Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello Diginza, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya daga nan sashen Hausa na BBC.

  2. Harin Isra'ila ya kashe ɗan kwallon Falasɗinawa Suleiman al-Obeid

    Falasɗinawa

    Asalin hoton, PFA

    Hukumar kwallon kafa ta Falasɗinawa ta sanar da cewa harin Isra'ila ya kashe ɗan wasanta Suleiman al-Obeid, lokacin da yake jiran karɓar jin-ƙai ranar Laraba.

    An haifi ɗan wasan mai shekara 41 ne a birnin Gaza, kuma ana yi masa lakabi da "Pele na kwallon kafar Falasɗinawa", a cewar sanarwar da aka fitar.

    Ya buga wa yankinsa wasanni 24, inda ya zura kwallo biyu, a cewar hukumar kwallon kafar ta Falasɗinawa.

    Ya zura kwallaye 100 a tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa, kuma an kwatanta shi da "ɗan wasan Falasɗinawa mafi hazaƙa".

  3. Mutum 50 sun ɓace bayan afkuwar ambaliya a Indiya

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 50 ne ba a gani ba har yanzu tun bayan ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa ta afku a wani gari da ke yankin tsaunukan Himalayas da ke gundumar Uttarkashi a Indiya.

    Ƴansandan yankin sun ce an ceto kusan mutum 400 a garin na Dharali.

    An tabbatar da mutuwar mutane huɗu sakamakon ambaliyar. Gadar da ta haɗa garin da sauran jihar ta lalace gaba ɗaya.

    Hukumar bayar da Agajin gaggawa ta Indiya ta ce za a ɗauki aƙalla kwanaki biyu kafin a iya samar da gadar da ta za ita iya ɗaukar motoci.

    Jiragen sama masu saukar ungulu na ƙoƙarin yin aiki a yankin amma suna fuskantar kalubalen samun wuraren da za su sauka.

    A shekarar 2021, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 200 a gundumar.

  4. Kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa saboda rashin wuraren adana - NAFDAC

    Abinci

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta ce kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa ne sakamakon rashin wuraren adana abinci da suka dace.

    Darakta-janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels, inda ta ce wuraren adana abinci sun yi kaɗan a ƙasar.

    Ta ce idan aka samu wuraren adana abinci masu kyau, dangin abinci irin ganyayyaki da su tumatiri duka ba za su ci gaba da lalacewa ba.

    Ta ce hakan ne ya sa suke ɗuakar matakai na ganin abinci da ake adanawa sun ɗauki lokaci ba su lalace ba ta hanyar samar da wuraren adana na zamani.

  5. Yarjeniyoyi huɗu da aka ƙulla tsakanin Nijar da Chadi

    Chadi da Nijar

    Asalin hoton, ActuNiger

    Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idriss Déby Itno da shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani

    Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idriss Déby Itno ya kammala ziyarar wuni biyu da ya kai birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

    Wannan ne karo na biyu da Deby ke kai ziyara Nijar tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi wa gwamnatin Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

    A lokacin ziyarar ta Mahamat Deby, an ga yadda ya yi jerin ganawa tare da shugaban Nijar Abdourahamane Tiani, inda aka cimma yarjeniyoyi da dama.

  6. An ƙaddamar da shirin tattara ayyukan da za a saka a kasafin kuɗin jihar Katsina

    Umar Dikko Radda

    Asalin hoton, Umar Dikko Radda

    Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da shirin tattara ayyukan da za a saka a kasafin kuɗin jihar na 2026.

    An saka wa shirin taken "dole ne cigaba ya fara daga matakin al'ummomi".

    Da yake magana a lokacin kaddamar da shirin, mataimakin gwamnan jihar, Faruq Lawal Jobe wanda ya wakilci gwamna Dikko Radda, ya kwatanta taron da aka gudanar don tattara ayyukan da za a sa a kasafin, a matsayin wani ci gaba a jihar - wajen ganin an samu cigaba daga matakin al'ummomi da kuma shugabanci na gari.

    "Wannan wani tsari ne na ƙarfafa dimokraɗiyya, yin gaskiya da kuma tabbatar da cewa kasafin kuɗin da za a gabatar ya tafi daidai da buƙatun al'ummomi," in ji mataimakin gwamnan.

    Ya ce shirin wanda ya samu haɗin gwiwar ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare, za a gudanar da shi a faɗin mazaɓu 361 da ke faɗin jihar.

    Ya ƙara da cewa shirin wata dama ce da mazauna jihar za su fito su faɗi matsaloli da suke fuskanta, irin ci gaban da suke so da kuma samar da mafita.

    An samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma shugabannin al'umma yayin kaddamar da shirin.

  7. 'An samu girman adadin yara da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a Gaza'

    Gaza

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce a watan da ya gabata ne aka samu mafi girman adadin ƙananan yara da ke fama da rashin abinci ma gina jiki a Gaza.

    Kusan yara ƴan ƙasa da shekara biyar su 12,000 ne abin ya shafa a watan Yuli.

    Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ana samun ƙaruwar mace-macen da ke da nasaba da yunwa, inda aka samu aƙalla mutum 99 tun farkon wannan shekara.

    Ya yi kira ga Isra'ila da ta ba da damar shiga da kayan agaji Gaza cikin gaggawa.

  8. Muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa - Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Team

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi Alla-wadai da kamawa tare da tsare fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore.

    Atiku ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido na sufeto janar na ƴansandanƙasar suka yi wa Sowore.

    "Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ba ya cikin ka'ida. Dole ne a yi tur da batun," in ji Atiku.

    Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin adalci da kuma kyayyawar shugabanci da ake yi a Nijeriya.

    Wasu rahotanni ma na bayyana cewa an lakaɗawa Sowore duka har ma ƙarya masa hannu, inda ake zargin ƴansanda da aikatawa.

    Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴansanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai bane, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Najeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.

    "Don haka muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa ba tare da ginɗaya wasu sharuɗa ba," in ji Atiku.

    A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami'an ƴansanda domin amsa wasu tambayoyi.

  9. Lebanon ta ce harin Isra'ila ya kashe mutum biyar a ƙasar

    Lebanon

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan wuta ne ke ci a lokacin da Isra'ila ta kai hari birnin Beirut a watan Yuni

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta ce wani harin da Isra'ila ta kai ta sama a gabashin ƙasar ya kashe mutum biyar.

    An bayyana cewa harin ya rutsa da wata mota kusa da kan iyaka da Syria.

    Yana ɗaya daga cikin hare-haren da sojojin Isra'ila suka ci gaba da kai wa tun bayan da aka amince da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah a watan Nuwamban bara.

    Isra'ila, wadda har yanzu ba ta ce uffan ba game da harin, ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da ƙungiyar Hezbollah take, har sai ƙungiyar ta kwance ɗamararta.

    Gwamnatin Lebanon dai tana tattaunawa kan wani kudurin Amurka da zai tabbatar da cimma hakan zuwa karshen wannan shekarar.

  10. Rahama Sadau ta kaddamar da bikin baje-kolin fina-finai a arewacin Najeriya

    Rahama Sadau

    Asalin hoton, Rahama Sadau/X

    Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta kaddamar da bikin baje-kolin fina-finan Arewacin Najeriya.

    Bikin dai na son laluɓo hanyoyin fito da ƙwarewar al'ummar arewacin Najeriya.

    An samu halartar ministar raya al'adun Najeriya, Hannatu Musawa da shugaban hukumar fina-finai, Ali Nuhu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

    Rahama Sadau

    Asalin hoton, Rahama Sadau/X

    Rahama Sadau

    Asalin hoton, Rahama Sadau/X

  11. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam ta shirin 'Labarina'

    A cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da Fatima Hussain, wadda aka fi sani da Maryam a Labarina.

    Fatima wadda tauraruwarta ta fara haske bayan fitowa a cikin shiri mai dogon zango na Labarina, ta kasance cikin masu yawan tayar da ƙura a arewacin Najeriya sanadiyyar wasu kalamanta.

    Ƴar asalin jihar Kaduna, Fatima ta yi ƙarin haske kan rawar da take takawa a masana'antar Kannywood da kuma irin mutumin da take ganin za ta iya zama da shi a matsayin miji.

    Tace bidiyo: Mohammed Fatawul

    Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
  12. Isra'ila na tattaunawa kan shirin mamaye zirin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu, ya kira taron majalisar ministocinsa ta tsaro domin tattaunawa kan shirin mamaye yankin zirin Gaza baki ɗaya.

    An bayar da rahoton cewa tun farko shirin zai mayar da hankali ne kan karɓe ikon birnin na Gaza gaba ɗaya, inda za a kori mazaunana yankin miliyan ɗaya zuwa yankin kudanci, lamarin da ya janyo suka daga shugaban rundunar sojin Isra'ila, Eyal Zamir.

    Wakilin BBC ya ce an zargi firaministan da tsawaita yaƙin domin cimma muradunsa na siyasa, kuma yana samun goyon bayan ministocinsa masu tsatsaurar ra'ayi.

    Majalisar Ɗinkin Duniya da kungiyoyin agaji na fargabar cewa duk wani ƙarin tashin hankali zai iya jefa Falasɗinawa da dama cikin haɗari da kuma barazana ga rayukan sauran Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su a Gaza.

  13. An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026

    Alhazai

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa an kayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026.

    NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar - don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.

    Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.

    Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.

    Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Najeriya - inda ya ce ƙoƙari da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.

  14. 'Fiye da yara 11,000 sun rasa matsugunansu saboda faɗa a Somalia'

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce mutane fiye da 22,000, ciki har da yara fiye da 11,000 ne aka raba su da muhallansu a yankin Mahaas da ke tsakiyar Somalia sakamakon kazancewar rikici a yankin.

    Rikici tsakanin dakarun gwamnati da masu tayar da ƙayar baya a yankin Hiraan ya ta'azzara a cikin watanni biyu da suka gabata, inda a ranar 27 ga watan Yuli, fiye da mutum 22,800 a garin Mahaas kawai suka rasa matsugunansu.

    Ƙungiyar ta ce waɗannan dubban mutanen na rayuwa ne a kauyuka makwafta a yanayi na cunkoso ko kuma a filaye ba tare da abubuwan da suke buƙata domin yin rayuwa ba.

    Ƙungiyar ta ce ta damu kan yadda aka dakatar da aiki a cibiyoyin lafiya 21 da take tallafa mawa saboda rikicin.

    '' A lokacin da yaƙin ya ta'azzara, fiye da yara 150 masu fama da tamowa da ke karɓar kulawa a Mahaas da kauyukan da ke kusa da su, suka tsere da iyalansu zuwa garuruwan Bulo Burte da Beledweyne'' in ji ta.

    Sai dai ƙungiyar ta ce tawagar ta da ke Beledweyne na ƙoƙarin lalubo yaran domin ci gaba da basu magunguna.

  15. Remi Tinubu ta tallafa wa iyalan ƴan wasan Kano da suka mutu a hatsari

    Remi Tinubu

    Asalin hoton, Remi Tinubu/X

    Mai ɗakin shugaban Najeriya Remi Tinubu ta tallafa wa iyalan yan wasan Kano 22 da suka rasu a hatsarin mota da kuɗi naira miliyan 110.

    Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Kanon Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce kowane iyali na mamatan ya karɓi naira miliyan biyar ta ƙarƙashin shirin na mai ɗakin shugaban ƙasa da aka yi wa laƙabai da 'Victim Support Fund'.

    Matakin na zuwa ne bayan da gwamnan jihar ya bayar da kyautar naira miliyan 130 da filiye, inda duka mutum 10 da suka jikkata, kowa zai samu naira miliyan biyu da file guda, yayin da iyalan waɗanda suka mutu za su samu naira miliyan biyar-biyar.

    Sanarwar ta ambato gwamnan na bayyana godiyarsa ga mai ɗakin shugaban ƙasar kan abin da ya kira tausaya wa da ta nuna wa ƴan wasan.

    Sanusi Bature ya kuma ce gwamnatin Kano ta samu ƙarin tallafi daga gwamnatocin jihohin Ogun da Jigawa da suka bayar da jimillar kuɗi naira miliyan 52 domin bai wa ƴan wasan.

  16. An haramta wa mawaƙi shiga jirgin sama saboda ƙoƙarin hana jirgi tashi

    Wasiu Ayinde Marshar

    Asalin hoton, Kwam 1 fans club

    Hukumomi a Najeriya sun haramta wa wani shararren mawaƙi Wasiu Ayinde Marshar shiga jirgin sama, kan ƙoƙarin hana jirgi tashi - saboda an hana shi ya shiga cikinsa.

    Wata sanarwa da ministan sufurin jiragen saman ƙasar Festus Keyamo ya fitar ranar Alhamis, ta ce mawaƙin ya tsaya kan hanyar da jirgin zai tashi da nufin hana shi tashi, bayan samun hatsaniya da ma'aikatan filin jirgin sama.

    Mawaƙin wanda aka fi sani da KWAM 1, ya yi niyyar balaguro ne daga Abuja zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru.

    A lokacin da ake ƙoƙarin shiga jirgi, jami'an tsaron filin jirgin saman sun faɗa wa mawaƙin cewa ba zai shiga da ma'adinan ruwa da ke hannunsa ba zuwa cikin jirgi ba, kamar yadda mai magana da hukumar kula da filayen jirgin sama Obiageli Orah ta bayyana.

    "Fasinjar ya yi watsi da lamarin inda ya watsa abin da ke cikin ma'adinan a jikin jami'in tsaron, daga bisani an gano cewa giya ce a ciki," in ji ta.

    Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, ciki har da wanda Keyamo ya yaɗa, sun nuna mawaƙin yana ƙoƙarin tsayawa a gaban jirgin lokacin da yake son tashi.

    An ruwaito cewa sai da Wasiu ya tsuguna domin kauce wa ferfelan jirgin.

    An dakatar da lasisin matukin jirgin da kuma mataimakinsa, in ji Keyamo.

    Mawaƙin dai sananne ne a yankin kudu maso yammacin Najeriya, inda waƙoƙinsa na gargajiya "fuji" wanda ya yi da harshen Yarabanci ya samo asali.

    Yana cikin mawaƙa da aka cashe da waƙarsa lokacin rantsar da shugaba Bola Tinubu a watan Mayun, 2023.

  17. Afirka ta Kudu ta janye ƙararta kan mutumin da ake zargi da hannu a kashe wasu mata biyu

    Adrian Rudolph de Wet

    Asalin hoton, Nomsa Maseko / BBC

    Babban mai shigar da ƙara na Afirka ta kudu ya janye ƙarar da aka shigar kan wani ma'aikacin gona bayan ya ce wanda ya ɗauke shi aiki ne ya tilasta masa ciyar da aladu gawarwakin wasu mata biyu baƙaƙen fata da nufin ɓoye shaidar kashe su.

    Mutumin mai suna Adrian Rudolph de Wet, na daga cikin maza uku da ke fuskantar shari'a bisa zargin kashe Maria Makgato da Lucia Ndlovu a bara, bayan rahotanni sun ce matan sun shiga wata gona a lardin Limpopo da ke arewacin ƙasar domin neman abinci.

    Mista de Wet dai ya bayar da shaida a kotu inda ya ce mai gonar ne ya harbe matan biyu.

    Za a sake zaman sauraron shari'ar a watan Oktoba.

  18. Rundunar ƴansanda ta gargaɗi jami'anta kan kamun ƙafa don neman ƙarin girma

    IGP zaune yana jawabi da abin magana, sanye da koriyar hula

    Asalin hoton, Nigerian Police

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta garagaɗi jami'anta dangane da kamun ƙafa da wasu masu ruwa da tsaki don neman ƙarin girma ko matsayi a cikin rundunar.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan na ƙasa DCP Muyiwa Adejobi ya fitar '' tun bayan yi wa wasu jami'an rundunar da suka cancanta ƙarin girma aka yi ta samun rahotonnin da ke cewa akwai jami'an da ke kamun ƙafa domin neman ƙarin girma''.

    ‎”Rundunar ƴansanda na son fayyace wa al'umma cewa ƙarin girman da aka yi a baya-bayan nan an yi shi ne bisa doka da ƙa'ida kamar yadda aikin ɗan sanda ya tanada'' a cewar sanarwar.

    “Akan yi ƙarin girma ne domin yaba wa ƙoƙarin da jami'ai ke yi na nuna jajircewa da ƙwarewar aiki da sadaukarwa da suke yi, ko aka saka musu ta hanyar cika wasu sharuɗɗa da hukumar ta gindaya'', in ji DCP Adejobi.

    ''Kan haka ne muke kira ga jami'an ƴansanda su guji kamun ƙafa don neman ƙarin girma ta hanyar da ta ba dace ko ta wace irin siga'', in ji shi.

  19. Yawan al'ummar Japan na raguwa cikin sauri

    Wasu muaten tsaye snya da kayyaki masu launka daban-daban

    Asalin hoton, Getty Images

    Alƙalumma sun nuna cewa a shekarar da ta gabata adadin mutanen Japan ya ragu da fiye da 900,000.

    Yawan al'ummar Japan ya shafe kusan shekara 20 yana raguwa-- amma wannan ita ce raguwa mafi girma da aka samu a ƙasar.

    Japan ta kwashe shekaru da dama tana fama da karancin haihuwa haɗe da ƙaruwar yawan tsofaffi, da kuma yawan mace-mace.

    Sauran ƙasashe a gabashin Asiya da kewaye na fuskantar irin wannan matasalar, kodayake na Japan ya fi muni.

    A halin da ake ciki adadin baƙi na ƙaruwa a ƙasar, amma yawancinsu ma'aikatan wucin gadi ne, da ke cike guraban ayyukan da ƴan kasar ba za su iya cikawa ba.

  20. UAE ta musanta kakkaɓo jirginta a Sudan

    Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta cewa a harbo ɗaya daga cikin jiragenta ɗauke da makamai da sojojin hayar Aolombia a yankin Darfur na Sudan.

    A ranar Laraba ne rundunar sojin Sudan ta ce ta kakkaɓo jirgin ɗauke da aƙalla sojojin haura 40 a cikinsa.

    Sojojin na Sudan na zargin ƙasar UAE da mara wa mayaƙan RSF baya tare da samar musu makamai da mayaƙa daga ƙetare.

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sha kuma musanta hannu a yaƙin na Sudan duk kuwa da Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun tabbatar da hannun ƙasar a yaƙin ciki har da samar da makamai ga RSF.