Sojojin Ukraine sun ce sun lalata sansanin horaswar Rasha
'Kutsawar magoya baya cikin fili don ɗaukar hoto da Ronaldo abin damuwa ne'
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdullahi Bello Diginza
Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda shida a Rasha
Wasu mahara sun kai hari a
cocin Orthodox da wani shingen
binciken na yan sanda a Dagestan dake kudancin Rasha.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce an kashe ƴan sanda
shida tare da jikkata wasu goma sha biyu.
Kafofi ƴaɗa labaran Rasha sun ruwaito cewa an kashe
limamin cocin.
Hukumomin sun ce an yi nasarar harbe biyu daga cikin
maharan, ana kuma ci gaba da bincike..
Ba a dai gane maharan ba, amma Dagestan ya zamo wani wuri da ke yawan samun hare-haren ƙungiyoyi masi iƙirarin jihadi.
Amurka na da hannu a harin da aka kai mana - Rasha
Rasha ta ce zata ɗora wa Amurka alhakin duk abin da ya faru, bayan makami mai linzamin da Ukraine ta harba ya kashe mutane aƙalla biyar a yankin Crimea, ciki harda ƙananan yara.
Hukumomin Rasha sun ce wasu mutum fiye da ɗari sun jikkata, bayan makamin ya faɗa a gefen teku, inda mutane ke shakatawa a kusa da Sevastopol.
Ma;aikatar tsaron Rasha ta ce an kai harin ne da makami mai linzami ƙirar ATACMS, wanda Amurka ta ƙera, kuma ta yi iƙirarin cewa ƙwararru daga Amurkan ne suka tsara yadda za a kai harin.
Ta kuma ce ta harbo huɗu daga cikin makamai masu linzamin da aka kai mata harin da su.
Ƴan sandan Kenya za su yi aikin tabbatar da tsaro a Haiti
Asalin hoton, AFP
Rahotanni sun ce tawagar ƴan sandan Kenya za ta bar ƙasar ranar Talata domin zuwa aikin tabbatar da tsaro na ƙasa da ƙasa a Hiati.
Wani jami'in gwamnatin Kenya ya tabbatar da hakan ga BBC amma babu cikakken bayanin yadda aikin zai kasance.
Jami'an za su jagoranci wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin kwantar da tarzoma a yankin Carribbean.
Gwamnatin Kenya ta yi tayin tura dubban ƴan sanda Hiati, daga cikin yarjejeniyar da suka ƙulla a watan Maris.
An yi jikirin tura jami'an ne saboda bin diddigin shari'a, amma shugaba William Ruto ya ce yarjejeniyar za ta fara aiki a cikin makonni masu zuwa.
Ƙungiyoyin kare ƴancin ɗan Adam suna zargin ƴan sandan Kenya da aikata kisan gilla.
Mutane miliyan ɗaya na cikin barazanar ambaliya a Amurka
Asalin hoton, Reuters
Mutane fiye da miliyan ɗaya ne aka yi gargaɗin suna iaya fuskantar ambaliya a muhallin su, bayan shafe kwanaki ana ruwan sama a tsakiya maso yammacin Amurka, lamarin da ya tilasta kwashe mutane a jihohi da dama.
Lamarin ya fi muni a Iowa da South Dokata, inda aka yi hasashen ambaliyar teku za ta kai mafi ƙololuwa a tarihi.
Gwamnan Iowa, Kim Reynolds ya kira lamarin a matsayin mummunan abin takaici, kuma ya ƙaddamar ayyukan ɗauki a yankuna 21.
Hotunan da aka ɗauka ta sama sun nuna yadda ruwan ya kusa shanye gidaje.
Sauran jihohin da ke fuskantar barzanar sun haɗa da Nebraska da Minnesota da Wisconsin da kuma wasu sassan Illinois.
Matan Faransa na zanga-zanga adawa da manufofin jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi
Asalin hoton, Getty Images
Dubban mata a Faransa na zanga-zangar nuna adawa da manufofin jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi a biranen ƙasar ciki har da Paris.
Jam'iyyar na kan gaba a zaɓen zagayen farko na majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar cikin mako, to sai dai ba lallai ne ta samu rinjaye a majalisar ba.
Masu zanga-zangar na fargabar cewa jam'iyyar ka iya tauye 'yancin mata, ciki har da tsiraru kamar 'yan ci-rani.
To sai dai jam'iyyar ta musanta iƙirarin tauye 'yancin mata da sauran haƙƙoƙinsu.
Jam'iyyar ta bayar da misalai kan alƙawuran da ta ɗauka na ƙarfafa hukunci kan laifukan da suka shafi jinsi.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa mata da dama ne suka zaɓi jam'iyyar a lokacin zaɓukan baya-bayan nan na majalisar tarayar Turai.
Netanyahu ya nuna damuwa kan jinkirin da Amurka ke yi na bai wa ƙasarsa makamai
Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya buƙaci kauce wa samun saɓani da Amurka kan abin da ya bayyana da jinkirin kai wa ƙasarsa makaman da Amurkan ta alƙawarta wa Isra'ila.
Jami'an Amurka sun bayyana damuwarsu da bayan da Mista Netanyahu ya zargi Amurka da hana ƙasarsa makamai da harsasai har na tsawon kusan wata huɗu.
To sai a ranar Lahadi netanyahu ya faɗa wa ministocinsa cewa an warware matsalar, yana mai cewa nan ba da jimawa komai zai wuce.
Jawabin Netanyahun na zuwa ne a daidai lokacin da ministan tsaron ƙasar, Yoav Gallant, ya je Amurka don tattauna mataki na gaba a yaƙin da ƙasar ke yi da ƙungiyar Hamas a Gaza.
Amurka dai ta dakatar da jigilar makaman da suka haɗa da manyan boma-bomai, saboda fargabar Isra'ila ka iya amfani da su a Rafah, to amma ta musanta samun gagarumin sauyi a ƙawancenta da Isra'ila.
Shugaban Kenya zai tattauna da masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Shugaba Ruta a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe
Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto ya ce zai tattauna da matasan ƙasar da ke zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin ƙasar na ƙarin kuɗin haraji.
Mista Ruto ya ce tattaunawar za ta warware matsalolin da suka haifar da zanga-zangar da matasan ƙasar ke gudanarwa.
Yayin da yake jawabi a taron ibada a wata coci da ke tsakiyar ƙasar, Shugaba Ruto ya nemi a yi sasanci, bayan da ya jinjina wa matasan kan kafewa kan muradunsu.
Zanga-zangar - da mafi yawan matasan ƙasar ke yi - ta ja hankalin gwamnatin ƙasar.
Mutum biyu ne suka mutu, yayin da gommai suka jikkata a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a birnin Nairobi da sauran biranen ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ta ce ta ƙara harajin ne domin samar da dala biliyan 2.6 na kasafin kuɗin ƙasar, don rage yawan karɓar bashi.
Ya kamata a rusa hukumar Nahcon saboda ta gaza - Bago
Asalin hoton, Mohammed Umar Bago/X
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji bana.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Saudiyya game da yadda aka gudanar da aikin, Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta binciki Nahcon kan yadda ta kashe kuɗin tallafin aikin hajji na naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar.
Gwamna Bago ya ce a matsayinsa na gwamna zai buƙaci ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta yi kiran rusa hukumar Nahcon, saboda a cewarsa hukumar ba ta da wani amfani, ta gaza ta kowane fanni.
Ya ce ya kamata shirya aikin Hajji ya koma ƙarƙashin ikon jihohi ba gwamnatin tarayya ba.
''Gwamnatin tarayya ta girmi shirya aikin Hajji, wannan abu ne da ƙaramar hukuma za ta iya shiryawa, don haka ina kira a bar jihohi su riƙa shirya aikin Hajjin jihohinsu, kamar yadda wasu ƙasashen duniya ke yi''.
Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce Nahcon ta kasa samar wa gwamnoni da sauran manyan mutane masaukai a Minna.
''A ce kakakin majalisar wakilai na Najeriya da wasu gwamnoni sun kasa samun wurin da za su kwanta a filin Minna wannan abin takaici ne''.
''Wasu na cewa muna ƙorafin ne saboda abin ya shafe mu, haƙiƙa ya shafe mu saboda haka lokaci ya yi da za mu tashi mu yi kiran a mayar da shirya aikin Hajji ƙarƙashin jihohi'', in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma koka kan yadda ya ce mahajjata sun biya kuɗi masu yawa amma suka kasa samun wadataccen kuɗin guzuri daga Nahcon.
''Ta yaya mutum zai biya naira miliyan takwas amma ace dala 400 kawai za a ba shi? wannan abu ne da hankali ba zai ɗauka ba''.
Gwamna Bago ya kuma koka kan abinci da masaukai da hukumar Nahcon ta tanadar wa mahajjatan ƙasar.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi hukumar Nahcon ta zama mai lura da ayyukan Hajji ba mai gudanar da shirye-shiryen aikin hajji ba.
Ya ce alhazan jihar Neja biyu ne suka rasu sakamakon rashin lafiya, yayin da huɗu suka mutu saboda tsananin zafi
Sai dai gwamnan ya ɗora alhakin mutuwar mutanen biyu - da suka rasu sakamakon rashin lafiya - kan hukumar Nahcon.
Ya ce inda hukumomin alhazan jihohi ne ke lura da lafiyar alhazan jihohin da an samu sauƙi wajen saurin gano cutar da alhazan ke ɗauke da ita da kuma magance ta makar yadda ya kamata.
''Amma babu wanda ya yi hakan, saboda Nahcon ce ke lura da ɓangaren lafiyar alhazai''
Gwamnan ya ce kamata ya yi hukumomin alhazai na jihohi su lura da alhazan jihohinsu.
''Ya kamata a bar jihohi su riƙa tantance alhazansu, su san irin lalurorin da alhazan ke ɗake da su, tare da irin magungunan da suke sha, domin sanin matakan da za su ɗauka na lura da waɗanna alhazan, amma babu wanda ya yi hakan , saboda Nahcon ce ke da alhakin gudanar da hakan'' in ji shi.
Ba wannan ne karon farko da wani gwamna a Najeriya ya yi ƙorafi kan yadda hukumar Nahcon ta tafiyar da ayyukan Hajjin bana ba.
Ko a makon da ya gabata ma jaridun ƙasar sun ambato gwamnan jihar, Bauchi Sanata Bala Mohammed na ƙorafin yadda hukumar Nahcon ta tafiyar da shirye-shiryen aikin Hajjin na bana.
'Yan sanda sun kama matashi kan zargin garkuwa da kansa
Asalin hoton, Benjamin Hundeyin/X
Rundunar 'yan sanda jihar Legas ta ce ta kama wani matashi kan zargin ƙaryar garkuwa da kansa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a shafinsa na X, a lokacin da yake tsokaci kan wani saƙo da wani matashi da ke amfani da shafin mai suna @Flacko ya wallafa a shafin.
FlackoT ya wallafa cewa an tsare shi a ofishin 'yan sanda na Ikeja kan zargin garkuwa da wani mutum da bai san komai game da shi ba.
''Jama'a an tsare ni a ofishin 'yan sanda. Bani da isasshen lokaci, kuma ban san abin da zan yi ba, wannan ita ce kawai hanyar da zan bayyana wa duniya halin da nake ciki, saboda ku san halin da nake ciki,'' kamar yadda matashin ya wallafa.
“Wani ne ya yi ƙaryar garkuwa da kansa, ya kuma buƙaci kuɗin fansa daga wajen mahaifinsa, mahaifin nasa ya kai rahoto wajen 'yan sanda, inda su kuma suka bibiyi wayata, wllh ba abin da na sani game da batun har sai da na isa ofishin 'yan sandan''.
Yayin da yake mayar da martani kan saƙon matashin, mai magana da yawun 'yan sandan na Legas, Hundeyin ya ce binciken 'yan sanda ya gano cewa wani matashi ne mai shekara 20 ya yi ƙaryar garkuwa da kansa. Inda aka riƙa kira mahifisna da lambobi daban-daban domin neman kuɗin fansa da yadda zai biya kuɗin.
“A ranar Alhamis ne jami'an bincike suka kai samame wani gida a unguwar Lekki inda suka samu Collins da wasu abokansa biyar da suka kwashe kwana 10 suna zaune a gidan''.
'Yan sanda sun ƙaddamar da binciken kisan tsohon Janar a Abuja
Asalin hoton, Nigeria Police/X
Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, ya bayar da umarnin gudanar da binciken kisan da wasu da ake zargi 'yan fashi suka yi wa wani tsohon Janar a gidansa da ke Abuja.
Maharan sun kutsa gidan marigayin - Burgediya Janar Uwem Udokwere mai ritaya - inda suka kashe shi.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin tarayyar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kashe tsohon janar ɗin a gidansa da ke rukunin gidajen Sunshine a unguwar Lokogoma da ke birnin tarayyar, ranar Asabar da tsakar dare.
Kwamishinan 'yan sandan ya kuma jajanta wa iyalan marigayin, tare da alƙawarta farauto waɗanda suka yi aika-aikar domin gurfanar da su a gaban shari'a.
''Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da kamo maharan domin gurfanar da su a gaban shari'a domin su girbi abin da suka shuka'', in ji sanarwar.
An kashe magajin gari biyu cikin mako guda a Mexico
Asalin hoton, EPA
Jami'ai a jihar Guerrero da ke kudancin Mexico sun ce an sake tsintar gawar wani magajin garin da aka kashe, karo na biyu da ake samun irin wannan kisan cikin ƙasa da mako guda.
An tsinci gawar Acacio Flores, magajin birnin Malinaltepec, a cikin mota tare da raunin harbin bindiga a kansa bayan an yi garkuwa da shi ranar Alhamis a lokacin da yake ziyara a wani ƙauye.
Mai shigar da ƙara na jihar Guerrero ya ce an fara gudanar da bincike kan batun kisan.
Zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a baya-bayan nan a ƙasar na cike da tashe-tashen hankula.
Kusan 'yan takara 30 aka kashe a lokacin zaɓen zagaye na biyu da bayan zaɓen.
'Kutsawar magoya baya cikin fili don ɗaukar hoto da Ronaldo abin damuwa ne'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutum biyar ne suka kutsa filin don ɗaukar hoto da Ronaldo a wasan Portugal da Turkiyya
Kocin Portugal, Roberto Martinez ya ce yadda magoya bayan tawagar ƙasar ke kutsawa cikin fili don ɗaukar hoto da Ronaldo 'abin damuwa' ne.
Martinez ya bayyana haka ne bayan nasarar da tawagar Portugal ta yi kan Turkiyya ta ci 3-0 a gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Turai ta 2024.
A lokacin fafatawar mutum biyar ne suka kutso cikin fili, tare da yunƙurin ɗaukar hoto da fitaccen ɗan wasan da ke taka leda a Al-Nasr ta Saudiyya.
Lamarin da ya harzuƙa wasu daga cikin 'yan kallo da kuma 'yan wasan.
Jami'an tsaro da ke filin wasan sun yi samau nasarar daƙile kutrsen magoya bayan.
"Abin damuwa ne ƙwarai. Sai dai a yau niyyar masu kutse cikin filin mai kyau ce. Muna ƙaunar magoya bayanmu,'' in ji Martinez.
"To amma ya kamata ku sani cewa akwai hatsari idan dmummunar niyya ce da su. Ya kamata mu kula sosai, bai kamata haka ta riƙa faruwa ba, akwai jami'an tsaro da dama a filin''.
"Muna son faɗa wa magoya bayanmu cewa, ba ta wana hanya za su nuna mana ƙauna ba, idan haka ta ci gaba da faruwa to abin zai yi ƙamari a nan gaba.''
Asalin hoton, Getty Images
Wani ɗan ƙaramin yaro ne dai ya fara kutsowa cikin filin ana tsaka da wasa, inda ya nufi wajen Ronaldo wanda shi kuma ya rungumi yaron tare da yi masa murmushi a lokacin da yaron ya zaro waya don ɗaukar hoto da ɗan wasan.
Sojojin Ukraine sun ce sun lalata sansanin horaswar Rasha
Asalin hoton, Reuters
Sojojin ruwan Ukraine sun wallafa hotunan tauraron ɗan'adam da ta ce sun nuna yadda aka lalata rumbun ajiyar kayyakin Rasha da abubuwan horaswa da ake amfani da su wajen ƙaddamar da jirage marasa matuƙa da Iran ta ƙera.
Sojojin ruwan na Ukraine sun ce sun kai hari kan wurin ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaron ƙasar ranar Juma'a a Krasnodar da ke kudu maso yammacin Rasha
Hakan na zuwa ne bayan da aka yaɗa bidiyon wata fashewa da ta auku a kusa da filin jirgin sojin saman Rasha da ke Yeysk, a Krasnodar da ke kusa da tekun Azov.
Kawo Rasha ba ta ce komai ba game da iƙirarin, sai dai a baya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine a yankin Krasnodar a lokacin faruwar harin.
MDD ta zargi sojojin Isra'ila da saɓa wa dokokin duniya
Mai bayar da rahoto na Majalisar Dinkin duniya ya zargi sojojin Isra'ila da amfani da Bafalasɗine wajen garkuwa, bayan abin da ya faru a birnin Jenin na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Francesca Albanese ya ce bidiyon da aka yaɗa na Balasɗine ɗaure cikin raunuka a gaban motar sojin Isra'ila bayan da suka kai samame yankin abin 'sosa zuciya' ne kuma ya saɓa wa dokokin duniya.
Isra'ila ta ce sojojinta suna saɓa wa tsari kuma za ta gudanar da bincike game da lamarin.
Ta ƙara da cewa sojojinta sun yi musayar wuta a lokaci samamen daƙile ta'addancin, lamarin da ya sa mutumin - wanda suke zargi ya jikkata, kafin su ɗauke shi a motarsu don kai shi asibit.
An samu ƙaruwar rikici a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun bayan ɓarkewar yaƙin Gaza na baya-bayan nan.
Sarkin Saudiyya ya bai wa mahajjata kyautar Al-Qur'ani
Asalin hoton, AFP/GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Kyautar wata alama ce ta girmamawa da sarkin ke yi wa alhazai
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya bai wa alhazan - da ke kan hanyar koma wa ƙasashensu bayan kamma aikin Hajji - kyautar Al-Qur'anai.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa a ranar Asabar ma'aikatar harkokin addinin musulunci da yaɗa da'awah ta ƙasar ta rabar da kofi 52,752 na Al-qur'ani mai girma ga alhazan da suka tashi a filin jirgin saman birnin Jedda.
Kyautar wata alama ce ta girmamawa da sarkin na Saudiyya ke yi wa alhazan da suka sauke farali.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce alhazan sun nuna jin dadinsu da yabo bisa kyautar karramawar da sarki Salman ya yi musu.
Kimanin mahajjata fiye da miliyan 1.8 daga ƙasashen duniya daban-daban ne suka sauke farali a wannan shekara.