zai fita da kuɗin a madadin kamfanin da ya ke yi wa aiki.

  3. Tarayyar turai ta soki matakin Taliban na hana mata karatun ungozoma

    Taliban

    Asalin hoton, Handout

    Ƙungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka ga matakin Taliban na dakatar da mata a Afghanistan shiga makarantun koyon aikin ungozoma da aikin jinya.

    Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin take haƙƙn ɗan'adam da kuma mataki mara hujja na hana mata samun ilimi. Daga nan ƙungiyar ta buƙaci Taliban ta soke matakin.

    Taliban dai ba ta ce uffan ba game da hukuncin, to amma dalibai sun shaida wa BBC cewa jami'an Taliban ɗin sun ba cibiyoyin bayar da horo umarnin cewa su dakatar da horar da mata har sai yadda hali ya yi.

    Sabrina Saqeb, tsohuwar mamba ce a majalisar dokokin Afghanistan wadda yanzu ke zaune a Canada ta shaida wa BBC cewa, ta ce matsalar ba wai ta ƴanci samun ilimi ko yin aiki ba ce, inda ta ƙara da cewa matakan za su shafi yanayin rayuwar ƴanƙasar a nan gaba.

  4. Matsin tattalin arziki ne kan gaba a yaƙin zaɓen Ghana

    Batun matsin tattalin arzikin da kasar Ghana ta shiga a baya-bayan nan ya kankane ajandar yakin neman zaben shugaban ƙasar da ke tafe ranar Assabar.

    Yanzu haka ƴan takarar manyan jam’iyyun NDC da NPP kowanensu na amfani da halin da ƙasar ta shiga na matsin tattalin arziki domin jan hankalin masu kaɗa ƙuri’a.

    Ƴanƙasar da dama sun bayyana takaicinsu kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

  5. Harin Isra'ila ya kashe mutum 12 a Gaza

    Aƙalla mutum 12 ciki har da ƙananan yara ne suka mutu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza.

    Likitoci sun ce harin ya faru ne a sansanin al Mawassi, wato wani yanki da Isra'ila ta keɓe a matsayin tudun mun tsira. Dubban Falasɗinawan da suka rasa muhallansu ne ke neman mafaka a wajen.

    Har kawo yanzu babu wani martani daga Isra'ila.

  6. Labarai da dumi-dumi, 'Yanmajalisar Faransa sun tsige Firaminista Michael Barnier

    Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yanmajalisa a Faransa sun kaɗa ƙuri'ar yanke-ƙauna, wadda ta yi sanadiyar tsige firaministan ƙasar Michel Banier.

    Jam'iyyun hamayya ne suka yi kira da aka kaɗa ƙuri'ar bayan da Mr Banier ya yi amfani ƙarfin ikonsa wajen tilasta garambawul a harkokin tsaro.

    Mafiya rinjayen ƴanmajalisar sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige shi - ƙuri'a 331 - kimanin wata uku bayan Shugaban Ƙasa Emmanuel Macron ya naɗa shi.

    Yanzu dai Barnier ne zai ci gaba da riƙe muƙamin kafin shugaban ƙasar ya naɗa wanda zai maye gurbinsa.

  7. Yadda tsofaffin sojojin Najeriya suka yi zanga-zanga a Abuja

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    A safiyar yau Laraba ne tsoffin sojojin Najeriya suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja, kan rashin biyansu haƙƙokinsu.

    Ɗaruruwan tsoffin sojojin waɗanda suka ɗaura baƙaƙen ƙyallaye a damatsansu, sun yi cincirindo a bakin kofar shiga ma'aikatar kuɗi ta Najeriya suna rera waƙoƙi tare ɗaga kwalaye.

    Tsofaffin sojojin na neman a biya su kashi 20 zuwa kashi 28 cikin ɗari na ƙarin albashi, sannan a ba su cikon kuɗin da aka biya su tun daga Watan Janairu zuwa Nuwambar 2024.

  8. 'Gobara ta janyo asarar sama da naira miliyan 130 a Kano'

    Gobara

    A jihar Kano, ya yin da yanayin sanyi da kaɗawar iska ke ƙaruwa, hukumar kashe gobara ta ce an yi asarar dukiya ta fiye da naira miliyan ɗari da talatin sanadiyar tashin gobara.

    Hukumar ta ce a cikin watan Nuwamban da ya gabata, an samu tashin gobara har arba’in da uku kuma a ciki mutum uku suka rasa rayukansu.

    A irin wannan lokaci na sanyi dai ana samun ƙaruwar amfani da wuta don ɗumama jiki ko tafasa ruwan zafi lamarin da ke haddasa gobara idan aka yi sakaci.

  9. Kwamatin kasuwanci tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu ya fara aiki

    Tinubu da Ramaphosa

    Asalin hoton, State House

    Najeriya da Afirka ta Kudu sun fara aiki da kwamatin da suka kafa a tsakaninsu na inganta harkokin zuba jari da kuma tattalin arziki, a cewar gwamnatin Afirka ta Kudun.

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyrill Ramaphosa ne ya sanar da hakan ranar Talata a birnin Cape Town yayin tattaunawa da 'yankasuwar manyan ƙsashen mafiya girman tattalin arziki a Afirka.

    Yayin ganawar, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa ƙasarsa za ta tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali, da dokokin da hajojin Afirka ta Kudu za su samu tagomashi a Najeriya.

    Tinubu ya kuma nemi Afirka ta Kudu da ta yi hakan ita ma.

    A yau Laraba ake sa ran Tinubu zai koma Najeriya bayan shafe kwana uku a ziyarar aikin, da kuma wasu kwana huɗun a Faransa.

  10. Ina neman afuwa kan goyon bayan ƙudurorin haraji - Kofa

    Haraji

    Asalin hoton, Abdulmumin Jibrin

    Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Ƙiru da Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ba ɗari bisa ɗari yake goyon bayan ƙudurorin gyara haraji ba, sannan ya ƙara da cewa yana bayar da haƙuri.

    Kofa ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba, inda a ciki ya ce, "babu wurin da ko sau ɗaya na ce ina goyon bayan sababbin dokokin haraji ɗari bisa ɗari."

    A cewarsa, "Abin da na ce (shi ne) akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga yankin arewa da ma Najeriya. Kuma mu ƴan majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a majalisa mu yi tsayin-daka mu goyi bayan duk wasu ƙudurorin da za su amfani arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankinmu da suke cikin kudurorin. Sannan mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su ta yadda ba za su cutar da mu ba."

    A cikin rubutun ya ƙara da cewa yana so ne yankin arewa su yi amfani damar dokar wajen bijiro da wasu sabbin hanyoyi, "mu shigar da su a cikin kundin ƙudirorin," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata ko Arewa da ma Najeriya ba."

  11. Nijar ta ƙwace harkokin haƙo ma'adinin uranium daga Faransa

    Uraniun

    Asalin hoton, ORTN

    Kamfanin makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya ce gwamnatin soji ta Nijar yanzu ta ƙwace ayyukan da ake yi na haƙo Uranium a ƙasar.

    A watan Yuni ne mahukuntan ƙasar suka soke lasisin aikin kamfanin na Orano a Nijar, ƙasar da take ɗaya daga cikin mafiya arziki Uranium a duniya, inda daga lokacin Orano ya dakatar da aikinsa.

    Wakilin BBC ya ce kamfanonin haƙar ma'adinai a Nijar sun jima a ƙasar fiye da shekaru 50, inda ake yawan samun rikici da gwamnatocin ƙasar dangane da ayyukan wasu kamfanonin haƙar ma'adinan.

    Tun bayan da suka yi juyin mulki a ƙasar a watan Yuli, sojojin suka ce za su yi garambawul a dokokin ayyukan kamfanonin da suke haƙar ma'adinai a ƙasar.

    Nijar ce take fitar da kusan kashi biyar da uraniun da ake amfani da shi a duniya, wanda hakan ya sa ta shiga cikin ƙasashen 10 da suka fi fitar da ma'adinin wanda ake amfani da shi wajen sana'anta nukiliya.

    Kafin juyin mulkin, Nijar ce take samar da kashi 15-20 na uraniun da Faransa ke amfani da shi.

    Orano ta kwashe watanni tana ƙorafin cewa ana kawo mata tangarɗa a harkokinta na haƙo ma'adininin a Somair, wanda kashi 36.6 na wurin mallakin Nijar ne.

    Nijar

    Asalin hoton, AFP

  12. Zaɓen Ghana: Manyan alƙawurra huɗu da Bawumia da Mahama suka yi wa masu zaɓe

    Ghana

    Asalin hoton, AFP

    Kusan dai za a ce dukkannin ‘yantakarar guda 12 na da muradai masu kama da juna a fannin lafiya da tattalin arziki da ilimi da samar da ayyukan yi ga al’ummar kasa musamman matasa.

    To sai dai an fi mayar da hankali kan alkawurran manyan ‘yantakarar guda biyu wato mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bamuwua na jam’iyyar NPP da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahma na jam’iyyar NDC kasancewarsu gaba-gaba a takarar.

    Ƙasar Ghana dai na cikin yanayin matsin tattalin arziƙi inda a yanzu haka take da nauyin bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 51.67, baya ga rashin aikin yi da kuma rashawa da cin hanci da suka yi wa ƙasar kakatutu.

    Bisa waɗannan alƙawurra ne da manufofin 'yantakarar, masu zaɓe a Ghana kimanin miliyan 19 za su yi zaɓe su darje domin duk inda ka je tattaunawar da ake yi ke nan.

  13. Alhamis za a rufe yaƙin neman zaɓe a Ghana

    Ghana

    Asalin hoton, AFP

    A gobe Alhamis ne ake sa ran rufe gangamin yaƙin neman zaɓe a babban zaɓen ƙasar Ghana.

    Mutum 12 ne ke takarar neman kujerar shugabancin ƙasar domin maye gurbin Shugaba Nana Akuffo Addo, wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.

    Sai dai an fi ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP, da John Dramani Mahama na jam’iyyar hamayya ta NDC.

    Za a kaɗa ƙuri'a a ranar Asabar, sannan za a iya samun sakamakon zaɓen cikin kwana uku.

  14. Kotu ta saki matar da ta shekara 40 a gidan yari bisa kuskure

    Kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Amurka ta amince da hukuncin ƴantar da wata mata da ta shafe fiye da shekara 40 a gidan yari ka kisan da ba ita ta aikata ba.

    Sandra Hemme tana da shekara ashirin kuma ba ta cikin hayyacinta lokacin da ta amsa laifin kisan wani ma'aikacin ɗakin karatu a jihar Missouri a shekarar alif ɗari tara da tamanin.

    An yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai, amma yanzu an soke hukuncin da aka yanke mata ne a watan Yuni lokacin da wani alƙali ya same ta da rashin laifi aka kuma samu kusan tabbacin cewa wani ɗansanda ne ya aikata laifin kisan. Lokacin da aka sake ta a watan Yuli ita ce macen da ta fi daɗewa a gidan yari a Amurka.

  15. Aƙalla mutum shida sun mutu, takwas sun ji rauni bayan motarsu ta taka bam a Zamfara

    Hadarin mota

    Asalin hoton, Channels TV

    Aƙalla mutum shida ne suka mutu wasu kuma aƙalla takwas suka ji munanan raunuka bayan da wata motar fasinja ta taka nakiya da ake zargin ‘yan bindiga ne suka dasa ta, a kan hanyar zuwa garin Ɗansadau da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Al’ummar garin na Ɗansadau sun tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda suka ce motar fasinjar ƙirar Golf, na tafiya ne lokacin da ta taka wannan nakiyar, wadda kuma ta yi fata-fata da motar.

    Mazauna yankin sun ce a yanzu, suna cikin fargabar fuskantar wannan sabon salon kai hari da ‘yan bindigar ke amfani da shi, domin hana jami’an tsaro kai musu hari da kuma ke zama wani matakin kashe jama’a musamman matafiya.

    Duk wani ƙoƙari da BBC ta yi na ji daga ɓangaren gwamnatin Zamfara, kan al'amarin ya ci tura, yayin da ita ma rundunar ‘yansandan jihar kiran wayar da BBC ta yi don jin ta bakinta ba ya shiga.

    Wannan shi ne karo na biyu a ɗan tsakanin nan da wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka dasa irin wannan nakiyar a wannan mako.

    A ranar Lahadin da ta gabata, ne ake zargin maharan sun dasa wata nakiya a garin Maru da ke jihar ta Zamfara, da wata motar haya ta taka, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya

  16. An kama wani fitaccen ɗan gwagwarmaya a Nijar

    A jamhuriyar Nijar wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kama, ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗanjarida, Moussa Tchangari.

    Kawo yanzu ba a san inda, mutumin wanda kuma shi ne sakataren ƙungiyar nan ta farar hula ta Alternative Espace Citoyens (AEC), yake, ba.

    Tun a jiya Talata ne wasu mutane suka kama Tchangari, a gidansa bayan ya bar filin jirgin sama daga wani bulaguro da ya je Abuja, babban birnin Najeriya.

    Wasu makusantansa sun yi bayanin cewa shigarsa gida ke da wuya mutanen suka shiga har ɗakinsa a gaban mata da yara suka yi awon-gaba da shi tare da wasu kayayyakinsa da suka haɗa da wayar salula da wata akwati da kuma kwamfuta.

    Sai dai wasu na ganin kamun na da nasaba da wata mahawara da ƙungiyar ta Alternative ta shirya inda masana suka yi Allah-wadarai da dokar shugaban mulkin sojan ƙasar ta ƙwace izinin zama dan ƙasa ga wanda aka kama da laifin ta’addanci ko aikata wani laifi na cin amanar ƙasa.

    Bayanai sun ce an jibge wata bataliyar sojoji a ƙofar gidansa - ba shiga ba fita.

    Ƙungiyoyin farar hula a Nijar ɗin na kira ga hukumomin sojin ƙasar da su fito su yi bayani kan dalilin kama shi da kuma inda yake.

  17. Majalisar dattijan Najeriya ta kafa kwamitin sake duba ƙudurin haraji

    Majalisa

    Asalin hoton, President of Senate/Twitter

    Majalisar dattijan Najeriya ta sanar da jingine tattaunawa kan ƙudurin sauye-sauye ga dokar haraji ta ƙasar a matakin kwamitin kuɗi, wadda shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatar mata.

    Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a yau Laraba lokacin muhawararta a zauren majalisar da ke Abuja.

    Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da gwamnatin ƙasar ta umarci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da Majalisar Dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.

    Tattaunawa kan ƙudurin ya janyo zazzafar muhawara a faɗin Najeriya, yayin da wasu ɓangarorin ƙasar suka yi zargin cewa an cusa wasu abubuwa da za su cutar da wasu yankunan ƙasar.

    A yanzu Majalisar ta umarci kwamitin da ta miƙa wa ƙudurin da ya jingine duk wani nazari a kansa, yayin da aka kafa wani kwamiti wanda zai yi aiki tare da ma'aikatar shari'a ta ƙasar domin duba ɓangarorin ƙudurin da ake taƙaddama a kai.

  18. Mutum 12 sun mutu a haɗarin mota a jihar Yobe

    Haɗari

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum goma sha biyu sun mutu a wani haɗarin mota da ya faru a daren da ya gabata na Talata, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Mutanen sun ƙunshi maza manya goma da babbar mace ɗaya da kuma wata 'yar ƙaramar yarinya ɗaya, kamar yadda shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar, reshen jihar ta Yobe, Livinus Yilzoom ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai, a babban birnin jihar, Damaturu.

    Kwamandan ya ce haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma na daren da ya gabata a ƙauyen Chelluri daidai kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam.

    Ya ce haɗarin ya afku ne lokacin da motar da mutanen da suka rasu ke ciki, kirar Sharon ta yi karo da wata babbar mota ƙirar Howo ta wani kamfanin aikin gine-gine wadda take tsaye a hanya.

    Mista Yilzoom, ya ce karon da Sharon ɗin ta yi ne ta kama da wuta kuma mutanen da ke cikinta suka ƙone yadda ba za a iya gane su ba.

  19. An zaɓi mace ta farko shugabar ƙasa a Namibia

    Netumbo Nandi-Ndaitwah

    Asalin hoton, Reuters

    'Yar takarar jam'iyya mai mulki a Namibia, Swapo, Netumbo Nandi-Ndaitwah, ta zama mace ta farko da aka zaɓa shugabar ƙasar a zaɓen makon da ya gabata wanda ake taƙaddama a kansa.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ce Nandi-Ndaitwah mai shekara 72, ta samu sama da kashi 57 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa inda ɗan takara mafi kusa da ita, Panduleni Itula ya samu kashi 26 cikin ɗari.

    Nandi-Ndaitwah, wadda ita ce mataimakiyar shugaban ƙasar a yanzu, da wannan nasara za ta kasanace shugaba ta biyar kenan tun bayan da ƙasar ta yankin kudancin Afirka ta samu 'yancin kai a 1990.

    Kuma jam'iyyarta, Swapo, ita ce ke mulki tun daga samun 'yancin har yanzu.

    Sakamakon matsalolin da aka gamu da su na kayan aiki da kuma ƙarin kwana uku da aka yi a zaɓen a wasu sassan ƙasar, Itula ya yi zargin an yi maguɗi a zaɓen.

    Yawancin jam'iyyun hamayya sun ƙaurace wa wajen bayyana sakamakon zaɓen a jiya Talata da daddare, a babban birnin ƙasar Windhoek.

    Idan aka rantsar da ita za ta zama mace ta biyu kenan da ke shugabanci a Afirka, inda a yanzu ake da Samia Suluhu Hassan a Tanzania.

  20. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana neman dala biliyan 47 don ayyukan agaji a 2025

    Wani yaro zaune da buhuna biyu

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana buƙatar dala biliyan 47 don taimakawa wajen gudanar da ayyukan agaji a shekara mai kamawa.

    Majalisar ta kuma yi kira da a sake daidaita batun tallafi ga mutanen da suka faɗa cikin bala'in rikice-rikice.

    Bincike ya nuna cewa a bana an samu ƙaruwar tashin hankali a duniya wanda ya yi sanadiyyar kashe ma'aikatan agaji da dama.

    Tuni wasu manyan ƙasashe masu bayar da tallafi kamar Burtaniya da Jamus suka ce za su rage tallafin da suke bai wa Majalisar a shekara mai zuwa.