Usman Minjibir da Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba
An kashe ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe ɗaya daga cikin ma'aikatanta a lokacin da aka kai hari a harabar ofishinta da ke tsakiyar Gaza.
Haka nan ta kuma bayyana cewa an kashe wani mutumin na daban sanadiyyar harin a Deir al-Balah.
Sai dai sojojin Isra'ila sun musanta kai hari a yankin.
Bayan sake ƙaddamar da hare-hare ta sama a Gaza, a yanzu dakarun Isra'ila sun ce za su faɗaɗa samamen nasu ta hanyar shiga yankin ta ƙasa.
Isra'ilar ta ce ta faɗaɗa ayyukanta zuwa wurin da ake kira mashigar Netzarim wanda ya raba arewaci da kudancin Zririn Gaza.
NLC ta bukaci Tinubu ya mayar da gwamnan Rivers kan mukaminsa nan take
Asalin hoton, NLC
Bayanan hoto, Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun yi kakkausan Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin saba doka da shugaba Tinubu ya yi, wajen kafa dokar ta-baci da dakatar da gwamnan jihar Siminilayi Fubara, da mataimakiyarsa, da yan majalisar dokokin jihar Rivers.
Kungiyoyin sun ce matakin ya saba wa tanadin sashe na biyu, da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, kuma ya zama cin zarafi ga ikon zartarwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar ranar Larabar nan,kwana guda bayan shugaba Tinubu ya sanar da matakin na sa, da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fadin kasar.
Sanarwar ta bukaci shugaban kasar ya gaggauta janye sanarwar da ya bayar, da ka iya dora kasar a kan tubalin sabawa doka a nan gaba.
Yadda ake dama kunun gyaɗa
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
A yau cikin filinmu na girke-girken Ramadan, Safiyya Jamil Nakwarai za ta nuna mana yadda ake hada kunun gyada.
Sojojin Najeriya sun ceto mutum 101 daga hannun ƴan fashi a Katsina da Zamfara
Asalin hoton, FANSAN YAMMA
Sojojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun ce sun ceto mutum 101 da aka yi garkuwa da su a ƙananan hukumomin Ƙanƙara da ke jihar Katsina da kuma Shinkafi a jihar Zamfara.
Shugaban sashen yaɗa labarai na rundunar, Laftanar-kanar Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce rundunar ta samu nasarar ce a wani samame da ta ƙaddamar kan dabobin ƴan fashin daji a ranakun 17 da 18 ga wannan wata na Maris.
Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin samamen an kashe ƴan fashi 10 a fafatawar da aka yi tsakanin dakaru da ƴan fashin a yankin Faru na ƙaramar hukumar Maradun.
Haka nan sanarwar ta ce an fara samamen ne daga yankin Tudun Pauwa na ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, inda aka kashe ƴan fashin daji uku tare da ceto mutum 83 da aka yi garkuwa da su.
Sannan bayan tattara bayanan sirri, rundunar ta kai farmaki a Bagabuzu na yankin Faru a jihar Zamfara, inda ta kashe ƴan fashi 7 da ƙwato wasu kayayyaki, ciki har da babur.
Zamfara da Katsina, jihohi ne da ke fama da matsalar ayyukan ƴan fashin daji wadanda ke kai farmaki a ƙauyuka, suna kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Dukkanin jihohin biyu sun kafa rundunonin sintiri wadanda ke taimaka wa dakarun sojin Najeriya wajen yaƙi da matsalar, wadda aka shafe shekara da shekaru ana fama da ita.
Hare-haren ƴan bindigan sun haifar da asarar rayuka da durƙusar da ayyukan tattalin arziƙi a yankunan, tare da tarwatsa mutane daga muhallansu.
Tinubu ya rantsar da mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Rivers
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan riƙo na jihar Rivers, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar, jiya Talata.
Bukin rantsuwar ya gudana ne yau Laraba a fadar shugaban Najeriyar da ke Abuja.
A ranar Talatar ne Tinubu ya sanar da sunan Ibas a matsayin wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar ta Rivers, bayan dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa jihar, lamarin da ke nufin an dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da kuma ƴanmajalisar dokokin jihar na tsawon wata shida.
Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Jihar Rivers ta kwashe tsawon lokaci cikin rikita-rikitar siyasa, lamarin da ya kai ga yunƙurin tsige gwamnan jihar da kuma rushe zauren majalisar dokokin jihar.
Matatar Dangote ta ce ta daina sayar da man fetur da Naira
Asalin hoton, X/@AlikoDangote
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetur da kuɗin Najeriya wato naira.
Kamfanin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aika wa dilallan man fetur kuma ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.
Sanarwar ta ce ''Matatar man fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da fetur a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kauce wa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.''
Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke sayar da man domin ya yi daidai da kuɗin da suke sayen ɗanyen mai na wani ɗan lokaci.
Sanarwar ta kuma ce da zarar matatar ta karɓi jiragen dakon mai da aka saya da naira daga kamfanin NNPC, za ta ci gaba da sayar da man fetur ɗin da naira.
Shugaban riƙon ƙwarya a Rivers ya isa fadar Shugaba Tinubu
Asalin hoton, PRESIDENCY
Shugaban riƙon ƙwarya na Rivers, Vice Admira Ibok-Ete Ibas da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa kan wannan mukamin ranar Talata ya isa fadar shugaban ƙasa.
Da alama zuwan nasa na da alaƙa da dokar ta-ɓacin da Tinubu ya ƙaƙaba a Rivers bayan da jihar ta faɗa rikicin siyasa.
Tuni dai wannan mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya janyo mabanbantan ra'ayoyi inda al'ummar ƙasar da ƴansiyasa da ma masana ɓangaren shar'a ke ta tsokaci a kai.
Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers
Asalin hoton, Nigerian Senate
Bayanan hoto, Godswill Akpabio
Majalisar dattawan Najeriya ta ɗage tattaunawa kan ƙudirin farko da za su tafka muhawara a zamansu na yau game da amincewa da dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ba tare da bayar da dalilin jinkirin ba.
A yanzu majalisar za ta zauna kan wannan batu da ƙarfe uku na rana.
An yi tsammanin za a tafka muhawara kan ƙudirin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya gabatar, da safiya sai dai ƴanmajalisar sun ɗage tattaunawar.
Ƙudirin dai ya bayyana damuwa game da ruruwar tashin hankali da ya jefa jihar Rivers cikin garari tare da haifar da koma-baya a tafiyar da al'amuran gwamnati.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa kafin dokar ta-ɓacin ta soma aiki, dole ne sai ƙudirin ya samu goyon bayan kashi ɗaya bisa uku na ƴanmajalisar - 73 cikin sanatoci 109.
A yanzu dai hankalin ƴan Najeriya ya karkata kan majalisar dokokin Najeriya domin jin yadda za ta kaya game da dokar ta-ɓacin da Shugaba Tinubu ya ƙaƙaba a Rivers ta tsawon wata shida.
Ƴansandan Bangladesh sun kama shugaban ƙungiyar musulmin Rohingya
Ƴansanda a Bangladesh sun ce sun kama shugaban ƙungiyar musulmai ƴangwagwarmaya ta ƙabilar Rohingya, inda ake tuhumarsa da laifin kisa da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba da kuma aikata ayyukan ta'addanci.
An kama tare da tsare Ataullah Abu Ammar Jununi da wasu ƙarin mutum goma a kusa da birnin Dhaka a jiya Talata.
Hukumomin Bangladesh sun ce ƙungiyar ita ce ke da alkhakin ayyukan ta'addancin da ake aikatawa a sansanin ƴangudun hijira na Rohingya da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne - Atiku
Asalin hoton, X
Bayanan hoto, Atiku Abubakar
Ɗantakarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP a babban zaɓen ƙasar na 2023, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka a jihar Rivers a amatsayin nuna iko a siyasa.
Ya bayyana cewa ga masu bibiyar yadda rikicin Rivers ke kasancewa sun san cewa Bola Tinubu ya kasance mai ruwa da tsaki a rikicin siyasar da ya mamaye Rivers.
"Kau da kai da kuma nuna ko oho wajen kare ta'azzarar rikicin abin kunya ne." kamar yadda Atiku ya bayyana.
Ya ce abu ne da ba za a yafe ba, yadda aka ƙara jefa yankin Neja Delta cikin rikici da rashin kwanciyar hankali - lamarin da ya warware ƙoƙarin samar da zaman lafiyar da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar'adua ya yi.
"An wanke shekarun da aka shafe da samun cigaba saboda kawai wata buƙata ta ƙashin kai." in ji Atiku.
A cewarsa, matakin na Tinubu ci zarafin dimokraɗiyya ne kuma ya zama dole a yi kakkausar suka.
An rufe jami'oi uku a Pakistan saboda ƙaruwar hargitsi a Baluchistan
Hukumomi a kudu maso yammacin Pakistan sun bayar da umarnin rufe jami'oi uku a Lardin Baluchistan har sai baba ta gani yayin da ake samun karuwar hare-haren sojoji.
Sakamakon fargabar tsaro ne aka dakatar da dukkan hada-hada sannan za a riƙa koyarwa ta intanet har sai yadda hali ya yi.
Za a sake bibiyar matakin domin buɗe makarantun bayan sallah da za a yi nan da mako biyu.
A makon da ya gabata ne, mayaka daga kabilar Baloch suka kai hari kan wani jirgin ƙasa ɗauke da ɗaruruwan fasnjoji lamarin da ya gomman mutane rasa ransu.
An tsananta tsaro a babban birnin lardin, Quetta inda aka ƙara yawan sojoji da kuma cibiyoyin bnciken ababen hawa.
Matakin Tinubu kan Rivers babbar barazana ce ga dimokraɗiyya - Gwamnonin PDP
Asalin hoton, Bala Muhammaed Facebook
Bayanan hoto, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun buƙaci Shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya janye dakatarwar da ya yi wa gwamnan Rivers Siminalayi Fubara.
Ƙungiyar Gwamnonin ta PDP ta bayyana dakatarwar da aka yi wa Fubara a matsayin "babban kuskure" sannan mummunan mataki ne da zai haifar da koma-baya."
A ranar Talata da daddare ne Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan jihar Rivers sakamakon ƙiƙi-ƙaƙar siyasa da aka daɗe ana gani a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Shugaban ya kuma dakatar da Fubara da mataimakinsa da ƴanmajalisar dokokin jihar tare kuma da naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon soji mai muƙamin vice-admiral, a matsayin wanda zai ja ragamar al'amuran jihar.
Cikin wata sanarwa ranar Laraba, Bala Mohammed wanda shi ne gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya ce ayyana dokar ta-ɓacin a Rivers abin damuwa ne kan makomar jihar.
Gwamna Bala Muhammad ya ce jan baki ya yi shiru da Tinubu ya yi kan rawar da Nyesom Wike, ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ke takawa a rikicin siyasar na Rivers kamar ba shi dama ce ya yi kiɗinsa kuma ya yi rawarsa.
Ya ce "Wike ya zama doka saboda yana yin abin da kake so. Yanzu mun sani. Wannan sam babu dattako, an nuna son kai da kuma rarraba kawuna," in ji sanarwar.
Kungiyar gwamnonin ta PDP ta ce matakin ƙarara barazana ce ga dimokraɗiyyar Najeriya sannan zai ƙara rura wutar rikici a ƙasar tare da ƙara janyo rashin yarda da lalata tattalin arziki da kuma zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.
Yadda gobara ta lalata dukiya ta biliyoyin naira a Kano
Asalin hoton, Abdullahi Kiyawa/Facebook
Bayanan hoto, Tawagar kwamishinan ƴansandan Kano bayan zuwa inda gobarar ta tashi
Wata gobara da ta tashi a wata kasuwar ƴan gwangwan da ke Dakata a jihar Kano ta lalata dukiya ta biliyoyn naira.
Kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da labarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba.
Bayanai sun ce gobarar ta soma ne bayan da aka ga tartsatsin wuta daga wasu sandunan wutar lantarki inda kuma nan da nan ta bazu zuwa masana'antar sarrafa gyaɗa.
Kwamishinan ƴansanda na Kano, Ahmed Bakori ya kai ziyara inda lamarin ya faru inda ya bayyana yanayin a matsayin abin takaici.
Ya kuma ce an kama wani mutum da ya yi koƙarin sace wasu kayayyaki a wurin gobarar.
A cewarsa za a gudanar da bincike mai zurfi domin kare sake afkuwar haka.
Ya kuma yi yaba da hanzarin da jami'an hukumar kashe gobara da sauran mutanen gari suka yi wajen kashe wutar.
Asalin hoton, Abdullahi Kiyawa/Facebook
Bayanan hoto, Wani ɓangare na irin ɓarnar da gobarar ta yi
Asalin hoton, Abdullahi Kiyawa/Facebook
Dokar hana fitar da aka sa a yankunan birnin Nagpur na Indiya na nan daram
Asalin hoton, ANI
Bayanan hoto, Hatsaniya ta kaure a birnin Nagpur na Indiya bayan da ƙungiyoyi suka nemi a rushe kabarin sarkin Mughal, Aurangzeb
Dokar hana fita da aka ƙaƙaba a wasu yankunan birnin Nagpur na Indiya na nan daram yayin da aka shiga kwana na biyu.
An saka dokar ne sakamakon zanga-zangar neman a lalata kabarin wani sarki da ya yi mulki a ƙarni na 17.
An jibge sama da ƴansanda dubu biyu a birnin domin tabbatar da tsaro.
A ranar Litinin ne, wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama suka ƙone hotunan sarkin Mughal, Aurangazeb da kuma kabarinsa da aka kwaikwaya wanda yake birnin Aurangabad.
Arangama ta kaure ne bayan yaɗa jita-jitar cewa an lalata wasu tambura na addini a lokacin zanga-zangar.
Masu fafutuka sun ce Aurangzeb ya muzgunawa mabiya addinin Hndu sai dai masu suka na ganin ana amfani da sunansa wajen bayyana Indiyawa musulmai a matsayin masu mugunta.
'Dakatar da Fubara da ƴan majalisar dokokin Rivers ya saɓawa tsarin mulki - NBA
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA ta ce sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da gwamnan Jihar Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar na watanni shida, ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Mazi Afam Osigwe SAN, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu ya ce ayyana dokar da shugaba Tinubu ya yi sakamakon rikicin siyasa a jihar zai yi wa dimokraɗiyya da tsarin mulin ƙasar illa mai yawa musamman ga sashe na 305 na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 wanda ya bayyana matakan ayyana dokar wanda kuma shugaban ƙasar ke iƙirarin ya dogara da su.
Sanarwar ta kuma ce tsarin mulkin ƙasar na 1999 bai bai wa shugaban ƙasa ƙarfin cire zaɓaɓɓen gwamna ko ƴan majalisu ba ta hanyar fakewa da dokar ta-ɓaci, sai dai tsarin mulkin ya zayyana matakan cire gwamna da mataimakin gwamna a ƙarƙashin sashe na 188.
Hakazalika, ƙungiyar ta ce cire ƴan majalisar dokoki da kuma rushe majalisa na ƙarƙashin tanadin tsarin mulki da dokokin zaɓe, waɗanda alamu ke nuna babu wanda aka bi cikinsu kafin ɗaukar wannan matakin.
Ƙungiyar ta NBA ta kuma jaddada cewa yanayin da ake ciki a Rivers na zazzafar rikicin siyasa, bai cika sharuɗɗan tsarin mulkin ƙasa na cire zaɓaɓɓun shugabanni ba.
An kama babban abokin hamayyar Shugaba Erdogan
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ekram Imamoglu
Hukumomi a Turkiyya sun tsare babban abokin hamayyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda kuma shi ne magajin garin Istanbul, Ekrem Imamoglu.
An kuma kama gomman ƴansiyasa da ƴanjarida da ƴankasuwa cikin samamen da aka kai cikin dare.
Ana zargin Mista Imamoglu da aikata rashawa da kuma tallafa wa ƙungiyar ta'addanci ta PKK.
A ranar Lahadi ne ake sa ran za a naɗa shi a matsayin ɗantakarar babbar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi nan da shekaru uku.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama a Turkiyya ta yi tur da tsarewar da aka yi wa Imamoglu, inda ya ce tsabagen cin fuskar tsarin shari'a ne.
An taƙaita amfani da wasu shafukan sada zumunta sannan an haramta gudanar da zanga-zanga a Instanbul na wani ɗan lokaci.
Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu - Fubara
Asalin hoton, X/@SimFubara
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara ya ce tun hawansa mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma kawo cigaba a jihar, sai dai ƴan majalisar dokokin jihar suna ta kawo cikas ga ƙoƙarin nasa.
Gwamnan da aka dakatar ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar bayan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da shi da mataimakiyarsa na watanni shida saboda rikicin siyarsa da ya ki ci ya ki cinyewa.
Fubara ya ce dukkanin abubuwan da ya yi da matakan da ya ɗauka ya yi su ne bisa rantsuwar da ya sha na kama aiki, inda ya ce hakan ne ya sa bayan da shugaba Tinubu ya shiga tsakani, ya yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar da aka amince ciki har da dawo da kwamishinonin da suka ajiye aiki.
Ya kuma ce ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin hukuncin kotun ƙolin domin dawo da zaman lafiya a jihar, sai dai a cewarsa, a kowane mataki ƙoƙarinsa ya gamu da cikas daga ɓangaren majalisar dokokin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da rikicin siyasar da ake yi, gwamnan ya ci gaba da gudanar da gwamnati yadda ya kamata, inda ya ce ana biyan ma'aikata albashinsu kuma an ƙaddamar da muhimman ayyukan cigaba a jihar.
Fubara ya buƙaci ƴan ƙasar su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga dokar ƙasa, inda ya ce za su ci gaba da tuntuɓar waɗanda suka dace wajen tabbatar da ɗorewar dimokraɗiyyar a jihar, kuma jihar ta ci gaba da bunƙasa.
Siyasar jihar ta Rivers ta damalmale ne tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da magabacinsa, ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike.
Lamarin ya kai ga cewa ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun yi barazanar tsige gwamna Fubara.
Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Gaza waɗanda rahotanni ke cewa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 13.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan abin da su ka kira sansanonin sojojin Hamas.
Hare-haren baya-bayan nan na zuwa ne bayan ruwan wutar da Israi'la ta yi a daren Litinin wanda ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta ta ce ya hallaka mutum fiye da 400.
Isra'ila ta kuma rarraba takardu a wasu sassan Gaza, tana gargaɗin mutane su fice daga yankunan, ciki har da ƙauyen Beit Hanoun.
Isra'ila da Hamas dai sun sami saɓani ne kan yadda za a kai yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar zuwa mataki na gaba bayan mataki na farko ya zo ƙarshe a farkon wannan watan.
A gefe guda kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta cigaba da kai ''hare-hare iya ƙarfinta'' kan Hamas a zirin Gaza, inda ya yi gargaɗin cewa za a cigaba da yarjejeniyar ne kawiai a cikin luguden wuta, kuma '' yanzu aka fara''
Shugabannin Kongo da Rwanda sun yi kiran tsagaita buɗe wuta a gabashin Kongo
Asalin hoton, Qatar's Ministry of Foreign Affairs
Shugaban Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo Felix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda, Paul Kagame sun yi kira da a tsagaita wuta a gabashin Kongo bayan tattaunawar ido da ido da suka yi a Qatar.
Wannan dai shi ne karon farko da shugabbanin biyu suka gana tun bayan da mayaƙan ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suka zafafa farmakin da suka kai wa gabashin DRC a watan Janairun da ya gabata.
Sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar ta ce ya kamata a dakatar da buɗe wuta cikin gaggawa ba tare da wani sharaɗi ba.
Sai dai ba bu tabbas akan ko kiran nasu zai yi tasiri kan ƙungiyar ta M23 wadda a yanzu ta mamaye yankuna fiye da kowane lokaci.
Rasha da Ukraine sun ƙaddamar da hare-hare kan ƙasashensu
Asalin hoton, Reuters
Rasha da Ukraine sun ƙaddamar da hare-hare ta sama waɗanda suka lalata ababen more rayuwa na kasashenu, sa'o'i bayan da shugaba Putin ya ce Rasha za ta daina kai hare-hare kan wuraren makamashin Ukraine.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce abubuwan da Rashan ta kai wa hari sun hada da asibitoci da tashohin wutar lantarki.
Ya ce shugaban na Rasha ya ƙi amincewa da tsagaita buɗe wuta a tattaunawarsa ta wayar tarho da shugaba Trump a jiya Talata.
Sai dai wani jami'in diflomasiyar Amurka ya ce kawo yanzu akwai wasu batutuwa da ya kamata su tattauna akai kuma za su yi haka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Jedda.
A ɗayan bangaren Rasha ta ce harin da jirgin Ukraine mara matuƙi ya kai ya haddasa gobara a wani wurin adana man fetur da ke yankin Krasnodar.