Bankwana
A nan muka kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ke cewa mu kwana lafiya.
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, na 22/06/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza
A nan muka kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ke cewa mu kwana lafiya.

Rahotonni daga Ethiopia na cewa dubban sojojin ƙasar sun shiga garin Mataban da ke tsakiyar yankin Hiraan na ƙasar Somaliya.
Mazauna yankin sun ce sun ga dubban sojojin Ethiopia ɗauke da makamai suna tsallaka kan iyakar ƙasar.
Wani jami'i a garin ya ce sojojin sun shiga garin ne domin fattakar mayaƙan Al-Shabaab.
Rahotanni sun ce sojojin sun fita daga ƙasar ne bayan ƴan sandan ƙasar sun buƙaci manyan kwamandojin soji kada su yi hakan ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba.

Asalin hoton, Reuters
Rasha ta harba makamai masu linzami a birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin Ukaraine.
Hukumomi sun ce harin ya kashe mutum uku, kuma wasu aƙalla 40 sun jikkata.
Hotuna da bidiyon da aka wallafa sun nun yadda masu aikin cetoo ke ƙoƙarin zaƙulo mutane a cikin ɓaraguzan wani gini mai hawa biyar da harin ya rusa.
Gwamnan yankin, Oleg Synegubov ya ce harin ya faɗa a kan shaguna da hanyoyin sufuri.
Kafin wannan hari, gwamnan yankin Belgorod na Rasha ya bayar da rahoton wani hari da Ukraine ta kai a wani ƙauye, wanda ya ce ya kashe wani farar hula.

Asalin hoton, FACEBOOK/Buhari Sallau
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP ya kai ziyarar ne tare da rakiyar wasu manyan abokan siyasarsa.
A saƙon da Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne domin yin ''gaisuwar Sallah''
Ziyarar ta Atiku Abubakar ta zo ne kwana uku bayan ya ziyarci tsaffin shugabannin Najeriya, Ibrahim Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar a gidajen su da ke jihar Niger.
Ana dai alaƙanta irin wannan ziyara da shirye shiryen babban zaɓen 2027.
Kasar Ghana ta sanar da mutuwar mahajjatanta shida sakamakon tsananin zafi da aka yi fama da shi a lokacin aikin hajjin bana.
Shugaban Hukumar aikin Hajjin kasar, Ben Abdallah Banda wanda ya sanar da hakan a wata hira da BBC ya kuma ce sun ci karo da matsalar cunkoso saboda yadda wasu ƙan ƙasar da suka je hajji ta ɓarauniyar hanya, suka yi satar shiga masaukai da haimomin Mahajjatan kasar.
Ben Abdallah ya fara da bayanin yadda Mahajjatan kasar su 4,000 suka gudanar da aikin hajjin bana.
Ya kuma bayyana matakan da hukumar ke ɗauka domin hana ƴan ƙasar Ghana shiga Saudiyya ba bisa ƙa'ida ba domin gudanar da akin hajji.
Shugaban Hukumar aikin Hajjin Ghana ya ce wannan mumumnar ɗabi'a ce da ke zubar da mutumcin ƙasar su a Saudiyya.

Asalin hoton, Reuters
Kafar yaɗa labaran Hamas ta ce harin da Isra'ila ta kai Gaza ya kashe mutane 38.
Tun da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari a gini biyu na ƙungiyar Hamas a Gaza.
Bidiyon da aka wallaf ya nuna hayaƙi ya turnuƙe da kuma yadda gini ya rushe a sansanin ƴan gudun hijira na al-Shati.
Akwai kuma wasu ƙazaman hare-hare da aka kai al-Tuffah mai maƙwabtaka da yankin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana bincike kan lamarin, amma bayanan farko sun nuna ba ta kai hari a wajen ba.

Asalin hoton, Social Media
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ɗaukar nauyin 'yan daba a Kano.
Yayin da yake jawabi a gabanin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Asabar a fadar gwamnatin jihar, Gwamnan Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan halin taɓarɓarewar tsaro da jihar ke fuskanta, musamman harkar dabanci.
''Kowa ya sani kafin mu shigo gwamnati, waccan gwamnatin da ta shuɗe ita ce ke ɗaukar nauyin 'yan daba, ita ce ke sa su suna yin abin da duk suka ga dama suna cutar da al'umma'', in ji gwamnan na Kano.
Gwamnan ya kuma ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi alƙawarin kakkaɓe matsalar daba a Kano.
Ya kuma ce bayan nasararsa a zaɓen gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin daƙile matsalar.
Amma ya ce a cikin wata biyu da suka gabata wasu da ya kira ''maƙiyan jihar'' suka maido da harkar daba.
Inda ya yi zargin cewa wasu sun ɗauko hayar wasu 'yan daba daga makwabtan jihohi domin su kawo wa zaman lafiyar jihar cikas.
Abba Kabir ya kuma yi barazanar fara kiran sunayen mutane da yake zargi da ɗaukar nauyin 'yan daba a jihar.
Haka kuma gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce wasu na zuwa ofishin 'yansanda domin fito da 'yan daba idan hukuma ta kama su.
Inda ya yi barazanar cewa duk mutumin da gwamnatinsa ta sake samu da wannan laifi to za a gurfanar da shi a gaban kotu, domin yin bayanin dalilinsa na ɗaukar nauyin 'yan daba a Kano.
A baya-bayan nan dai jihar Kano na fuskantar faɗace-faɗacen 'yan daba, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a wasu unguwannin jihar.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotonni daga Ethiopia na cewa dubban sojojin ƙasar sun shiga garin Mataban da ke tsakiyar yankin Hiraan na ƙasar Somaliya.
Mazauna yankin sun ce sun ga dubban sojojin Ethiopia ɗauke da makamai suna tsallaka kan iyakar ƙasar.
Wani jami'i a garin ya ce sojojin sun shiga garin ne domin fattakar mayaƙan Al-Shabaab.
Sojojin sun fita daga ƙasar ne bayan 'yan sandan ƙasar sun buƙaci manyan kwamandojin sojin ƙasar kada su yi hakan ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba.
Matakin na zuwa ne ksa mako biyu bayan wani rukunin sojojin ƙasar sun shigar garuruwan yankunan Hiraan da Bakool, inda dakarun ƙasar ke aiki ƙarƙashin Tarayyar Afirka.
A ƙarshen shekarar nan ne ake sa ran dakarun za su fice a wani ɓangare na janye dakarun wanzar da zaman lafiya a ƙasar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai wa wasu gine-ginen Hamas biyu hari a birin Gaza.
Ƙungiyar Hamas ta ce fiye da mutuj 40 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai kan sansanonin 'yan gudun hijira na al-Shati da na Tuffah da ke birnin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce daga baya za ta yi ƙarain haske kan adadin mutanen da suka mutu.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce an kashe wani babban kwamandan Hamas Ra'id Sa'd a lokacin harin.
Mai magana da yawun jami'an sibil difens a Gaza, Mahmoud Basal ya ce harin ya lalata katangar sansanin 'yan gudun hijira na al'Shati.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka (CAF) ta ce za a gudanar da gasar nahiyar ƙasashen Afirka ta Afcon a watannin Disamban 2025 da kuma Janairun 2026.
Hukumar Caf ta ce ƙasar Morocco ce za ta ɗauki nauyin gasar ta 2025 da za fara ranar 21 ga watan Disamban 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Gasar wadda ƙasashe 24 za su fafata za ta ci karo da lokacin da ake tsaka da gasar Premier.
Wannan ne karo na farko da za a buga gasar Afcon a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Haka kuma hukumar ta Caf ta sanar da ɗage gasar ƙwallon ƙafar mata ta 2024 zuwa watan Yulin shekara mai zuwa.
Gasar ta mata - wadda ita ma za a buga a Morocco - za a fara ta ne daga rabar 5 zuwa 26 ga watan na Yulin shekara mai zuwa.

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta ce wani hari ya lalata ginin ofishinta da ke Gaza, tare da kashe mutum 22 da ke zaune a harabar ginin.
"Wani mummunan hari ya sauka 'yan mitoci kusa da harabar ginin ofishin ƙungiyar agaji ta Red Cross ranar Juma'a da maraice," kamar yadda sanarwar ƙungiyar ta nuna.
Ƙungiyar ta yi kira ga ɓangarorin da ke yaƙi da juna su ɗauki matakan hana cutar da fararen hula da lalata wuraren gudanar ayyukan jin ƙai.
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya shaida wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa Isra'ila ba ta kai hari yankin ba, to sai dai ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin.
To sai dai sanarwar ƙungiyar ta ce "Harin ya lalata ginin ofishin, wanda ke cike da ɗaruruwan farare hula da suka rasa muhallansu da ke zaune a tantuna, ciki har da ma'aitanmu Falaɗinawa.''
"Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da ke zaune kusa da asibitinmu na wucin gadi, inda aka kai gawar mutum 22 tare da wasu 45 da suka jikkata."
Ma'aikatar lafiyar Hamasa da ke Gaza - wadda ta ɗora alhakin harin kan Isra'il - ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin yakai 25 yayin da mutum 50 suka jikkata

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya zargi gwamnatin tarayya da janye sojojin da ke aiki a wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jihar
Yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin A Faɗa A Cika da BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar Mac Athur ke shirya wa, gwamna Lawal ya ce ''muna zaune a wasu lokuta sai a turo daga Abuja a ce a cire waɗannan jami'an tsaro, to ya zan yi''?
Gwamnan ya ce rashin ikon da yake da shi kan jami'an tsaro ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar tsaron jihar
"'Ba ni da iko kan 'yan sanda, ba ni da iko kan sojoji, Wallahi billahi ina mai tabbatar maka cewa idan na ina da iko kan wadannan da yanzu matsalar tsaro a Zamfara ta zama tarihi'', in gwamnan.
Gwamna ya kuma ce duk dokar da ya bai wa jami'an tsaron da ke aiki a jihar, ba su binta, sai abin da aka umarce su daga Abuja.
Ya ce ya gana da shugaban rundunar sojin ƙasa a lokuta da dama a Abuja, sannan sun sha ganawa a Zamfara.
''Na koka masa kan matsalar, kuma suna amsa mana cewa za su yi, amma shiru, a lokacin da 'yan bindiga suka addabi Tsafe na gana da babban hafsan tsaro na ƙasar, na gana da shugaban ƙasa, na kuma gaya masa matsalar da muke ciki''.
Gwamnan ya ce a lokacin ganawarsa da shugaban ƙasar, ya fahimci cewa akwai abubuwa da dama da aka gaya wa shugaban ƙasar, wanda kuma a zahirin gaskiya ba haka suke ba.
Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar tsaro, inda 'yan bindiga ke sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyun siyasa sun ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar da ke tafe cikin wata mai zuwa.
A ranar 15 ga watan Yuli ne masu zaɓe za su fita rumfuna don kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar da za a fafata tsakanin mutum uku ciki har da shugaban ƙasar mai ci, Paul Kagame
Masu zaɓe miliyan biyar ne za su kaɗa ƙuri'unsu a z aben da ke tafe.
Tuni dai hukumar zaɓen ƙasar ta tantance 'yan takara 500 da za su fafata don neman kujerun majalisun dokokin ƙasar 80.
'Yan takara na mako uku daga yanzu zuwa lokacin zaɓen, domin yaɗa manufofinsu don farautar ƙuri'un masu zaɓe.
Shugaba Kagame - wanda ya jagoranci ƙasar na tsawon shekara 20 - na neman wa'adin mulki na huɗu.
Akwai mutum biyu da ke fafatawa tare da Mista Kagame a zaɓen da suka haɗa da Frank Habineza na jam'iyyar hamayya ta DGP da kuma Philippe Mpayimana, ɗan takara na indifenda.
Mista Kagame ya lashe zaɓuka uku da suka gabata da gagarumin rinjaye, inda yake samun fiye da kashi 90 na ƙuri'un da aka kaɗa.
'Yan ƙasar na yaba masa kan maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, to sai dai masu sukarsa na zarginsa da cuzguna wa 'yan hamayya, zargin da ya sha musantawa.

Asalin hoton, Reuters
Giwa ta kashe wata Ba'amurkiya mai yawon buɗe-Idanu a Zambiya, bayan ta farmaki motar masu yawon buɗe-idon.
Jami'ai sun ce giwar ta fito da Juliana Gle Tourneau, mai shekara 64 daga cikin motar tare da tattake ta har sai da ta mutu.
'Yan sanda sun ce motar da Ms Tourneau tare da sauran mutanen ke ciki ta tsaya ne a tsakiyar gandun daji sakamakon cunkoson da wata giwar ta haddasa a hanyarsu da ke cikin gandun dajin.
Wannan ne karo na biyu cikin shekara guda da giwa ke kashe Amurkawa masu yawon buɗe ido a ƙasar da ke kudancin Afirka.
A watan Maris ɗin da ya gabata ne wata giwa ta kashe wata mata mai suna Gail Mattson, mai shekara 79 daga jihar Minnesota a gandun dajin Kafue na ƙasar ta Zambiya, bayan ta tare motar da suke ciki, ta kuma hantsula motar.
Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Ms Mattson da jikkata mutum biyar.
Hukumomin ƙasar sun yi kira ga masu yawon buɗe ido su riƙa ɗaukar matakan kariya a lokacin da suke kai ziyara gandun dazukan ƙasar don ganin nau'ikan namun dajin da Ubangiji ya huwacewa ƙasar.
Jamai'ai a DR Kongo sun ce masu tayar da ƙayar baya sun kai hare-hare tare da kisan gomman mutane a ƙasar.
Magajin garin lardin Ituri ya ce masu tayar da ƙayar baya na ƙungiyar Codeco sun ƙaddamar da samame a ranakun Alhamis da Juma'a, inda suka riƙa cinna wa gidaje da shaguna wuta.
Ana fargabar cewa mayaƙan sun yi garkuwa da mutane masu yawa a lokacin samamen.
Jami'ai a lardin sun yi kira ga gwamnatin ƙasar ta kai musu ɗauki domin kar rayukansu daga barazanar masu tayar da ƙayar bayan.
Suna masu cewa sojojin ƙasar da suka je wurin, sun isa ne bayan mayaƙan sun gama cin karensu babu babbaka.
Mayaƙan Codeco na iƙirarin ƙwato 'yancin al'ummar Lendu manoma daga hare-haren al'ummar Hema, makiyaya.
To sai dai masu sharhi na cewa mafi yawan rikicin da ake samu a yankin na da alaƙa da arzikin ma'adinan da ke yankin.

Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya naɗa sarkin Apara, Eze Chike Worlu Wodo a matsayin sabon shugaban majalisar sarakunan gargajiyar jihar bayan sauke Sergeant Awuse - wanda amini ne ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa majalisar sarakunan gargajiyar jihar da aka gudanar ranar Juma'a a Fatakwal Fadar gwamnatin jihar.
Mista Fubara ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rashin sanin makamar aiki ƙarƙashin jagorancin Sergeant Awuse.
Haka kuma gwamnan ya zargi Awuse da rashin magance matsalar haɗin kai tsakanin sarakunan da kuma gwamnatin jihar.
Gwamnan ya ce majalisar sarakunan ƙarƙashin Eze Sergeat Awuse, ta fitar da kalandar majalisar ta shekarar 2024, amma ta ƙi sanya hoton gwamna da na mataimakinsa cikin kalandar, lamarin da gwamna Fubara ya ce tamkar wulaƙanci ne ga gwamnatin jihar.
Toshon gwamna jihar Nyesom Wike ne ya naɗa sarkin Opobo,Dandeson Douglas Jaja a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar kwanaki kafin saukarsa daga gwamnan jihar a shekarar da ta gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa 'yan tawaye sun lalata bututun da ke kai ɗanyen man fetur na ƙasar zuwa Jamhuriyar Benin mai maƙwabtata
Kafofin yaɗa labaran ƙasar, sun ɗora alhakin hakan kan mutanen da suka ce na yi wa tattalin arziƙin ƙasar ''zagon-ƙasa'', waɗanda hukumomin suka ce nan ba da jimawa ba, za su kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Ƙungiyar 'Patriotic Liberation Front' (PLF) - da ke rajin neman sakin tsohon hamɓararren shugaban ƙasar Mohammed Bazoum - ta ɗauki alhakin fasa bututun.
Ƙungiyar ta kuma yi barazanar kai hare-hare kan sauran kayayyakin man fetur na ƙasar, tare da kiran kamfanonin ƙasar China da ke gudanar da bututan su dakatar da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin mulkin sojin ƙasar.
Sojojin mulkin ƙasar dai na ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum tun bayan hamɓarar da shi da suka yi shekara guda da ya wuce.
A cikin watan nan ne dai wata kotu a ƙasar ta cire masa rigar kariya tare da bayar da damar tuhumarsa a gaban kotu.

Asalin hoton, ..
Dakarun sojin saman Ukraine sun ce Rasha ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a cikin dare, yayin da aka ji ƙarar abubuwan fashewa a yankunan ƙasar da dama.
Babban kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar (Ukrenergo), ya ce Rasha ta ƙaddamar da mummunan hari na takwas kan tasoshin samar da lantarki na ƙasar.
Kamfanin ya ƙara da cewa an kai hare-hare a yankunan Zaporizhzhia da ke kudu maso gabashin ƙasar, da kuma Lviv da ke yammacin ƙasar.
Injiniyoyi biyu ne suka samu raunuka a tashar lantarki da ke Zaporizhzhia, kamar yadda rahotonni suka bayyana.
A yankin Ivano-Frankivsk, da ke kudu maso yammacin ƙasar, hukumomi sun ce an lalata gidaje da wurin wasan yara.

Asalin hoton, NAHCON
Nan gaba a yau ne Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON), za ta fara jigilar alhazan ƙasar daga Saudiyya zuwa Najeriya bayan kammala aikin Hajjin bana.
Hukumar ta Nahcon, za ta fara jigilar ne da alhazan Jihohin Kebbi da Nasarawa da kuma birnin tarayya Abuja, waɗanda dama su ne suka fara zuwa ƙasar mai tsarki.
Wakilin BBC da ya ziyarci wurin da ake aikin tantance kayan alhazan jihar Kebbi ya ce ya ga yadda ake auna jakankunan alhazan a mataki na ƙarshe kafin ɗaukar su zuwa filin jirgin saman Jedda domin su shiga jirgi zuwa Najeriya.
Alhazzan da suka fito daga ƙananan hukumomin Arewa da Jega dakuma Kalgo ne za su fara tashi a Jirgin farko.

Cikin sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ahmed Idris ya fitar, ya ambato shugaban hukumar Alhazan jihar, Alhaji Faruku Aliyu-Enabo na cewa alhazan da suka fara zuwa a jirgin farko, su ne za su fara tashi a jirgin farko da zai tashi daga Saudiyya.
"Haka kuma alhazan da suka je a jirgin ƙarshe, za su zama a jirgin ƙarshe da zai kammala jigilar mahajjatanmu", in ji Alhaji Faruku Aliyu-Enabo.

Kimanin jirage 121 ne suka yi jigilar mahajjatan Najeriya fiye da 50,000, a wannan shekara, kamar yadda hukumar ta Nahcon ta bayyana.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkan mu da safiyar wannan ranar ta Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a wasu sassan duniya daban-daban, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Kada ku manta kuna iya tamka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.
Ku biyo mu.