Ibrahim Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar
An kashe fitaccen ɗanbindiga, Isuhu Yellow a Zamfara
Asalin hoton, NPF
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an kashe fitaccen ɗanbindigar nan da ya yi fice wajen garkuwa da jama'a don neman kuɗin fansa, wato Kachalla Isuhu Yellow.
Lamarin ya auku ne da yammacin yau Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewacin ƙasar.
Ɗanjarida mai bincike kan harkokin ƴanbindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗanbindigar.
Isuhu ya fi yin fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
Humphrey Nwosu: Hayaniya ka kaure a majalisar dattawa kan neman girmama shugaban hukumar zaɓen 1993
Asalin hoton, facebook
Sanatocin kudu maso gabas sun yi kira ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ya karrama Farfesa Humphrey Nwosu da girmamawa ta musamman saboda rawar da ya taka wajen shirya zaɓen 1993.
Humphrey Nwosu shi ne shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a lokacin da aka gudanar da zaɓen 12 ga watan Yulin shekarar 1993, wanda aka soke.
Tun da farko, an yi musayar yawu tare da cacar-baki tsakanin sanatoci a zauren majalisar dattawa, inda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, sannan daga ƙarshe ya sanar da ƙin amincewa da buƙatar.
Daga cikin abubuwan da suke buƙata, akwai sanya wa ofishin INEC na Abuja sunan Humphrey Nwosu, da ba shi karramawa ta ƙasa, da kuma yin shirun minti ɗaya domin girmama shi a majalisar.
Bayan kaɗa ƙuri'ar murya ce, shugaban majalsar ya ce waɗanda ba su amince ba sun fi yawa, don haka ba za a amince da manyan buƙatun biyu ba, amma za a yi shirun minti ɗaya na girmamawa.
Daga bisani ne sanatocin suka nuna rashin jin daɗinsu a zantawarsu da manema labarai, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Sun ce ana yi wa Tinubu kallon 'gwarzon zaɓen 12 ga Yuni', don haka suke fata ya karrama Farfesa Humphrey Nwosu domin rawar da ya taka a zaɓen.
Jagoran kwamitin sanatocin, Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce, "ba don zaɓen ba, da ba za a yi maganar ranar 12 ga Yuni ba.
"Jajircewar Farfesa Humphrey Nwosu ce ta sa aka san wanda ya ci zaɓen, duk da barazana daga sojoji."
Majalisar Isra'ila ta ƙara wa Netanyahu ƙarfi a ɓangaren shari'a
Asalin hoton, EPA
Majalisar dokokin Isra'ila ta zartas da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce da za ta bai wa firiminista Benjamin Netanyahu damar aiwatar da sauye-sauye a fannin shari'ar ƙasar.
Jim kaɗan bayan ƙada ƙuri'ar amincewa da dokar, ƴan hamayya sun shigar da ƙorafi kan matakin a kotun ƙolin ƙasar.
Dokar za ta ba ƴansiyasa damar naɗa alƙalan kotunan Isra'ilar, tana kuma ɗaya daga cikin tsare-tsaren da firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya gabatar ciki har da ci gaba da yaƙi a Gaza, lamarin da ya haifar da sabuwar zanga-zanga a ƙasar.
Rahotanni na cewa matakin da ya ɗauka na ci gaba da kai hare-hare kan Hamas a Gaza, ya haifar da fargaba da rashin tabbas kan makomar sauran mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Ƴansandan Kano sun ƙwato wa mutumin da aka yi garkuwa da shi kuɗin fansar da ya biya
Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook
Rundunar ƴansandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴansandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ta ƙwato tare da miƙa kuɗi naira 4,850,000 ga mutumin da aka yi garkuwa da shi, bayan ƴansandan sun ceto shi, tare da ƙwato kuɗin daga hannun masu garkuwa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce ƴanbindigar sun yi garkuwa da mutumin a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, sannan da farko suka buƙaci suka buƙaci kuɗin fansa naira miliyan 15.
"Da muka samu labari, sai jami'anmu suka ƙaddamar da farautar ƴanbindigar, inda suka kama waɗanda ake zargi guda biyar, sannan aka ceto mutumin a ranar 17 ga watan Maris."
Sanarwar ta ƙara da cewa an mayar da kuɗin ne ta hannun shugaban ƙaramar hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya yi godiya a madadin mutumin da al'ummar mutanen yankin.
A ƙarshe kwamishinan ƴansandan ya buƙaci mutanen jihar su zama masu sa ido, tare da kai bayanin duk wani abu da suke zargi ko ya ɗaure musu kai.
Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin kare lafiya da rayukan ɗalibai
Asalin hoton, Tinubu Facebook
Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani shiri na ƙara inganta tsaro a manyan makarantu da na sakandare mallakarta da ke ɗaukacin faɗin ƙasar.
Ma'aikatar ilimin ta ce ta ɗauki matakin ne ganin yadda ake samun ƙaruwar ɗaliban da ke mutuwa a faɗin ƙasar, sakamakon harin ƴanbindiga, ko ƙwacen waya, ko wani rikici da ke haɗawa da su ko ɓarkewar annoba.
Babban sakataren ma'aikatar Ilimi ta Najeriya, Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya ce za a aiwatar da shirin da aka sake farfaɗo da shi, haɗin gwiwa da ma'aikatar kuɗi da sauran hukumomin tsaron ƙasar don tabbatar da tsare rayuka da lafiyar ɗaliban.
Ya ce ana samun ƙaruwar sace sacen ɗalibai da kai musu hari, inda ya ce za kuma a yi wa ɗalibai bita kan matakan kare kansu daga shiga cikin haɗari.
Mutane miliyan 28 ke fama da ƙarancin abinci a Kongo - MDD
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Ƴan gudun hijira dauke da kayansu daga sansanin Munigi da Kibati a kokarin tserewa daga birnin Goma
Shirin samar da abinci na majalisar ɗinkin duniya ya ce mutane miliyan 28 a Jamhuriyar dimokraɗiyyar Kongo ne ke fama da matsananciyar ƙarancin abinci.
Shirin ya ce wannan adadi ne da ba a taɓa gani ba kuma an samu ƙarin mutane miliyan biyu da rabi a cikin watanni uku da suka gabata.
Ana samun rikice-rikicen ne a gabashin Kongo.
Ta'azarar rikicin yanki da kuma ƙaranci sammun tallafin jinƙai na ƙara jefa alummar cikin ƙarancin abinci.
Ƙasashen Turai da NATO sun sha alwashin ci gaba da goya wa Ukraine baya
Shugabannin ƙasashen Turai da ƙungiyar NATO da ke gudanar da taro a Paris sun sha alwashin ci gaba da goya wa Ukraine da sojojinta baya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya jagoranci taron na ƙasashe 31 ya ce sun kuma amince da kar a ɗage takunkuman Rasha har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kan batun tabbacin tsaro, Macron ya ce abin da ya fi komai muhimmanci shi ne dakarun Ukraine su kasance masu ƙarfi da isassun kayyayakin soji.
Ya kuma yi alƙawarin samar da dakaru a Ukraine da za su hana farmaki daga Rasha nan gaba.
Majalisar wakilai ta janye amincewa da ƙudurin cire rigar kariya ga gwamnoni bayan karatu na biyu
Asalin hoton, Benjamin Kalu
Majalisar wakilan Najeriya ta janye matakin da ta ɗauka na amincewa da karatu na biyu na ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.
Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.
Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin.
Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Ƴan yawon buɗe ido shida sun mutu bayan nutsewar jirginsu a tekun Maliya
Asalin hoton, Sindbad Submarines
An tabbatar da mutuwar mutane shida, yayin da ake ci gaba da neman wasu bayan wani jirgin ruwa na masu yawon buɗe ido da ke tafiya a ƙarƙashin teku ya nutse a tekun Maliya da ta gaɓar birnin Hurghada a Masar.
Ofishin jakadancin Rasha da ke Masar ya ce fasinjoji 45 ne ke cikin jirgin, kuma dukkaninsu ƴan Rasha ne.
Jami'ai a yankin sun ce zuwa yanzu an ceto mutum 29, yayin da aka garzaya da wasu daga cikinsu zuwa asibiti domin samun kulawa.
Jirgin ruwan na hanyarsa ce ta zuwa yawon buɗe ido a ƙarƙashin tekun.
Wannan ne karo na biyu da ake samun nutsewar jirgi a tekun Maliya da ke Masar cikin watanni shida.
Turkiyya ta kori ɗan jaridar BBC daga Istanbul
Hukumomi a Turkiyya sun kori ɗan jaridar BBC, Mark Lowen daga birnin Istanbul inda yake aiki na wucin gadi kan zanga-zangar da ake yi a baya bayan nan.
A jiya Laraba ne aka kai shi ofishin ƴansanda tare da tsare shi na wasu sa'o'i kafin sanar da shi cewa za a kore shi saboda a cewar su ya kasance ''barazana ga zaman lafiyar jama'a'
Shugaban sashen labarai na BBC ya kira wannan matakin da ''lamari mai matuƙar sanya damuwa''.
Hukumomin Turkiyya dai sun tsare ƴan jarida da dama lokacin zanga-zangar.
An aika wa Sanata Natasha wasiƙar da ƴan mazaɓarta suka tura na neman yi mata kiranye
Asalin hoton, Natasha Akpoti/X
Hukumar zaɓen Najeriya INEC, ta aike wa Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan sanarwa a hukumance kan koken da ƴan mazaɓarta suka kai na ƙoƙarin yi mata kiranye daga majalisa.
INEC ta kuma tabbatar da samun cikakkun lambobi da adireshin wakilan da suka tura koken da takardun sanya hannu kan batun yi mata kiranyen.
Wakilan sun aika bayanan nasu masu muhimmanci ne cikin wata wasiƙa ga shugaban hukumar.
A cewar ƴan mazaɓarta, suna ƙoƙarin yi wa sanatan kiranye ne saboda ba ta wakiltar su yadda ya kamata.
A baya INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa'idojin da doka ta gindaya.
Sanata Natasha dai na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da shugaban majalisar dattijan Najeriya Godswill Akpabio bayan ta zarge shi da yunƙurin cin zarafi na lalata.
Poland ta dakatar da baƙin haure daga Belarus shiga ƙasar neman mafaka
Poland ta dakatar da ƴancin baƙin haure daga Belarus shiga ƙasar domin neman mafaka.
Ministan harkokin cikin gida Tomasz Siemoniak ne ya wallafa dakatarwar na wucin gadi - wanda ya fara aiki a daren jiya Laraba - wanda kuma ya bai wa masu tsaron iyakoki damar yaƙi da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
Poland dai na samun ƙaruwar kwararowar baƙin haure a iyakarta ta gabashi.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce matakin ya saɓa doka, kuma ba zai hana mutane shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya ba.
Shugaban Faransa na jagorantar taron shugabanni ƙasashen Turai kan tsaron Ukraine
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na karɓar baƙuncin taron shugabannin ƙasashen Turai da wasu ƙasashen ƙungiyar NATO a Paris domin tattauna batun tsaron Ukraine.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na daga cikin shugabbanin da ke aiki wajen samar da dabarun soji domin daidaita alaƙa da Amurka.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwa kamar tallafin soji ga Kyiv, da kuma waɗanne tabbacin tsaro ƙawayen za su iya samarwa idan an cimma tsagaita wuta, ciki har da mai yiwuwa girke dakaru a Ukraine.
Hotunan yadda wutar daji ke ci gaba da yaɗuwa a Koriya ta Kudu
Hukumomi a Koriya ta Kudu sun ce wutar dajin da ke ci gaba da yaɗuwa a kudu maso gabashin ƙasar ta ƙona dazuka fiye da ɓarnar da aka gani a baya, lamarin da ya sa ta zama mafi muni a ƙasar.
Zuwa yanzu mutum 27 aka tabbatar sun mutu sanadiyyar ibtila'in.
Jirage masu saukar angulu fiye da 120 aka aika yankuna uku da ake samun iftila'in.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wutar daji da ta laƙume birnin Andong
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Rabin iftila'in wutar dajin da ake samu a Koriya ta Kudu a shekaru 10 da suka gabata a lokacin bazara ne
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Iftila'in wutar dajin Koriya ta Kudu ta zarce girmar wanda aka samu a baya bayan nan a kudancin California da yammacin Japan
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani kamfanin haɗa abincin dabbobi da ke ƙonewa
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Ma'aikata na binciken wata mota da ta ƙone a kan titi a arewacin lardin Gyeongsang
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu kashe gobara suna watsa ruwa kan rufin gidaje yayin da wutar ke gabato kauyen Hahoe
Masu iƙirarin jihadi sun hallaka sojojin Kamaru 12 a arewacin Najeriya
Asalin hoton, AFP
Rundunar Sojin Kamaru ta tabbatar da kisan sojojinta 12 a garin Wulgo a arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai musu, da ya bar wasu da raunuka.
Wata Sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ta Kamaru Cyrille Serge Atonfack ya fitar, ya ce masu iƙirarin jihadin a baya-bayan nan sun kutsa ɗaya daga cikin wuraren rundunar haɗin guwiwar ƙasa da ƙasa da ke kusa da garin Fotokol mai iyaka da Kamaru, nan ma suka kai hari kan dakarun.
An aike da gawarwaki ga iyalan su, wasu kuwa suna ɗakin ajiyar gawarwaki, yayin da waɗanda suka sami raunuka an aike da su asibiti a Chadi.
Rundunar sojin ta kuma ce an hallaka masu iƙirarin jihadi da dama, sai dai bata bayar da adadin su ba ko kuma ƴan wani ɓangare ne.
Tsawon shekaru yankin tafkin Chadi na fama da hare-hare da kisan mutane da ake zargin yan ƙungiyar boko haram da mayaƙan ISWAP ne keyi, sai dai duk da irin ƙokarin da dakarun haɗin gwiwa na ƙasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar ke yi, har yanzu masu iƙirarin jihadin na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin.
An kama mataimakin shugaban Sudan ta Kudu
Asalin hoton, Reuters
An kama mataimakin shugaban ƙasa na farko a Sudan ta Kudu Riek Machar a babban birnin ƙasar Juba, a yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar zaman tankiya tsakaninsa da Shugaba Salva Kiir.
Faɗa tsakanin dakarun da ke goya wa shugabannin biyu baya ya tsananta a yankunan Rejaf da ke kudancin Juba da Wunaliet da ke yammaci.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama shi ne tare da uwargidansa Angekina Teny.
Ana samun fargabar cewa kama shi zai iya kawo tarnaƙi ga yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasar.
Kama Machar na zuwa ne bayan shafe makonni ana samun tashe tashe hankula bayan shugaba Kiir ya tsare wasu daga cikin abokan Machar a farkon watan nan.
Tawagar majalisar ɗinkin duniya da ke Sudan ta Kudu tayi gargaɗin cewa ƙasar na cikin barazanar sake faɗawa cikin yaƙi, inda ta buƙaci ɓangarorin biyu suyi aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun Sallah
Asalin hoton, TINUBU FACEBOOK
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma'aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.
A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu'ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
Abokan kasuwancin Amurka sun soki matakin Trump na sanya haraji kan shigo da motoci
Asalin hoton, Getty Images
Galibin manyan abokan kasuwancin Amurka sun yi allawadai da matakin Shugaba Trump na baya-bayan nan da ya lafta sabon harajin kashi 25 cikin 100 kan motocin da aka shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje.
Matakin zai soma aiki ne a ranar 3 ga watan Afrilu.
Shugaba Trump ya ce a Indiana, kamfanin Honda yana gina ɗaya daga cikin tashoshin ƙera motoci mafi girma kuma yanzu suka fara.
A cewar da, a baya ba za su iya abin da suke yi ba idan ba su ɗauki matakin nan ba.
Firaiministan Japan ya ce gwamnatinsa tana nazari kan matakan da za ta ɗauka a matsayin martani.
Firaiministan Canada kuwa ya bayyana matakin a matsayin harin kai tsaye kan ma'aikatan ƙasarsa yayin da shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula Von Der Leyen, ta ce matakan za su yi illa ga ƴan kasuwa da abokan hulɗarsu.
Mista Trump dai ya yi iƙirarin cewa matakin zai ƙara bunƙasa masana'antar ƙera motoci a Amurka tare kuma da samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa hannun jari.
Buɗewa
Masu bibyarmu barkan ku da zuwa shafin BBC Hausa na labaran duniya kai-tsaye na Najeriya da sauran sassan duniya na yau Alhamis, 27 ga watan Maris, 2025.
Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu har ƙarshen wannan rana.
Kuna iya faɗin albarkacin bakinku kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na facebook, X, Instagram, sannan ku kalli ƙayatattun bidiyoyi a shafinmu na YouTube, kuma ku shiga tasharmu ta WhatsApp domin samun labarai da zarar sun faru.