Rigar Ka'aba: Bayanai sun nuna cewa an tura wa Jeffrey Epstein wani sashe na Kiswa

Musulmai suna zagaye Ka'aba, wuri mafi tsarki a Musulunci, a al-Masjid al-Haram, Babban Masallacin Makkah, yayin shirye-shiryen fara aikin Hajji (hajji) na 2024

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ka'aba, ginin dutse ne wanda aka lulluɓe da Kiswa (tufafi) mai launin baƙi da zinare, shi ne wuri mafi tsarki a addinin Musulunci.
Lokacin karatu: Minti 8

Grace Tsoi

Global Journalism team, BBC World Service

Fairouz Hosny

BBC News Arabic Trending

Musulman duniya sun bayyana ɓacin ransu kan wasu takardu da ke nuna cewa an aika da wani ɓanagren tufafin da ke rufe ɗakin Ka'aba - wurin ibada mafi tsarki a Musulunci - zuwa ga marigayin attajirin da aka samu da laifukan lalata Jeffrey Epstein.

A cikin kundin bayanan Epstein da Ma'aikatar shari'a ta Amurka (DOJ) ta fitar a ranar 30 ga watan Janairu, akwai sakonnin imel da aka fara aikawa a shekarar 2017 da ke nuna cewa an yi safarar sassa uku na abin da ake iƙirarin rigar Ka’aba ne, wanda aka sani da Kiswa, daga Saudiyya zuwa gidan Epstein da ke yankin Caribbean.

"Ka yi tunanin an aika sashen wani abu daga wuri mafi tsarki a duniya zuwa wuri mafi ƙazanta!" Wani ya rubuta a shafinsa na dandalin X.

Wani hoto da aka ce an ɗauka a shekarar 2014, ya nuna Epstein da wani mutum suna kallon wani yadi da aka shimfiɗa a ƙasa, wanda yayi kama da mafi kyawun ɓangaren Kiswa da ke rufe kofar Ka'aba.

Wani hoto da ya fito daga ma'aikatar shari'a ta Amurka da ke nuna Jeffrey Epstein da wani mutum, suna tsaye gefe da gefe, suna kallon wani yadi da aka ƙawata da ke shimfiɗe a ƙasa.

Asalin hoton, Source: US Department of Justice

Wani mai amfani da X ya ce hoton "ya sanya mun matuƙar baƙin ciki a zuciyata" yadda ga kiswa a "shimfiɗe a ƙasa kamar kafet".

Duk da haka dai, wannan hoton ba ya da alaƙa da bayanan da ke nuni da cewa an yi wa Epstein safarar Kiswa a 2017. Kuma ba a tabbatar da cewa ko yadin da ke cikin hoton ainihin ɓangaren Kiswa ba ne.

'Masallacin'

Yayin da aka yi shi da baƙin yadi nau'in siliki, an yi wa Kiswa ado da rubutun Alƙur'ani wanda aka saƙa da zare mai launin zinare da azurfa. An yi amfani da shi wurin lulluɓe duka bangon Ka'aba guda huɗu, wanda ginin dutse ne a tsakiyar babban masallacin Makkah.

A kowace shekara, bayan miliyoyin alhazai sun taɓa shi, ana sauya Kiswa da wani sabo yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Kowace shekara, ƙungiyoyin ma'aikata suna gudanar da aikin sauya Kiswa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kowace shekara, ƙungiyoyin ma'aikata suna gudanar da aikin sauya Kiswa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kundin bayanan ma'aikatar DOJ ta ƙunshi rubutattun wasiƙu tsakanin ma'aikatan Epstein da kuma wani adireshin imel mai suna "Aziza al-Ahmadi" da ke nuni kamar ana shiryan safarar ɓangarorin Kiswa guda uku zuwa ga Epstein a shekarar 2017: an bayyana ɗaya a matsayin kore, daga cikin Ka'aba; wani mai launin baƙi da aka yi amfani da shi a waje; da kuma wanda aka saƙa rubutu a kansa amma ba a yi amfani da shi ba.

Wani saƙon imel mai ɗauke da kwanan wata 1 ga watan Fabrairu 2017 ya yi nuni da cewa wani mataimaki na wani da ake kira Ahmadi ya fada wa ma'aikatan Epstein cewa za su "aiko da wasu sassa na Ka’aba don masallacin". Ba a sani ba ko inda suka kira "masallaci" wani wuri ne da ya ke tsibirin Epstein.

Daga bayanan Epstein da aka samu yin nazarinsu ya zuwa yanzu, ba a ambaci wani masallaci a tsibirin ba. Amma dai, bisa ga takardun da aka ɗora akan shafin intanet ɗin ma'aikatar DOJ, an bayyana wani ƙaramin gini a matsayin "Temple" ko wurin bauta. Ba a tabbatar da abin da ake nufi da haka a cikin wasiƙun ba.

Bai kamata a ɗauki "Masallacin" da aka ambata a cikin takardar da nufin babban masallacin Makkah ba, inda ya ke Ka'aba.

Takardu sun nuna cewa kayan sun isa gidan Epstein da ke Palm Beach a ranar 4 ga Maris 2017 sannan an tura su zuwa St Thomas da ke tsibirin Virgin Island. Yana kusa da 'Little St James', kyallataccen tsibirin Epstein inda mata da dama suka yi zargin an yi safarara tare da cin zarafinsu.

A kan wata takardar Kwastam ɗin Amurka mai kwanan wata 14 ga watan Maris 2017, an bayyana kayayyakin da aka yi safara a matsayin "zane-zane" wadandav ke da darajar $10,980. Wani saƙon imel mai kwanan wata 21 ga watan Maris ya tabbatar da isarɓangarorin Kiswa zuwa "gidan Mista Epstein".

Bayan jigilar kaya, wani saƙon imel da kamar aka aika daga adireshin Ahmadi ya shaida wa Epstein cewa "Aƙalla Musulmi miliyan 10 ne mabiya ɗarikoki daban-daban, Sunni, da Shi'a da sauransu suka taɓa wannan baƙin yadin".

"Suna zagaya ɗakin Ka'aba sau bakwai, sannan kowa ya na iya ƙoƙarinsa ya taɓa shi kuma sun sanya addu'o'insu da burinsu, da hawaye da duk fatansu a kan wannan yadin," aka rubuta saƙon imel ɗin.

Babu tabbacin cewa ko Epstein ya karɓi ɓangarorin Kiswar a matsayin kyauta ko kuma ko masu inganci ne.

Ɓangarorin KIswa guda uku da aka ambata a mundin bayanan Epstein.

Asalin hoton, Source: US Department of Justice

Bayanan hoto, Bayanin kowane daga cikin ɓangaren Kiswa guda uku da ke ɗaya daga cikin saƙƙnnin Imel ɗin.

Amma dai bayanan ma'aikatar DOJ sun nuna, cewa waɗannan ba su ne kaya na farko da aka kai wa Epstein daga Saudi Arabiya ba.

A cikin wani saƙon imel a ranar 27 ga watan Janairu, 2017, mutumin da aka ce mataimakin Ahmadi ne ya ce ya na "neman hotunan cikin masallacin" don samun damar shirya "wani abu a cikin masallacin". Tun da farko a cikin wannan jerin saƙonnin, wani mai taimakawa Epstein ya tabbatar da isar "tanti da sauran kayan gida" zuwa gidan Epstein.

A cikin kundin bayanan, ma'aikatar DOJ, akwai takarda da ke nuna hoton tantin ulu na Larabawa na gargajiya da sauran abubuwa kamar kafet da tukwanen shayi da kofuna da kwanduna. Amma dai, ba za a iya sanin ko sune abubuwan da aka kai wa Epstein a cikin wannan ƙunshin kayan ba.

Dukkanin kayayyakin da aka jigilar an yi su ne bayan da aka yanke masa hukunci a matsayin mai aikata laifukan lalata a shekara ta 2008 bayan ya amsa laifi a tuhumar da aka yi masa na neman aikata lalata sau biyu ciki har da ƙaranar yarinya.

Ahmadi bai amsa buƙatar BBC ta neman ya yi tsokaci ba. Bayyanar sunaye a cikin takaddun ba shaidar aikata laifi ba ce.

 Wani ma'aikaci yana shirya Kiswa a wata masana'anta gabanin aikin Hajji na shekara shekara a Makka, Saudi Arabia, 06 Yuli 2022.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A baya akan yi Kiswa ne a ƙasar Masar amma daga baya na mayar da gaba ɗaya aikin zuwa Saudiyya

Mene ne matsayin Kiswa?

Hukumomin Saudiyya ne ke da cikakken iko a kan Kiswa, tun daga yadda ake ƙera ta, zuwa amfani da ita da kuma cire shi, zuwa yadda ake amfani da tsofaffin. Amma babu wata doka da ta shafi yadda ake yi da tsohuwar Kiswa.

BBC ta tuntuɓi hukumomin Saudiyya don samun ƙarin bayani, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton ba ta samu amsa ba.

Marubuci Ahmed al-Halabi, wani marubuci da ya ƙware a aikin Hajji da Umrah, ya shaida wa BBC cewa, "Sassan da ke ɗauke da rubuce-rubucen zinare da azurfa da aka fi sani da 'Belt' da 'Samadiya' jami'an fadar masarautar Saudiyya ne kaɗai ke iya kyautar da su.

"Akan bayar da da waɗannan sassan ne ga shugabannin ƙasashen musulmi da jami'an gwamnatocinsu".

Halabi ya ƙara da cewa, "Sauran baƙin yadin da ya rage yawanci ana yanka shi ne gunduwa-gunduwa kuma ana iya ba da shi ga jami'ai masu ƙaramin muƙami."

Dokta Simon O'Meara, masanin tarihin fasahar addinin Musulunci a Jami'ar SOAS da ke Landan, ya ce Kiswa ba "abu ma tsarki ba ce", amma ana mutunta ta a duniyar musulmi.

"Yana girmama ginin Ka'aba - kamar rigar sarki.

"Da zarar Kiswa ta fito, ba za a wulakanta ta ba, ba za a taka ta a ƙasa ba."

A ɗaya ɓangaren kuma, Halabi ta yi tambaya kan sahihancin sassan da aka ambata a cikin wasikun da DOJ ta fitar. Ya kuma ce ba a bayar da kyautar Kiswa ga waɗanda ba musulmi ba.

Ɗaya daga cikin takardun da ke nuna yadda aka yi jigilar kaya zuwa adireshin Epstein da ke Florida da aka karɓa a ranar 16 ga Maris 2017

Asalin hoton, Source: US Department of Justice

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin takardun da ke nuna yadda aka yi jigilar kaya zuwa adireshin Epstein da ke Florida da aka karɓa a ranar 16 ga Maris 2017

Alaƙa da Saudiyya

Alamu dai sun nuna an yi musayar sakonnin imel iri-iri kan abubuwa daban-daban da Epstein daga farkon 2016 har zuwa farkon 2019 waɗanda ke ɗauke da sanya hannu tare da sunan Ahmadi, bisa ga takardun na ma'aikatar DOJ. Wasu daga cikin sakonnin sun yi masa laƙabi da "boss" da "master", kuma takardun sun nuna cewa sun haɗu a wurare da yawa ciki har da New York da Paris.

Epstein da alama ya nemi yin tasiri kan gwamnati Saudiyya ta hanyar Ahmadi, a cewar takardun da ma'aikatar DOJ ta fitar.

A watan Yulin 2016, wani imel da sunan Ahmadi ya nuna cewa ta na shirya haɗa Epstein da wani mai suna "HE Raafat", wanda saƙon imel ɗin ya bayyana a matsayin wadda zai yi farin cikin kasancewa tare da Epstein. Mai yiwuwa hakan na nufi "His Excellency", lakabin girmamawa da ake yi wa manyan jami'an gwamnatin Saudiya amfani da shi.

Takardun da ma'aikatar D0J ta fitar sun nuna Epstein ya ba da "binciken batutuwan kuɗi" kuma ya nuna adawa da sanya kamfanin Aramco a kasuwa musayar hannun jari, wanda mai yiwuwa ya na magana ne kan kamfanin mai na ƙasar Saudiyya, a cikin wani saƙon imel zuwa wani da ake kira Ahmadi a watan Agusta 2016. Daga baya, Ahmadi ta bayyana cewa za ta "nazari'' a kai ta kuma haɗa da adireshin imel ɗin mai suna "Raafat Alsabbagh" a martanin da ta yi.

Wani saƙon imel na watan Nuwamba 2016 daga adireshin ɗaya daga cikin mataimakan Epstein ya ce: "Aziza mataimakiyar HE Raafat ce." a cikin sakonnin imel da dama zuwa ga mutane daban-daban, ana ganin Epstein yana bayyana "Raafat Alsabbagh" a matsayin "mai ba da shawara" ga "yariman Saudiyya mai jiran gado".

Sanarwar da Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya fitar a shekarar 2017 ta bayyana sunan shi a matsayin "mai ba da shawara a fadar masarautar".

Bayanan da ke ƙunshe a cikin takardun ma'aikatar DOJ sun nuna alamun cewa wani da ake kira "Sabbagh" ya yi musayar saƙonni da dama da Epstein. A cikin wani saƙon waya da aka aika a 2016, wani adireshi mai suna "Raafat Al-Sabbagh" ya aike wa Epstein saƙo cewa: "Ina ƙaunar kaina da abotar da ke tsakanin mu."

Saƙon imel da aka aika daga wani mai suna "Raafat Alsabbagh" zuwa Epstein ya aika masa wani adireshin shafin intanet ɗauke da labarin wata sarauniyar kyau ƴar Rasha mai shekaru 17 da aka ruwaito ta gudu zuwa Dubai don sayar da budurcinta. Mai lalatar ya amsa da cewa: " sai yanzu ka aiko mun da wani abu mai daraja."

A gefe guda kuma, babu bayanai maus yawa game da ita kanta Ahmadi a kundin bayanan. Amma a cikin saƙon imel ɗin da aka aika a cikin watan Satumba 2018, wani mai irin wannan sunan ya nemi shawarar Epstein kan kamfanin gyam ɗinta na wayar hannu.

Akwai tambayoyi da dama da suka rage akan batun Kiswa da alaƙar Epstein da mutanen da aka yi maganarsu a cikin saƙonnin imel ɗin da ke cikin kundin bayanan. A duk faɗin duniyar musulmi, ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga mahukuntan Saudiyya da su ƙaddamar da cikakken bincike.

Additional reporting by Global Journalism Reactive Team's Kawoon Khamoosh.

Editor: Kate Forbes.