Saka ya tsawaita zaman shi a Arsenal
Bukayo Saka ya amince da tsawaita zaman shi a kungiyar Arsenal ta hanyar sanya hannu kan kwantaragi na dogon wa’adi.
Mun fahimci cewa sabon kwantaragin zai sanya Saka, mai shekara 24 ya zama dan wasa da ya fi kowane daukan albashi mai tsoka.
Wannan kwantaragi na daga cikin dabarun Arsenal na baya-bayan nan domin rike manyan ‘yanwasanta, a kokarin ganin ta lashe kofi.
William Saliba, da Gabriel Magalhaes, da Ethan Nwaneri da kuma Myles Lewis-Skelly dukkaninsu sun sanya hannu kan sabbin kwantaragi masu dogon wa’adi a baya-bayan nan.
Saka, mai buga wa Ingila wasa ya zama babban ginshiki a Arsenal tun bayan fara wasa a shekarar 2018, bayan ya samu horo a tawagar yara ta kungiyar.
A kakar wasa da ta gabata Saka ya ci wa Arsenal kwallo 12, sannan ya taimaka aka zura 13 a wasa 37 da ya buga duk da cewa ya yi fama da rauni na tsawon watanni uku.
Ya zama kyaftin din kungiyar karon farko a kakar wasa ta 2023-24, inda ya kammala kakar a matsayin dan wasan da ya fi yawan kwallaye bayan ya ci kwallo 20.