Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Dangin fursunonin siyasa a Venezuela sun fara yajin cin abinci don neman sakin yan uwansu.
Iyalai sun yi dandazo a kurkukun zone 7 da ke Caracas babban birnin ƙasar inda ake tsare da ƴan'uwansu.
Fursunonin siyasa da ke cikin gidan kurkukun sun bi sahun dangin nasu wajen yajin cin abincin.
A ranar Alhamis ne aka ɗage ƙuri'ar ƙudirin yin afuwa sakamakon rabuwar kai cikin gwamnati.
Diyar Xiomara Ortiz - fitacciyar yar fafutuka ta shaida wa BBC cewa tana da shakku game da zartar da ƙudirin.
Aƙalla mutum 200,000 ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Munich na ƙasar Jamus don nuna adawa da gwamnatin Iran yayin da shugabannin ƙasashen Turai ke halartar taron tsaro.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da yadda gwamnatin Iran ta murƙushe masu zanga-zangar a faɗin ƙasar a watan Janairu.
Da yake jawabi a birnin Munich 'dan tsohon sarkin Iran Reza Pahlavi, ya nemi Shugaba Trump na Amurka ya taimaka wa al'ummar Iran.
A ranar Juma'a Mista Trump ya ce sauyin gwamnati a Iran shi ne mafita bayan ya aike da jiragen yaƙi biyu a Gabas ta Tsakiya.

Asalin hoton, Getty Images
Wata sabuwar gobara ta sake ɓarkewa a kasuwar sayar da kayan masarufi ta Singa da ke jihar Kano.
Bayanai da ke fitowa daga kasuwar na cewa gobarar ta tashi ne wasu rukunin shaguna da ake yi wa laƙabi da Gidan Gilas, inda aka yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.
Hotuna da bidiyo da aka yaɗa sun nuna yadda yadda hayaƙi suka turnuƙe saman kasuwar, yayin da shaguna suka kama da wuta tare da ƙonewar kayayyakin masarufi masu ɗimbin yawa
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, wadda ta kwashe sa'o'i tana ci.
Jami'an hukumar kashe gobara da sauran hukumar bayar da agajin gaggawa na ci gaba da aikin kashe gobarar.
Lamarin na zuwa ne ƴan kwanaki bayan tashin wata gobara da ta haddasa mummunan ɓarna da asara a kasuwar, da ta yi fishe a arewacin Najeriya.

Asalin hoton, Nuhu Ribadu/X
Fadar shugaban Najeriya ta yi kiran gudanar da cikakken bincike kan iƙirarin da tsohon gwamman jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi game da suna kutse a kayin wayar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da sauraron wayarsa.
Cikin wata hira da El-Rufai ya yi da wani gidan talbijin a ƙasar ranar Juma'a, ya yi iƙirarin cewa yana sane da batun yunƙurin kama shi da aka yi lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja ranar Alhamis.
El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da bayar da umarnin kama shi, inda ya ce ya ji wayar da Nuhu Ribadu ya yi lokacin da yake bayar da umarni, bayan da wasu suka yi masa kutse tare da sauraron wayar.
To sai dai kakakin shugaban Najeriya, Bayo Onanuga cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana iƙirarin El-Rufai a matsayin amsa laifi, tare da aza ayar tambayar cewa ko tsohon gwamnan da mutanen da ke masa aikin na da damar yin hakan.
''Ya kamata a yi cikakken bincike game da batun a kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi, saboda ba wanda ya fi ƙarfin doka'', a cewa Bayo Onanuga.

Abubakar Usman daga ƙaramar hukumar Maiyama na jihar Kebbi ne ya lashe gasar kamun kifin Arugungu ta 2026.
Kifin da ya kama na da nauyin kilogiram 59 kamar yadda alƙalan gasar suka sanar.
Abubakar ya samu kyautar motoci biyu da naira miliyan ɗaya.
Dubban masunta ne uska shigar gasar kamun kifin - da aka jima ba a ba.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne babban baƙon da ya halarci gasar, wadda dubban mutane daga ciki da wajen Najeriya suka halarta.

Asalin hoton, Getty Images
Jagoran ƴan adawa na ƙasar Iran Reza Pahlavi ya yi kira ga ƙasashen yammacin duniya da su goyi bayan al'ummar Iran su kuma tallafawa shirinsa na kifar da gwamnatin Iran.
Pahlavi, ɗan tsohon Shah na Iran da aka hamɓarar a juyin juya halin 1979, ya shaida wa manema labarai a gefen taron tsaro na Munich cewa: ''Ƴan ƙasata sun yi kira gare ni da in jagoranci sauya mulki.''
A yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran a watan da ya gabata, wasu masu zanga-zangar da dama sun yi kira ga Pahlavi.
Masu sukarsa sun ce ya kasance mai raba kan al'ummar Iran kuma ba zai iya haɗa kan dukkan Iraniyawa ƙarƙashin tuta daya ba, abin da Pahlavi ya ki amincewa da shi a taron manema labaran inda ya shaidawa BBC cewa: "Tabbas ba na wakiltar ƴan ta'adda ko ƴan aware."
Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar Iran da ke sauran ƙasashen duniya da su fito kan titunan biranen Munich da Toronto da kuma Los Angeles a yau domin nuna goyon bayansu ga Iraniyawa da ke cikin ƙasar.

A lokacin azumin Ramadana mukan yi girke-girke na musamman domin ɗebe kewa da kuma samar mana sinadaran gina jiki.
Haka nan mukan zauna tare domin shan ruwa da iyalai cikin raha da jin dadi.
Ku sanya bidiyon abincin buɗe-baki na musamman da kuka haɗa wa iyalanku ta yadda wasu za su iya kallo su kwaikwaya.
Za kuma ku iya sanya bidiyon yadda kuka yi buɗe-baki tare da iyalanku a cikin nishaɗi.
Kada bidiyonku ya zarce tsawon minti uku, sannan a ɗauki bidiyon da kyau, domin bidiyon da ba a ɗauka da kyau ba ba zai samu shiga ba.

Dole ne nahiyar Turai ta kasance a shirye don yin gwagwarmaya don kare al'ummarta, da dabi'unsu, da salon rayuwarsu, in ji Firaminista Sir Keir Starmer ya faɗawa shugabannin duniya a ranar Asabar.
Da yake magana a taron tsaro na Munich, Starmer ya kuma yi kira da a ƙara zurfafa alaƙa da haɗin gwiwa, gami da alaƙar tattalin arziki, tsakanin Birtaniya da ƙungiyarEU.
Firaministan ya jaddada cewa dole ne nahiyar ta "tsaya da kafarta" a duk batutuwan da suka shafi tsaro.
A yayin jawabin nasa, Starmer ya kuma ce Birtaniya za ta tura dakarun sojinta zuwa yankin Arctic a wani ɓangare na yankurin ƙarfafa tsaro daga barazanar Rasha.
Starmer ya ce Amurka da Canada da sauran ƙasashen da ke ƙawancen NATO suma za su shiga shirin yaƙi da barazanar da Rasha ke yi a yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Democrat da Republican na Majalisar Dokokin Amurka suna zargin junansu da alhakin dakatar da ayyukan gwamnati na ɗan wani lokaci da ke shirin fara aiki ba da jimawa ba.
Kuɗaɗen da ake bai wa Ma'aikatar tsaron cikin gida za su ƙare a cikin dare, abun da ke nufin za a tursasa wa ma'aikata yin aiki daga gida a kyauta ba tare da an biya su ba, ko kuma ƙin yin aikin baki ɗaya, daga yau Asabar.
Ƴan Democrat sun ƙi amincewa da kasafin kuɗin ma'aikatar saboda ƙoƙarin ganin an yi gyara kan ayyukan hukumar kula da shige da fice ta ICE da ke ƙarƙashin ma'aikatar.
Ana zargin jami'an da wuce gona da iri a ayyukansu, wajen kashe mutum biyu a jihar Minnesota.
Fadar White House ta ce ƴan Democrat sun ƙi su amince da sakin kuɗaɗen ma'aikatar ne saboda dalilan siyasa.

Asalin hoton, PT
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi fatali da iƙirarin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi na alaƙanta shi da ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
A martaninsa da ke ƙunshe cikin wata sanarwa da ta fito daga tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya bayyana zargin a matsayin sakaci da rashin gaskiya da kuma ƙoƙarin karkatar da alhakin wani lamari da ya auku a jihar Kaduna.
Sanarwar ta jaddada cewa Dadiyata ya gudanar da rayuwarsa ne a jihar Kaduna, inda ya shahara wajen yin suka ga gwamnatin jihar Kaduna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, babu wata hujja da ta nuna cewa ɗan gwagwarmayar ya mayar da hankali ne kan gwamnatin jihar Kano ko Ganduje.
Sanarwar ta yi kira da a yi bincike kan kalaman El-Rufai na baya-bayan nan, inda ta jaddada cewa irin waɗannan munanan zarge-zargen sukan zama maganganun siyasa ne kawai, muddin ba a gabatar da wasu ƙwararan hujjoji ba.

Asalin hoton, House of Reps
Majalisar Wakilan Najeriya ta sanar da cewa za ta yi zaman gaggawa a ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, 2026, domin duba batutuwan da suka taso dangane da fitar da jadawalin zaɓen 2027 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi.
Sanarwar wadda mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi ya fitar ta bayyana cewa an sanar da mambobin ne ta wata takarda ta cikin gida da ofishin shugaban majalisar ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Sanarwar ta jaddada cewa zaman gaggawar ya nuna ƙudurin majalisar na ɗaukar matakin daidaita al’amuran da ke da matuƙar tasiri ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi sanarwar INEC, daidai da ayyukan majalisa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
A ranar Juma’a ne INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 202, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Sai dai kuma wasu ƴan Najeriya musamman musulmi sun nuna damuwa kan ranar da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar, inda suka yi nuni da cewar ya zo ne a cikin watan Ramadan.

An kammala duk shirye-shiryen da suka kamata domin fara kamun kifi a Argungu, inda ake jiran isowar shugaban ƙasa bola Ahmed Tinubu.
An samu tangarɗa bayan da masunta suka faɗa ruwa ba tare da an ba da izinin shiga ba, lamarin da ya kai ga jami'an tsaro da Sarkin Kabin Arugungu suka ɗauki matakin daidaita al'amura.



Amma a halin yanzu komai ya daidaita inda ake ci gaba da dakon isowar shugaban ƙasa kafin a fara kamun kifin.


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta da ta gaggauta sake duba ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaɓe na 2027, yana mai cewa lokacin ya yi karo da azumin watan Ramadan.
A ranar Juma'a INEC ta sanar cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ranar 20 ga Fabrairu ta faɗo "a tsakiyar watan Ramadan," yana mai bayyana lokacin a matsayin na gudanar da azumi da ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya.
"Sanya lokacin gudanar da wannan muhimmin al'amari na jama'a a tsakiyar lokacin ibada yana nuna rashin fahimta da rashin kulawa ga al'amuran zamantakewa da addini na ƙasar," in ji sanarwar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa yana da mauƙar muhimmanci a yi la'akari da yadda Najeriya ta ƙushi al'ummomi daban-daban kafin a yanke shawarar da za ta shafi rayuwar ƴan ƙasar.
A nata ɓangaren hukuma zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa an zaɓi ranakun zaɓen ne bisa la'akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na 1999.

A yau ne ake shirin gudanar da bikin kamun kifi na Argungu, inda masunta daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashe Afrika za su nuna bajintarsu




Asalin hoton, Reuters
Japan ta saki kyaftin da ma'aikatan wani jirgin ruwan kamun kifi na ƙasar China da aka tsare a yankin tattalin arzikinta na musamman.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ce China ta ba da tabbacin biyan kuɗin jingina kafin sakin mutanen.
Wannan ne karo na farko cikin shekaru huɗu da Tokyo ta kama wani jirgin ruwan kamun kifi na ƙasar China kuma lamarin ya faru ne a daidai lokacin da dangantaka ke taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Trump ya ce zai kauce wa Majalisar Dokoki tare da tilasta sabbin dokoki masu tsauri na tantance masu kaɗa ƙuri'a kafin zaɓen tsakiyar wa'adi na watan Nuwamba.
Majalisar ta amince da wani ƙudiri da ke buƙatar masu son kaɗa ƙuri'a su gabatar da shaidar zama ƴan ƙasa, amma da wuya ya samu karɓuwa a Majalisar Dattawa.
Mista Trump bai yi bayanin yadda zai sanya irin waɗannan dokoki ba, waɗanda masu suka ke cewa za su hana miliyoyin masu kaɗa ƙuri'a shiga zaɓen.
Sai dai ya sha iƙirarin cewa magudin zaɓe ya zama ruwan dare a Amurka, ba tare da gabatar da wata shaida ba.

Yayin wani jawabi a a wani taro a garin Tumbler Ridge domin tunawa da mutane takwas da wani matashi ya harbe, Firaministan Canada, Mark Carney, ya yaba wa mutanen garin saboda ƙarfafa zukatansu, "lokacin da duniya kidime da kisan yan uwan na su''.
Ya ce babu wata kalma daga gare shi da za ta iya lallashinsu, ko ta maye gurbin ƴan uwansu da suka rasa.
Wakiliyar BBC ta ce ya shaida masu cewa ya je ne domin nuna musu cewa al'ummar Canada na tare da dangin mutanen su a wannan yanayi da suke ciki.
Yayin ziyarar, Mista Carney ya samu rakiyar shugabannin dukkan jam'iyyun siyasar Canada, waɗanda suka bi shi zuwa garin da mutane ke alhinin abun da ya faru.
Mutane tara ne da suka haɗa da wanda ake zargi da harbin ne suka mutu a a lamarin. Sun haɗa da yara biyar da babban malami ɗaya a makarantar sakandare ta Tumbler Ridge, da kuma biyu daga cikin dangin wanda ake zargi da harbin.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce tana da “muhimmiyar damuwa” game da shirin da aka dakatar na gudanar da gwajin allurar rigakafin ciwon hanta (Hepatitis B) a Guinea-Bissau, tana mai nuni da shakku game da dalilan kimiyya da aka gabatar na gudanar da shi.
Sshirin gwajin rigakafin da aka tsara zai ƙunshi dubban jarirai. Masu bincike sun yi shirin bai wa wasu jarirai rigakafin ciwon hanta a lokacin haihuwa, yayin da wasu kuma za a jinkirta ba su har zuwa bayan makonni shida da haihuwa.
Manufar ita ce yin nazarin tasirin rigakafin kan lafiyar jariran a lokacin da aka bayar da shi tare sauran rigakafin yau da kullum.
Hepatitis B ya yaɗu a Guinea-Bissau, inda kusan mutum ɗaya cikin biyar na manya da kusan kashi 11 cikin 100 na yara ƙanana ke kamuwa da cutar.
Hukumar ta WHO ta ba da shawarar cewa a yi wa duk jarirai allurar rigakafin cutar cikin sa'o'i 24 bayan haihuwarsu.

Asalin hoton, Reuters
Wata jami'ar Falasɗinawa a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye ya bayyana sabuwar faɗada ikon da Isra'ila ke yi yankin a matsayin "matakin ƙarshe" da zai wargaza duk wata tattaunawa da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Asma al-Sharabati, magajiyar garin Hebron mai rikon kwarya, ta ce sabbin sauye-sauyen shari'a da ministocin gwamnatin ƙasar Isra'ila suka sanar a baya-bayan nan, za su yi wa mahukuntan Falasɗinawan ɗan waken zagaye a duk wata shawara kan tsare-tsare da raya birane, hatta a yankunan da ke ƙarƙashin ikon Falasɗinawa.
Hebron wani wuri ne da aka dɗe ana ɗauki ba daɗi a yankin. Ya kasance birni da ke ɗuke da mutane daban daban, inda sojoji ke gadin ɗaruruwan Isra'ilawa ƴan kama-wuri-zauna da ke zaune tare da Falasdinawa a wani barikin sojin Isra'ila.
A makon da ya gabata majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta zartas da manyan sauye-sauye kan tsarin raba madafun iko a gaɓar yamman, wanda aka kafa shekaru 30 da suka gabata a ƙarƙashin yarjejeniyar Oslo da Amurka ke marawa baya, wanda shugabannin Isra'ila da Falasdinawa suka rattabawa hannu.