Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Sanata Abaribe ya koma ADC daga APGA

    Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Eyinnaya Abaribe ya fice daga jam'iyyar APGA, inda ya sanar da komawarsa jam'iyyar ADC ta haɗaka.

    Abaribe ya koma jam'iyyar a rana ɗaya da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya sanar da komawa jam'iyyar ta ADC.

    A wata sanarwa da ADC ta fitar a shafinta na X, ta ce, "Sanata Eyinnaya Abaribe ya fice daga jam'iyyar APGA, sannan ya koma jam'iyyar ADC a hukumance."

  2. Gwamnan Sokoto ya bukaci jami'an tsaro su kawo ƙarshen ƴanbindiga a 2026

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya buƙaci mutanen jihar da su dage wajen bai wa jami'an tsaro goyon bayan domin magance matsalar hare-haren ƴanbindiga da jihar ke fuskanta ta hanyar taimaka musu da bayanan sirri da sauransu.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙonsa na sabuwar shekarar, wanda mai magana da yawunsa Abubakar Bawa ya fitar, inda gwamnan ya ce za su ƙara ƙaimi domin ganin shekarar ta 2026 ta fi 2025 a kowane ɓangare.

    "Za mu ci gaba da ba jami'an tsaronmu goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara. Mun riga mun fitar da tsare-tsaren da za mu yi musamman wajen tattara bayanan sirri da ganowa tare da daƙile hanyoyin da maharan ke bi wajen kai hare-hare musamman a ƙananan hukumomi 13 da ke fuskantar matsalar."

    Gwamna Aliyu gwamnatinsa za ta muhimmantar inganta ababen more rayuwa a jihar, "kamar yadda suke a ƙunshe a cikin muradunmu guda 9. Sannan za mu inganta sauran ɓangarorin lafiya da jin ƙai da sauransu."

    Gwamnan ya ƙara da cewa za su gina sabbin makarantun Islamiyya, sannan su sabunta tsofaffi, "sannan duk gyare-gyaren da ake yi a makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu duk za mu ba su muhimmanci," in ji shi, sannan ya ce za su kammala ayyukan wasu manyan titunan jihar kafin ƙarshen rubu'i na farko na sabuwar shekarar.

  3. Turkiyya na bincike kan kashe sojojinta 3

    Jami'an tsaro a Turkiyya na ci gaba da aikin gano masu kaifin kishin Islama da ake zargi da hannu a mummunar taho mu gama da sojoji a ranar Litinin da ya hallaka sojoji 3.

    Ministan cikin gida Ali Yerlikaya, ya sanar da cewa da safiyar yau Laraba an kara kama kaarin mutum 125 da ake zargi da mambobin kungiyar IS ne, a samamen hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro.

    Kawo yanzu an kama sama da mutum 500 aka kama tun bayan sanarwar da hukumomi suka yi a makon da ya wuce, kan samun bayanan sirri na harin da suke son kai wa lokacin bikin Kirsimati da Sabuwar shekara.

  4. Ukraine ta kai hari a matatun man Rasha

    Sojojin Ukraine sun ce sun kai hari da jirage marassa matuka, wadanda suka fada kan matatun mai biyu da ke gabar tekun Red Sea wato Baharul Aswad da ke Rasha a daren jiya.

    Bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wuta ta tashi a matatun mai na Tuapse da yankin Krasnodar.

    Moscow ta tabbatar da kai harin inda ta ce mutum biyu sun jikkata. Shugaban ma'aikatan sojin Ukraine ya ce harin ya fada matatar mai ta Taman da ke gabashin yankin Crimea da Rasha ta mamaye.

    Sai dai Rasha ta ce harin Crimea tsoho ne da Ukraine ta kai a farkon makon nan wanda aka kai gidan shugaba Vladimir Putin a yankin Norgorod.

    Bidiyon ya nuna jirgi maras matuki da sojin Rasha suka kakkabo, sai dai Ukraine ta ce babu wani hari makamancin wannan da suka kai.

  5. Fitattun ƴan Najeriya da suka rasu a shekarar 2025

    Kamar kowace shekara 2025 ta zo kuma ta wuce da abubuwa da farin cikin da kuma akasin haka.

    Shekarar ta 2025 ta kasance ɗaya daga cikin shekaru mafiya tarihi ga Najeriya, ta yadda ƴan ƙasar da dama ba za su taɓa mantawa da su ba.

    Abubuwa da dama sun faru waɗanda za su ci gaba da zama a zukatan wasu ƴan ƙasar har natsawon laokaci.

    Shekara ce da fitattun ƴan ƙasar - kama da shugabanni da ƴansiyasa da malamai da ƴan kasuwa da dama suka mutu.

  6. Abubuwan da ba su kamata a faɗa wa mace mai ciki ba

    Shin abu ne mai kyau a yi wa mata masu juna biyu hirar da ta shafi ciki da yadda ake haihuwa, ko kuwa hakan zai iya janyo masu fargaba da tsoro?

    Lokacin da ƴar jarida, Rose Stokes ta samu cikinta na farko, ta sha fama da labarai masu ban tsoro da tayar da hankali da suka shafi yadda ake haihuwa da kuma rainon ƴaƴa, daga ƙawaye da abokan arziki da ma baƙi.

  7. Atiku ya yi maraba da komawar Peter Obi ADC

    Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP kuma jigo a jam'iyyar ADC a yanzu, Atiku Abubakar ya ce yana maraba da komawar tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi cikin jam'iyyar ta haɗaka.

    Atiku ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce komawar Obi jam'iyyar wani babban mataki ne mai muhimmanci a tarihin haɗaka a siyasar Najeriya.

    "Ina maraba da komawar Peter Obi cikin jam'iyyar ADC a hukumance, wanda yake cikin ƙoƙarin da muke na samar da haɗaka mai ƙarfi da za ta ƙalubalanci jam'iyya mai mulki. Jam'iyyar da za ta kafa mulkin da zai tabbatar da zaman lafiya da cigaban ƙasa."

    Atiku ya ce yana fata komawar Obi cikin jam'iyyar za ta buɗe ƙofar da wasu waɗanda ya bayyana da 'masu kishi' za su biyo domin shiga jirgin haɗakar.

  8. Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko da ya kashe Hanifa

    Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa da babbar kotu ta yanke a kan Abdulmalik Tanko, wanda aka samu da laifin sacewa tare da kashe ƙaramar yarinya Hanifa Abubakar.

    Hukuncin ya biyo bayan shari’ar da ta ja hankalin al’umma baki, inda kotu ta same shi da laifin aikata kisan.

    Wannan mataki, a cewar gwamnatin jihar Kano, wata babbar nasara ce domin tabbatar da adalci, wanda ke ƙarfafa gwiwar mutane domin su ƙara al’umma da ɓangaren, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata manyan laifuka, musamman waɗanda suka shafi kisan yara, ba za su tafi a banza ba.

    Sanarwar tabbatar da hukuncin na ɗauke ne a wani rubutu da babban lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude ya sanar, inda ya yaba da hukuncin yana mai cewa hakan ya nuna ƙarfin doka da jajircewar ɓangaren shari’a wajen kare rayuka, musamman na yara da sauran masu rauni a cikin al’umma.

    Ya ce "Wannan hukunci ya sake jaddada cewa doka tana aiki ba tare da tsoro ko nuna son kai ba."

    Maude ya kuma yaba wa Barrista Lamido Abba Sorondinki, lauyan gwamnati a ma’aikatar shari’a ta jihar bisa abin da ya kira jajircewa da ƙwarewarsa wajen bin diddigin shari’ar har zuwa matakin tabbatar da hukuncin.

    A watan Disambar 2021 ne Abdulmalik Tanko ya sace Hanifa inda daga bisani ya kashe ta lamarin da ya girgiza al’umma a Kano da ma ƙasar baki ɗaya.

    An kama Abdulmalik Tanko a watan Janairun 2022 bayan binciken jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga gurfanar da shi a gaban kotu da kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya wanda yanzu kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar.

  9. Sudan za ta ci gaba da buɗe iyakar Adre domin shigar da agaji

    Gwamnatin sojin Sudan ta ce za a ci gaba da barin iyakar Adre da ke tsakanin ƙasar da Chadi a buɗe har tsawon watanni 3 masu zuwa, domin shigar da kayan agaji ga farar hula da ke tsananin bukatar taimako.

    Shugaban hukumar agaji a Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi maraba da matakin da zai taimaka wajen ceton rayukan al'umma.

    Yaƙin da Sudan ta faɗa na kokawar karɓar iko tsakanin sojin gwamnatin Janar AbdulFatta al-Burhan da madugun 'yantawayen RSF Muhammad Hamdan Dagalo ko Himeti ya janyo asarar rayukan dubban farar hula.

    Yaƙin ya haddasa wasu miliyoyi sun rasa muhallansu, da Majalisar Dinkin Duniya ta ce shi ne aikin jin ƙai mafi muni a duniya.

  10. Cambodia ta yi wa sojojinta 18 tarbar girma bayan Thailand ta sake su

    An yi wa sojojin Cambodia 18 tarbar girma bayan sakinsu da Thailand ta yi a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu kan rikicin iyaka.

    A watan Yuli ne aka kama sojojin lokacin wani gwabza fada a iyakokin kasashen biyu.

    Sojojin na ta murmushi da dagawa dandazon mutane hannu, da daga tutar kasarsu lokacin da motocin da ke dauke da su suka iso babban birnin kasar Phnom Penh.

    Wata mata da ke cikin dandazon mutanen ta ce komawar su gida tamkar murnar shiga sabuwar shekara ne.

    Cambodia da Thailand sun dauki lokaci su na fada da juna musamman farkon watan nan, amma an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu a karshen mako.

  11. EU ta soki shirin Isra'ila na hana ƙungiyoyin ajaji 37 shiga Gaza

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce sabuwar dokar Isra'ila da ta haramta wa ƙungiyoyin agaji sama da 30 gudanar da aiki a Zirin Gaza da gaɓar yamma da Kogin Jordan za tayi tarnaki wajen isa ga Faladinawan da ke tsananin buƙatar taimako.

    Gwamnatin Isra'ila ta ce ƙungiyoyin sun gaza bada cikakkun bayanai Faladinawan da suke yi wa aiki, da ta ce dole ta ɗauki mataki domin kaucewa fadawar kayan agaji ga ƙungiyar Hamas.

    Shugabar hukumar agaji a Tarayyar Turai Hadja Lahbib, ta ce dokokin kare-haƙƙin danadam na duniya sun bayyana ƙarara dole a bai wa masu buƙatar agaji taimako a duk inda suke.

    Sai dai Isra'ilar ta ce za a ci gaba da shigar da agajin ta hannun waɗanda aka aminta da su ciki har da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

  12. Peter Obi ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC

    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC.

    Obi ya bayyana hakan ne a wani taro da magoya bayansa da shugabannin siyasa suka gudanar a Enugu, babban birnin Jihar Enugu.

    Da yake jawabi a taron, Peter Obi ya ce bayan watanni na tuntuɓa da tattaunawa, su da sauran shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun yanke shawarar shiga ADC domin haɗa ƙarfi da sauran jam’iyyun adawa.

    Ya ce burinsu shi ne “Ceto Nijeriya daga mummunar shugabanci tare da yin duk mai yiwuwa don daƙile maguɗi da murɗiyar zaɓe a shekarar 2027.

    Manyan shugabannin siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar da wasu tsofaffin gwamnoni da manyan jiga-jigan siyasa da shugabannin siyasar Kudu maso Gabas ne suka halarci taron lamarin da ya nuna yunƙurin ƙarfafa haɗin kan adawa gabanin zaɓen 2027..

  13. Bankuna za su fara cire naira 50 a duk 10,000 da aka tura

    Bankuna a Najeriya za su fara cire naira 50 a matsayin harajin da banki ke cirewa kan kudin da aka tura ko aka cire da ya wuce naira 10, 000 daga ranar 1 ga Janairun 2026 bisa sabuwa dokar haraji da aka kafa.

    An sanar da hakan ne a cikin wasiƙu da bankuna suka aika wa kwastomominsu kafin fara aiwatar da wannan sabon tsarin.

    Harajin yana nufin cire naira 50 kai tsaye a kan kowanne kuɗi da ya shiga ko ya fita daga cikin asusun banki da ya wuce naira 10,000.

    Wannan tsarin ba zai shafin kuɗin albashin mutum da ke shiga asusun bankinsa ba da kuma kuɗin da aka tura daga banki iri ɗaya.

    A da, wanda aka tura wa kudi kadai ake cirewa wannan harajin, amma yanzu tsarin zai shafi wanda ya tura kuɗin ma.

    Bankunan sun fayyace cewa wannan harajin ya bambanta da harajin da bankuna ke yi da aka saba gani kuma za a nuna wa mutum a lokacin da yake tura kuɗi.

  14. Burkina Faso da Mali sun hana ƴan Amurka samun bizar shiga ƙasar

    Gwamnatin sojin Burkina Faso da ta Mali sun sanar da hana bayar da biza baki ɗaya ga ‘yan ƙasar Amurka a matsayin martani ga takunkumin da Amurka ta sanya mata kamar yadda rahoton gidan labaran RTB ta ƙasar ya nuna.

    Ministan harkokin wajen Burkina Faso, Karamoko Traore Jean-Marie, ya bayyana cewa matakin na Burkina Faso martani ne ga matakan da Amurka ta ɗauka na ƙara tsaurara sharuɗɗan shiga ƙasarta ga ƴan Burkina Faso.

    "Saboda haka gwamnati na sanar da al’umma ta ƙasa da ta duniya matakin da ta ɗauka na amfani da matakin takunkumi iri ɗaya da Amurka ta ɗauka ga ‘yan Amurka ɗin.” in ji ministan.

    Matakin Burkina Faso ya biyo bayan irin wannan mataki na takunkumi da Nijar ta sanya wa ‘yan Amurka kwanan nan, inda Mali ma ta ɗauki irin matakin.

    Dangantaka tsakanin ƙasashen AES, wato Mali da Burkina Faso da Nijar, da yawancin ƙasashen Yamma ta ragu sosai tun bayan shugabancin soji a shekarar 2020 da 2022 da kuma 2023.

  15. Shugaban mulkin sojin Guinea Mamadi Doumbouya ya lashe zaben shugaban ƙasar

    Shugaban mulkin sojin Guinea Mamadi Doumbouya ya lashe zaben da aka yi a karon farko a ƙasar tun bayan ƙwace mulki a 2021.

    Sakamakon zaɓen ya nuna cewa shi ke da rinjaye a ƙuri'un da aka kaɗa abin ya nuna cewa ba za aje ga zagaye na biyu a zaɓen ba.

    Masu sanya idanu daga ƙungiyar tarayyar Afirka sun bayyana zaɓen a matsayin sahihi wanda kuma aka yi shi cikin kwanciyar hankali.

    To amma ƙungiyoyin farar hular da suka rinka kiraye-kirayen a dawo da mulkin farar hula sun bayyana shakku a game da batun cewa kashi 80 cikin 100 na masu kaɗa kuri'a sun fito sun yi zaɓe.

    Doumbouya ya hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde wanda ya jima a ka mulkin kasar shekaru hudu da suka wuce.

  16. Yau za a yi jana'izar Khalida Zia, firaminista mace ta farko a Bangladesh

    A yau ne za a gudanar da jan'izar ban girma ga jagorar adawar Bangladesh, Khalida Zia, wadda ta rasu a jiya Talata tana da shekaru 80.

    Zia, wadda ita ce firaiministar kasar mace ta farko ta yi fama da dogon jinya kafin ta rasu.

    Za a binneta a kusa da kabarin mijinta Ziaur Rahman, wanda aka kashe a shekarar 1981 a lokacin da ya ke shugabancin ƙasar.

    Marigayiyar ta jagoranci jam'iyyar BNP inda ta kai ta ga samun nasara a 1991, wato a zaɓen farko da aka gudanar a cikin shekaru 20.

    Za a kuma yi zaman makoki na kwanaki uku a faɗin ƙasar.

    Ministan harkokin wajen India S. Jaishankar zai halarci jana'izar.

  17. Peter Obi ya faɗa min cewa zai fice daga Jam’iyyar Labour – Gwamnan Abia

    Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa Peter Obi ya sanar da shi da kansa cewa yana shirin ficewa daga Jam’iyyar Labour.

    Otti ya yi wannan bayani ne yayin da yake watsi da jita-jitar da ke cewa shi ma yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar, a taron manema labarai na wata-wata da ya gudanar a Umuahia, babban birnin jihar.

    Gwamnan ya ce Obi, wanda shine ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, ya sanar da shi wannan mataki da kansa kuma ya samu cikakken goyon baya daga gare shi.

    “Na kasance a cikin Jam’iyyar Labour tun kafin shigowar Peter Obi, saboda haka ba tare da shi muka shiga jam’iyyar ba,” in ji Otti.

    “Ya sanar da ni cewa zai bar Jam’iyyar Labour, na kuma nuna masa goyon baya na. Amma ni zan ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar domin ita ce ta kai ni ga mulki."

    "Za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu domin farfaɗo da jam’iyyar, amma idan har muka gaza, nan ne za mu fara tattauna wasu mafita,” gwamnan ya ƙara da cewa.

    Sai dai gwamnan Otti bai bayyana wacce jam’iyyar Peter Obi zai koma ba.

  18. Isra’ila za ta hana ƙungiyoyin agaji 37 shiga Gaza

    Isra'ila ta shirya haramtawa ƙungiyoyin agaji 37 da ke aiki a Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan gudanar da ayyukansu daga ranar daya ga watan Janairun 2026.

    Isra'ila ta ce ƙungoyoyin sun gaza gabatar da cikakken bayanan ma'aikatansu, wanda ta ce yana da matuƙar muhimmanci domin kare yaɗuwar 'yan ta'adda.

    Tuni dai aka dakatar da ayyukan fitattun ƙungiyoyin agaji kamar ActionAid da dai sauransu.

    Za su kawo ƙarshen ayyukansu a tsakanin kwanaki 60 masu zuwa.

    Tuni dai wakilai daga ƙasashe da dama suka yi allawadai da matakin na Isra'ila a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa inda suka ce matakin zai ƙara jefa ayyukan jin ƙai cikin mawuyacin yanayi kamar ayyukan kula da lafiya a Gaza.

  19. Amurka ta ƙaƙaba wa Iran da Venezuela ƙarin takunkumi

    Amurka ta ƙaƙaba wa mutane da kamfanoni 10 daga Iran da Venezuela takunkumi, bisa zargin cewa suna da alaƙa da samar da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran, waɗanda gwamnatin Amurka ta ce suna barazana ga tsaron ƙasar da na ƙawayenta.

    Wani babban jami’i a gwamnatin Amurka, John Hurley, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan abin da ya kira rawar da ƙasashen biyu ke takawa wajen samar da “muggan makamai” da ke bazuwa a sassan duniya.

    Daga cikin waɗanda takunkumin ya shafa akwai wani kamfani daga Venezuela da shugabansa, waɗanda ake zargi da siyan jiragen yaƙi marasa matuƙa daga Iran.

    Haka kuma, akwai wasu ’yan Iran uku da ake zargin suna da hannu wajen samar da sinadarai da ake amfani da su wajen kera makamai masu linzami.

    Ana ganin matakin kara wa jami'an Venezuela da na Iran takunkumi a wannan gabar akan batun jirage marassa matuka a matsayin kara matsawa gwamnatin Venezuela lamba.

  20. Sojojin Najeriya sun kama ɗan ƙunar baƙin wake a Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun kama wani mutum da ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake ne a Jihar Borno, tare da ƙwace kayayyakin da ake amfani da su wajen haɗa bam.

    Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X.

    Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ɗan asalin ƙaramar hukumar Bama ne, kuma an gano yana da wasu ƙarin kayayyaki ko makamai masu alaƙa da ayyukan ta’addanci.

    Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, laftanar kanar Sani Uba, ya ce an same wanda aka kama ɗin da kayayyakin bama-bamai da aka riga aka haɗa, abin da ke nuna shirin kai hari.

    Rundunar ta ce, a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro domin zurfafa bincike don gano masu ɗaukar nauyinsa da abokan aikinsa da kuma alaƙarsa da ƙungiyoyin ta’addanci a yankin.