An buɗe taron matasan Najeriya na 2026 a Abuja

Asalin hoton, NIG YOUTH
Ministan Matasa na Najeriya, Ayodele Olawande, ya ce gwamnati ta faɗaɗa damar da ake bai wa matasa ta hanyar shirye-shirye a fannonin ilimi, koyon sana’o’i, kasuwanci, fasaha da samar da ayyukan yi.
Da yake jawabi a wajen buɗe Taron Ƙasa na Matasa na 2026 a Abuja, Mista Olawande ya ce gwamnati na da ƙudurin samar da hanyoyin da za su taimaka wa matasan Najeriya su samu ƙwarewa, su kafa kasuwanci, su sami ayyukan yi, tare da taka rawa wajen ci gaban ƙasa.
Ya ce ya kamata a riƙa kallon matasa a matsayin abokan hulɗa, masu ƙirƙire-ƙirƙire, ’yan kasuwa da shugabanni, ba kawai masu amfana daga shirye-shiryen gwamnati ba. Ya bayyana cewa fannoni kamar faɗaɗa ƙwarewa, kasuwanci, samar da ayyukan yi, fasaha, wasanni, masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire da kuma shiga harkokin jama’a na buƙatar ci gaba da saka hannun jari.
Mista Olawande ya ce matsaloli kamar rashin aikin yi, ƙarancin damar samun kuɗaɗen tallafi da ilimi, rashin shiga duniyar fasahar zamani da kuma ƙarancin kariyar zamantakewa suna da alaƙa da juna, kuma suna buƙatar haɗin gwiwa wajen magance su.

Asalin hoton, NIG YOUTH
Ya ƙara da cewa ma’aikatar na aiki tare da hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, abokan hulɗar ci gaba, ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyin matasa domin shawo kan waɗannan ƙalubale.
Ministan ya ƙalubalanci mahalarta taron da su gabatar da shawarwari masu amfani da za su inganta shirye-shiryen matasa da ake da su yanzu, tare da fayyace waɗanda za su ɗauki alhakin aiwatar da su da kuma hanyoyin tabbatar da nasara.
Ya ce za a auna nasarar taron ne da abin da zai biyo baya, musamman ko shawarwarin da aka bayar za su haifar da sakamako, ƙarin damar samun ci gaba da kuma ƙara tabbatar da yin abin da ya dace daga masu ruwa da tsaki..

Asalin hoton, NIG YOUTH
Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Maryam Kashinro, ta ce muhimmiyar rawa da matasa ke takawa wajen yanke shawara na da matuƙar tasiri ga ci gaban Najeriya, inda ta nuna cewa kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar ƙasar ba su kai shekara 30 ba.
A gefe guda kuma, Shi ma shugaban Hukumar NITDA, Kashifu Abdullahi, ya ce za a yi amfani da ƙirƙirarriyar Fasahar AI wajen nazarin gudummawar da mahalarta taron za su bayar.
Shi ma Darakta Janar na NYSC, Olakunle Nafiu, ya buƙaci matasan Najeriya da su yi amfani da basira da ƙirƙire-ƙiren su wajen bayar da gudummawa ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar ƙasar





































