Ƙarshen rahotonni
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na yau Juma'a.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 07/11/2025
Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na yau Juma'a.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.

Asalin hoton, Reuters
Masu shigar da ƙara a Turkiyya sun bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaro da wasu jami'ai 35.
Ofishin mai shigar da ƙara na birnin Istanbul ya ce ana neman mutane ne bisa laifukan yaƙi da kisan ƙare-dangi da suka aikata a zirin Gaza, da wani jirgin kayan agaji.
Isra'ila ta sha musanta zargin aikata laifukan kisan ƙare-dangi a Gaza.
Matakin na Turkiyya na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke kambama rawar da Turkiyyan ta taka wajen ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila.
Kazalika, Turkiyyar na shirin tura dakaru domin aiki da takwarorinsu wajen kiyaye zaman lafiya a Zirin Gaza.

Asalin hoton, Nigerian Army
Sabon Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu ya kai ziyarar aiki karon farko birnin Maiduguri domin ganawa da rundunar yaƙi da Boko Haram.
Yayin ziyarar ta kwana biyu, janar ɗin ya yaba wa rundunar Operation Hadin Kai bisa "ƙoƙarinsu na yin amfani da sababbin dabaru wajen yaƙi da 'yanbindiga", kamar yadda wata sanarwa daga rundunar ta bayyana.
Kazalika, ya yi alƙawarin inganta walwala da kuma kyautata aikin dakaru a fadin Najeriya. Ya kuma kai wa Shehun Borno ziyara Dr. Abubakar Umar Garbai El-Kanemi a fadarsa.
A makon da ya gabata ne Janar Shaibu ya kama aiki a matsayin hafsan sojan ƙasa bayan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya maye gurbin hafsoshin rundunar sojin ƙasar da sababbi.

Asalin hoton, Nigerian Army

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubaka III a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da barazanar Trump ta kai hari ƙasar ke ci gaba da jan hankali.
Ganawar tasu na zuwa ne bayan Tinubu ya gana da Archbishop na Abuja Ignatius Kaigama.
Fadar shugaban ba ta bayyana abin da suka tattauna ba, amma ana sa ran ba za ta wuce yunƙurin kwantar da hankali ba yayin da wasu ke yaɗa iƙirarin yi wa mabiya addinin Kirista kisan ƙare-dangi.
Daga baya sarkin ya bi sawun shugaban ƙasar wajen yin sallar Juma'a a fadar shugaban ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun Ƙolin Indiya ta bayar da umarnin fitar da karnuka daga ofisoshin gwamnati saboda yawaitar cizon karnukan.
Alƙalan kotun sun ce za a yi wa makarantu da asibitoci da wuraren wasanni shinge da waya, sannan a kai karnukan gidajen kula da dabbobi.
Kazalika, an haramta wa ma'aikatan gwamnati ciyar da karnuka yayin da suke bakin aiki, kuma za a aiwatar da umarnin kotun cikin mako takwas.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun sha sukar kotun game da yunƙurin hana karnuka marasa iyayen gida yawo a bainar jama'a.

Asalin hoton, FCTA
Reshen jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta tare da samun goyon byan Nyesom Wike ya zaɓi Mao Ohabunwa a matsayin shugaban kwamatin amintattun jam'iyyar.
Tsagin jam'iyyar ya zaɓi Mao ne bayan wani biki da aka gudanar a ofis ɗin hukumar kula da birnin Abuja FCTA a yau Juma'a.
Ministan Abuja Nyesom Wike, shi ne jagoran tsagin da ke adawa da shugabancin jam'iyyar na asali kuma shi ne ya jagoranci kafa kwamatin. Haka nan, sun naɗa Isa Dansidi a matsayin sakataren kwamatin.
Da yake jawabi bayan rantsar da kwamatin, Abdulrahman ya ce tsohon kwamatin da Sanata Adolphus Wabara ke jagoranta ya tashi daga aiki.
Rukunin da ke yi wa Wike biyayya ya ɗauki wannan mataki ne bayan kwamatin gudanarwa na jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa Iliya Damagun ya dakatar da sakatarenta Anyanwu da wasu muƙarraban Wike.
Bayan haka ne kuma su ma ɓangaren Wike suka yi taron manema labarai tare da sanar da dakatar da Damagun da wasu manyan shugabanni.
PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa ranar 15 ga watan Nuwamba domin zaɓen sababbin shugabanni, abin da ɓangaren Wike ke adawa da shi wanda ya sa har suka kai jam'iyyar kotu.

Asalin hoton, FCTA

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban jami’in Tigray a arewacin ƙasar Ethiopia ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da hari da jirgin yaƙi mara matuƙi a kan tsofaffin mayaƙan Tigray yayin da ake ta ƙara tsoron cewa sabon rikici na iya ɓarkewa a yankin.
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan rahotannin da suka ce mayakan Tigray ɗin sun shiga wata jiha mai makwabtaka da su tare da karɓe da iko da wasu kauyuka shida.
Rahoton ya ce wannan ne karo na farko da aka samu rikici tsakanin gwamnati da mayaƙan Tigray tun bayan yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo ƙarshen rikicin da ya kashe mutane da dama shekaru uku da suka wuce.
Wani jami'in Tigray ya ce harin bai yi wata babban ɓarna ba.
Har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin kasar, kuma BBC ba ta tabbatar da faruwar wannan harin kai-tsaye ba.
A ranar Alhamis, jami’an jihar Afar da ke makwabtaka da yankin Tigray sun zargi mayaƙan Tigray da karya yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar kutsa kai cikin yankinsu.
An kiyasta cewa dubun dubatar mutane sun mutu a yaki tsakanin ɓangarorin biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Hungary, Viktor Orban, na ziyara a birnin Washington domin ganawa da Shugaba Amurka, Donald Trump karo na farko tun bayan dawowar Trump kan mulki.
Kafin tafiyarsa, Orban ya ce zai nemi sassauci a takunkumin da Amurka ta kakaba kan fitar da man fetur na Rasha saboda yaƙin da take yi a Ukraine.
Hungary na ɗaya daga cikin ƙawaye mafi kusa da Moscow a cikin Tarayyar Turai, kuma har yanzu kasar ta dogara ne sosai da shigo da mai daga Rasha.
Sai dai gwamnatin Amurka tana son ganin wannan dogaro ya tsaya.

Asalin hoton, Seyi Makinde/X
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gana da shugabannin jam'iyyar PDP na jihohi gabanin babban taron jam'iyyar na ƙasa da za a zaɓi sabbin shugabannin na ƙasa.
Za a gudanar da babban taron ne a Ibada, babban birnin jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Makinde ya gana da shugabannin a gidan sauƙar baƙi na gwamnatin jihar Oyo da ke Asokoro a Abuja, babban birnin ƙasar.
Sai dai babu cikakken bayani kan abin da Makinde ya tattauna da shugabannin jihohi na babbar jam'iyyar hamayyar ba.
Sai dai wasu na ganin ganawar ba ta rasa nasaba da abin da ake son tattaunawa a babban taron jam'iyyar.
Babban taron jam'iyyar ya fuskanci tarnaƙi mai yawa, sakamakon rikicin da ya kai har gaban kotu.

Asalin hoton, Getty Images
Tarayyar Turai ta ce za ta gabatar da sabbin ka'idoji masu tsauri na samun bisa ga yan Rasha, a yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar gilmawar jirage marasa matuƙa da abin da suka kira 'maƙarƙashiya' bayan kusan shekara huɗu ana yaƙi.
A ƙarƙashin sabbin dokokin, za a daina bai wa yan Rasha bizar shiga ƙasashen da dama a lokaci guda, kuma wajibi ne su nemi takardar shiga a duk lokacin da za su yi tafiya zuwa ɗaya daga cikin ƙasashen da ke Tarayyar Turai.
Sai dai sabbin matakan ba za su shafi wasu yan jarida masu zaman kansu ba.
Shugabar kula da harkokin ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce ''babu yadda za a yi su soma yaƙi kuma su yi tunanin za su riƙa yin tafiye tafiye cikin sauƙi''.

Asalin hoton, Getty Images
An gurfanar da mutum fiye da 100 a gaban kotun majistare a Tanzania bisa zargin aikata laifin cin amanar ƙasa.
A cewar takardar tuhumar, waɗannan mutanen ana zarginsu da tada zanga-zanga a lokuta daban-daban da nufin hana gudanar da zaɓen ƙasa da aka yi a ranar 29 ga Oktoba.
Daga cikin su akwai fitacciyar ’yar kasuwar Tanzania, Jenifer Jovin, wadda ake iƙirarin ta karfafa mutane su sayi abin rufe fuska domin kare kansu daga hayakin me sa hawaye da ’yan sanda ke amfani da shi wajen tarwatsa masu zanga-zanga.
’Yan adawa da masu fafutukar kare haƙƙin jama’a sun ce ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu a yayin zanga-zangar neman gyaran tsarin zaɓe..
Shugaba Samia ce ta lashe zaɓen da kashi 98 cikin ɗari, amma ’yan adawa sun bayyana nasararta a matsayin raina dimokuraɗiyya.

Hukumar zaɓen Najeriya ta fara raba muhimman kayayyakin zaɓe a shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar gobe Asabar.

Ana raba kayayyakin ne a gaban wakilan jam'iyyun siyasa da ƴanjarida da jami'an tsaro.

Dama dai tun a ranar Alhamis aka fara raba wasu kayayyakin zaɓen marasa muhimmanci.

Mutum 16 ne ke takarar kujerar gwamnan, ciki har da gwamnan mai ci, Chukwuma Soludo, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu.


Asalin hoton, Reuters
Fiye da mutum 50 ne suka jikkata bayan wata fashewa ta auku a wata makaranta a Jakarta, babban birnin Indonesia
Rahotonni sun ce mutum uku daga ciki sun samu munanan raunuka a fashewar da ta auku lokacin da ɗaliban da malamansu ke tsaka da Sallar Juma'a.
Ƴan sanda sun kuma tabbatar da cewa ɗalibin makarantar ne ya kai harin bayan da ya ƙi Sai dai ya ƙi cewa komai kan rahotonnin kafofin yaɗa labaran ƙasar.
An samu wasu kayayyaki masu kama da bindigogin wasa a wurin lamarin ya faru, inda aka samu rubutun da ke nuna harin - maƙiya musulunci a New Zealand.

Asalin hoton, Hilda Baci/IG
Kundin bajinta na 'Guinness World Records' ya karrama matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci saboda girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.
A watan Satumban da ya gabata ne matashiyar ta yi wani gagarumin aikin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa cikin tukunya ɗaya a duniya.

Asalin hoton, Bilda Baci/IG
Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da 'jollof' abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.

Asalin hoton, Hilda Baci/IG
Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa'a 93 da minti 11

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar 20 ga watan Nuwamba domin yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci.
Alƙalin Kotun Maishari'a, James Omotosho ne ya bayyana haka a zaman kotun na yau kan shari'ar da ake yi wa Mista Kanu kan zargin ta'addanci.
Maishari'a Omotosho ya ɗauki matakin ne bayan da Nnamdi Kanu ya kasa fara kare kansa bayan kwana shida kotun ta ba shi domin yin hakan.
Kotun ta ce bayan Kanu ya gaza amfani da damar da aka ba shi domin kare kansa daga tuhumar da ake yi amsa, bai kamata ya ci gaba da iƙirarin da yake yi cewa an hana damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na jin bahasinsa.
A ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai kotun ta ɗage zamanta domin bai wa wanda ake ƙara damar kare kansa kamar yadda ya buƙata a baya.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Sudan ta yi kira ga ƙasashen duniya su tabbatar da mayaƙan RSF sun girmama yarjejeniyar tsagaita wuta da suka gabatar kafin gwamnatin ta amince da ita.
Fatan da ake da shi kan dakatar da yaƙin ya gamu da cikas yayin da aka samu rahotonnin hare-haren jirage marasa matuƙa a kusa da sansanin sojoji tashar lantarki ta babban birnin ƙasar Khartoum da sojojin ke iko da shi a safiyar ranar Juma'a.
Jakadan Sudan a Sudan ta Kudu, Osman Abufatima Adam Mohammed ya ce dakarun RSF ba ta martaba yarjejeniyoyin da aka cimma a baya ba, a maimakon haka sun riƙa amfani da su wajen faɗaɗa ikonsu.
Ɓangarorin biyu na cikin matsin lambar ƙasashen duniya su amince da jarneneiyar tsagaita wuta ta wata uku da za ta bayar da damar shigar da agaji, wadda za ta bayar da damar cimma yarjejeniyar dindindin.

Asalin hoton, Pablo Porciuncula/AFP
Shugabannin ƙasashen duniya da dama da suka halarci taron sauyin yanayi na duniya da aka gudanar a Brazil sun soki Shugaba Trump na Amurka kan matsayinsa game da sauyin yanayi.
Shugabannin ƙasashen Chile da Colombia sun kira shugaban na Amurka da ''maƙaryaci'' saboda matsayin da ya ɗauka da suka ce ya saɓa wa kimiyya kan ɗumamar yanayi.
Ƙasar Amurka ba ta tura wakilai zuwa taron na COP30 ba, da ake yi a birnin Belem na ƙasar Brazil.
Haka ma shugabannin China da Indiya - da ke fitar da hayaƙi mai yawa - ba su halarci taron ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum ya mutu sakamakon ƙonewar da ya samu a filin jirgin saman Melbourne na ƙasar Australia bayan da na'urarsa ta fawa bank - da ake caji da ita - ta fashe.
Mutumin mai shekara 50 na cikin babban zauren da fasinjoji ke jiran jirgi, a lokacin da na'urar cajin tasa ta kama da yahaƙi, lamarin da ya tilasta wa mutanen da ke cikin zauren kusan 150 gaggawar ficewa, kafin fashewarta
Ma'aikatan filin jirgin sun kai wa mutumin taimakon gaggawa kafin a garzaya da shi asibiti, inda ya mutu a can.
Kamfanin jirgin sama na Qantas - da mutumin zai shiga - na nazarin dokokinsa kan barin fasinjoji su riƙe na'urar fawa bank, inda ake sa ran zai fitar da sabbin dokoki a nan gaba.
Kamfanonin jiragen sama da dama na shawartar fasinjoji kan riƙe na'urar fawa bank, a lokacin da za su shiga jirgi.
A watan Yuli ma na'urar fawa bank ta haddasa tashin hayaƙi a cikin wani jirgin kamfanin Virgin Australia da ya tashi daga birnin Sydney zuwa Hobart.
Haka ma watan Janairun wannan shekara na'urar ta lalata wani jirgin fasinja a Koriya ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta gabatar wa shugaba Trump tsare- tsaren yadda za a kai wa Najeriya hari, bayan umarnin da shugaban ya ba wa shalkwatar tsaron ƙasar ta Pentagon bayan zargin ana kisan Kiristoci Najeriyar.
Jaridar New York Times ta bayyana cewa tsare-tsaren su ƙushi zaɓi uku na yadda sojojin MAurkan za su iya shiga Najeriya da suka haɗa da:
Gagarumin hari, wanda zai ƙunshi aika wata rundunar mayaƙan ruwa ta musamman zuwa gaɓar tekun Guinea tare da rakiyar manyan jiragen sama na yaƙi, waɗanda za su iya yin ɓarin wuta kan ƴanbindiga a yankin arewacin Najeriya.
Matsakaicin hari, wanda zai kunshi aika jirage marasa matuƙa, domin tattara bayanan sirri da ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin masu tayar da ƙayar baya, da ayarinsu da ababen hawansu.
Sassauƙan hari, wanda zai fi mayar da hankali ga batun samar da bayanan sirri, da bayar da taimakon kayan aiki, da kuma gudanar da sintirin haɗin gwiwa da dakarun Najeriya domin ganin an kakkaɓe ƴan ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kamar yadda jaridar ta wallafa.
Wannan dai na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurkar Donald Trump, ya yi na kai hari Najeriyar saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Image
Mayaƙan RSF sun ce sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin samun damar shigar da agaji cikin ƙasar.
To sai dai sojojin Sudan ba su amince da shawarar hakan ba - wadda ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da wasu ƙasashen Larabawa suka gabatar.
Mayaƙan na RSF sun kuma ce a shirye rundunar take domin kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar tsakaninta da sojojin gwamnati da aka kwashe fiye da shekara biyu ana gwabzawa.
Matakin na RSF na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan ƙwace iko da birnin El-Fasher da Arewacin Darfur.
An zargi RSF da kisan fararen hula masu yawa a birnin da kuma take haƙƙin bil'adam ciki har da cin zarafin mata.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta buƙaci duka ɓangarorin biyu su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu.
Sudan ta faɗa yaƙin basasa ne a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF.