Sharuɗɗa 17 da Jama'atu ta gindaya wa masu tafsiri a Najeriya

Daular Usmaniyya

Asalin hoton, Daular Usmaniyya

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da al'ummar Musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan, ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam ta fitar da ƙa'idojin tafsirin Alqur'ani, waɗanda suka kamata malami ya cika kafin ya hau mambari ya fara karantarwa.

Ta ce ƙaruwar malaman da ke kafa tafsiri suna habaici da zage-zage da raba kawunan jama'a, babban abin damuwa ne.

Tafsirin Alqur'ani wata dabara ce ta fassarawa da bayanin saƙonnin da ke ƙunshe a cikin littafin zuwa yaruka da dama, daga asalin yaren Larabci da aka saukar da shi.

Sai dai a wasu lokutan, a kan samu musayar kalamai da muhawara a tsakanin malaman, wanda sukan rikiɗe zuwa cacar-baki da caccakar juna.

Irin waɗannan matsalolin ne suke taruwa su jefa saɓani mai zafi a tsakanin malamai da wasu ɗaliba.

Wannan da ma wasu dalilan ne suka sa JNI ta fitar da wasu sharuɗɗa da ta ce su ne masu tafsiri ya kamata su kiyaye.

Sharuɗa 15

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon
  • Sanin Alqur'ani mai girma
  • Ilimin harshen Larabci
  • Fahimtar ilimin sarfu
  • Fahimtar ƙa'idojin luggar Larabci
  • Fahimtar balaga
  • Iya bayanin abubuwan da ke ƙunshe a cikin balaga
  • Sanin ayoyi masu kama da juna
  • Sanin ƙira'a wato na'ukan karatun
  • Sanin ƙa'idojin wasulla
  • Ya zama yana da ilimin aƙida
  • Sanin ilimin hukunce-hukunce na fiqihu
  • Sanin dalilan saukar da ayoyi
  • Sanin ilimin ayoyi da suke soke wasu da waɗanda ake soke
  • Sanin Ilimin hadisi
  • Basira
  • Wayewa
  • Fahimtar irin mutanen da yake karantarwa

Abin da ya sa aka gindaya sharuɗan

Da yake bayani kan dalilan da suka sa JNI ta gindaya sharuɗan, sakatare-janar na ƙungiyar, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya ce dama can akwai sharuɗɗan ba wai yanzu suka ƙirƙiro su ba.

Ya ce shekara 16 da suka gabata ne suka fara sanya sharuɗɗa, bayan sun fahimci an fara sauka daga asalin layin tafsirin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Kimanin shekara 16 ne muka lura tafsirin na ta haɓaka a Najeriya. Amma kuma sai haɓakar ta zo da sabon salo, sai aka ga an fara samun an fara sakin layi an fara shiga wasu abubuwa daban," in ji shi.

Ya ce wannan ne ya sa ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam ta yunƙura domin gindaya sharuɗɗa ga masu tafirin.

"Kasan ita ce uwar ƙungiyoyin addinin Musulunci a Najeriya, wadda take a ƙarƙashin Sarkin Musulmi, Mai alfarma Muhammad Sa'ad, da wasu sarakuna, sai aka yanke shawarar a yi wa tufkar hanci."

Ya ce wannan ne ya sa malamai da masana suka zauna suka yi aikin tsarawa da gindaya sharuɗɗan.

"Amma dama can akwai sharuɗɗa ga masu tafsiri tun a littattafan magabata. Ko da yake yanzu tarjama ake yi, an riga an rubuta tafsirai, amma duk da haka, sai ya zama tarjamar ma wasu na canjawa wasu abubuwan."

A game da malaman da suke gudanar da tafsirin, amma kuma ba su cika sharuɗɗan da JNI ɗin ta gindaya ba, Khalid Aliyu ya ce zai fi kyau irin waɗannan malaman su haƙura su je su ƙara karatu.

"Kamata ya yi ya haƙura kawai domin kada ya ja wa kansa matsala da Allah. Allah Ya ce kada ka yi haƙilo a kan abin da ba ka ilimi a kai. Kuma Allah zai tambaye mu abubuwan da muka aiki," in ji shi a tattaunawar.