Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, da Umar Mikail
Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta da suka maƙale a Congo
Asalin hoton, @YusufTuggar
Gwamnatin Na ta bayyana cewa tana shirin kwashe wasu ma'aikata ƴan Najeriya da suka makale a yankin Bambari da ke Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya bayan da aka bar su ba tare da kulawa ba.
Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Bangui sun tuntubi mutanen da abin ya shafa kuma suna aiki tare da hukumomin cikin gida don tabbatar da lafiyarsu da kuma dawowarsu gida cikin gaggawa.
Ma’aikatar ta kuma shawarci ’yan Najeriya da ke neman aiki a ƙasashen waje su duba sahihancin masu ɗaukar aiki da kuma tabbatar da cewa dukkan takardunsu sun cika kafin tafiya.
Kirista mai nakasa da ke gina rayuwar matasan Musulmi a arewacin Najeriya
Haɗa takalmi wata sana'a ce da ake koya domin dogaro da kai da ɗaukar ɗawainiyar wasu ta hanyar tsarawa da haɗa ƙayatattun takalma a cikin gida da ake kasuwancinsu domin samun kuɗin shiga.
Amma shi a wajen Chris, wanda ake kira da Sir Chris, sana'ar ba tsaya a hanyar samun abinci kaɗai ba, a wajensa, sana'a ce da za a yi amfani da ita domin haɗin kai tsakanin musulmi da kirista da ƙaunar juna.
A Kaduna - jihar da ta daɗe tana fama da rikice-rikicen kaɓilanci da suke riƙewa zuwa na addini - an wayi gari da samun wani matashi mai suna Chris, wanda ɗan ƙabilar Urhobo a jihar Delta ta yankin Niger Delta.
Matashin wanda kuma Kirista ne yana yunƙurin kawo sauyi wajen samar da haɗin kai da ƙaunar juna tare da watsi da yaƙi da wariya ga nakasassu ta hanyar amfani da haɗa takalma.
Shagonsa ya zama wata matattara matasan Hausawa da suke koyon sana'a cikin wasa da dariya, inda suke koyon sana'a da kuma koyon muhimmancin ƙaunar juna ba tare da bambancin addini ba ƙabila ba.
Asalin sunansa Christopher Difference, amma an fi saninsa da Sir Chris, amma daga baya wasu suka koma kiransa "United", sunan da ya ce har yanzu bai san me ya sa aka laƙana masa ba.
Daga shiga shagon, za ka ci karo da matasa - yawanci Hausawa - kowa na ta aiki. Daga masu yanka fatar haɗa takalma sai masu ɗinki da masu buga ƙusa da masu shafa gam.
A can gefe kuma gwanin sha'awa ga oga Chris a keken guragu yane aiki, sannan yana bayar da umarnin wasu aikace-aikace cikin wasa da dariya. Sannan kuma ga sauti na tashi kamar yadda Hausawa suke cewa taɓa kiɗi taɓa karatu.
Volker Turk ya soki haramta ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Falasɗinawa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar kare haƙƙin bil'adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce haramcin da Birtaniya ta yi wa ƙungiyar rajin kare hakkin bil'adama ta Palestine Action' abin takaici ne.
Volker Turk ya ce matakin abu ne da bai dace ba, inda ya buƙaci gwamnati ta sake duba lamarin.
A farkon wannan watan ne Birtaniya ta haramta ayyukan ƙungiyar Palestine Action bayan kutsen da wani ɗan kungiyar ya yi a sansanin sojin saman ƙasar.
Shiga kungiyar na iya janyo wa mutum daurin shekara 14 a kurkuku.
'Yanmajlisar Birtaniya na neman ƙasar ta amince da ƙasar Falasɗinu
Wata tawagar 'yanmajalisar Birtaniya za su aika wa Firaminista Keir Starmer wasiƙa domin neman gwamnati ta amince da ƙasar Falasɗinawa.
Firaministan na shan matsin lamba a kwanan nan kan kiraye-kirayen gwamnatinsa ta ayyana amincewa da ƙasar Falasɗinu, kamar yadda BBC ta fahimta.
'Yanmajalisar na jam'iyyu da dama za su nemi Birtaniya ta bi sawun Faransa ne, wadda za ta yi hakan a watan Satumba mai zuwa.
Kotu ta ɗaure G Fresh da Hamisu Breaker wata biyar a gidan yari kan wulaƙanta naira
Asalin hoton, EFCC
Bayanan hoto, G Fresh mawaƙin Rap ne na Hausa wanda a yanzu ya fi shahara a dandalin TikTok
Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa.
Cikin rahoton daEFCC ta fitar, kotun ta kama G Fresh da laifin "liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000" a shagon Rahama Saidu a watan Nuwamban 2024.
Kazalika, kotun ta kama Breaker da laifin "wulaƙanta takardun naira na N200 da suka kai N30,000" yayin wani biki a garin Hadeja da ke jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.
Mai Shari'a S.M Shuaibu ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya CBN ta 2007, kuma ya yanke wa kowannensu ɗaurin wata biyar a gidan yari ko kuma tarar naira 200,000.
Asalin hoton, Facebook/Hamisu Breaker
Bayanan hoto, Hamisu Breaker ya shahara da waƙoƙin Hausa irin na zamani
Yunwa ta kashe ƙarin mutum 9 cikin kwana ɗaya a Gaza
Ma'aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce ƙarin mutum tara sun mutu cikin awa 24 da suka gabata saboda yunwa.
Jimillar mutum 122 ne, ciki har da yara 83, suka mutu saboda ƙarancin abinci tun daga fara yaƙin, in ji ma'aikatar.
Isra'ila ta amince a riƙa jefa wa Falasdinawa abinci ta sama
Asalin hoton, Reuters
Israila ta ce nan ba da jimawa ba za ta bar ƙasashen Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa su koma jefa wa al'ummar Gaza kayan agaji ta sama.
Hukumomin Isra'ila sun ce watakila ma a yau Jordan za ta soma jefa musu abincin.
Matakin Isra'ila na toshe hanyoyin shiga yankunan Falasɗinawa ya janyo mummunan bala'in yunwa, wanda ya sa ƙasashen duniya da kungiyoyin agaji suka yi ta.
Ƙungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Doctors without Borders (MSF) ta ce ɗaya cikin huɗu na ƙananan yaran da aka yi wa gwaji a asibitocinta na fama da yunwa.
Wata uwa ta shaida wa BBC cewa: "Muna fama da yunwa. Idan muka shiga kasuwa ba mu samun komai. Fulawa da ake amfani da ita a kullum, yanzu babu ita a kasuwa"
Najeriya na shirin kwaso 'yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya
Asalin hoton, Nema
Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar.
Wata sanarwa da Ma'iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen.
"An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui," a cewar sanarwar.
"Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami'an tsaro a ranar Asabar."
Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da naɗa Ladan Bosso a matsayin sabon kocinta kafin fara kakar wasa ta bana.
Wata sanarwa da kulbo ɗin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce nan gaba zai yi ƙarin bayani kan yarjejeniyar da ya ƙulla da Boso.
Wannan ne karon farko da ƙungiyar ta jihar Kano za ta buga babbar gasar firimiya ta Najeriya NPFL bayan samun gurbi a kakar wasa ta 2024-25 a gasar NNL.
Ladan Bosso ya jagoranci tawagar Najeriya ta 'yan ƙasa da shekara 20 wato Flying Eagles zuwa kofin ƙasashen Afrka da kuma Kofin Duniya daga 2020 zuwa 2023.
Haka nan ya yi aikin horar da ƙungiyoyi a Najeriya da suka haɗa da Bayelsa United da kuma El-kanemi Warriors.
Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa
Asalin hoton, Jigawa state police command
Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.
Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025.
Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa'ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta SP Shi'isu Lawan Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya.,
Rundunar ta kuma sanar da cewa mutumin na hanunta, a sashen binciken laifuka da ke Dutse, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da shi gaban kotu.
Shugabannin Najeriya nawa ne suka rasu tun bayan samun ƴanci?
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar 13 ga watan Yulin 2025, BBC ta duba tare da kawo bayanai game tsofaffin shugabannin ƙasar da suka rasu da kuma dalilan mutuwarsu.
Kwankwaso ya yi kuskure - Tinubu bai manta da Arewa ba — Fadar Shugaban ƙasa
Asalin hoton, Tinubu/facebook
Fadar shugaban Najeriya ta mayar wa tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso martani kan ikirarinsa na cewa gwamnatin Bola Tinubu na nuna bambanci tsakanin yankunan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan sadarwa, Sunday Dare ya fitar a yau Juma'a, ya ce, tun bayan hawan sa mulki, shugaba Tinubu ya gudanar da muhimman ayyuka da dama a Arewacin ƙasar da suka shafi harkoki daban-daban.
Ya bayar da misali da wasu ayyuka fiye da arba’in da ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar, ko ke aiwatarwa a Arewacin ƙasar daga hawa kan mulki.
Daga cikin manyan ayyukan da ya lissafa akwai gina tituna da bangaren noma da bangaren lafiya da ayyukan ɓaagren makamashi da dai sauransu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dai ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna wariya ga Arewacin Najeriya ta hanyar mayar da yawancin albarkatun ƙasar zuwa Kudancin ƙasar.
A wani taron masu ruwa da tsaki na jihar Kano da ya gudana a ranar Alhamis, Kwankwaso ya ce "Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan," in ji Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ya yi wa jam'iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya zargi jam'iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Najeriya.
Likitoci sun fara yajin aikin kwana biyar a Birtaniya
Asalin hoton, PA Media
Dubban likitoci a Birtaniya sun fara yajin aikin kwana biyar a safiyar yau, Juma’a bayan kasa cimma matsaya da gwamnatin ƙasar ta jam’iyyar Labour kan batun ƙarin albashi.
Sakataren Lafiya, Wes Streeting, ya ce gwamnati na kokarin ganin ayyukan lafiya sun ci gaba, tare da rage cikas da yakin aikin zai haifar ga marasa lafiya.
Ya bayyana cewa asibitoci za su dakatar da jinya ne kawai idan lamarin ya zama dole.
A baya, yajin aikin ya fi shafar sashen masu buƙatar kulawar gaggawa, amma a wannan karon, hukumar kula da lafiya ta NHS na ƙoƙarin tabbatar da cewa ayyukan da ba na gaggawa ba sun ci gaba da gudana.
Streeting ya ce yajin aiki zai jawo babbar hasara ga NHS da ƙasar gaba ɗaya, yana zargin ƙungiyar Likitocin Birtaniya (BMA) da gaggauta shiga yajin aiki.
Shugaban jam’iyyar Labour, Sir Keir Starmer, ya ce yajin na iya rusa cigaban da aka samu wajen gyaran NHS cikin shekarar da ta gabata.
Duk da haka, Streeting ya jaddada cewa: “Zan tabbatar mun rage cikas da yajin aikin zai haifar ga marasa lafiya.”
Isra’ila da Amurka sun fice daga tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wakilan Isra’ila da Amurka sun fice daga tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da ake yi a birnin Doha na ƙasar Qatar, inda Amurka ta zargi Hamas da rashin nuna gaskiya a shirin zaman lafiya.
Wakilin musamman na Amurka, Steve Witkoff, ya faɗa a wata sanarwa cewa Hamas ta nuna rashin niyya wajen kawo ƙarshen rikicin, shi ya sa suka yanke shawarar komawa gida domin yin shawara.
Isra’ila ba ta bayyana dalilin ficewarta daga tattaunawar kai tsaye ba, sai dai wani jami’inta ya ce tattaunawar ba ta rushe ba, kuma za su koma idan lokaci ya yi.
Hamas ta bayyana mamakinta kan wannan mataki na ficewarsu tana mai cewa tana da niyyar ci gaba da tattaunawa.
Duk da ƙoƙarin masu shiga tsakani, ana ci gaba da samun babban gibi tsakanin ɓangarorin da ke cikin tattaunawar.
Hare-haren ƴan bindiga sun kashe mutum 14 a Filato
Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 14 da wani ɗan sanda na MOPOL ne suka mutu a hare-hare biyu da wasu 'yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato a ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025.
Rahotanni sun ce an kai ɗaya daga cikin hare-haren ne da misalin ƙarfe 4 na yamma, yayin da mutanen da lamarin ya shafa mafi yawansu daga ƙauyen Chirang ke dawowa daga kasuwar Bokkos zuwa ƙauyen Mangor.
Shugaban masu sa ido kan zaman lafiya na ƙaramar hukumar Bokkos, Kefas Mallai ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch inda ya ce mutane 14 ne suka mutu, yayin da wasu uku kuma suka jikkata.
A cewar Mallai, kafin wannan harin, wasu ‘yan bindiga sun harbe wani ɗan sandan MOPOL a wani shingen bincike da ke hanyar Richa a safiyar ranar.
Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos, Amalau Amalau, ya bayyana lamarin a matsayin “taƙaici da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa,” yana mai cewa an riga an kai gawarwaki da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai samu damar bayyana komai ba a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.
Sarkin Gusau ya rasu yana da shekara 71
Asalin hoton, Zamfara state government
Sarkin Gusau na jihar Zamfara, Dr. Ibrahim Bello, ya rasu a ranar Juma’a yana da shekara 71, bayan fama da doguwar jinya a birnin Abuja.
Marigayin shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Gusau, kuma ya gaji mahaifinsa da ya rasu a ranar 16 ga Maris, 2015.
Marigayin ya shafe shekaru 10 da wasu watanni yana kan karagar mulki.
Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya tabbatar da rasuwar sarkin a cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa Suleiman Idris ya fitar tare da bayyana jimamin gwamnatin jihar bisa wannan babban rashi.
Gwamnan ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi yana mai cewa marigayin babban uba ne kuma shugaba mai kishin ci gaban Zamfara.
“Ina matuƙar alhini da jin labarin rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello." in ji sanarwar.
“Ina mika ta’aziyya ta ga majalisar sarakunan jihar da iyalan marigayin da masarautar Gusau da kuma ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara." gwamnan ya cewa.
Za a yi wa sarkin jana'iza ne yau Juma'a a garin Gusa.
Thailand ta gargaɗi cewa rikicinta da Cambodia na iya rikidewa ya koma yaƙi
Asalin hoton, Getty Images
Thailand ta gargaɗi cewa rikicinta da Cambodia na iya rikidewa ya koma yaƙi yayin da sojojin ƙasashen biyu su ka ci gaba da musayar wuta a kan iyakar da ke haɗa su, kwana ɗaya bayan ɓarkewar sabon rikici mai tsanani.
Rahotanni daga hukumomin Thailand na cewa aƙalla mutum 14 – dukkansu fararen hula – ne suka rasa rayukansu a rikicin.
Haka kuma, ɗaruruwan mutane sun jikkata, yayin da dubban mazauna yankunan da ke kusa da iyakar suka tsere domin tsira da rayukansu.
Babban ƙalubalen yanzu shi ne yadda dakarun kowanne bangare ke ci gaba da kai farmaki, lamarin da ke haddasa asara ga ɓangarorin biyu.
A ɓangaren Cambodia kuma, hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a rikicin.
Wannan rikici dai na daga cikin mafi muni da ya taɓa faruwa tsakanin Thailand da Cambodia cikin sama da shekaru goma.
Isra'ila da Amurka sun soki shirin Faransa na amincewa da kafuwar ƙasar Falasɗinawa
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila da Amurka sun yi Allah-wadai da matakin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke shirin ɗauka na amincewa da kafa ƙasar Falasdinawa a watan Satumba mai zuwa.
Faransa ita ce ƙasa ta farko cikin ƙasashen G7 – ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya – da za ta fito fili ta bayyana matsayinta na goyon bayan kafa ƙasar Falasdinawa.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa wannan mataki na Macron yana da haɗari, yana mai cewa Hamas za ta yi amfani da shi wajen yaɗa farfaganda.
Haka zalika firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce wannan mataki tamkar ƙarfafa ayyukan 'yan ta’adda ne.
Sai dai ƙasar Saudiyya ta yabawa shirin shugaban Faransa, tana mai cewa Macron ya kafa tarihi da wannan mataki.
Mahukuntan Falasdinu da ƙungiyar Hamas ma sun nuna gamsuwa tare da maraba da wannan yunkuri.
Assalamu Alaikum
Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'atu babbar rana.
Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.