Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 09/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 09/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Nan za mu rufe wannan shafi na yau Lahadi, kafin mu zo da wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.

    Sunana Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Guguwar Fung-wong ta dira a Philippines

    Mummunar guguwar Fung-wong ta dira a Philippines, wanda shi ne karo na biyu da aka samu hakan da ta yi wa ƙasar lahani a cikin mako guda.

    Ana ruwa kamar da bakin ƙwarya a birnin Cabanatuan da ke gabashin Luzon, abin da ya yi sanadiyar ɗaukewar lantarki.

    Mutum biyu ne suka mutu yayin wata ambaliyar ruwa tun ma kafin mumunar guguwar ta kai ga gaɓar ruwa.

    Fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka bar gidajensu saboda fargabar da ake yi cewar mummunar guguwar ta Fung-wong ka iya fin guguwar Kalmaegi haɗari.

    Kalmaegi ta halaka mutum 200 da ɓarnata dukiyoyi masu yawa.

  3. Shugabannin BBC sun ajiye aiki kan zargin rashin adalci a fim ɗin rayuwar Trump

    Shugaban kafar yaɗa labarai ta BBC Tim Davie ya ajiya muƙaminsa tare da mai kula da sashen labarai da al'amuran yau da kullum Deborah Turness.

    Dukkansu sun fuskanci matsi a kwanan nan bayan wani rahoton bincike na cikin gida ya nuna alamun an nuna wariya game da wani fim na rayuwar Shugaban Amurka Donald Trump.

    An jera bidiyo a fim ɗin ta hanyar nuna kamar shugaban na ƙarfafa wa magoya bayansa gwiwar su kai hari kan ginin majalisar dokokin Amurka a 2020, ba tare da haɗawa da ɓangaren da ya ce a yi zanga-zangar cikin lumana ba.

  4. Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar aikin Hajjin bana

    Gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 yayin wani biki a birnin Jeddah na Saudiyyar.

    Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar.

    Hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta ce yarjejeniyar hujja ce cewa Najeriya ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a bana.

    Zuwa yanzu babu tabbas game da adadin maniyyatan da za su je Saudiyya a bana, musamman saboda sanarwar Nahcon ta watan Oktoba cewa hukumomin Saudiyya sun rage yawan kujerun Hajjin na Najeriya daga 95,000 zuwa 66,000.

    Hukumar ta ce Saudiyya ta ɗauki matakin ne saboda Najeriya ba ta cike dukkan guraben da aka ware mata a bara, inda aka samu giɓin alhazai 35,872.

  5. Rasha ta ce hare-haren Ukraine sun katse lantarki a yankunan kan iyaka

    Jami'a a Rasha sun ce hare-haren da Ukraine ta kai kan cibiyoyin makamashi da jirage marasa matuƙa sun jefa mazauna yankunan da ke kan iyakar ƙasashen biyu cikin duhu.

    Gwamnan yankin Belgorod Vyacheslav Gladkov ya ce fiye da mutum 20,000 ne ke zaune babu lantarki da na'urorin ɗumama gida.

    Su ma gwamnonin Kursk da Voronezh sun bayar da rahoton hare-hare kan gine-gine da suka tayar da gobara a tashoshin lantarki.

    Tun da farko ministan harkokin wajen Ukraine ya zargi Rasha da kai wa tashoshin lantarkin da ke samar wa tashoshin nukilya biyu wuta hari da gangan ranar Juma'a da dare.

  6. An ci tarar Katsina United miliyan 9 da hana ta buga wasa a gida

    Hukumar NPFL mai kula da gasar ƙwallon ƙafa ta firimiyar Najeriya ta ci tarar ƙungiyar Katsina United naira miliyan tara sakamakon hatsaniyar da magoya bayanta suka tayar ranar Asabar.

    Wata sanarwa da NPFL ta fitar a yau ta ce mahukuntan Katsina United sun gaza "samar da cikakken tsaro abin da ya jawo magoya baya suka shiga cikin fili" a wasansu da Barau FC a garin na Katsina.

    Wasu magoya bayan Katsina sun auka cikin filin ne jim kaɗan bayan Barau ta farke ƙwallon da Katsina ta zira mata, kuma wasu suka jefi ɗanwasan Barau FC Nana Abraham tare da ji masa rauni a wuya.

    "An ci tarar kulob ɗin naira miliyan ɗaya kan kowane laifi uku da suka haɗa da jefa abubuwa cikin fili, da rashin tsawatar wa magoya, da kuma haddasa hatsaniya yayin wasa," in ji sanarwar.

    "Haka kuma, Katsina za ta biya tarar miliyan biyu kan gazawa wajen samar da cikakken tsaro a filin wasa.

    "Sannan za ta biya miliyan biyu kan kowane laifi biyu na ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata, da kuma ɓata wa alƙalan wasa da 'yan Barau FC lokaci bayan tashi daga wasan."

    Jimilla Katsina United za ta biya tarar naira miliyan tara kenan, sannan kuma Katsina za ta buga sauran wasanninta na gida a kakar wasa ta bana a garin Jos na jihar Filato.

    Hukumar NPFL ta bai wa ƙungiyar awa 48 na ɗaukaka ƙarar hukuncin idan bai yi mata daɗi ba.

  7. Tinubu ya taya Soludo murnar lashe zaɓen gwamnan Anambra

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo bisa samun nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar, inda ya yaba wa mutanen jihar bisa gudanar da zaɓen cikin lumana.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa, Tinubu ya kuma yaba wa ƙoƙarin da ya ce hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi.

    "Ina taya mutanen jihar Anambra da jami'an tsaro da hukumar zaɓe bisa yadda aka samu nasarar gudanar zaɓen cikin lumana ba tare da samun matsala ba."

    Tinubu ya ce nasarar da Soludo ya samu na nuna "cewa yana gudanar da mulki mai kyau. Gwamnan ya nuna cewa lallai ilimi na da amfani a mulki, kuma za a yi amfani da ilimi wajen magance matsalolin da mutane suke fuskanta."

    Shugaban ya ce ya ziyarci jihar a watan Mayun da ya gabata domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan ya yi, waɗanda ya bayyana da ayyuka masu muhimmanci da nagarta

    "In yaba wa Soluo bisa yadda yake gudanar a mulki mai kyau domin ciyar da jihar Anambra gaba. Sannan ina kira gare shi da ya janyo abokan takararsa kusa domin haɗa ƙarfi da ƙarfi su ciyar da jihar gaba."

  8. Gwamnatin Iran ta buƙaci mutanen Mashhad su rage amfani da ruwa saboda ƙarancinsa

    Hukumomi a ƙasar Iran sun buƙaci mazauna birnin Mashhad, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a ƙasar da su rage amfani da ruwan sha saboda ƙarancinsa.

    Tun da farko, an sanar da cewa za a samu ƙarancin ruwa a birnin saboda matsanancin fari da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

    Rumdunan adana ruwan sha na birnin da ke kai ruwa arewa maso gabashi ya ja baya zuwa ƙasa da kashi uku, wanda shi ne mataki mafi muni da aka fuskanta a cikin gomman shekaru.

    A farkon wannan watan ne shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya yi gargaɗin cewa za a iya kwashe mutanen birnin a sauya musu mazauni idan har matsalar ta ci gaba da ƙamari, kuma ba a samu hanyar magance ta ba.

  9. Bolivia da Amurka sun farfado da huldar diflomasiya

    Bolivia da Amurka sun sake farfado da huldar diflomasiyarsu - a matakin jakadanci - bayan shekara 17 da yanke alaka.

    Shagan Bolivia Rodrigo Paz ne ya sanar da matakin da kuma mataimakin sakataren harakokin wajen Amurka wanda ya kai ziyara kasar.

    A 2008 ne tsohon shugaban Bolivia Evo Morales ya kori jekadan Amurka daga kasar bayan zarginsa da goyon bayan wata makarkashiya, matakin da ya sa ita ma Amurka ta mayar da martani.

    A ranar Asabar aka rantsar da Mr Paz a matsayin sabon shugaban Bolivia, wanda ya kawo karshen mulkin shekara kusan 20 na yan gurguzu.

  10. Ƙwallo ba yaƙi ba ce - Ɗanwasan Barau da aka ji wa rauni

    Ɗanwasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Barau FC, Nana Abraham ya ce yanzu ya fara samun sauƙi daga raunukan da ya samu bayan harin da aka kai musu.

    Da Nana da wani ma'aikacin ƙungiyar Jabir Hassan ne suka samu raunuka a wasa na 12 tsakanin ƙungiyar Barau da Katsina United a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina.

    An fara hatsaniya ne bayan ɗan wasan Barau, Orji Kalu ya farke ƙwallo a minti 69 da fara wasan, inda wasu ƴan kallo suka kutsa cikin filin, lamarin da ya sa dole aka dakatar da wasan.

    A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Ahmed Hamisu Gwale ya fitar, Nana ya ce, "Ina godiya ga Allah, yanzu na fara samun sauƙi. Ma'aikatan jinyarmu sun yi ƙoƙari. Abin takaici ne abin da ya faru, ƙwallo ba yaƙi ba ne. Mun buga wasa biyar a gida, mun samu nasara, mun yi kunnen doki uku, sannan aka doke mu a wasa ɗaya, amma babu abin da ya faru. Don hake ma ya sa mu za a kai mana farmaki?"

  11. An kwashe mutum 900,000 da ke fuskantar barazanar mahaukaciya guguwa a Philippines

    Wata sabuwar guguwa da ta abka wa Philippines ta kara ruruwa zuwa mahaukaciyar guguwa.

    Sama da mutum 900,000 ne aka kwashe da yankunan daga yankunan da ake tunanin mahaukaciyar guguwar za ta cimmawa, wadda ake tunanin za ta fi ƙamari a yau ranar Lahadi.

    Wakilyar BBC ta ce ana sa ran isowar Goguwar ta Fun gwong mai tafe da iska nan da sa'o'i.

    Tuni aka kwashe mutane daga gidajensu, yayin da ake fargabar samun ruwan sama da tsawa - inda wasu suka nemi mafaka a coci.

    Goguwar na zuwa ne, kwanaki kadan bayan wata mahaukaciyar guguwa da ta yi barna tare da kashe akalla mutum 200 a Philippines.

  12. Bincike ya nuna yadda Amurka da Japan suka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a 1945

    Wani mai bincike a Biritaniya ya gano cewa sojojin Amurka da na Japan sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a lokacin kazamin yakin Okinawa a 1945, inda bangarorin biyu suka tattauna har ma suka gudanar da addu'o'i a tare.

    Farfesa Nick na Jami'ar Newcastle, wanda a baya ya wallafa bincike kan sulhun da aka yi na Kirsimeti 1914, lokacin da sojojin Birtaniya da na Jamus suka daina fada.

    Ya je kasar Japan a farkon wannan shekarar domin gudanar da bincike kan abin da ya faru a tsibirin Aka.

    An dai tsagaita wuta har sai da 'yan Japan suka mika wuya bayan watanni biyu. Hakan ta faru ne bayan da aka dora wa wani Laftanar na Amurka alhakin kwace tsibirin, amma maimakon fada, ya yi kira ga sojojin Japan da su mika wuya

  13. An shiga kwana 40 na dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka

    An shiga kwana na 40 na dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka, ba tare da kawo karshen takun-sakar da ke tsakanin 'yan Republican da Democrats ba a majalisa.

    Ana sa ran za su yi wani zama a yau Lahadi na musamman da ba kasafai suke yi ba. An dai dakatarar ayyukan gwamnati ne a Amurka sakamakon rashin jituwa kan amincewa da bukatar 'yan Democrat ta saka tallafin insorar lafiya cikin kudirin kudi wanda 'yan Republican suka ki amincewa.

    Wakilin BBC ya ce wannan ne batun da ya raba kan jam'iyyun biyu tun dakatar da ayyukan gwamnatin dakatar da harakokin gwamnatin ya dagula harakokin sufirin jiragen sama inda aka soke tashin dubban jiragen sakamakon karancin ma'aikata, wanda ya shafi miliyoyin Amurkawa

  14. Shugaban Syria Ahmed al-Sharaa zai gana da Trump a Amurka

    Shugaban ƙasar Syria Ahmed al-Sharaa wanda ya isa Amurka inda zai tattauna da shugaba Trump a Washington.

    Mr Sharaa wanda Amurka ta taba saka ladar miliyan 10 domin kama shi - zai kasance shugaban Syria na farko da ya kai ziyara Fadar White House.

    Wakilin BBC ya ce a ziyararsa a Washington ana sa ran zai jaddada goyon baya ga kawancen da Amurka ke jagoranta na yaki da kungiyar IS.

    Haka kuma ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna batun sake gina kasar Syria bayan shafe shekaru ana yakin basasa.

    Tun da farko ma'aikatar harkokin cikin gidan Syria ta sanar da kai wasu jerin hare-hare kan mayakan IS a larduna da dama, wanda ya kai ga kama mutum sama da 70 tare da kama makamai

  15. Soludo ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra

    Hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC ta sanar da Charles Soludo na Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba.

    Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi.

    Ya ce Soludo ya samu ƙuri'a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na Jam'iyyar APC mai biye masa da ƙuri'a 99,445.

    George Moghalu na Jam'iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri'a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri'a 1401.

    Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne, ya lashe zaɓen ne domin yin sake mulkin jihar a karo na biyu.

  16. Shugaban taron COP30 ya buƙaci ƙasashen duniya su rage ɗumamar yanayi

    Shugaban taron sauyin yanayi na Cop30 a Brazil ya yi kira ga kasashen duniya su karfafa hadin kai domin rage dumamar yanayi.

    A wata wasika ga mahalarta taron kafin bude shi a gobe Litinin, André Corrêa do Lago ya jaddada bukatar cimma burin rage karuwar dumamar da kashi daya da rabi na ma'aunin celsius.

    Ya ce kasashe suna da zabi - ko dai su ba masana'atu damar durkusar da su ko kuma su hada kai wajen tabbatar da samar da ci gaba a duniya

  17. Ƴanbindiga sun saki mataimakin shugaban majalisar jihar Kebbi

    Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa an sako mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi dan ƴanbindiga suka yi garkuwa da shi kwanan baya.

    Wata majiya daga majalisar ta shaida wa BBC cewa Muhammad Samaila Bagudo ya dawo cikin ƙoshi lafiya bayan kwanaki a hannun masu garkuwa.

    Har zuwa lokacin haɗa wannan labarin dai babu cikakken bayani game da ko an biya kuɗin fansa kafin a sako shi, amma dai majiyar ta ce majalisar ta yi godiya ga dukkan waɗanda suka yi aiki tare don ganin ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da shi.

    A ranar 31 ga watan Oktoba ne aka sace shi daura da gidansa da ke garin Bagudo.

  18. Farawa

    Barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    A yau ma za mu ɗaura ne daga inda muka tsaya a jiya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.