Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 17 ga watan Fabrairun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran a yau.

    Muna kuma yi muku maraba da shiga watan azumin Ramadan mai alfarma.

    Muna fatan Allah ya sada mu da alkairan da ke cikinsa, ya sa muna cikin ƴantattun bayi.

    Mu kwana lafiya.

  2. An ga watan Azumin Ramadan a Nijar

    Azumi

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Jamhuriyar Nijar ta sanar da ganin jinjirin watan Azumin Ramadan.

    Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce ta samu labarin ganin watan a jihohin Damagaram da Dosso.

    Don haka ne majalisar ta buƙaci al'ummar Musulman ƙasar su tashi da azumin watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairu.

    Tuni dai ƙasashen Saudiyya da Najeriya suka sanar da ganin watan, tare da bayar da umarnin fara azumin a ranar Laraba.

  3. Majalisar dattawa ta buƙaci a ƙarfafa tsaro a jihohin Neja da Kwara

    Sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci a ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a jihohin Neja da Kwara.

    Yayin zaman majalisar na yau, mambobin majalisar sun buƙaci kwamitocin ayyukan soji da na ƴansanda da kuma na tattara bayanan sirri su nazarci yanayin tsaro a yankin arewa ta tsakiyar ƙasar.

    Majalisar ta kuma buƙaci kwamitocin su gabatar mata da rahoto nan da mako huɗu masu zuwa.

    Matakin na zuwa ne ƴankwanaki bayan wani mummunan hari da ya yi sanadin kisan gomman mutane da sace wasu da dama galibi mata da ƙananan yara a jihar Neja.

    A baya-bayan nan jihohin Neja da Kwara sun fuskanci ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga waɗanda ke kashe mutane tare da sace wasu domin neman kuɗin fansa.

  4. NiMet ta yi hasashen samun hazo a arewacin Najeriya ranar Laraba

    hazo

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun hazo mai duhu a arewacin Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce za a yi hazon ne a ɗaukacin jihohin arewacin ƙasar.

    Ta kuma bayar da shawara ga masu matsalar numfashi su ɗauki matakin kauce wa shaƙar hazon.

    Haka ma Nimet ta buƙaci kamfanononin jiragen sama su kula da kyau tare da ɗaukar muhimman matakai a lokacin jigilar jirage musamman a yankin arewacin ƙasar.

    Hukumar ta kuma ce za a samu gajimare da yiwuwar ruwan sama a jihohin kudancin ƙasar.

  5. Masu shiga tsakanin Rasha da Ukraine na tattaunawa a Geneva

    Masu shiga tsakani na Rasha da Ukaraine na ci gaba da gudanar da wata tattaunawar zaman lafiya wadda Amurka ke jagoranta a Geneva.

    Fatan da ake da shi na cimma matsaya ya ragu, saboda yadda Rasha ke ci gaba nuna buƙatar a sallama mata yankin Donbas bakiɗaya, wani abu da Kyiv ta yi watsi da shi.

    Ana sa ran za a ci gaba da tattaunawar har a gobe Laraba.

    Sao'i kafin soma tattaunawar, Moscow ta kai jerin wasu hare-hare ta sama cikin dare kan kayayyakin samar da makamashi a Ukraine.

    Ya ce an kai hare haren ne da niyyar su yi ɓarna mai yawa.

  6. An yi hatsaniya kan dokar zaɓe a Majalisar Wakilan Najeriya

    Ƴan majalisa

    Asalin hoton, NASS

    An samu hatsaniya a zaman da Majalisar Wakilan Najeriya ta gudanar kan gyaran dokar zaɓen ƙasar ta 2025.

    Sashe na 60 na dokar, wanda ya tanadi aika sakamakon zaɓe ta hanyar laturoni kuma nan take, da kuma sashe na 84 da ya tanadi bai wa jam’iyyu damar fitar da ɗan takara, ne suka haifar da rikicin.

    Hatsaniyar ta kaure ne bayan da kwamitin da majalisar ta kafa domin yin gyare-gyare kan dokar a watan Disamban da ya gabata, ya gabatar da rahotonsa a zauren majalisar.

    Bayan gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Francis Waive, ya buƙaci majalisar ta amince da amfani da hanyar aika sakamakon zaɓe ta laturoni, tare da ci gaba da amfani da takarda a matsayin madadi idan an samu tangarɗa, kamar yadda Majalisar Dattawa ta amince.

    Haka kuma, rahoton ya ƙunshi batun bai wa jam’iyyu damar fitar da ƴan takara ta hanyar zaɓen fidda gwani kai tsaye, ko tsarin wakilai, da kuma sulhu tsakanin ƴan takara.

    Daga nan ne Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, ya tambayi mambobin majalisar su bayyana ra’ayinsu na “e ko a’a”, lamarin da ya ƙara ɗaga hankula a zauren, inda ya buga hatimin majalisar bayan da ya ce waɗanda suka amince sun fi rinjaye.

    Sai dai lamarin da bai yi wasu mambobin daɗi ba, musamman ƴan hamayya, inda suka fita daga majalisar a fusace tare da rera waƙar suka ga takwarorinsu na APC.

  7. An kammala tattaunawar Iran da Amurka a Geneva

    An kammala tattaunawa karo na biyu wadda ba ta ido da ido ba tsakanin Amurka da Iran a Geneva.

    Zuwa yanzu ɓangarorin biyu ba su ce uffan ba game da yadda tattaunawar ta kasance.

    Amurka ta nemi a faɗaɗa batutuwan da za a tattauna a kansu, domin su haɗa har da batutuwan da ba na nukiliya ba.

    Sai dai Iran ta dage cewa ita abin da ta yarda a tattauna a kai kawai shi ne shirinta na Nukiliya da kuma batun Amurka ta ɗage takunkuman da ta sanya mata.

    A yayin da ake tsaka da tattaunawar, Iran ta sanar da cewa za ta rufe wani ɓangare na Mashigar Hormuz saboda wani atisayen soji da dakarun juyin juya hali za su yi.

    A makon da ya gabata Shugaba Trump ya sanar da shirin aika jirgin ruwa na biyu mai ɗauke da jiragen saman yaƙi zuwa gabas ta tsakiya.

  8. Me zai faru idan ba a ga wata ba a Najeriya duk da an gani a Saudiyya?

    Ƙasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadana na shekarar 1447 bayan hijira, wanda hakan ke nufin za a tashi da azumi a Saudiyyar ranar Laraba 18 ga watan Fabarairun 2026.

    A Najeriya kuwa sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar ya umarci al'ummar ƙasar su duba jinjirin watan Ramadana a yau Talata, sai dai tuni labarin ganin watan na Saudiyya ya karaɗe kafafen sada zumunta.

    To amma ganin watan Ramadana a Saudiyya ya wadaci sauran ƙasashen Musulmi?

    Sheikh Halliru Maraya, wanda malamin addinin Musulunci ne a Najeriya ya ce akwai abubuwa biyu game da haka:

    "In da a ce akwai tsarin shugabanci na bai-ɗaya tsakanin Musulmin duniya, to ganin wata a wani wuri zai zama ya shafi kowa," in ji Sheikh Maraya.

    Sai dai ya ce "Misali, a yanzu Najeriya tana da shugabanta, kuma shi ne yake sanar da gani ko rashin ganin wata ga al'ummar Musulmin Najeriya, haka nan ma sauran ƙasashen duniya suna da nasu shugabannin.

    "Saboda haka domin guje wa rarrabuwar kawuna zai fi kyau kowace al'umma ta yi amfani da sanarwar shugabanta, tun da ai yanzu Saudiyya ba za ta yi aiki da ganin watan Najeriya ba, duk kuwa da cewa wani lokaci akan fara ganin wata a Najeriya kafin Saudiyya," kamar yadda Sheikh Maraya ya bayyana wa BBC.

  9. An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya

    Azumi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin ƙasar sun sanar da ganin jinjirin watan azumin watan Ramadan na bana, wanda hakan ke nufin za a fara azumin daga gobe Laraba 17 ga watan Fabrairu a ƙasar ta Saudiyya.

    Shafin Haramain ne ya sanar da haka a kafar X, inda shafin ya ruwaito cewa, "an ga jinjirin wata a ƙasar Saudiyya. Don haka za a fara azumin wata Ramadan na shekarar 1447 daga gobe," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Tuni dai hukumomi a Najeriya suka buƙaci musulman ƙasar su nemi jinjirin watan a yau Talata 17 ga Fabrairu 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH.

    Buƙatar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar.

    Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fara neman jinjirin watan azumi a wannan rana, tare da umartar duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ga shugaban ƙaramar hukuma ko Dagaci mafi kusa domin a isar da saƙon ga fadar Sarkin Musulmi.

  10. Gwamnatin Najeriya za ta sallami daraktocin lafiya da suka daɗe a aiki

    ...

    Asalin hoton, @Fmohnigeria

    Ma’aikatar Lafiyar Najeriya ta bayar da umarnin sallamar duka daraktocin da suka shafe shekaru takwas a muƙamansu, nan take.

    Wannan mataki na zuwa ne bisa ga manufofin wa’adin shekaru takwas da dokokin sabunta aikin gwamnati suka tanada, inda ake buƙatar daraktoci su yi ritaya bayan cikar wa’adin.

    Sanarwar da ma’aikatar ta fitar "ta umurci shugabannin hukumomi su tabbatar an sallami duk wanda ya cika wannan wa’adin daga 31 ga Disamba, 2025."

    Haka kuma an buƙaci "karɓar takardu da kadarorin gwamnati daga hannun ma’aikatan da abin ya shafa."

    Ma'aikatar ta kuma umarci "sassan da abin ya shafa su dakatar da albashin daraktocin daga sashen IPPIS, sannan su tilasta musu mayar da duka alawus da aka biya bayan ranar da ya kamata su bar aiki."

    Wannan mataki ya sake jaddada wata sanarwa ta baya daga ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya wadda aka fitar a ranar 10 ga Fabrairu, 2026.

    Hukumomin ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati da ma’aikatar za su gudanar da bincike don tabbatar da aiwatar da wannan umarni, inda rashin bin umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.

    Ma’aikatar ta yi kira ga dukkan shugabanni su ɗauki wannan mataki da muhimmanci domin kiyaye tsari da doka.

  11. An rantsar da Tarique Rahman a matsayin sabon firaministan Bangladesh

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da Tarique Rahman a matsayin sabon Firaministan Bangladesh, wanda zai jagoranci gwamnati ta farko da aka zaɓa, tun bayan zanga-zangar gama gari da aka yi watanni 18 da suka gabata, wanda ya kai ga hamɓarar da Sheikh Hasina.

    A wani taro da aka yi a wajen majalisar dokokin ƙasar, shugaban jami'yyar BNP, ya sha alwashin gudanar da mulki kamar yadda doka ta tanada.

    Sabuwar gwamnatin za ta fuskanci kalubale wajen farfado da tattalin arziƙin ƙasar, da kuma dawo ƙasar kan turbar dimokraɗiyya bayan shafe shekaru goma sha biyar ana mulkin kama karya ƙarƙashin Sheikh Hasina da jamiyyar ta ta Awami League.

  12. Mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a Amurka Jesse Jackson ya rasu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jesse Jackson, shahararren mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a Amurka, ya rasu yana da shekaru 84. duniya.

    Marigayin ya taɓa neman tsayawa takarar shugaban ƙasa sau biyu a jam’iyyar Democrats.

    Kimani shekaru goma da suka wuce ne aka gano yana fama da cutar kakkarwa, wato Parkinsons disease.

    Jackson, wanda babban limimi mai wa'azin addinin kirista ne, ya taso ne a yankin kudanci wanda aka ware wa masu launin fata, kuma ya kasance na kusa da Matin Luther King.

    A wata sanarwa da suka fitar, iyalansa sun bayyana shi a matsayin jagoran al'umma, musamman waɗanda aka zalunta, ko aka tauye wa haƙƙi ko kuma aka yi watsi da su a faɗin duniya.

    Shugaba Trump ya miƙa ta'aziyyarsa, inda ya bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

  13. Amurka da Iran sun kammala tattaunawa karo na biyu a Geneva

    ...

    Asalin hoton, Reuters / Getty Images

    An kammala tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran a Geneva.

    Zuwa yanzu ɓangarorin biyu ba su ce uffan ba game da yadda tattaunawar ta kasance.

    Amurka ta nemi a faɗada batutuwan da za a tattauna a kansu, domin su haɗa har da batutuwan da ba na nukiliya ba.

    Sai dai Iran ta dage cewa ita abin da ta yarda a tattauna a kai kawai shi ne shirinta na Nukiliya da kuma batun Amurka ta ɗage takunkuman da ta sanya mata.

    A yayin da ake tsaka da tattaunawar, Iran ta sanar da cewa za ta rufe wani ɓangare na Mashigar Hormuz saboda wani atisayen soji da dakarun juyin juya hali za su yi.

    A makon da ya gabata ne Shugaba Trump ya sanar da shirin aika jirgin ruwa na biyu mai ɗauke da jiragen saman yaƙi zuwa gabas ta tsakiya.

  14. A fara duba jinjirin watan azumi daga yau - Sarkin Musulmi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An sanar da al’ummar Musulmi cewa a yau, ranar Talata 17 ga Fabrairu 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH, ita ce ranar da za a fara duba jinjirin watan Ramadan.

    Wannan na ƙunshe ne a ciki wata sanarwa da ta fito daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar.

    Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fara neman jinjirin watan azumi a wannan rana, tare da umartar duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ga shugaban ƙaramar hukuma ko Dagaci mafi kusa domin a isar da saƙon ga fadar Sarkin Musulmi.

    Fadar Sarkin Musulmi da ke jihar Sokoto ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba wa Musulmi ikon gudanar da ibada yadda ya dace, tare da fatan alheri ga duk masu bibiyar ganin jinjirin watan Ramadan na bana.

  15. Gwamnatin Najeriya ta bayar da tallafin naira biliyan 5 ga ‘yan kasuwar Singer

    ...

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Gwamnatin Najeriya ta bayar da tallafin naira biliyan 5 ga ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwar Singer da ke birnin Kano.

    Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana tallafin a ranar Litinin lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa kasuwar domin jajanta wa ‘yan kasuwar a madadin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

    Gobarar ta lalata manyan sassan kasuwar tare da haddasa asarar dukiya mai yawa ga ‘yan kasuwar.

    Haka kuma, wasu gwamnonin sun sanar da bayar da gudummawar naira biliyan 3 domin tallafa wa waɗanda ibtila’in ya shafa.

    Jimillar kuɗin tallafin daga ɓangarorin biyu ya zama naira biliyan takwas kenan domin rage radadin asarar da ‘yan kasuwar suka fuskanta.

    A ranar ta Litinin ɗin kuma, Shettima ya karɓi gwamna Abba Kabir a jamʼiyyar ta APC a hukumance yayin ziyarar.

    ...

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

  16. Mutum 28 sun mutu a harin jirgi mara matuƙi kan kasuwa a Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 28 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan harin jirgi mara matuƙi da aka kai a wata kasuwa a jihar Kordofan ta Arewa da ke ƙasar Sudan, kamar yadda wata ƙungiya mai sa ido kan asarar rayukan fararen hula ta bayyana a ranar Litinin.

    Harin ya auku ne a kasuwar al‑Safiya kusa da garin Sodari a yammacin Lahadi lokacin da kasuwar ta cika da jama’a, a cewar ƙungiyar Lauyoyin gaggawa.

    Ƙungiyar ta ce adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa domin da dama daga cikin waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

    Ƙungiyar ta bayyana cewa amfani da jirage marasa matuƙa a wuraren fararen hula na nuna babbar rashin kula da rayukan jama’a, tare da kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikici su mutunta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.

    Ba ta ambaci wanda ta zarga kai tsaye ba, amma rahotannin cikin gida sun nuna cewa dakarun RSF ta ƙara kai hare-hare da jirgi mara matuƙi a yankin Kordofan a kwanakin baya.

    Jami’an soji kuma sun musanta kai hari kan wuraren fararen hula.

    Rikicin Sudan ya ɓarke ne a watan Afrilun 2023 bayan tashin hankali tsakanin rundunar sojin ƙasar da kuma dakarun RSF ya rikiɗe zuwa yaƙi bayan gazawar shirin miƙa mulki ga farar hula.

    Tun daga lokacin rikicin ya bazu daga babban birnin Khartoum zuwa yankunan Darfur da Kordofan da sauran sassan ƙasar.

  17. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 31 - NCDC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa NCDC ta ce mutum 31 ne suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a cikin makonni biyar kacal, a cewar sabon rahoton da ta fitar a ranar Litinin.

    Rahoton ya nuna cewa mutum 754 ne ake zargin sun kamu da cutar inda aka tabbatar da cewa 165 suna ɗauke da cutar.

    Daga cikin waɗanda suka kamu akwai ma’aikatan lafiya tara.

    A cewar rahoton, jihohi tara sun riga sun samu aƙalla mutum ɗaya da aka tabbatar ya kamu a ƙananan hukumomi 33.

    Kashi 92 na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu sun fito ne daga jihohin Bauchi da Ondo da Taraba da Edo da Plateau yayin da sauran kashi takwas suka fito daga wasu jihohi huɗu.

    Zazzabin Lassa cuta ce mai tsanani wadda kwayar cutar Lassa ke haddasawa, kuma tana daga cikin cututtukan zubar jini masu haɗari da ke iya sa mace-mace idan ba a gano ta da wuri ba ko a samu kulawar gaggawa ba.

  18. 'Har yanzu El-Rufai na hannun EFCC'

    ...

    Asalin hoton, Muyiwa Adekeye/X

    Mai bai wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa har yanzu El-Rufai yana hannun EFCC.

    Adekeye ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X inda ya ce El-Rufai ya amsa gayyatar da hukumar ta aika masa a jiya Litinin, inda ya je ya amsa tambayoyi kamar yadda aka buƙace shi.

    Ya ƙara da cewa "ganawar da aka yi tsakanin El-Rufai da jami’an hukumar ta kasance mai amfani kuma cikin fahimta.

    A cewarsa, "lauyan tsohon gwamnan ya lura cewa jami’an da suka karɓe shi sun nuna ƙwarewa da mutunci wajen gudanar da aikinsu"

    Sanarwar ta kuma bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan yana tare da jami’an hukumar, ba tare da bayyana ko yaushe za a sallame shi ba, ko kuma ko an kammala tambayoyin da ake masa ba.

    Hukumar EFCC dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

    El-Rufai dai wanda ke cikin jagororin adawa a ADC da ke shirin ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu na APC a zaɓe mai zuwa, ya zargi gwamnati da matsa wa ‘yan adawa lamba ta hanyar binciken rashawa. Ya kuma ce an riga an kama kusan mutane huɗu da suka yi aiki tare da shi a Kaduna, yana mai cewa yana ganin lokaci ne kawai kafin a gayyace shi, abin da yanzu ya tabbata.

  19. Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu da kashi 15.10 a watan Janairun bana, lamarin da ke nuna alamun samun sauki daga tsadar rayuwa da aka daɗe ana fama da ita.

    Wannan sauyin ya faru ne sakamakon daidaita tsarin lissafin da hukumar ke amfani da shi domin ya dace da yanayin kasuwanci a ƙasar.

    Hakan ya sa farashin kayayyakin ya ragu idan aka kwatanta da kashi 27.61% a bara.

    Shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa wannan raguwa ta faru ne sakamakon sabon tsarin lissafi daga salon kasuwanci na shekarar 2024.

    Wannan sabon tsarin ya sa alƙaluman hauhawar farashi sun yi kasa, amma kamar yadda masana suka yi gargadi, wannan ba yana nufin farashin dukkan wasu kayayyaki ya riga ya karye a kasuwanni ba.

  20. Me dokokin Najeriya suka ce game da satar jin wayar wani?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a Najeriya game da iƙirarin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, mallam Nasir El-Rufai na satar jin wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai El-Rufai cikin wata hira da gidan talbijin na Arise ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu ne ya bayar da umarnin kama shi a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja bayan komawa ƙasar da ƙasashen waje.

    Da mai gabatar da shirin ya tambaye shi hujjarsa sai ya ce daga satar jin wayar Ribadun ne aka tabbatar da hakan.

    ''Sun ɗauka su kaɗai ne suke satar jin wayar mutane, to mu ma muna da masu yi mana aikin satar jin wayarsu, kuma muna yi'', a cewar El-Rufai.

    Wannan batu dai ya ɗauki hankali ƴanƙasar da dama, inda masana ke bayyana muhawara kan lamarin.

    Mallam Nuhu Ribadu ne babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, wanda ɗaya daga cikin muhimman muƙamai ne a fannin tsaron ƙasar.