Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana ta Talata.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa da mu.

    Sai kuma gobe Laraba, inda za mu ɗaura.

    Mu kwana lafiya.

  2. 'Hare-hare a Gaza sun yi ajalin mutum biyu'

    Hukumomi a Isra'ila sun ce akalla mutum daya ya rasa ransa yayin da uku suka samu munanan raunuka bayan wani hari da aka kai da mota da kuma suka da wuka a Gabar Yamma da Kogin Jodan.

    Rundunar sojojin Isra'ila ta ce dakarunta sun harbe Falasdinawa biyu, an kuma samu abubuwan fashewa a cikin motar da suka yi amfani da ita wurin kai harin.

    Hamas da wata Kungiyar Fasdinawa mai ikirarin jihadi sun yi maraba da harin wanda mutanen biyu suka kai.

  3. 'Hare-hare a Gaza sun yi ajalin mutum biyu'

    Hukumomi a Isra'ila sun ce akalla mutum daya ya rasa ransa yayin da uku suka samu munanan raunuka bayan wani hari da aka kai da mota da kuma suka da wuka a Gabar Yamma da Kogin Jodan.

    Rundunar sojojin Isra'ila ta ce dakarunta sun harbe Falasdinawa biyu, an kuma samu abubuwan fashewa a cikin motar da suka yi amfani da ita wurin kai harin.

    Hamas da wata Kungiyar Fasdinawa mai ikirarin jihadi sun yi maraba da harin wanda mutanen biyu suka kai.

  4. Shugabar Tanzania ta ce matsaloli za su iya hana ƙasar samun rance daga ƙasashen waje

    Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassana ta ce sakamakon yadda kasarta ta fada jerin kasashen da ke da tabo a duniya, hakan zai iya sa ta fuskanci kalubale wajen samun damar rancen kudade daga manyan kasashe.

    An samu tashe-tashen hankali a kasar Tanzaniya bayan sanar da Mis Suluhu Hassana a matsayin shugabar kasa.

    Majalisar Dinkin Duniya Da Kungiyoyin fararen hula sun ce jami'an tsaro sun kashe daruruwan masu zanga-zanga, sai dai gwamnatin Tanzaniyar ta musanta wadannan bayanai.

  5. Ƴansandan Indiya sun kashe wani jagoran ƴantawayen Maoist

    'Yansanda a kudancin Indiya sun ce sun kashe daya daga cikin shugabannin 'yan tawayen Maoist da suka dade suna nema ruwa a jallo.

    Shugaban 'yansandan jihar Andhra Pradesh Harish Kumar Gupta, ya ce an kashe shugaban kungiyar mai suna Madvi Hidma tare da wasu 'yan tawaye shida a wata fafatawa da 'yansanda.

    Wakilin BBC ya ce ana zargin Madvi Hidma da kai hare-hare da dama ciki har da na kwanton bauna a 2013 da ya yi sanadiyyar muwar mutum 27 ciki har da manyan 'yan siysar kasar ta Indiya.

  6. MDD ta ce duniya na fuskantar barazanar ƙaruwar yunwa

    Shirin Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa ana samun karuwar yunwa a duniya sakamakon raguwar samar da tallafin jinkai ga kasashen masu fama da talauci.

    Shirin na WFP ya ce kimanin mutum miliyan dari uku da sha takwas ne za su yi fama da yunwa a shekarar 2026 mai kamawa.

    Ya ce tsanani rashin abinci da ake fama da shi a Gaza da Sudan ya zama wajibi a kaucewa ci gaba da hakan a karni na ashirin da daya.

    Amurka da sauran kasashen da ke samar da agaji a duniya sun rage yawan kudaden tallafi da suke samarwa Shirin Samar da Abincin na Majalisar Dinkin Duniya da kuma ake ganin babban gibi ne a bangaren yaki da yunwa da talauci a duniya.

  7. Zelensky zai kai ziyara ƙasar Turkiya

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce zai yi tafiya zuwa Turkiyya a ranar Laraba a wani matakin yukurin da yake na sake farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya tsakaninsa da Rasha.

    Sanarwar wadda shugaban Ukraine ya fitar na zuwa ne a yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da kai hare-hare ta ƙasa.

    A lokaci guda kuma wasu jerin hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami sun lalata wasu cibiyoyin samar da makamashi na Ukraine.

    A baya Turkiyya ta karɓi baƙuncin tawagogin Ukraine da Rasha a tattaunawar da gudanar, sai dai zuwa yanzu ba a tabbatar da ko da wa Zelensky zai gana ba, amma majiyoyi daga Turkiyya sun ce wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff na daga cikin wadanda za su dafa masa baya.

  8. Saudiya za ta ƙara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan 1

    Ƙasar Saudiyya za ta ƙara hannun jarinta a ƙasar Amurka zuwa dala tiriliyan ɗaya, daga dala biliyan 600 da ƙasar ta kasance ta zuba a baya.

    Yarima Mohammed bn Salman ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi.

    Tun da farko, Trump ne ya bayyana buƙatar Saudiyya ta ƙara hannun jarinta a Amurka, sannan ya buƙaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, "tabbas."

    Da wani ɗan jarida ya tambaya yariman ko Saudiyya za ta iya ƙara hannun jarin zuwa dala tiriliyan 1 duba da yanayin faɗuwar farashin man fetur a duniya, inda farashin gangan mai ya koma dala 60 daga kusan dala 80, sai bin Salman ya ce, "ba damarmakin bogi za mu samar domin daɗaɗa wa Amurka ko Shugaba Trump ba. Damarmaki na gaskiya za mu samar."

    Ya bayar da misali da ƙirƙirarriyar basira da ya ce Saudiyya na matuƙar buƙata, sannan ya ce ƙulla alaƙar da Amurka za ta Saudiyya abubuwan da take buƙata a ɓangaren.

    Trump ya nanata wa bn Salam cewa yana "alfahari" da kasancewa abokinsa, sannan ya ƙara da cewa Amurka na "godiya da zuba jarin."

    "Yanzu kuma jarin zai koma dala tiriliyan 1," in ji Trump. "Na ji daɗi da ka fito da maganar da kanka domin ba zan so a ce ni ne na faɗa ba."

  9. Netanyahu ya yi maraba ƙudurin MDD na amincewa da tsarin Trump kan zaman lafiya a Gaza

    Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya yi maraba da amincewa da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya, da ke goyon bayan shirin shugaba Trump na na samar da zaman lafiya a Gaza da kuma share fagen fara aiwatar da mataki na biyu na shirin.

    Wakilyar BBC ta ce: Isra'ila da kasashen Larabawa da Amurka, na kan tattaunawar da ake ganin za ta jagoranci kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar dunkin Duniya akan wanzar da zaman lafiya a Gaza, mataki na biyu.

    Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Falasdinawa ta yi maraba da shirin sai dai kungiyar Famas ta sa kafa ta yi fatali da shi, inda ta ce ba za ta taba ajiye makamanta ba har sai an samar da 'yantacciyar kasar Falasdinawa.

  10. Sowore ya ziyarci Sheikh Abduljabbar a gidan yarin Kuje

    Fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore ya ziyarci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

    Sowore ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya sanya hotunan ziyarar sannan ya rubuta cewa, "yau na kai wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje tare da rakiyar Barista Hamza Nuhu Dantani.

    "An yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ne a Kano bisa zarginsa da ɓatanci a zamanin tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje," in ji shi, inda ya ce ɗaurin na da alaƙa da siyasa.

    Sowore ya ce ya yi mamakin yadda, "aka haɗa baki da wasu na kusa da malamin wajen ganin an tasa ƙeyarsa gidan yari."

    Ya ce sun samu malamain cikin karsashi da walwala, "inda ya bayyana mana cewa Allah ne yake tsare da shi, kuma zai ci gaba da riƙo da koyarwar Allah har zuwa ƙarshen rayuwarsa."

    Sowore ya ce babu mutumin da ya cancanci rashin adalci, sannan ya ce dole ne a tabbaar da adalci ga Abduljabbar tare da kawo ƙarshen abin da ya bayyana da amfani da addini da wasu "gurɓatattun ƴansiyasa ke yi."

  11. 'Cristiano Ronaldo ya isa fadar White House domin ganawa da Trump'

    Rahotanni na cewa kyaftin ɗin tawagar Portugal da ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya Cristiano Ronaldo shi ma ya isa Amurka domin ganawa da Trump, kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana.

    Sai dai babu tabbacin ko ya kasance a cikin tawagar Yariman Mohammed bn Salma ne, ko kuma jirgi daban ya hau.

    Ronaldo ya daɗe bai shiga Amurka ba saboda zarginsa da aka yi da yi wa wata ƴar ƙasar fyaɗe, zargin da ya musanta.

  12. Yariman Saudiyya ya isa Amurka domin ganawa da Trump

    Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman ya isa fadar White House domin ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump.

    Wannan ce ziyarar bin Salman da farko zuwa fadar gwamnatin Amurka tun a shekarar 2018, shekarar da aka aka kashe fitaccen ɗanjarida Jamal Khashoggi.

    Daga cikin abubuwan da ake tunanin jagororin ƙasashen biyu za su tattauna akwai ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsaro da zuba jari a ƙirƙirarriyar basira da yaƙin Gaza.

    Wannan na zuwa ne bayan Trump ya sanar a ranar Litinin cewa Amurka za ta sayar wa Saudiyya da jirgin yaƙin Amurka ƙirar F-35.

    A watan Mayu ne Trump ya ziyarci Saudiya, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyoyi da dama, waɗanda Amurka ta ce sun kai na dala biliyan 456.

    Wakilin BBC ya ce yariman na Saudiyya ya samu tarba mai kyau, inda ya ce an yi wa babban baƙon tarba ta alfarma da girmamawa.

    Sai dai daga cikin abubuwan da suka ja hankali kan ziyarar akwai zuwan Cristiano Ronaldo, wanda zai kasance cikin waɗanda za su gana da Trump.

    Ronaldo dai ya daɗe bai shiga Amurka ba, kasancewar yana fuskantar zargin yi w wata ƴar ƙasar fyade tun a shekarar 2009, zargin da ya musanta.

  13. Ɗaliban Kebbi biyu sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa

    Aƙalla ɗalibai biyu cikin 25 da ƴanbindiga suka sace a Makarantar Sakandiren ƴanmata dake garin Maga a jihar Kebbi sun kuɓuta.

    Mazauna garin da BBC ta zanta da su sun bayyana cewa ƴanmatan biyu sun samu sulalewa a lokacin da ƴanbindigar ke kora su a cikin daji.

    Yanzu haka jami'an tsaro sun bazama domin neman sauran ɗaliban 23 da ke hannun ƴanbindigar.

    Wani malamin makarantar ya shaida wa BBC cewa hukumomin makarantar na bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin taimaka wa aikin ceton.

    Da asubahin ranar Litinin ne wasu ƴanbindiga ɗauke da muggan makamai suka far wa makarantar ƴanmatan tae da sace ɗalibai 25.

  14. Majalisa ta buƙaci Tinubu ya ɗauki sabbin sojoji 100,000

    Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci Tinubu ya umarci rundunonin sojin ƙasar su ɗauki ƙairin jami'an aƙalla 100,000 domin ƙarfafa yaƙin da gwamnati ke yi da matalar tsaro a ƙasar.

    Matakin na zuwa ne bayan da ɗan majalisar dattawa daga jihar Kebbi, Yahaya Abdullahi ya gabatar da ƙudiri kan batun, inda ya alaƙanta hakan da sace ɗalibai 25 na sakandiren yanmata a jihar Kebbi.

    Sanata Yahaya ya ce ace ɗaliban cin fuska ne ga hukumomin ƙasar, yana mai cewa sace ɗalibai a makarantu zai hana ɗalibai mata zuwa makarantu a ƙasar.

    A nasa ɓangare Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya nuna damuwarsa kan yadda ake yawan sace ɗalibai a makarantunsu a ƙasar.

    Tuni dai majalisar ta kafa kwamiti da zai binciki lamarin da yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka ware wa shirin kare makarantu na ƙasar.

  15. Gwamnatin Katsina ta buƙaci Sheikh Masussuka ya bayyana gaban kwamitin malamai

    Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirya zama tsakanin fitaccen malamin nan na Sheikh Yahya Masussuka da kwamitinin malaman jihar domin ya kare kansa.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta buƙaci malamin ya bayyana a gaban kwamitin malaman jihar domin kare kansa game wasu kalaman da yake furtawa a karatunsa.

    Tun da farko wasu malamai a jihar ne suka shigar da ƙorafinsu ga gwamnatin jihar saboda zarginsa da wuce gona da iri a karatuttukansa.

    Bayan ƙorafin malaman ne kuma sai wasu malaman da ke goyon bayansa suka shigar da ƙorafinsu gaban gwamnati cewa wasu na yi wa Sheikh Masussuka barazana da cin mutuncinsa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Sanarwar ta ce bayan zaman da za a yi tsakanin malamin da kwamitin malaman jihar za a samar da wasu ƙa'idojin wa'azi a jihar.

    Inda gwamnatin ta ce za ta tabbatar abin duka ƙa'idojin da aka cimma tare da hukunta duk wanda ya kauce musu.

  16. Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin kuɓutar da ɗaliban Kebbi

    Gwamnatin Najeriya ta yi Alla -wadai da harin da ƴanbindiga suka kai makarantar sakadiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi, wanda ya kai ga kashe jam'ian makarantar da sace ɗalibai 25.

    Cikin wata sanarwar da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa jami'an taro da jami'an tattara bayanan sirri umarnin gano inda aka ɓoye yaran domin kuɓutar da su ba tare da wata matsala ba.

    Gwamnatin ta nuna matuƙar damuwa da alhininta ga iyayen ɗaliban da aka sace.

    Mohammed Idris ya ce gwamnati na tare da iyalan a wannan lokaci na alhini, kuma za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar an kuɓutar da ɗaliban.

  17. Netanyahu ya yi maraba da mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi maraba da shawarar kwamitin tsaro na MDD na goyon bayan mataki na biyu na yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da Trump ya kawo.

    Ofishin Netanyahu ya ce shirin zai samar da zaman lafiya da ci gaba a Gaza, tana mai jaddada janyewar sojoji daga yankin.

    Ma'aikatar wajen Falasɗinawa ta yi maraba da shawarwarin amma Hamas ta yi watsi da su.

    Tana mai cewa ba za ta bayar da makamanta ba matsawar ba a amince da kafa ƙasar Falasɗinu ba.

    Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa yaƙ da Isra'ila halastaccen turjiya ne a gareta.

  18. An samu hargitsi a sakatariyar PDP da ke Abuja

    An samu wata hatsaniya a shalkwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja, sakamakon cin karo da juna daga ɓangarorin jam'iyyar masu hamayya da juna.

    Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ɓangarori biyu na jam'iyyar suka yi yunƙurin ƙwace iko da shalkwatar da ke Wadata Plaza.

    Tun da farko ɓangarorin jam'iyyar biyu sun kira mabambantan taruka a harabar shalkwatar jam'iyyar.

    Ɓangarorin biyu sun haɗa da na gwamnan Bauchi, Bala Mohammed wanda Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, Sai kuma tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya ƙunshi tsohon sakataren jam'iyyar, Samuel Anyanwu.

    Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ce sai da jami'an tsaro suka hana wasu jiga-jigan jam'iyyar shiga shalkwatar.

  19. Babban hafsan sojin Najeriya ya kai ziyara jihar Kebbi

    Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu ya umurci dakarun operation Fansan Yamma su ƙara kaimi a ƙoƙarinsu na kuɓutar da ɗaliban da aka yi garkuwa da su daga makarantar sakadire ta ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi.

    Da ya ke yi wa dakarun jawabi a lokacin da ya kai ziyara jihar, babban hafsan sojan ya buƙace su su yi amfani da bayanan sirrin da suke samu yadda ya kamata wajen gudanar da ayyukansu, kuma su ci gaba da farautar ƴan bindigar ba dare ba rana ba tare da gajiyawa ba.

    Cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na Operation Fansan Yamma Captain David Adewusi ya fitar, ya kuma ce Janar Shaibu ya gana da jam'ian sa kai da masu farauta, inda ya bayyana su a matsayin abokanan aiki masu muhimmanci.

    Ya kuma buƙace su da su yi amfani da ilimin su na sannin lungu da saƙo na yankin tare da haɗin gwiwar sojojin domin gano tare da hallaka ƴan bindigar.

    ''Wajibi ne mu ceto yaran nan, ku yi aiki bisa ƙwarewa kan bayanan da za ku samu, wajibi ne a yi nasara.'' a cewar shi.

  20. An rufe gidajen yin ruwan leda sama da ashirin a Yamai

    Ma’aikatar kasuwancin jamhuriyar Nijar ta rufe gidajen sarrafa ruwan leda guda 21 a cikin birnin Yamai.

    Ma'aikatar ta ce ta ɗauki matakin ne a matsayin ladabtarwa ga kamfanonin da suka ƙi mutunta dokokin tsafta da ta gindaya masu.

    Wani mai bayar da shawara a ofishin ministan ya ce wasu daga cikinsu ba su da isassun kayan aiki ne, wasu kuma rashin tsafta, inda ya ce an bayyanawa kowa kura kurensa, kuma sun amince da hakan saboda sun san saboda alumma ake yi.

    Ya ƙara da cewa an basu lokaci su gyara, kuma da zarar sun gyara kura kuren za a buɗe su cigaba da ayyukan su.

    Wani mai sayar da ruwa a birnin na Yamai, ya ce tabbas akan samu ruwan da ake kawo musu da ke da dauda a ciki, inda a wasu lokutan mutane kan dawo musu da ruwan idan suka gane ruwa ne mara kyau.

    Ibrahim Hamisu, wani mai kamfanin samar da ruwa, ya kuma ce an fi samun matsalar ne daga masu amfani da rijiyar burtsatsai, kuma watakil ba su da na'urorin tacewa mai karfi.

    Ya ce domin kaucewa irin wannan matsala, su sukan samo ruwansu ne daga gidan ruwa na ƙasa, kuma su kan sake tacewa a wurin su domin tabbatar da kyan sa.

    Wani mai fafutukar kare haƙƙin masu sayen kaya a ƙasar Mamman Nouri, ya yabawa ma'aikatar, musamman kan matakin ta na hana ajiye ruwan a cikin rana, inda ya ce wannan mataki ne mai muhimmmanci da suka daɗe suna buƙata.

    Wannan dai ba shi ne karon farko da ake ɗaukar irin wannan matakin ba, ko a watannin da suka gabata sai da aka rufe wasu gidajen biredi.