Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 19/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye. Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

  2. Haɗarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum 34 a Vietnam

    Aƙalla mutum 34 aka kashe bayan da wani jirgin ƴan yawon buɗe ido ya kife a gaɓar ruwan Vietnam sakamakon rashin kyawun yanayi.

    Lamarin na yau Asabar ya faru ne a wani fitaccen wuri na ƴan yawon buɗe ido da ke arewacin ƙasar yayin da iska mai ƙarfin gaske da ruwa haɗe da walƙiya suka afka wa yankin.

    Kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ce galibin mutanen da ke cikin jirgin iyalai ne ƴan Vietnam da ke ziyara daga Hanoi, babban birnin ƙasar.

    A cewar wakiliyar BBC, mamakon ruwan sama na kawo cikas a ƙoƙarin nemo masu sauran numfashi. Jami'ai sun ce mutum hamsin da uku ne suke cikin jirgin lokacin da lamarin ya afku.

  3. Gwamnatin Congo da M23 za su ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya

    M23

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Congo da ƴantawayen M23 sun amince su ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya, da Qatar ta shiga tsakani wadda za a rattaba mata hannu cikin wata mai zuwa.

    Yarjejeniyar za ta ƙunshi tsagaita wuta na dindindin da kuma dawo da mutanen da suka ɗaiɗaita.

    Sai dai babu haske kan ko mayaƙan M23 sun amince su miƙa wasu yankunan gabashin Congo da suka ƙwace ikonsu ga gwamnati.

    Wakilin BBC ya ce mutane da dama suna neman sanin ko wannan yarjejeniya ta ƙarshe da ake sa ran za a rattaba hannu kan ta a cikin watan Agusta za ta yi tasiri.

    Akwai kuma rahotannin ƙaruwar tashin hankali tsakanin ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a yankin, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane tserewa.

  4. Domin neman yardar ƴan arewa Tinubu ke sababbin naɗe-naɗe - ADC

    ADC

    Asalin hoton, X/Nasir El-Rufa'i

    Jam'iyyar hamayya a Najeriya ADC ta ce sababbin naɗe-naɗen da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi ba za su sauya komai ba, domin a cewar jam'iyyar, "bakin alƙamin ya bushe."

    A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce sababbin naɗa-naɗen da Tinubu a arewa, "wani yunƙuri ne na sake neman amincewar ƴan yankin."

    "Ba zai yiwu ka ware yanki na tsawon kimanin wata 25 ba, sannan ka yi zaton za su tafa maka kawai don yanzu ga gane cewa Najeriya ba Legas ba ce," in ji Bolaji, wanda a faɗa a cikin sanarwar cewa waɗannan naɗe-naɗe "ƙoƙarin magance raunin da aka yi wa ƴan arewa ne."

    "Kusan shekara ɗaya ke nan da wannan gwamnatin ta kawar da idonta daga irin ɓarnar da ƴanbindiga ke yi a ƙauyukan Najeriya, wanda ya tursasa manomanmu suka bar gonakinsu, kuma tattalin arzikin mutanen karkara ya karye suka shiga ƙangin talauci tun bayan cire tallafin kuɗi.

    "Sai yanzu saboda da Tinubu ya fara jin wuta daga mutane sai ya gane ashe akwai ƴan Najeriya da ya kamata ya naɗa."

    Bolaji ya ce duk matakan da gwamnatin nan ta ɗauka, "tun daga cire tallafin man fetur da yawancin naɗe-naɗe duk an yi ne ba tare da damuwa da matsalar arewa ba, yanzu ne da Tinubu ya fara ganin alamar sakamakon abin da ya yi, sai yake so ya fara gyara, amma ba zai iya ruɗar ƴan arewa da irin wannnan ba, suna gane cewa ba na gaskiya ba ne.

    A ƙarshe ADC ta yi kira ga shugaban ƙasar ya ɗauki matakin haɗin kan ƙasar ta hanyar tafiya da kowane ɓangare a naɗe-naɗensa.

  5. Haɗarin jirgin ƙasa ya yi ajalin mutum 21 a Iran

    Aƙalla mutum 21 ne suka rasu, sannan wasu kimanin 30 suka jikkata bayan taragon jirgin ƙasa ya kife a kudancin Iran a ranar Asabar, kamar yadda kafofin wata labaran gwamnatin ƙasar suka ruwaito.

    Lamarin, wanda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a kai ga gano asalin musabbinsa ba, ya faru da a wani gari mai nisan kilomita 1,000 dag babban birnin ƙasar, Tehran.

    "Mutum 21 sun rasu a haɗarin," kamar yadda daraktan asibitin Kavar, Mohsen Afrasiabi ya bayyana a zantawarsa da talabijin ƙasar.

    Daraktan ya kuma da cewa bayan waɗanda suka rasun, akwai mutum 29 da suka ji raunuka, kuma yanzu suke jinya.

    Kafofin watsa labaran sun nuna wani tarago a kwance a ƙasa bayn faɗuwar.

    Aƙalla mutum 20,000 ne suka rasu a sanadiyar haɗarurruka a cikin wata 12 , kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ruwaito.

  6. Abubuwan da suka na yi nasara a kirifto - Ahmed XM

    Ahmed

    Asalin hoton, Ahmed XM

    Fitaccen ɗan kirifto a arewacin Najeriya, Ahmed XM, ya ce haƙuri da jajircewa ne sirrukan da duk wani wanda yake son shiga harkar zai riƙa, matuƙar yana so ya samu tarin arziƙi.

    Matashin, wanda asalin sunansa Ahmed Yusuf Saifullahi ne ya ce ya fara harkar kirifto ne a lokacin da yake jami'a a shekarar 2018, inda ya ce a hankali ya fara, har ya kai matakin da yake a yanzu.

    Ya ce gwagwarmayar karatu da rashin isasshen kuɗi a lokacin da yake makaranta ne suka sauya tunaninsa, har ya fara neman mafita, "Ni ba ɗan masu kuɗi ba ne gaskiya. Lokacin ina makaranta sai ya zama kuɗin da ake ba mu, ba ya isa. Hakan ya sa na fara tunanin wani abu ne ya kamata in fara."

  7. Ƴansanda sun kama 'ƙasurgumin ɗanbindiga' a Kaduna

    Ɗanbiniga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun samu nasarar kama wani 'ƙasurgumin ɗanbindiga' a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Tashar Channels mai zaman kanta ta ruwaito ƴansandan suna cewa sun kama ɗanbindigar mai suna Mati Bagio ne bayan kimanin shekara 11 suna nemansa ruwa a jallo.

    Kakakin rundunar, Mansir Hassan ya ce Bagio mai kimanin shekara 34 ya daɗe yana addabar yankunan Giwa da Hunkuyi a Kaduna, da Faskari da Dandume da Funtua a jihar Katsina.

    "Mun kama shi ne a ranar 18 ga watn Yulin tare da makamai da dama irin su alburusai da bindiga ƙirar AK-47 da sauran su."

  8. Iran ta zartar wa mutum uku hukuncin kisa saboda laifin fyaɗe

    Hukuncin kisa

    Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin kisa sakamakon kama su da laifin aikata fyaɗe, kamar yadda kamfanin labarai na Mizan mai alaƙa da ma'akatar shari'a ya ruwaito.

    An aiwatar da hukuncin ne da tsakar daren da ya gabata a wani gidan yari da ke birnin Gorgan.

    Heidar Asiabi, shugaban sashen shari'a na lardin, ya ce an fara bincike ne bayan wata mace ta shigar da ƙorafin yin garkuwa da ita.

    Bayan tsananta bincike ne kuma wasu matan uku suka fito da zargin aikata fyaɗe. "Saboda girma da kuma kamanceceniya wajen aikata laifin aka kafa wata tawaga ta musamman da ta ƙunshi alƙalai da jami'an tsaro," in ji Asiabi.

    Bayan gano gungun mutum ukun cikin gaggawa, an kai su kotu tare da yanke musu hukunci, inda ita ma kotun ƙoli ta amince da shi.

    Iran ta zartar wa aƙalla mutum 901 hukuncin kisa a 2024 kaɗai, a cewar Volker Turk, shugaban hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

  9. Direba ya raunata mutum 28 bayan auka musu da mota a Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla mutum 28 ne suka jikkata sakamakon wani direba da ya auka cikin dandazon mutane da mota a birnin Los Angeles na Amurka.

    Ma'aikatar kashe gobara ta LA ta ce biyar daga cikinsu sun ji munanan raunuka, kuma kamar 10 ne ke cikin matsananinci yanayi.

    Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren da ya gabata (9:00 na safe agogon Najeriya) a unguwar East Hollywood yayin da mutanen ke kan layin shiga wani gidan casu.

    Zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa hatsarin ba.

  10. Rundunar 'yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

    Peter Obi

    Asalin hoton, Peter Obi

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Peter Obi, ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023.

    An shirya tattakin ne domin yin bikin murnar cika shekara 64 da haihuwar Mista Obi.

    Mai magana da yawun rundunar DSP Mansir Hassan ya ce bayanai sun nuna cewa akwai wasu "miyagu da ke shirin fakewa da gangamin domin haddasa fitina" a jihar.

    DSP ya ce rundunar ta dakatar da duk wani taron jama'a mai kama da na siyasa har sai "lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓe a hukumance kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa Inec ta tsara".

    A cewar sanarwar: "Yayin da ake gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyu a ranar da magoya bayan Obi suka tsara gangamin, rundunar 'yansandan Kaduna na ganin hakan zai haddasa rikici a wuraren da za a yi zaɓukan, abin da zai jawo rashin doka da oda a jihar."

    Rundunar ta kuma ci alwashin ɗaukar matakin shari'a kan duk wanda ya ƙi bin umarnin dakatar da gangamin siyasar.

  11. Shugaban Laberiya ya je ta'aziyyar Buhari a Monrovia

    Laberiya

    Asalin hoton, @NigeriaMFA

    Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar ta'aziyya ofishin jakdancin Najeriya da ke birnin Monrovia domin jajanta rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

    Yayin ziyarar tasa a ranar Laraba, Mista Boakai ya sanya hannu kan rajistar makoki a ofishin bayan ya samu tarɓa daga jakadan Najeriya R.O Mohammed.

    Alaƙar Najeriya da Laberiya na da tarihi sosai. A shekarun 1990, Najeriya ta tura sojojinta domin kawo ƙarsen yaƙin basasar ƙasar.

    Laberiya

    Asalin hoton, @NigeriaMFA

  12. Dalilin da ya sa Ganduje bai je tarɓar Tinubu ba a Kano - Muhammad Garba

    Ganduje da Tinubu

    Asalin hoton, APC

    Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai je tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba a Kano ranar Juma’a saboda balaguron da ya yi zuwa birnin Landan, a cewar makusancinsa Muhammad Garba.

    Ganduje wanda ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a watan Yuni ya shirya tafiyar ne kwana biyar kacal da saukarsa daga muƙamin, kamar yadda Muhammad Garba ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Asabar.

    Tinubu ya je Kano ne domin yin ta’aziyyar attajiri Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan Yuni, kuma rashin ganin Ganduje a wurin ya jawo cecekuce tsakanin magoya baya da ‘yan’adawa a jihar.

    “Ba kamar abin da ake yaɗawa ba cewa da gangan ya ƙi zuwa ko kuma ba shi da lafiya, Ganduje ya je Landan ne saboda tafiyar da aka shirya da daɗewa tun kafin ziyarar,” in ji sanarwar.

    Garba ya tabbatar cewa an sanar da Ganduje game da ziyarar shugaban ƙasar, “kuma ya yi niyyar zuwa amma duk ƙoƙarin da ya yi na sauya lokacin tashin jirginsa bai yi nasara ba”.

    “Sauka daga muƙamin da Ganduje ya yi bai shafi alaƙarsa da Tinubu ba ko kaɗan, wadda ta ginu tsawon shekaru cikin girmamawa da buƙata irin ta siyasa,” a cewar Garba.

    Garba wanda tsohon kwamashinan yaɗa labarai ne a gwamnatin Ganduje, bai bayyana abin da mai gidan nasa ya je yi Landan ba.

  13. An ceto masu haƙar ma'adanai 18 bayan awa 18 a cikin rami

    Mahaƙa

    Asalin hoton, EPA

    An ceto ma'aikatan haƙar ma'adanai 18 bayan sun shafe awa 18 a cikin ramin mahaƙar gwal da ke arewacin ƙasar Colombia.

    Gwamnatin ƙasar ta ce ma'aikatan sun maƙale ne a ranar Alhamis a mahaƙar El Minón sakamakon matsalar kayan aiki, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.

    Bayan shafe awa 12 ana aikin ceto, mutanen sun fito cikin ƙoshin lafiya, in ji hukumar kula da haƙar ma'adanai ta Colombia.

    Cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnatin tarayya, magajin garin Remedios ya ce mahaƙar ba ta da lasisi.

    Sai a ranar Juma'a da ƙarfe 3:00 na rana agogon ƙasar (9:00 na dare agogon Najeriya) aka kammala aikin zaƙulo su.

  14. An sake mayar da 'yan Najeriya 294 gida daga Nijar a makon nan - Nema

    'Yan Najeriya

    Asalin hoton, Nema

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta ce ta sake karɓar 'yan ƙasar 294 a ranar Litinin da aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar.

    Wata sanarwa daga hukumar ta ce jirgi biyu ne ya kwaso mutanen daga garin Agadez na Nijar zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ne da ke Kano bayan sun maƙale a can.

    Ta ce jirgin farko ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:30 ɗauke da mutum 148, na biyun kuma ya sauka da mutum 146 da misalin ƙarfe 4:29 na yamma.

    Bayanai sun nuna akasarin mutanen kan maƙale ne bayan yin zango a Agadez yayin da suke kan hanyarsu ta kaiwa ƙasashen Aljeriya ko Libya ko kuma nahiyar Turai.

    Ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasashen duniya ne ke taimakawa tare da hadin gwiwar gwamnati wajen mayar da su gida a jirgi.

  15. Mun gano motoci 35 da aka sace a wata shidan 2025 - Road Safety

    Wata mota

    Asalin hoton, FRSC

    Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce ta yi nasarar gano ababen hawa 35 da aka sace a faɗin ƙasar cikin wata shidan farko na shekarar 2025.

    Mai magana da yawun hukumar ta Federal Road Safety Corps (FRSC), Olusegun Ogungbemide, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Juma'a cewa sun yi nasarar ne sakamakon tsarinsu na rajistar ababen hawa ta intanet mai suna National Vehicle Identification Scheme (NVIS).

    Ya ce an sace motocin ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da fashi, da garkuwa da mutane, da zamba.

    "Domin tabbatar da nasarar yunƙurin, hukumar ta haɗa kai da sauran jami'an tsaro da kuma gwamnatocin jiha domin bin sawun ababen hawan," in ji Mista Ogungbemide.

  16. Amurka ta ce Isra'ila da Siriya sun amince da tsagaita wuta

    Siriya

    Asalin hoton, EPA

    Amurka ta ce Isra'ila da Siriya sun amince da tsagaita wuta wadda ƙasashen Amurkan da Turkiyya da Jordan suka shiga tsakani.

    Sanarwar na zuwa ne 'yan kwanaki bayan Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a Damascus babban birnin Siriya.

    Sai dai Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin lardin Sweida na kasar Siriyan da ke cikin wani mummunan tashin hankali mai nasaba na kabilanci tsakanin al'ummomin Druze da Bedouin.

    Wakilin BBC ya ce mutane a Swieda sun bayyana yadda gawawwaki ke jibge a kan tituna da kuma yadda aka yi wa wasu mutane kisan gilla.

    Sama da mutum 600 ne aka kashe a Sweida tun ranar Lahadi kuma hukumomin kasar Syria sun ce za su tura dakaru na musamman domin kawo karshen fadan.

  17. Maraba

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Asabar.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙabtansu.