Ukraine ta kai hari kan wata tankar mai daga Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar leƙen asirin Ukraine ta ce ta yi amfani da jirgin yaki marar matuƙi wajen kai wa wata tankar mai daga Rasha hari a tekun Bahar Rum.
Jami'ai sun ce an yi wa tankar lahani sosai.
Rahotanni sun ce tankar ba ta ɗauke da komi, don haka babu wata fargaba da hatsarin fashewa.
Ukraine ta ce matakin bai saɗa doka ba, tun da a cewar jami'an ta ƙetara takunkumi tare da kuma samar da kudi ga yakin Rasha.
Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11
Asalin hoton, Burkina Faso Presidency
Sojoji 11 da suka maƙale tare da jirgi ƙirar C-130 a ƙasar Burkina Faso na kan hanyarsu ta zuwa Portugal inda tun farko can suka dosa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce Burkina Faso ta ƙyale su su bar ƙasar, inda da ya ce za su fara isa birnin Accra kafin daga bisani su ƙarasa zuwa ƙasar da suka nemi zuwa wato Portugal.
Wata tawaga daga Najeriya ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ce dai ta je birnin Ouagadougou inda ta tattauna da shugaban ƙasar Kyaftin Ibrahim Traore.a kan sojoji, bayan sama da mako ɗaya da faruwar lamarin,
A daren ranar Litinin ɗin 8 ga watan Disamba ne ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES, wadda ta ƙunshi Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar suka fitar da sanarwar yin tir da abin da suka kira keta musu sararin samaniya da wani jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.
Sai dai jim kaɗan bayan haka, hukumomin Najeriya sun fitar da nasu bayanin inda suka ce "tangarɗar na'ura ce ta sanya jirgin ya sauka a ƙasar ta Burkina Faso".
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Najeriya ta sanar da cewa ta kai ɗaukin gaggawa zuwa Jamhuriyar Benin, inda jiragen samanta suka daƙile ayyukan masu yunƙurin juyin mulki.
'Tallafin da ake bai wa ƴan gudun hijira a Habasha na dab da rugujewe'
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Habasha tare da hukumar kula da ƴan gudun hijira da masu komawa gida da kuma shirin abinci na duniya (WFP) sun yi gargaɗin cewa shirin tallafa wa ‘yan gudun hijira a ƙasar na dab da rushewa sakamakon ƙarancin kuɗaɗe.
Sun ce idan ba a samu tallafin gaggawa ba, ayyukan ceto rayuka kamar abinci da ruwa da kula da lafiya za su tsaya cik a cikin ‘yan makonni, lamarin da zai shafi sama da ‘yan gudun hijira miliyan 1.1.
Habasha, wadda ita ce ƙasa ta biyu a Afirka da ke karɓar ‘yan gudun hijira mafi yawa, na ci gaba da fuskantar ƙarin masu shigowa daga rikice-rikice a Sudan da Sudan ta Kudu, da kuma fari a Somaliya.
Duk da haka, matsanancin ƙarancin kuɗi ya tilasta hukumomin agaji rage kayan tallafin gaggawa da kashi 70 cikin 100 a shekarar 2025.
A watan Oktoba, WFP ya rage rabon abinci ga ‘yan gudun hijira 780,000 zuwa kashi 40 cikin 100 kawai.
Hukumomin sun ce rage tallafin ya haifar da ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki a sansanonin ‘yan gudun hijira, wanda ya haura kashi 15 cikin 100.
Rahotanni sun nuna cewa mace-macen jarirai da yara ƙasa da shekara ɗaya sun kai kashi 4.7 a 2025, yayin da adadin yaran da ke fama da rashin abinci mai tsanani ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da bara.
Tinubu ya ware kaso mafi tsoka ga fannin tsaro, Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin naira tiriliyan 58.47
Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ya gabatar da naira tiriliyan 58.47.
A kasafin, Tinubu ya tsara kashe naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya tsara kasafin ne a bisa hasashen farahin gangar ɗanyen man fetur a kan dala 64.85.
Haka an yi hasashen sama da gangar ɗanyen man fetur miliyan 1.84 a kullum, sannan ya ayyana canjin dala a kan naira 1,400.
Ƴan jihar Kano uku da suka rasa muƙamansu saboda siyasa
Asalin hoton, BBC COLLAGE
Masu nazarin siyasa na ganin cewa idan dai har ba ƴan siyasar jihar Kano ba su gyara zamansu ba da haɗa kai, to jihar ka iya fuskantar koma-baya ta fuskar wasu muƙaman gwamnatin tarayya.
Rikicin siyasa tsakanin jiga-jigan ƴan siyasar jihar ya janyo kodai wasu yin asarar wani muƙami sakamakon sauya su ko kuma jihar ta rasa baki ɗaya.
Rashin jituwa tsakanin ƴan siyasa a jihar ya janyo mummunar taƙaddama da aka daɗe ba a gani ba a baya-bayan nan inda har yanzu ake da mutum biyu da ke iƙrarin sarautar jihar.
Irin wannan rikici a baya-bayan nan ne ya so ya tayar da zaune tsaye lokacin da ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi ƙoƙarin kafa rundunar Hisba wadda ɓangaren gwamna, Abba Kabir Yusuf ke ganin za ta kishiyanci hukumar Hisba da ke ƙarƙashin gwamnatin jiha.
BBC ta yi nazari wasu muƙamai da aka yi dambarwa a kansu inda aka samu sauyin waɗanda aka naɗa ko kuma aka rasa kujerar kwata-kwata.
Ɗansandan da ake zargi da kai wa ƴanbindiga makamai a Neja ya kashe kansa
Asalin hoton, Getty Images
Wani ɗansanda da ake zargi da hannu a harkokin kai wa ƴanbindiga makamai ya kashe kansa yayin da ake gudanar da binciken makamai a ofishinsa.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na ƴansandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya fitar.
Rahotanni sun nuna cewa ɗansandan mai suna, Abdullahi Isah wanda shi mataimakin sufetan ɗansanda (DSP) ne.
An kama ɗansandan ne tun ranar 15 ga watan Disamba, 2025 bisa zargin safarar makamai ba bisa ka’ida ba kuma aka dawo da shi ofishinsa domin ci gaba da bincike da gudanar da audit na makamai.
A cewar SP Wasiu, yayin bincike da kuma ƙirga makamai da aka gudanar ranar 16 ga Disamba, 2025 domin gano bindigogi da harsasai da suka bace, Isah ya harbi kansa a ka da bindigar pistol da ya dauka daga ofis, inda ya mutu nan take.
SP Wasiu ya ƙara da cewa an kama jami’an da aka tura domin gudanar da bincike da kirga makaman saboda sakaci, saboda sun bari wanda ake zargi ya mutu ba tare da an kammala bincike ba.
Bangladesh ta nemi kwantar da hankali bayan tarzomar cikin dare a biranen ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin rikon ƙwarya a Bangladesh ta yi kiran kwantar da hankali bayan ɓarkewar tarzoma a cikin dare a wasu biranen ƙasar.
Tarzomar ta barke ne bayan labarin mutuwar wani matashin ɗan siyasa wanda aka harbe a makon da ya gabata yayin da yake yaƙin neman zaɓen da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Masu zanga-zangar dai sun abka ofishin wasu manyan jaridun kasar guda biyu a Dhaka, babban birnin kasar.
Magoya bayan matashin Sharif Osman Hadi, wanda ya yi fice wajen sukar hamɓararraiyar shugabar ƙasar Bangladesh Sheikh Hasina sun haɗa gangami ne suna yayata wasu kalamai na adawa.
Tinubu na gabatar da kasafin kuɗin Najeriya na 2026
Asalin hoton, presidency
Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya fara gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga zauren majalisar dokokin ƙasar.
Manyan jami’an majalisar ƙasa, ciki har da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, tare da wasu manyan mutane, sun halarci taron.
Zuma ta kashe yara biyu a Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Yara biyu ƙasa da shekara 10 sun mutu yayin da wasu suka jikkata bayan wani hari na zuma a makarantar firamare ta Evangelical Presbyterian da ke gundumar Anloga a yankin Volta na kudancin Ghana,
Rahotanni sun ce yaran na shirin hutun makaranta ne lokacin da zuma ta fito daga cikin bishiya a harabar makarantar, bayan wasu yara sun jefa wa ramin zumar duwatsu yayin wasan ƙwallo.
Shugaban makarantar, Thywill Deynu, ya ce yara ƙanana musamman na ajin ƙananen yara sun fi shan wahala domin ba su iya guduwa ba.
An garzaya da yara huɗu asibitin Keta Municipal, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwar biyu.
Likita Fiifi Agyemang ya ce ɗaya daga cikin wadanda suka jikkata ya farfaɗo, yayin da aka sallami wani da ya nuna alamar samun sauƙi.
Iyalan waɗanda suka rasu sun shiga alhini.
Masana sun yi gargaɗi cewa harin zuma na iya jawo mummunar rashin lafiyar anaphylaxis wadda ke hana numfashi, har ma ta kai ga bugun zuciya.
Mutum kusan dubu 100 a Gaza na fama da matsananciyar yunwa - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Masana samar da abinci a Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutum kusan dubu 100 a Gaza na ci gaba da fama da matsananciyar yunwa duk da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
Rahotonsu ya ƙunshi ci gaba da aka samu wajen shigar da abinci a yankin, amma sun yi gargaɗin cewa kusan mutane rabin miliyan na cikin buƙatar gaggawa.
A watan Agusta masanan sun ce kusan mutanen Gaza rabin miliyan na fama da abin da suka kira yunwar da aka haddasa.
Isra'ila dai ta yi watsi da rahoton na masanan na MDD, bayan zarginta Isra'ila da hana shigar da kayan agaji.
Bai kamata a riƙa yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ba - Fagbemi
Asalin hoton, Lateef Fagbemi/X
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ƙudirin majalisar dattawa na gyara dokar yaƙi da ta’addanci wadda ta ce a riƙa yanke wa masu sace mutane hukuncin kisa.
Wannan na zuwa ne bayan lauyan gwamnati kuma ministan Shari’a na ƙasar, Lateef Fagbemi ya ce bai kamata a riƙa yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ba.
Fagbemi ya nuna damuwa kan yiwuwar cewa ƙasashen duniya za su iya ƙin miƙa wa Najeriya masu laifi bisa dogaro da kauce wa hukuncin kisa da kuma dalilan jin ƙan ɗan'adam.
Ya ce, "Dole ne mu yi la’akari da matsalolin da ke tattare da sanya hukuncin kisa a cikin doka, musamman yadda hakan zai iya kawo cikas ga haɗin gwiwar ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta’addanci."
"Yawancin ƙasashe abokan hulɗarmu za su iya ƙin mika wa Najeriya manyan masu laifi idan suna fuskantar barazanar hukuncin kisa."
Ministan ya kara da cewa, "Ta hanyar saka wannan hukunci, zai iya samar da mafaka ga manyan masu laifi a ƙasashen waje, domin kotunan ƙasashen waje za su hana a mayar da su Najeriya bisa dalilan kare hakkokin ɗan'adam."
Ƙudirin dai ya ƙunshi yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ba tare da yiwuwar sassaucin kotu ko tara ba, inda aka fara karantawa a majalisar a ranar 27 ga watan Nuwamba, sai na biyu kuma a ranar 3 ga watan Disamba.
Fagbemi ya bayyana waɗannan hujjoji ne a lokacin taron jin ra’ayin jama’a da majalisar ta shirya tare da haɗin gwiwar kwamitocin haƙƙokin ɗan'adam da Shari’a da tsaro da tattara bayanan sirri, da ma’aikatar cikin gida.
EFCC ta gurfanar da ƴan Indiya a kotu kan zargin zamba cikin aminci
Asalin hoton, EFCC/X
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da wasu ƴan Indiya uku tare da wani ɗan Najeriya a gaban kotun jiha ta Kwara dake Ilorin, ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025.
Ana tuhumarsu ne da laifuka biyu da suka shafi haɗin baki da aikata lafin zamba cikin aminci yayin da suke ma’aikata a Kamfanin KAM Steel tsakanin watan Nuwambar 2024 zuwa Satumba 2025.
Waɗanda ake tuhuma sun musanta dukkan zargin da ake musu a lokacin da aka karanta musu ƙarar.
Bayan haka, lauyan EFCC, Cosmas Ugwu, ya nemi a tsare su a hannun hukumar gyaran hali har zuwa lokacin shari’a.
Sai dai lauyoyin wadanda ake tuhuma sun nemi a a basu beli saboda laifukan da ake tuhumarsu da shi za su iya neman beli.
Amma kuma lauyan EFCC ya ce wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ‘yan kasar waje ne kuma suna iya tserewa idan har aka sakesu, sannan ya nemi kotu ta hanzarta shari’ar.
Bayan sauraron hujjoji daga bangarorin biyu, Alkalin ƙotun, Sulaiman Akanbi ya ɗage shari’ar zuwa ranar Juma’a, 19 ga Disamba, 2025.
A shirye nake a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine - Putin
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa ƙasarsa ta shirya kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine, duk da cewa bai nuna alamar sassauci ba a kan batun.
A cikin jawabin sa a farkon shirin talabijin na shekara-shekara da yake yi, Putin ya ce Rasha na ganin wasu alamun cewa birnin Kyiv na nuna sha’awar shiga tattaunawa domin kawo maslaha.
Sai dai, shugaban ya jaddada cewa duk wani yarjejeniya da za a cimma zai kasance ne bisa sharuddan Rasha, da kuma sharaɗin cewa an magance tushen rikicin gaba ɗaya.
A yayin jawabin, Putin ya yaba da ci gaban sojojin Rasha a fagen daga, inda ya ce suna amfani da dabaru masu ƙwari duk da cewa dakarun ƙasar na fuskantar turjiya a fagen fama.
Sojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a Borno
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Haɗin Kai daƙile yaƙunrin hain ƴanbindiga ina sun kashe su daga tsaunukan Mandara a lokacin da suka yunƙurin kai hari a cikin al’ummar Bitta da ke Borno.
Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar daren ranar 18 ga Disamba, 2025 lokacin da sojojin suka gano wannan yunƙuri na ‘yanbindig da ke tafiya zuwa yankin.
A cewar rundunar, sai da sojojin suka bari ƴanbindigar suka shiga wani yanki da aka musu tarko kafin buɗe musu wuta, inda suka kashe wasu daga cikin maharan, ciki har da wani kwamandansu da mai ɗaukar musu hoto.
Rundunar ta ƙara da cewa, daga baya rundunar sojojin sama ta Operation Haɗin Kai ta kai farmaki kan waɗanda suka tsere lamarin da ya ƙara hallaka wasu tare da tarwatsa hanyoyin gudunsu.
A lokacin da ake fafatawa a yankin, an ruwaito cewa sojoji sun bi diddigin hanyoyi da dama, kuma sun gano kaburbura marasa zurfi, wanda ke nuna ƙarin asarar rayuka da aka yi wa ‘yan ta’addan a lokacin fafatawar.
Bayan fafatawar, sojoji sun gudanar da bincike a yankin inda suka ƙwato kayayyaki da makamai da dama.
Rundunar ta ce sojoji na ci gaba da ayyukansu domin hana masu ta da ƙayar baya samun damar kai hari, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
An gano wanda ake zargi da harbin jama'a a jami’ar Brown a mace – Ƴan sanda
Asalin hoton, Providence Police/Handout via Reuters
'Yansandan Amurka sun ce sun gano mutumin da ake zargi da harbin jama'a masu yawa a jami'ar Brown a makon da ya gabata mace a wani ginin ajiyar kaya a New Hampshire.
Sun ce mutumin mai suna, Claudio Neves Valente, ɗan kasar Portugal, wanda tsohon ɗalibin jamiar ne, ya kashe kansa ne bayan da jami'an suka yi wa ginin ƙawanya.
Ƴansanadn sun kuma ce shi ne ake zargi da kashe wani farfesa ɗan ƙasar Portugal, wanda aka harbe a gidansa a Boston ranar Litinin
Ƴansanda sun kama waɗanda suka shirya garkuwa da mutane na ƙarya a Legas
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan Jihar Legas ta kama mutum biyar da ake zargi da shirya garkuwa da mutane na ƙarya, lamarin da ya shafi wani ɗalibi ɗan makaranta da abokansa huɗu domin yaudara da karɓar kuɗi daga iyayensa.
An kama waɗanda ake zargin ne a ranakun 17 da 18 ga Disambar 2025, bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga yaron yana roƙon a tausaya masa, kamar yana cikin maɓoyar masu garkuwa da mutane kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar ranar Juma’a, ta ce binciken farko ya nuna cewa lamarin, wanda ya tayar da hankalin jama’a, an fara kai rahotonsa ga ƴansanda a matsayin ɓatan mutum a ranar 26 ga Nuwamba, 2025.
Ta ƙara da cewa daga bisani bincike ya tabbatar da cewa garkuwar da ake iƙirari, yaron da abokansa ne suka shirya inda suka yi amfani da ɗakin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin wajen aiwatar da wannan shiri.
Ƴansandan sun kama su ne a yankin Volkswagen Roundabout da kuma Ago Palace a jihar Legas.
Masu bincike sun ce waɗanda ake zargin sun shirya garkuwa da yaron ne domin karɓar kuɗi daga mahaifiyarsa mai suna Aligwo, wadda ta karɓi naira miliyan huɗu kwanan nan daga wata gudummawa.
SP Abimbola ta bayyana cewa mahaifiyar yaron har ta biya kuɗin fansa na naira miliyan 1.7, inda aka tura kuɗin zuwa asusun ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, daga bisani kuma suka raba kuɗin a tsakaninsu.
"Bayan biyan kuɗin ne ƴansanda suka gano na’urar POS ɗin da aka yi amfani da ita wajen tura kuɗin, abin da ya kai ga cafke su gaba ɗaya."
Australia na shirin saye bindigogin hannun jama'a bayan harin Bondi
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Australian, Anthony Albanese ya ce gwamnatinsa za ta bullo da shirin saye bindigogin da ke hannun jama'a, a fadin kasar sakamakon kisan da ɗanbindiga ya yi wa jama'a a wajen shakatawa na bakin teku na Bondi.
Ya ce a bisa tsarin suna sa ran karɓa da kuma lalata dubban bindigogi da suka haɗa da waɗanda ba a mallaka da doka ba, da sababbin waɗanda aka haramta.
Firaministan ya kuma ce wannan Lahadin za ta kasance ranar tunawa da karrama mutum 15 da aka kashe a harin na wajen bikin bautar yahudawa.
Za a sakko da tutoci kasa kasa sannan a yi shiru na minti daya.
Tarayyar Turai za ta ba Ukraine kuɗi don ci gaba da yaƙi da Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin Tarayyar Turai sun cimma wata yarjejeniya ta bai wa Ukraine bashin sama da dala biliyan 100 a shekara biyu mai zuwa domin samun kuɗin da za ta ci gaba da yaƙi da Rasha.
Wannan yarjejeniyar ta samu ne bayan kasa cimma muhawara kan bai wa Ukraine kadarorin Rasha.
Ya ce a matsayin mataki na gaggawa za mu samar da kuɗin da tallafin kasafin.
Tarayyar Turai Sun cimma matsayar ne bayan tattaunawar da ta kai su tsakar dare bayan da suka kasa cimma matsaya kan yadda za su yi amfani da kadarori da kudaden rasha da suka riƙe - wajen bai wa Ukraine din .
Ukraine za ta biya bashin ne kawai idan Rasha ta biya diyyar yaƙin.
Shugaban majalisar magabatan Turai Antonio Costa ya ce matakin ya nuna karara cewa Turai ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimakomn Ukraine, kuma rasha ta sani ba za ta taba nasara yakin ba.
Mece ce gaskiya kan zargin sauya dokar haraji ta Najeriya?
Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Tuni dai ƴan najeriya suka fara musayar yawu bisa rahotanni da ke yawo dangane da zargin sauya ko kuma yin cushe a dokar haraji ta Najeriya da ake sa ran za ta fara aiki a ranar 1 Janairu 2026.
Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sokoto Abdulsammad Dasuki ne dai ya ja hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da bambance-bambance da ya ce ya gano a tsakanin ƙudurin dokar haraji da majalisar ta amince da shi, da kuma wanda aka sanya wa hannu ya zama dokar da za a yi amfani da ita.
A watan Yunin 2025 ɗin ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.
Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Juma'a daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.